Thursday, 1 December 2016

KARNINMU 3


KARNINMU...
©Fikra Writers Association

BABI NA UKU

Cike da sanyin jiki ta karasa gidansu, zuciyar ta na mata kuna,  wai a ce mutum bai da daman fita sai an sami wanda ya maida sa ido sana'a da ya zage ka ko ya faɗi maka magana.
   "Mtsww!!"  Ta ja tsaki da karfi har sai da ɗan sandar da ke gaban motar ya waigo ya kalle ta.  Motar na tsayawa ya buɗe mata kofa ta fita ya sara mata.
     "in ka isa ka ce gobe da safe ne zani  tafiyar. Don Allah ban son African time"  bata jira cewansa ba ta shige cikin gidansu.
     Tun daga sauron gidansu ta san mahaifinta ya dawo. Bata tsaya ko ina ba sai ɗakin shi, inda ta same shi kwance yana jiran a kira sallah.
     "Allah sarki uba nagari Ɗan Aljanna, Allah ya kara maka lafiya"  ta faɗi tana zama gefen gadon da yake kwance,  bayan ta shiga ɗakin cike da sallama.
     "Anya bakin da yai addu'ar yana da zuciyar tausayi kuwa,  sai in ga kamar ni kaɗai ke dakon soyayya fa Lubaba. Kiyi hakuri ki yi halin mahaifiyarki albarkacin Kasan da ya rufe idanunta,  mahaifiyarki mutumiyar kirki ce,  ta kasance tana mai tsoron aikata ƙaramin zunubi balle Alkabaira " ya faɗi yana mammatse tafin hannayenta duka biyu da ya rike tunda ta shigo.
 
" zan bari Abby, ka min addu'a" ga faɗi tana shessheka.
     "Allah ya miki Albarka ya shirya min ke"
    "Aameen Abby,  ta tashi ta nufi ɗakinta.
   Kwanciya tayi kafin a kira sallah nan ta zurfafa tunanin Wacece ita.

                     ***
Cike da tashin hankali ta dinga mutsu-mutsu da kaffaffunta amma hakan ya hanata kuɓuta daga kyakkyawan rikon data samu. Cikin jigata ta yi shiru tana maida numfashi tafiyar sa'o'i uku shuuuuu!
    Ta buɗe ido ta riski kanta a wani waje mai matsanancin duhu ta kara kulle idanunta gam tana maraba da kaddararta a hankali taji an direta kan wani abu da takasa tantance tabarmace ko dandagaryar kasa saboda yanayin ruɗun da take ciki. Sautin dariya ya karaɗe kunnuwanta ta toshe kunnan tana zubda hawaye, wani kakkauran hannu taji ya lallabi tsakanin kunkuminta ana neman rabata da zanin jikinta ta rike wajan gam zuciyarta na tsananta bugawa.
Make hannunta da aka yi ne yasata sakin wata gigitaciyar kara da bata shirya fitowarta ba a ruɗe ɗaya daga cikinsu ya furta

"haba Rabs wannan fa yawa ne ya zaka kulla mana jakar tsaba?"

"Mtsss! Kika sake yi mana ihu saina mauje ki wallahi, shima tsohon kawai yaki zuwa ko mu musha lagwadar ne?"
Cewar Rabs yana lasar laɓɓansa.
Messi ya dubeshi fuska turɓune babu walwala, duk da a duhune hakan bai hanashi wurga masa harara ba.
"Kaifa baka da mutunci me zamu yi kuma, ni banma iya ba duka duka nawa muke?"

Baaba ya kwashe da dariya ya ce,
"ni banda rashin kuɗi ma mai zai sani ɗaukota, ina son hawa gajimare ne amma babu kuma ɗan kashin gadangaran ma ya yi wuyar samu saboda damuna amma wallahi yarinyar ta bani tausayi  shima Lad....".

Doke bakinsa da Rabs ya yi ya sa shi gimtse maganar dake shirin fitowa babu shiri, a hankali suke sauke numfarfashi duk da cikin duhu ne taso fahimtar muryoyinsu ta waiga ta karewa in da suke kallo duhu dundum babu motsin komai sai duhun shukoki da suka zama mafakarsu.

