Sunday, 25 December 2016

Sakaci 4

       💔💘 *SAKACI* 💘💔

                   0⃣4⃣

© Fatima A Garba.

Zaune ta ke amma sam hankalinta baya ta re da ita da alama ta luluk'a duniyar tunani wanda ya zame mata kamar ibada saboda kullum a cikinshi ta ke.

K'aran da wayarta ta ke ne ya dawo da ita da ga duniyan tunanin da ta jima aciki, har sai da kiran ya kusan katse wa kafin ta tashi cikin kasala ta isa inda ta ajiye wayar.

Ganin sunan da ya baiyyana akan screen d'in wayar shi yayi sanadin k'aruwan bugun zuciyarta, sanin halin mai kiran da rashin raina laifi komin k'ank'antashi yasa ta d'aga wayan gami da karawa a kunnenta kafin kuma ta yi sallama.

Sallamarta kawai ya ansa gami da cewa  " kije asibitina akwai wata mai haihuwa da dole sai anyi ma ta CS, ni ba zan samu zuwa ba, domin ni ne on call yau a T.H"

"toh" kawai ta ce da shi, ita dai kam ta na mamakin izza irin ta Dr Umar jibi yadda ya ke ba ta umarni! ba ruwanshi da ko ta na da wani uziri, tabbas baza ta iya mai musu ba dan bai can-canci hakan daga gareta ba.

Muryashi ta tsinkaya ya na cewa "karki kuma tsaya 6ata lokaci, domin ta na bukatar taimakon gaggawa" ba ta re da ya jira cewarta ba ya kashe wayarshi, ita d'in ma dama ba ta da ta cewa.

Kaya kawai ta sauya domin ba ta jima da yin wanka ba, gyara fuskarta ta yi,  kafin kuma ta feshe jikinta da turarukanta masu k'amshi.

Sannan ta d'auki dukkan abinda za ta buk'ata, jin muryar Auntynta a kitchen ya sa ta nufi kitchen d'in kai tsaye, a kitchen ta same ta, ta na ta faman shirya abinci, ido waje ta ce "Aunty yaushe ki ka dawo da ga kafin madakin"?

Cikin sakewar fuskar Aunty ta ce " tun d'azu na dawo na lek'a d'akinki naji kamar kinsawa kofar key sai na yi zaton bacci kike, sai kawai na kyaleki"

" Ya kuka bar su Hajiya Baban?" Farida ta fad'a, Aunty ta ce "suna nan kalau, ta ban sak'o ma na kawo miki" Farida ta ce "Allah sarki Hajiya baba"

Aunty ta k'ara da cewa "na ga kamar fita ma zakiyi ina aka nufa ne" Farida ta Sosa kunnenta da key d'in motar da ke hannunta had'e da cewa.

"Dr ne ya ce naje na duba wata mai haihuwa da za'a mata operation ga shi kuma shi ne on call a T.H"

Aunty ta ce "to ma za yi sauri ki tafi don bamu san halin da ta ke ciki ba inkin dawo mayi magana" "sai na dawo Aunty" kawai ta ce da Auntyn, ita kuma Aunty ta bita da addu'an dawowa lafiya.

                  **************

Gumi ta had'a sosai wani bak'in ciki ne ya ziyarce ta, ace mota ba'a rufa sati biyu sai ta kawo ma ta matsala, gaskiya dole ne ta canja motar nan, ga dare yayi karfe kusan goma (10am) kuma tak'i tashi, ba kuma samun abun hawa za ta yi har zuwa unguwar da ta ke ba, tsaki taja had'e da dukan sitiyarin motar.

Hango motarshi a gefe anyi parking d'inta yasata yin hamdala domin ta na da tabbacin ya dawo.

Zuciyarta ce ta gargad'eta da ce wa "Idan dai gunshi za ki neman alfarma, tabbas za ki had'u da 6acin rai gara dai kiyi tunanin wata mafitar" d'aya 6ari na zuciyarta kuma ya ce " zakiyi ta zama ne anan yanzu haka hankalin su Baba ya fara ta shi, toh wai ita ya zata yi ne"

Wani 6ari na zuciyarta ya ce "ba ki da mafita illah dai kawai kije ki same shi" gama wannan tunanin kawai ta rufe motar kaitsaye office d'inshi ta nufa.

Bubbugawa ta yi gami da yin sallama aciki taji ya ansa, bud'e kofar ta yi had'e da shiga kafin kuma ta ce "ina wuni" bai ansa ba hasalima ko kallonta baiyi ba idonshi nakan na'uwar laptop.

Ita d'in ma dama ba ta sa aranta zai ansa ba, ba ta kuma yi gigin zama ba tunda tafi kowa sanin k'a'idarshi da sai ya bada izini kafin azauna.

Kusan minti goma (10mns) ta na tsaye ba ta re da yako d'aga ido ya kalleta ba, har ta fara ji kafarta na mata zugi don dama ta gaji bayan Tiyatan sai da ta duba marasa lafiya.

Muryarshi ta tsinkaya ya na ce wa "ya dai" yadda yayi maganar cikin sanyin murya abun har ya ba ta mamaki, kallonshi ta yi don ta tabbatarwa da kanta shi d'in ne kuwa yayi maganar, kafin ta bashi ansa ta sa ke tsinkayar muryashi ya na ce wa " tambayarki na ke kin wani kafeni da ido tamkar mayya" wannan karan yayi ne cikin fad'a.

Cikin sanyi murya ta ce "dama motata ce tak'i tashi kusan awa d'aya ina fama amma tak'i tashi gashi dare yayi"

Ta kuma kasa kunnenta don jin masifar da zata kuma biyo baya, mutum kamar mai aljanu dubi fa d'azu ita dai tasan tunda ta shiga office d'in bai ko d'aga ido ya kalleta ba, to ya'akayi yasan ta na kallonshi, a zuciyarta ta ce "Allah ya kyauta"

Sai da ya sa ke d'iban lokaci kafin ya sa ke ce wa " yanzu me kikeso na miki "

Toh mai za ta ce mai sai kawai taja bakinta ta yi shuru had'e da sunkuyar da kai, wannan karan ma ya sa ke d'aukan wasu mintoci kafin ya sake ce wa.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment