DAN ADAM
@Rufaida Omar
(02)
"Wai kina ina ne? Baki kammala shirya tsummokaran naki ba?"
Ummi dake d'aki tana kuka, ta tsinci muryar Baba Saude wacce ta sanyata rud'ewa babu shiri. Cikin rawar murya ta amsa a tsorace.
"Na gama Baba, ganinan."
Daga haka ta mik'e da saurinta ta dauki ledarta ta fito har lokacin kuka takeyi sosai.
Baba Saude na zaune tare da Habiba sai wata mata wacce ita ke dillancin mata zuwa gidajen aikatau, a gefe kuwa, Mariya ce ke faman cin masara hankalinta kwance, ta yi filo da cinyar uwarta.
Wata harara Baba Saude ta watsawa Ummi.
"Shegen bakin hali, kukan me kikeyi na kinibibi toh? Gwara ki share hawayenki ma, don babu abinda zai hana yau ki bar gidan nan."
Ummi ta durkushe a gefe tana share hawaye yayinda wasu ke k'ara kwaranyowa har da majina tana gogewa da hijabinta.
Baba Saude ta juya ga dillaliya.
"Ina jinki Yaha, yanzu dai duk wata zaki dunga aiko da albashin nata?"
Wacce aka kira da Yaha ya gyara zaman mayafinta lokacin da ta mike tsaye.
"Karki damu, duk wani abin arziki da ta samu ma, naki ne Saude. Komai zan tattaro na kawomaki. Kedai ki kwantar da hankalinki kamar kin kashe d'an maigari."
Sukayi dariya sannan Yahanasu ta dubi Ummi tana yamutse fuska.
"Wannan dogon gashin idan bakiyi wasa ba sai na yankeshi kafin mu k'arasa, yarinya sai shegen munafunci. Zaki maidashi cikin hijabin ko kuwa?"
Jiki na rawa Ummi ta ja jelar kitson kalbar da ta jagwalgwala a kanta ta maidashi cikin hijabi. Don kuwa bata isa ta je gidan kitso ba har ya saka ran samun mai kyau. Ta mike ta bi bayan Yaha wacce tuni tayi sallama da su ta bata umarnin ta taso.
Suna ficewa Habiba da Saude suka tafa suna shewar jin dadi.
"Ina sonki wallahi aminiya, bani da tamkar ki." Cewar Saude wacce ke jin ranta yayi wani mugun sanyi.
Habiba ta gwaguyi masarar hannunta tana wani rausaya kai.
"Ni ce fa, sai ma idan kudi sun soma shigomaki a hannu zakisan cewa ba k'aramin gata nayi miki ba. Ai ba'a saurin illata d'iya mace haka, ita tamkar jari ce, ko zata bi duniya in dai zata nemo ta kawomaki to kada ki damu kanki, ke dai ki more rayuwarki ta jikinta. Amma fa 'yar kishiya nake nufi."
Sukayi shewa da dariyar farin ciki. Koda Malam Balarabe ya iso suka sanar mishi cewar Ummi ta tafi, ko a jikinsa, karshe ma watsar da zancen yayi ya bi Mariya da tsarabar 'yar tsanar da ya siyomata.
* * *
Tun Ummi na kuka a motar kasuwa, har ta gaji tayi shiru tana kallon hanya kafin bacci kuma mai nauyi yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin kuma ta ji Yaha na tashinta.
"Ke! Ke!" Firgigit ta farka tana dubanta. "Na'am." Ta amsa a tsorace don kuwa kusan zuwa yanzu Ummi ta saba da hakan, da wuya tayi bacci a tasheta batare da ta firgita ba. Don sau da yawa ruwan sanyi ake kwara mata ko kuma a sanya k'afa a haureta, wani sa'in kuwa da bulala ake tashinta. Yaha ta watsa mata mugun kallo.
"Sai ki sauko tunda motar bata ubanki bace ko? Shashashar yarinya."
Ummi ta lura su kadai ya rage a motar, cikin rawar jiki ta bi bayan Yaha suka fito. Sai lokacin ta lura cewar cikin wani babban gari suke lura da yawan mutanen da ta ga suna faman zirga-zirga. Haka tayi ta bin bayan Yaha har suka fito daga tashar zuwa bakin titi. Saida gabanta ya fad'i ganin ababen hawa da yawa saman kwalta. Ta tsorata sosao da yawan mutanen da ke zirga-zirga awajen. A kauyensu na Ringim babu motoci har haka. Yaha ta tsayar da d'an sahu. Nan Ummi ta ji tace ya kaisu Gadon K'aya.