Haske siriri ya ratso tsakanin in da suke, da alamu hasken fitilane gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗar,

"yauwa gashi nan, gashi nan"

Sai dai me? Turus! Suka tsaya sakammakon gane wanda ya nufosu dalilin hasken fitilar hannunsa cikin takaici suka haɗa baki wajan faɗar

"Nuhu wai kai mayye ne?"

Bai basu amsa ba sai sunkuyawa da ya yi ya kama hannunta ya mikar da ita, jikinta ya hau rawa kwanyarta ta tafi tunanin dama Nuhu kanin Lubabatu Gimbiya shi ne yasa akamota. Janta kawai ya ke cikin kunar rai Rabs ya kawowa hannun cafka, dunkule hannu ya yi ya daki hancinsa take jini ya yi fitar burgu ya saki kara ya yi baya yana dafe wajan. Cikin shaka biyun suka dumfaro shi   ya yi baya da ita tare da mika mata karamar fitilar ya naɗe hannun rigarsa. Nan suka soma ɗauki ba daɗi Nuhu ya yi musu lillis saboda karfin ɗan mayye da lafiyyayan mutum ba ɗaya ba.
   Cikin kankanin lokaci ya gama dasu ya juya ya karɓi fitilar

"muje"

Ya faɗa murya a cunkushe babu walwala sum-sum tabi bayansa, gab da zasu bar hayin sawayawan suka yi kiciɓus da Lado ya kare musu kallo kana ya wuce abinsa yana tafe yana waiwaye.

Babu wanda ya tanka masa suka wuce suna shirin shiga unguwar hayin majaj ne Nuhu yaja ya tsaya yana dubanta,

"kinsan wancan daya wuce?"

Cikin rawar baki tace,
"eh Lado ne da muka yi faɗa ɗazu cikin kasuwa dashi"

Ya jinjina kai yana mamaki,
"me kika je yi cikin kasuwa da yamma kina mace?"

"Talla na kai"
Ta bashi amsa a gajarce,

"talla?".
Ya furta yana jinjina kai sai ta yi gum tana share hawaye bai kuma magana ba ya ce,
"ina ne gidanku?"

"Gidan Malam Mudi maɗinki"

Cike da shakku ya dubeta,
"ke kanwar Sani Mudi ce".
Kai ta ɗaga masa, bai kuma magana ba suka ɗauki hanya tafiya suke tamkar kurame har suka kawo kan kwanar gidansu dake unguwar santa kwatsam suka yi kiciɓus da Sani hankalinsa a matukar tashe.

"Daga ina kike?".
Ya faɗa yana zazzare ido, cikin tashin hankali ta yi bayan Nuhu.

"Mama ce ta ɗoramin talla aka sace tace saina nemo kuɗin duk in da suke"

Kansa ya sara ya dafe shi cikin nuna takaici,
"shi kuma wannan meya haɗaku?"

Yana dubansa a lallace,
"taimakona ya yi"

Tiryan-tiryan ta bayyana masa komai game da abin da ya faru tana direwa ya mika masa hannu suka  gaisa ya furta,
"nayi mamaki kwarai Nuhu tunanina duk gidansu Gimbiya lallatatune ashe akwai nagari?"

"Hmmm Sani nasanka ai kaine shugaban ajin yan makarantar maigari da suka fita shekarar nan. Amma zan baka shawara ku daina fassara mutum kai tsaye duk da cewar Gimbiya yar uwata ce bawai ina kareta bane ka bincika sossai sai kasan wacece Gimbiya na barka lafiya"

Ya saki hannunsa kai tsaye yana murmushi ya bar wajan babu alamun ɓacin rai tare dashi. Suka bishi da kallon mamaki......

