Saturday, 10 December 2016

ANA KUKAN TARGAƊE 8

ANA KUKAN TARGADE...
part 8⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001

...wani irin tuki yake mai kama dana ganganci ko saida rai, gaba daya notikan kansa sun kwance yama rasa ya zasuyi da wannan gagarumar matsala dake kusanto abokin nasa "innalillahi wa'inna ilaihi raju'un" yaketa maimaitawa tunda suka fito daga cikin gidan har kawo yanzu dasuke tafe yana tauna taura biyu, wato driving da tunanin mafita.
         Daga gefen mai zaman banza kwalisa ne ya kifa kansa a gaban motar yana fida numfashi a wahalce, zuciyarsa sai luguden duka take kamar ta tsago kirjinsa ta fito.
    Wannan wace irin bakar rana ce a rayuwarsa? Wai duk son dayakewa chuchu hajiya ke furta masa kalmar ya rabu da ita, koda yake inya kalli abin ta fuskar A.A wanda yanzu ya bayyana a BUKHAR saiyaga hajiya batada laifi, amma kuma meye nasa shida chuchu da ake son rabasu, bayan ba wanine daga cikinsu yai laifin ba, hasalima sanda akai duk cikinsu ba wanda ke duniya, amma yau rana tsaka hajiya ta halarto musu kalmar rabuwa a tsakaninsu, tayaya zai iya karbar wannan bahagon hukunci?
   Jiyake dama yai kuka ko yaji sauki a ransa amma kukanma yaki yazo, sai zafi da zugin daketa hayayyafa a kirjinsa, idonsa yai jajir kamar garwashi, gaba daya kwakwalwarsa ta toshe ya rasa yin tunanin abinda ya dace, hakan yasa ya kifa kansa a gaban motar kawai tareda runtse ido yana fatan allah yasa ya bude ido yaga duk abinda yake faruwa mafarki ne.
           Daga gidan baya kuwa h.iyami ce wacce halin datake ciki na tunowa BELI ya boye burin fansar datake burin dauka, kuka take da murya marar sauti, yayinda duk kofofin zuciyarta ke ciki da alwashin raba chuchu da kwalisa, bawai tana nufin itama chuchun ta mutu bane, a'a kawai ita bazata ta6a yarda su hada jini dako makoftan bukhar bane, bare shi kansa.
       Gyalenta kawai ta jawo ta rufe fuskarta dashi tareda ci gaba da nazartar zaren sake saken da zuciyarta ke saka mata, sarai taji irin tukin da md keyi duk yadda takai da tsanar tukin ganganci amma wai yau ita ake ja dashi ta kasa ko tankawa bare ta hana, tasan su duka ukun basuda wata nutsuwar gano wani abu mai kyau ko ru6a66e a halin dasuke ciki, tana tausayin halin da kwalisa zai shiga inta rabashi da chuchu, amma tasan danta mai biyayya ne bata fargabar bashi ko wane irin umarnine, ta tabbatar in so cuta ne to hakuri zai zame masa magani.
     Allah kadai ya kawosu gida lafiya, md nayi parking h.iyami ta fito bata tsaya jiran komai ba tai shigewar ta cikin gidan, kai tsaye bed room dinta ta wuce tareda murzawa kofar key.
         Md kuwa yai zugum yana kallon kwalisa dahar yanzu kansa ke durkushe a gaban motar, yaga alama baima san sun zo ba bare yasa haramar fita, hannu yasa tareda dan bubbuga bayansa, kamar dole akai masa haka ya ringa dago da kansa idonsa yakuma rinewa tareda kankancewa, numfashin sa nata fita da sauri da sauri, wani kallo yakewa md tamkar mai kallon ruwa, kwayoyin idon nasa a shanye cikin rawar murya md yace "mun iso fa"
    Juyawa yai kawai tareda zuro kafafunsa wajen motar, amma tsananin rawar da jikinsa keyi ya hanashi sake yin wani yunkurin, ganin halin dayake ciki yasa md fitowa ya kamashi sukai cikin gidan "kaini daki na md" abinda yace dashi kenan da wata irin karyayyar murya, ba musu ya nufi dakin nasa dashi.