A hanya Ummi tayi ta rarraba ido tana duban tituna. Abin bai gama bata mamaki ba, saida ta ga sun hau wani dogon kwalta ta sama.
Ta kankame ledar kayanta, basuyi aune ba sai ji sukayi ta fashe da kuka.
"Wayyo Allah zan mutu!" Ta fad'a iyakar k'arfinta. D'an sahun harda kokarin juyowa.
"Lafiya?!" Yaha ta rankwashi kanta.
"Ka bar 'yar iskar yarinya mana, "yar kauye. Ta ji ta a titin 'yan birni zata kawomin iskanci. Yanzun nan zan bubbugeki idan baki rufemin wannan karamin bakin naki ba mai kama da na tsutsa."
Dariya d'an sahun ya kwashe da shi. Ita kuwa Ummi da sauri ta rufe bakinta, tana kuka a ciki-ciki har suka sauka idanunta a runtse yayinda jikinta ke kad'awa.
D'an sahun kuwa har da labarin tsohuwar da tayi makamancin hakan ya shiga bawa Yaha. Kasancewar Yahar itama ba baya ba wajen surutu, nan ta biyemishi suna tayi tana 6a6aka dariya. Ummi dai tana jinsu, alokacin ta bar kukan.
Sunyi kusan rabin awa suna tafiya sannan suka iso unguwar da ta ji Yaha tayi kira da Gadon K'aya. Haka ta ji Yaha nayita zuba mishi kwatance har suka iso wani gida d'an flat da shi. Ta biyashi kudinsa sannan ta dubi Ummi. "Sauka muje."
Ba musu Ummi ta sauka da saurinta. Yaha tayi gaba ta bi bayanta tana wulk'a idanu tana duban layin. Yaha ta shiga kwankwasa k'ofar tana sallama. Can ta tsinci muryar maigadin na cewa.
"Ana zuwa."
Yaha ta rik'e k'ugu tana taunar cingam ta dubi Ummi. Ganin haka yasa Ummi kauda nata idanun cikin sauri.
"Don ubanki saura kiyi min halin kauyenci sai na shak'e ki kin mutu har lahira. Banason yawan kalle-kalle. Kiyi ladabi so..."
Sauran maganar ya mak'ale a fatar bakinta ganin an soma k'ok'arin bud'e k'ofar.
Maigadin ya d'an lek'o da kansa. Farin buzu ne. Ganin Yaha ya sanyashi sakin fuska.
"A'a mai yara, kaine?"
Hakanan yake kiranta. Tayi dariya.
"Ni ce dai Baba. Hajiyar na ciki ko?"
Ya bata hanya ta shigo yana amsa mata.
"Eh yana nan. Ina ka samo d'an garinmu?"
Ya fad'a yana duban Ummi wacce ta durkusa da rawar jiki ta gaisheshi.
Yaha ta dubeta tayi mata alamun ta mik'e.
"Wannan ba 'yar garinku bace. 'Yar Maiduguri ce."
"Anya? Yana kama da mu." Yaha dariya kawai ta d'anyi batace uffan ba.
Daga haka sukayi ciki.
Ummi na bin farfajiyar da kallo a sace don bataso Yaha ta kamata tana kallon bayan ta ja mata kunne. Babban gida ne sosai, an k'awatashi da shuke-shuke. Daga wajen ka rantse ba shi da wani kyau ko girma don kuwa ko fenti ba'ayi ba daga wajen.
Haka suka isa har bakin wata k'ofa. Yaha ta murd'a ta shiga. Suka cigaba da tafiya a doguwar barandar dake wajen har suka iso tsakar gidan. Acan bakin rariya, wata babbar mace dattijuwa ce ke zaune saman kujera irin ta tsakar gida tana wanke-wanke. Ganin Yaha ta washe baki.
"A'a, lale marhabin da Hajiya Yaha. Yau kuma zuwan rana ce?"
Yaha ta numfasa fuskarta na nuna gajiya.
"Bari kawai Ramma, duk a gajiye nake. Hajiyar na ciki mu k'arasa?"
Ramma fuska a sake ta amsa tana duban Ummi wacce ke takure jikin bango.
"Eh tana ciki." Ummi da sauri ta gaisheta. Ramma ta amsa. Har suka kama hanya Ramma na binta da kallo, yarinyar da alamu zasu d'asa da Hajiya Madina, don kuwa da alama nutsastsiya ce.
No comments:
Post a Comment