                       ****

   K'arfe goma dai-dai a gida ta yiwa Ahmad. Ya na mai alfahari da Malam domin kuwa aikin sa ya yi kyau,dan har aka yi taro aka gama ba wanda ya yiwa Minister ko da kuwa kallan banza ne,bare a kai ga d'aga maganar. Duk da shi kan shi ya san ba su isa su iya rufe bakin duka jama'ar da ke cikin birnin Dunotsi ba,musamman mutane irin matar shi, wato Hajja Bilkis. Da wannan tunanin ne,ta faɗo ma sa a rai,
"wa ya sani ma ko ta dawo?" Abun da ya ayyana a ran sa kenan kafin ya faɗa wanka ya na mai godiya ga Allah da ya sa cikin sa cike ya ke dam da abinci hani'an, dan kuwa Ahmad ma'abocin cin abinci a waje ne, idan aka ɗauke hada hadan siyasa, matar shi ba k'aramin rawa ta taka ba wajan ba da gudunmawar faruwar hakan.
   Canza kaya yayi zuwa farin singileti da gajeran wando ya yi kwance bisa gadan sa, ba tare da ya damu ya je ya duba lafiyar Hajja Bilkis ba, bare ma ya san ta dawo ko ba ta dawo ba saboda takaicin bakin cikin da ta ɗana masa kan ta fita. Amma me gaba ɗaya hankalin sa ya kasa kwanciya, kamar wanda ta ke masa kiranye haka ya ji ya na bala'in so ya sanya ta a idanun sa. Tun ya na jurewa ya na dan juye juye bisa gado, har ya ji ba zai iya ba, ya tashi a hanzarce ya na mai k'ok'arin sanya farar jallabiya ya ke magana a fili.

  "Mace dai irin Bilkis matsala ce wallahi,babban takaici shi ne ba ta jin na Malam, da tuni na mallake ta na huta da wannan azabtar da ni da ta ke, har ni Sadisu zai gwadawa Luba, ga Yayar Luba nan gida na aje!"
    Ya faɗi a bayyane ya na  sanya jallabiyar , takalmi kawai ya saka, ya fito ya na mai surutai kamar gwaula. Kai tsaye bangaran Hajja Bilkis ya nufa.

  A ɓangaren Hajja Bilkis da ba ta fi awa ɗaya da dawowa ba, takaici ne fal ranta. Na rashin isowar kayan ta,a sanadiyar tarewar da hukumar fasa k'auri na k'asar Haurobiya su ka yi.
"In banda lalacewa na zamani ya ma za a yi da kuɗin ka, da gumin ka ka shigo da kaya, Amma isowar su ya gagara har sai ka biya wani kud'i daban na cin hanci! Toh Allah ga wannan zamani,Allah ka mana magani!" ta faɗi tare da jan tsaki a bayyane.
  Haka ta k'araci zaman ta a offishin hukumar fasa k'auri, abin da ya k'ara tsananta abin shi ne ma'aikatan da ta sani ta saba hurɗa da su duk an mu su canji zuwa sauran birane,duk sababbin fuskoki ne a ofishin. Gashi ta na son kiran Ahmad ko zai sa baki abu ya zo mata da sauk'i, tun da dai gwamnatin ta su ce amma yanayin rabuwar da su ka yi, da kuma jin kai irin na Hajja Bilkis ta gwammaci dawowa gida hannu na dukan cinya.
    Ko da Ahmad ya k'araso bangaran na ta, ɗakin ta ya dosa, ganin kofar a rufe ya san ta yi bacci, yayi tunanin juyawa,amma sai ya gwada sa'ar sa,tare da yiwa kan sa alkawarin ganin ta kawai zai yi ya juyo ba tare da ya rashe ta ba. Ya sa hannu ya murd'a cikin shakkun kar dai ta rufe da mukulli ta ciki. Ya  ko ci sa'a ba ta rufe ɗin ba, ya tura kofar a hankali, yayinda tafikan k'afar sa su ka sauka bisa lallausar carpet din da ke shimfiɗe tsakar ɗakin, wani sanyi mai daɗi ne ya bak'unci fatar jikin sa,ga wani ni'imantaccen kamshi na turaren wuta da ke tashi a d'akin.

    Idan aka ɗauke hasken farin wata da ya sami huɗowa ta taga, ta cikin labule,duhu ne ya mamaye ɗakin, domin kuwa Hajja Bilkis ta bi duka kwayayen lanatarkin ɗakin ta kashe. Sabon sa da ɗakin ya sa ya iya kaiwa ga gadon Hajja Bilkis ba tare da ya nemi gudunmawar hasken lantarki ba. Yayi kusan minti biyu kafin ya sa hannu ya dan yaye labulen tagar da ke daidai setin gadon na ta, hasken farin wata ya daɗa ratsowa cikin ɗakin, in da idanun sa su ka sauka kan ta.