        Kwantar dashi yai akan gado tareda kashe a.c dake cikin dakin ganin yadda hakoransa keta karo da juna "ina first aid box dinka?"
      Ya tambayeshi tareda mikewa yana dan dube-dube, da hannu yai masa nuni da lokar dake jikin cabinet, zarota yai tareda fiddo paracetamol da wani magani dabaisan kona meye ba shidai fatansa kawai abokinsa ya samu lafiya, gorar faro ya daukko a fridge marar sanyi tareda tallafo shi yasa masa magungunan a baki, bai musa ba ya hadiye tareda shan ruwan da md ke bashi, saida ya dauke kansa sannan ya janye gorar ruwan, yakuma shimfideshi tareda daukko towel yana goge masa goshinsa da ragowar ruwan, ko kafin ya gama kwalisan yai bacci dan haka kawai kwanciya ya gyara masa tareda fitowa dan fara lalla6a h.iyami batun daya kunno musu kai.
          Ganin falon wayam yasa yace da mai aiki ta duba mishi hajiya a dakin baccinta, dawowa tai tareda cemasa tana ciki amma ta kulle da mukulli.
      Baikuma saurarenta ba kawai yai hanyar fita daga cikin falon.
           *         *         *
A tsaye suke su duka hudun kamar gumaka inka dauke h.deejah daketa nanata kalmar "innalillahi...."
A.A kuwa gaba daya ya rasa yanayin dayake ciki, wata irin tsumammiyar nadama keta ratso mishi tun daga ma6oyarta zuwa zahirin fuskar sa, ya shiga tsananin shock da ganin wai kwalisa dan gidan iyami ne.... Ba wannan yafi firgita shi ba irin kalamanta na karshe datake cewa ko 'yarsa mutuwa take tana dawowa danta bazai aureta ba, tabbas yasan maganarta ba barazana bace ko kada ciki, danya hango gaskiyar hakan cikin kwayar idonta, har yanzu tana nan a iyamin daya sani mai masifa da rashin tsoro, babban tashin hankalinsa inya tuna da ran tilon 'yarsa dake reto bisa soyayyar kwalisa, yasan mutuwa ta allah ce amma ko chuchu zata rayu inba kwalisa a duniyarta yasan saidai su kare a jinya kawai dayi mata fatan kyakykyawan karshe, a hankali rayuwarsa ta baya ta ringa dawo masa cikin kwanya tabbas yasan ya biyewa son zuciya kwarai wajen yaudarar beli, dama zaiga beli ya nemi afuwarta, gabansa yakuma bugawa lokacin daya tuno tuni dacin rashin sa ya sheke beli gidanta na gaskiya, tabbas yasan ba yadda za'ayi ta yarda kwalisa ya auri chuchu koda kuwa shi iya yaudarar 'yar uwarta kawai yai, bare yai mata mai dungurungum yaudarar tasa ta tafi harda ruhi da burikan beli, yai tsai kawai tunanin sa nata hada masa bara da bana, yana kallon h.iyami na karasa ficewa daga cikin falon amma yakasa tsaida ita, wata irin kunya, nadama da dana sani keta karya masa duk wata ga6a dake jikinsa, hakan ya hana samar da sauti ko kadan a fatar bakinsa.
           Chuchu da vocal kuwa tsananin shock din abu biyu ya mikar dasu wato kasancewar wai bukhar shine A.A mahaifin chuchu dakuma kalaman h.iyami na karshe, chuchu kikam tai kawai tana kallon mahaifinta tareda cigaba da tono tsanar bukhar dake lilli6e cikin duniyarta tun lokacin da kwalisa ya basu labarin, ta kurawa mahaifinta ido tana masa kallon wani gawurtaccen dan ta'adda tunda har ya iya sarayar da rai, ran ma na mace mai rauni dan kawai son zuciyarsa, yanzu gashi ita datake 'yarsa yana neman tilasta mata girbe shukar daba ita ta dasa ba, dama ance son zuciya 6acinta.