   Bacci ta ke hankalin ta kwance. Duk da dai ba ado ta yi ba,ba kuma kayan ado ba ne jikin ta,amma sai ta masa kyau har ya kasa aje labulan bare ya kai ga ɗauke idanun sa kan ta. Sanye ta ke cikin kayan bacci fari kal kallo ɗaya za a mata a tabbatar da tsaftar da ke tattare da ita. Ya tabbata idan da zai shinshini fatar jikin ta a yanzo kamshi ne zai bakunci hancin shi,haka ma idan da za ta buɗi baki ta masa magana, idan be ji kamshi ba, toh lalle ba zai ji kishiyar hakan ba. Ba kamar sauran matan da ya aura ya saki ba,wasun su ma sai su ci tuwan su miyar kuka,su yi kwanciyar su ba tare da sun damu su goge bakin su ba, sai idan bukatar magana da maigida ta tashi cikin dare,da sun bud'e baki sai ka ji kamar an harba harsashin wari. Kai ko ma ba miyar kuka ba,ko wani irin abunci kaci,in dai ya mak'ale cikin hak'oran na tsawan wani lokaci,gashi dama baki rufe dole ya haddasa wari.
  Gogan na mu Ahmad be san sanda ya shagala ba,sai tsintar kan sa yayi ya na mai sunkuyawa domin shafar fuskar Hajja Bilkis,wanda hakan ya sa ta tashi a firgice ta na mai sakar masa ihu dake sam ba ta da nauyin bacci,ta na fad'in
"Wayyo Allah!!"
Tuni yayi saurin sakin labulan,sai gashi bisa gadon yana mai k'ok'arin rik'o ta ko ta samu ta dena ihu kar ta tada masu aiki da maigadi.
  Ita kuwa Hajja Bilkis tuni ta bingire d'ayan gefen,har ta dira k'asa ba ta dena ihun ba duk da jin muryar Ahmad ya na Faɗin

"in kina ma Allah ki yi shiru Maman Hanif! Kar ki d'agawa jama'a hankali! Menene haka wai!"

   Hannu na rawa ta kai ga makunnin wutan lantarkin da ke manne kusa da gadon ta,ta kunna. Tuni haske ya gauraya cikin ɗakin mai adon kore da fari. Babban ɗaki ne wanda girman sa ya ci a ce a kira sa da falo. Abin burgewa da d'akin girman sa be sa an cika shi da kayan takarce ba,kayan ne kaɗan na more rayuwa amma tsadaddu kuma na gani na fad'a. Hajja Bilkis da ke tsaye gefan godon nan irin na saraki,hannayen ta biyu bisa k'irjin ta na maida numfashi, ganin ba kowa ba ne ya firgita illa Ahmad wanda ke zaune tsakiyar gadon ya na mai duban ta.
   Sai da ta ɗan nutsu kafin ta sauke hannun ta zuwa kugun ta tana mai fad'in

"Haba Honourable! Haba dan Allah!dare mahutar bawa amma ba za ka sarara min ba! Kawai ina bacci na hankali kwance ka zo ka firgita ni! Ka san hukunci tsorata musulmi kuwa?"

    Ahmad ya dube cikin lallami ya ce
"Maman Hanif kenan,ba da niyar tsorata ki na zo ba. A matsayi na na maigidan ki ya kamata ace da  ki ka ji dawowa ta ki zo ki min ko da sannu da zuwa ne,amma hakan ya gagare ki ummm Bilkis? Hakan ya dace?"
   Hannu ta sa domin rufe bakin ta sanadiyar hammar da ta yi,cike da yar tsiwar da ya riga ya zame mata jiki ta ce

"Kai kuwa Honourable da rashin san zaman lafiya ka ke, da me zan ji? da gajiyar tawa da na kwaso zan ji ko kuwa da kasawa da tsarewa har sai ka shigo na ma ka sannu da zuwa zan ji?kai da ka dawo me ya hana ka shigo ka ga ya lafiya ta?"