            Kallo kawai take binsa dashi cikin wata irin tsanar rashin imani da tausayinsa, tama rasa mai zatayi dan rage zafi da zugin dake zuciyarta hannu tasa a ka tareda dagewa iya karfinta ta zabga ihun daya amsa kuwwa a cikin falon "wayyo allah naaaaaa" kawai tace tana zare ido, ihunta shiya farkar dasu halin tunanina da fargabar dasuke ciki duk su ukun sukayo kanta da tambayar lafiya, kallonsu kawai take su duka tareda jin haushin yadda wai suke tambayarta lafiya? Bayan inda wanda ya dace yai korafin rashin kwanciyar hankali yanzu a duniya to ya biyo bayanta, wai kuma dan karfin hali harda dadynta a nuna alhinin ihun datai, ihun dabe rage mata komai ba sai bugu da zugin da zuciyarta ta kara.
           Bangaje vocal tai kawai tareda runtumawa da gudu hanyar kitchen ta mako kofa garam, jin karar kofar yasa h.deejah fargabar karfa bacin rai yasa taiwa kanta wani lahani, tana gama tuno haka ta rufa mata baya itama da nata gudun.
         A.A da vocal basu san tunanin dataiba amma koma dai tunanin mai tayi sunga kamatuwar suma su rufa mata baya.
         Sai gasu suna ruge-rugen bude kofar tunda taji motsin tahowarsu ta leka ta window taga kitchen din suka nufo yasa ta kuma mikewa da sauri ta bude kofar store din dake ciki ta shige tareda garkama sakata, zuwa lokacin kam kuka take cin karfinta dan saida ta shigo sannan tunaninta yaci gaba da hasko mata babbar matsalar dake kusanto ta.
       Cirko cirko sukai bayan bude kofar sunga wayam, amma jin sautin kukanta a cikin store yasa suka tabatar tana ciki, jin kofar a kulle yasa vocal ta ringa bugawa da karfi amma ko a jikinta danko motsi batai ba bare susa ran zata bude musu, suna ganin hakanne ta windown dake tsakanin kitchen din da store, vocal bata gaji ba taci gaba da bugawa a sanyaye h.deejah ta juyo tareda cewa "daina wahalar da kanki sa'ada bazata bude ba"
        Da sauri vocal din ta karaso zuwa windown dasuke leken chuchun ta nan, bata gaji ba taci gaba da kwala mata kira cin karfinta "chuchuuu ! Chuchun gayu !! Chuchulazation !!!" Kiranta take da sunaye mabanbanta datake amfani dasu wajen kiranta insuna cikin nishadi, hakika da da ne ba yadda za'ai chuchu taji daya daga cikin wadandan sunayen bata amsa ba da tagomashin dariyarta, amma wai yau karshen volume vocal ta bude tana kiranta da sunan amma tai mata kunnen uwar shegu, wani irin tausayin halin datake tsintar kanta yakuma tsirgawa vocal saiga hawaye shar-shar na fita daga idanuwanta, bazata iya jurewa ganin chuchu cikin wannan halin ba dan haka juyawa tai kawai tareda ficewa daga cikin kitchen din.
           A.A ma dayake namiji wannan karon da kwallar yake fiddawa, nadama ce da tausayin tilon yarsa keta bashi kashi yanzu, yama rasa ta ina zai fara da warware wannan matsalar, tabbas yasan ya aikata kuren dabazai ta6a gyaruwa ba duk dan saboda son zuciya irin nasa da wata irin kunya ya dago yana duban h.deejah "yanzu mene mafita?"
       Duk da kukan datake ciki hakan bai hanata dakatawa ba tana galla masa harara harda murguda baki, dan tana ganin duk wannan matsalar dasuke ciki shiyai cikin abarsa yakuma haifeta da kansa amma da aka tashi renonta sai aka kasawa mutane dayawa ita, ciki kuwa harda wanda basu ji basu gani ba, musamman md da vocal da kyakykyawar zuciyarsu ke kara musu wani irin girma da kima a idonta, uwa uba tilon 'yarta da sirikinta data gama yi masa shaidar kulawa da gudan jininta tsakani da allah kobasa raye, sai gashi yau duk son zuciyar mutum daya ya jefasu cikin matsalar daba suyi tunani ba, a gefe daya takuma hango fuskar h.iyami data gaskata tarin kauna da tausayin Chuchu data gani shimfide a kamalalliyar fuskarta, ta tsinci kanta a farin ciki da godiya ga allah data fuskanci hakan tasan 'yarta tayi dacen surukar da ko a dubu sai an tona, saidai fatan kyakykyawar rayuwa kawai da zuri'a dayyiba.
           Wai amma duk wannan burin data gama ci awanni kadan dasuka wuce shine yanzu yai warwas a kasa, ya ruguje ta yarda bawata hanya daza'a bi dan dori ko gyarashi, cikeda kunan rai tace masa "meyasa zaka tambayeni ya za'ayi bayan *tarihi ke maimaita kansa* lokacin dakai waccen yaudarar aiba hannuna a ciki, dan haka yanzu data kwabe maka ma ba nawa hannun, ka barni inji da alhinin halin daka jefa mu" tana gama fada bata jira amsar sa ba ta fice.
          Saidai abinta ya bata mamaki bai wuce ganin vocal bata nan ba, ko tantama batayi tasan gida ta wuce, dan haka batada za6i sai sulalewa akan dima-diman kujerun falon tana cigaba da hawaye, sakawa take tareda kwance abubuwa da dama.
         *           *           *
Shiru yai yana saurarenta harsai da takai karshen abinda take son gaya masa bai dakatar da ita ba, haka data gama gaya masan ma ya jima bai tanka ba harsaida takuma magantuwa "Alhaji kayi shiru" h.iyami tafada tana nacewa kallon fuskar mijin nata datake son karanto yadda ya kar6i zancen nata, saidai fuskar tasa tayi ba yabo ba fallasa yadda zai wuya ta farad daya tace ga inda ya dosa.
        Alh.nafseen ya muskuta badan zaman ya gundireshi ba, sai maganganun h.iyami dasuka sa yaji duniyar ma na neman fice masa daga rai gaba daya bama zaman ba, amma hakika inya kalli abin da wata fuskar yasan itama abar aiwa uzuri ce a kuma tausayawa musamman saboda tafi kowa cutuwa a cikin maganar tunda ita ta rasa ran shakikiyar 'yar uwarta, amma kuma ba yadda za'ai ya goya mata baya akan abinda ta zartar, yasan bakomai ya ja hakanba sai tsana da fansar datake son dauka akan bukhar, duk da yai mutukar buguwa dajin cewa wai A.A ne bukhar, amma koma dai yaya ne shi a ganinsa laifinsa bazai shafi 'yarsa ba dabata ma duniya lokacin daya aikata laifin, bare dansu dake son raya sunnar ma'aiki s.a.w dan haka yai gyaran murya "to mekike so nace hajiyata bayan kin zartar da hukunci" ya fada da yake fal a fuskarsa.
         Kada kai tayi kawai "ban gama zartar da hukuncin ba tukunna"
Ya dubeta da sauri yana fatan shawara zatace ya bata a hankali saiya nusarshe da ita illar danyen hukuncin datake son ta yanke, dan haka da sauri yace "kina bukatar shawarata kenan" ya karashe da fatan cikar buri.
       Ta kalleshi kawai da mamakin yadda bakinsa yake sauri har hardewa yake wajen fadar maganar, kawai saita ji ranta na son jin meyake son sanar mata dan haka saita kara tattara masa kafatanin hankalinta da cewa "eh shawararka nake jira" dukda ba haka tai niyyar cewa dashi ba.
      Ya dan kalleta shima da nazartar fuskarta da yake yanada dogon tsinkaye nan da nan ya karanto inda tasa gaba wato bata yarda da kamfen bayan za6e ba, tunda tariga ta yanke hukunci ta yanke kawai, saidai bata ki bin karin maganar bahaushe ba dayace mutum baya kin ta mutane ance da barawo ya gudu, ya fahimci tabashi damar fadar shawarar sa ne kawai danta ji me zaice, amma bawai dan tai amfani da abinda zai fada dinba, dan haka kawai sai 6ige da cewa "aikinma gama yanke hukunci kawai dai abu kadanne ya rage"
          "Wannne kenan?" Ta fada tana gyara daurin dan kwalinta daya fara zamewa.