     "Ai shi ne yanzun na zo na ga lafiyar ta ki,dan ba zan iya kwanciya ban ɗora idanuna kan ki ba"
Fad'in Ahmad kenan. Sai da ta kalle sa na wani dakikai ta na mai nazartar shi,kafin daga bisani ta haye gado ta na mai rarubar bargo,ta rufa,sannan ta bashi amsa da
"Ai ka ganni ɗin dai ko? toh dan Allah ka tura min kofa da kyau idan ka tashi fita,asuba ta gari!"
Ta yi kwanciyar ta abun ta.

   Ahmad yayi kasake ya na kallan ta,dan kuwa shi yanzu da abin da kuma yake buk'ata,amma shakku ya hana ya furta. Ganin har  bacci ya fara kwasar Hajja Bilkis,yayi saurin sake taɓo ta,hakan ya sa ta yaye bargon ta tashi a fusace ta na mai furta
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Wannan masifa wannan jaraba har ina ! Wai me-ne-ne! Eh Honourable! Ka barni ni na yi bacci mana saboda Allah!!"
  Cikin kame kame ya ce
"Yi hakuri Bilkis,zan bar ki,eh za ki yi baccin ai,amma kafin nan ki d'an ji da ni,ki bani hakki na" Baki bud'e ta ke duban sa,kana ta ce
"Lalle Honourable ka cika maras imani! Duk gajiyar da ksa kwaso yau,sam ban sami zama ba,kana gani ko da yammaci lokaci guda mu ka fita,amma ka lallab'o ka zo min wai neman hakkin ka,Haba mana,ai banza ba ta kai zomo kasuwa,shi ne da za ka wani wayence min da ka zo duba lafiya ta! Ashe ta ka lafiyar ka zo dubawa! Toh da Allah ka barni na ji da bakin cikin yan fasa k'auri kad'ai ya ishe ni,ka barni na huta!"
   Rai ɓace,amma cikin sassauta murya ya ce
"Kin san dai ba sai ina da wata buk'ata na daban na ke zuwa duba lafiyar ki ba! Ki ji tsoran Allah mana Bilkis,har kya min zancen yau sam ba ki huta ba? cikin hakkoki na na aure da ke kan ki wanne daga ciki ya hana ki hutawa? Wanne ki ka sauke a yau? Ko kuwa shi ma rashin zaman na ki a gida duk sanadin zaman auren ne sila?har kya min maganar na bari ki ji da takaicin yan fasa k'auri?bayan ba ni na kar zoman ba,kai ni ko rataya ma ba a bani ba! Ba ki san malaiku kwana su ke suna tsinewa macen da mijin ta ya nemi hakkin sa ta hana ba.....?"

    Hannu ta ɗaga masa,
"Toh fatsima tsima ni in tsamin! Malam araramma Honourable! Amma fa sai buk'atar ka ta taso ka ke nunawa ka san Allah,ba dai ni za a tsinewa ba?ba kai ba ko?toh inshaAllahu kuwa gobe ni zan wuni ina istigifari yayinda na ke kan kasuwanci na,a daren nan dai ko kai maye ne wallahi sai dai ka ci kan ka,kuliya ta kul!"
Ta koma ta kwanta gami da jan bargo ta rufa.
   A fusace Ahmad ya tashi ya na mai maimaita
"Ni ne mayen Bilkis! Ni Ahmad ni ki ke kira da maye,toh ba dai dan na nemi hakkin na bane har ki ka sami damar cimin fuska haka?toh na kyale ki da kan ki,amma ki sani duk randa na fad'a harkar neman matan banza ki kuka da kanki!"

  Ta na daga kwance ta ce
"Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazawara! Dan Allah ka rufo min k'ofa da kyau,idan kuma ka ji ka kasa sukuni ka iya zuwa kitchen ka duba na tabbata ba za mu rasa kanwa ba, ka jik'a ka sha,watakila ya sa ka sami lafiya"
   Dan takaici kasa bata amsa yayi ya kama hanyar fita a fusace har da buga mata kofa da k'arfi. Daga cikin bargo ta saki ajiyar zuciya jin ya fice,tare da gyara kwanci tana mai faɗin

"Kan ka ake ji wai mahaukaci ya fad'a rijiya ya ce ni wanka na nake...."

No comments:

Post a Comment