            "Kinsan mukhtar na tsananin son yarinyar nan a yadda na lura kamar bayan sun rabu mun kashe miciji ne munbar kai, tunda karshe danmu ma zai iya tashi a cikin matsalar soyayya wacce a sanadinta kika rasa *beli* wannan karonma kinga bamuda tabbacin bazamu rasa mukhtar ba tunda ba karfin rai yafita ba, bare ince tunda ita takasa tsallake juriyar rashin masoyi toshi zai iya, amma wace mafita kika samar akan hakan?"
              Kwarai jikinta yai sanyi akan maganar maigidan nata, lura da hakan dayai shima saiya hau addu'a a ransa allah yasa ta sauka daga dokin data hau na raba yaran.
      Ita kuwa h.iyami zuciyarta nata kai komo akan maganar, a hankali ta lumshe idonta dan tsayar da mafita, kamar majigi haka idonta ya ringa hasko mata hoton beli lokacin datake aman jini ranta na sallama da duniya, wai kuma yanzu ace ta yarda ta hada jini da mutumin daya kashe mata 'yar uwa, anya kuwa intai haka ta kyautawa beli? Ai kamar ma taci amanarta ne tunda ta nuna bata kishin ruhinta da aka salwantar, haka taringa tunani da tariyo wasu shudadden abubuwa a rayuwarta, tabbas tunda ta iya rasa yar uwar haihuwarta a duniya ta hakura toba wanda bazata rasa ta hakura ba kuwa, ciki kuwa harda mukhtar datake jin kozai hadiyi zuciya shima bazata bari ya auri diyar bukhar ba, sai gashi ta bude idonta tarwai akan Alh.nafseen "bada yawuna ba alhaji, komai zai sami mukhtar bazan lamunci aurensa da 'yar gidan bukhar ba, idan so cuta ne hakuri maganine, zai iya samun kowace irin mace yakeso a duniya tunda bawata tawaya gareshi a halitta ko a dabi'arsa, hasalima nasan dana nagartaccene da kowace mace zatai burin mallakarsa, dan haka ba damuwa bace alhaji inya rabu da ita ga 'yan mata nan dayawa a duniya"
    Ta karashe da wani irin kumaji dayake tasowa tun daga kolin zuciyarta.
          Zuru yai mata da ido kawai yana kallo shi kansa yasan ba abu bane mai sauki fuskantar da ita a lokaci kankani, ganin yadda tsayin shekara kusan 32 harda watanni amma takasa mantawa da tsanar bukhar a filin duniyarta, bayyanar chuchu a matsayin 'yarsa yasa mata kwadayin daukar fansa a kansa ta hanyar hana mukhtar aurenta duk da ta kwana da sanin irin tarin soyayyar datake masa, ya lura ba kin hada jini dashi ne yasa take son raba yaran ba, fansar kusan itace jigon hakan, koma dai yaya ne zai yunkurin nemo mafitar dabazata cutar da wadanda basu sukai laifi ba, saidai zaibi komai a sannu batare da ya konawa matarsa dake neman farin cikinsa koda yaushe raiba, yasan itama abar a duba ce, musamman da yake har yau takasa sabawa da rashin yar uwartata, numfasawa yai kawai tareda cewa "Allah ya kyauta".
        Binsa tai da kallo dan son fuskanto inda yasa gaba, amma yadda yai kadaran kadaham da fuskar yasa ta kasa gano komai, saita bige da cewa "ameen" kawai.
        Mikewa yai tareda gyara hannun babbar rigarsa "ni zan wuce hajiyata"
Itama mikewar tai tareda daukar brief case dinshi suka nufi hanyar fita.
           Har bakin motarsa ta rakashi tana masa addu'ar adawo lafiya allah ya tsare, yana daga mata hannu shima ya karasa ficewa daga cikin get din.
      A dai-dai kwanar link dinsu ya tsaya ganin motar md ta doso zai wuce gidansa, hon yai masa danya kula kamar bai ganshi ba, aiko harya gifta ya yo ribos danya gane motar alh.nafseen din, yai parking a gefe daya tareda fitowa ya karasa wajensa.
  "Alhaji barka da safiya" ya fada tareda durkusawa
"Barka dai Muhammad yaka baro mutan gidan" ya fada yana karasa fitowa daga cikin motar.
     "Lafiya qlau sunce a gaishe ku da mai jiki"
          "Muna amsawa mai jiki ma ya fara warwarewa dan jiya da likita ya dubashi yace jinin nasa ya fara sauka"
     Ya gyada kai "allah ya kara sauki"
        "Ameen, a gurguje Muhammad abinda nake so dakai shine koka je karkai yunkurin bawa hajiya hakuri akan kudiranta na raba mukhtar da wannan yarinyar, yanzu tana kan jin zafin abin ne, duk wanda ya bata hakuri zataga kamar bai damu da rashin yar uwar datai bane, dadin dadawa kuma zata ga kamar ana goyuwa da bayan A.A ne, kaidai kawai yanzu abinda nake so dakai kayi yunkurin kwantarwa da mukhtar din hankali saboda samun lafiyarsa, ita kuma hajiya ku barni nasan yadda zan bullo mata"
         "Insha allahu alhaji ba abinda zai faru sa6anin fadarka" ya fada kansa a kasa.
Shigewa motar yana fadin "ok saina dawo"
            "A sauka lafiya" yace tareda nufar inda yai parking din tasa motar.
          Lokacin daya karasa gidan h.iyami na falo tana sauya channel, ya gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da walwala, yai mata ya mai jiki "da sauki yana cikin dakinsa yanzun nan dawowata kenan daga raka alhaji na lekashi naga ko farkawa baiyi ba, amma kaje kobai farka ba ka tashe shi haka ai rana tayi" ta karashe fada tana kallon agogo.
         "To" kawai yace tareda mikewa ya nufi hanyar dakin kwalisan.
Bai farka dinba, yana nan a yadda ya barshi jiya saidai kawai an cire masa rigarsa an barshi da vest yanzun, a hanakali yaci gaba da kare masa kallo ganin yadda yai wata rama cikin kwana daya rak, idonsa duk yai loko tareda bayyanar wasu kasusuwa a wuyansa.
     "Allah sarki abokina allah ya baka lafiya"
Ya fada yana dan bubbuga gefen filon dayake kwance.
            *           *           *
Zaune yake kan farar kujera a farfajiyar gidan, news paper ce a hannunsa yana dubawa, amma a zahirin gaskiya hankalinsa na can tunanin yadda zai samawa kansa mafita, gaba daya rayuwar ta gundireshi, baiki yanzu allah ya aiko mala'ikan mutuwa ya dauke shi ba.
     Yau kwana hudu kenan da faruwar lamarin amma inka ganshi zaka zaci yayi jinyar shekara ne, yai wata irin rama tareda baki da fatars tai, wanda yasan A.A da inya ganshi yanzu bazai ce shi bane, ko abincin kirki baya samu ya ci duk wata walwala da farin ciki dayake samu a cikin gidansa yanzu kam an haramta masa shi, tun ranar dasu kwalisa suka zo haryau A.A baiga dariyar yar sa ko matar sa, dan har garama h.deejah yana samun ganin fuskarta dako arzikin murmushi baya samu yanzu, batai masa magana saita zama dole a hakanma inta ringa kunci tana cin magani abin har mamaki yake bashi, kamar dama sun tanadi fuskar tararsa inya zo musu a bukhar.
        Shi wuni yau ma gaba daya baisa chuchu a idonsa ba, haka jiya ma sukai bai ganta ba sai wajen yamma daya dawo daga office, abin ya daure masa kai dan ganin yadda chuchu tana ganinsa amma ko sannu da zuwa bata hadasu ba, karshe ma saita kama hanyar dakinta  ta tafi.
      "Nayi kuskure* ya fada a fili yana share kwallar data tarar masa a gefen ido.
    A hankali wani sashi na zuciyarsa ke kitsa masa matakin dazai dauka akan hakan, wani murmushi ya saki bayan yai amanna da shawarar daya yanke da zuciyarsa.
   Mikewa yai yana ninke jaridar da kwarin gwaiwarsa dan yama gama hango nasara a matakin daya shirya dauka.......

Mu tara a ANA KUKAN TARGADE.... 9 dan jin wane irin mataki A.A ya shirya dauka?

©
Prince av
09032724001

No comments:

Post a Comment