ANA KUKAN TARGADE...
part 7⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001
...hannu yasa da sauri tareda toshe kunnuwansa, kafin ya kifa kansa a jikin gadon da chuchu ke kwance yana fidda kuka mai sauti.
Vocal nata kokawa da mamakin daketa kwalata da kasa, yayinda mafi rinjayen zuciyarta ke tabbatar mata dacewa wannan dai mafarki ne, kwalisan daya tsani chuchu, ace wai yau shine a gabanta yake kuka har yana sambatun bai mata adalci ba, takama dan yatsanta ta ciza da sauri ta saki saboda zafin dataji ya isa ya tabbatar mata a duniyar farke take, tambayoyine fal a bakinta amma tama rasa wazata yiwa su a cikin su ukun A.A , Md ko kwalisa amma dai tasan koma dai ya akai A.A ne ya taho dasu.
Da sauri md y karasa bakin gadon yana bawa kwalisa baki A.A shima karasawa yai yana bashi hakuri cikin dimbin mamakin bayan wannan kulawa to wace irin kauna vocal da chuchu suke fatan ya bata, danshi dai tunda ya hadu dasu ya gano tsananin son chuchun da babu algus a idonsa, to amma raina son tai ko me? Shikadai yakewa kansa wadannan tambayoyin cikin zuciyarsa, da sauri wata zuciyar tace kasani ko bayan daina ganinta dayai ya fara son nata, tabbas hakannema ya raya a ransa dan a yadda vocal tabashi labari rabuwar chuchu da kwalisa ta karshe ma rigima ce, kenan hasashen ya zama gaskiya kwalisa ya fara son 'yar sa ne wani irin dadi ya ziyarce shi a fili ya furta "ALHAMDULILLAH"
* * *
Yadda kwalisa ke bawa zuwa duba chuchu muhimmanci abin har mamaki yake bawa kowa musamman md da vocal da suka kwana da sanin irin tsumammiyar tsanar da yai mata, "Allah buwayi gagara misali" kalmar da vocal ke fada kenan intana son tsokanar kwalisa, aiko nan da nan zai fara aiko mata da harara intaci sa'a bai tanka mata ba "ni wai vocal jinya kika zo tayamu koni kike zuwa sawa ido"
Inya fadi haka dariya yake bata "au nice ma nazo tayaku bakai kazo tayamu ba, lallai kwalisa Allah ya damke ka" inta fadi irin haka dama indai h.deejah na nan ba tankawa yake ba, dan yana jin kunyarta da nauyinta musamman da vocal tabashi labari cewa bata boyewa iyayen chuchu irin tsanar daya nuna mata ba, lokacin dayaji haka ya shiga damuwa sosai dan gani yake zasu ringa kallonsa a matsayin dan ta'ardan dake san sheka 'yar su daya kiyama, md da vocal ne suka bashi baki tareda cewa yanzune yakeda time din dazai gyara wancen tsohon kuskuren dayai.
Aiko gyaran yake tukuru dan indai basuda lecture to nan yake yada zango, inko lecture 5 to 6 gareshi to yawanci sai h.deejah ta korashi yake tafiya, dan A.A ysnzu shima ya koma bakin aiki, vocal ma tana zuwa skull saboda jikin chuchun yayi sauki sosai, farfadowar ce dai har yanzu allah bai nufa ba.
* * *
Da sauri ya fito daga dakin yana kokarin daura agogo a hannunsa, h.iyami dake yanke farcenta da nai cutter ta dubeshi "mukhtar wannan saurin dakake fa kamar ka tashi sama" ya dan dakata yana sosa keya
"Hajiya asibiti zani wallahi shiyasa" ta kare masa kallo ta tabbatar babu alamun ciwo a jikinshi sannan ta maida kanta ci gaba da yanke farcen "waye ba lafiya?" Ta jefeshi da tambayar.
Baisan zata tambayeshi ba hakan yasa bai shiryawa amsar bata da wuri ba, saima ya dan diririce "amm... Innn wannan ne abokina ne"
Ganin yadda ya rude yasa h.iyami kallonsa da sauri "mukhtar ka gayamin gaskiya kodai wani ka kade a mota garin tukin ganganci"
"Hajiya wallahi ki yarda ba wanda na kade, dubiyar itace hadina kawai da marar lafiyar" ya fada yana karasa balle maballi hannun rigarshi "a'uzibillahi" ya fada a ransa dan tunawa da cewa shine silar kai chuchun asibiti, dan haka dashi da mai kadewar matsayin su daya, ya tabbatar ma ya fishi laifi tunda shi wance kila tsautsayi ne shikuma kowa yaji abinda yai yasan kadanne zasuyi masa uzuri.
H.iyami taso yarda da abinda ya fada amma ganin yadda ya tafi tunani yasata shakku akan maganar kawai saita 6ige da cemasa "jeka allah ya kiyaye ya tashi kafadun marar lafiyar" har tuntuben harshe yake wajen cewa "ameen ameen" ya fice da sauri daga falon, tana jin tashin motarsa daxai fice daga ji shima dai a kagaucen yayi shi, dan haka kawai saitaji hankalinta bai kwanta ba akan hakan.
Waya ta zaro tareda shiga contact dinta ta kira number md, ringing daya biyu ya daga " hello hajiya antashi lafiya" ya fada daga daya barin.
"Lafiya kalau md" tace tareda saurin katse shi daga abinda yai niyyar fada "koka san wajen wa mukhtar ke zuwa a asibiti"
"Eh hajiya chuchu ce" md ya amsa
"Chuchuuu" ta nanata sunan kafin ta kuma ce masa "wacece haka"
Md bai tsaya kwana kwana ba wajen bata labarin duk abinda ya faru har nemansu da A.A yai.
H.iyami ta kadu mutuka da jin wannan zance dadinta daya daya kasance hankalin mukhtar koma kan yarinyar, ba abinda ya fado mata sai MAIMUNA, muryarta na rawa taiwa md sallama kawai ta kashe wayar.
"Allah sarki beli allah ya jikanki ya saka miki abinda bukhar yai miki ya......" Kuka yaci karfinta kawai ta kifa kanta jikin sofa tana yi.
Alh nafseen ya dade a kanta batare data sani ba, basai ya tambaya ba, yasan abinda yasata kuka, yana mutukar tausayin yadda ta kasa mancewa da soyayya da sabon dataiwa 'yar uwarta tsawon wannan lokaci, har yanzu ta tuno da beli takan 6ata lokaci wajen kuka da sambatun kalaman tsanar bukhar, danma alh nafseen din ba karamin kulawa da tattali yake bata ba da koda da minti daya bazata manta da beli ba, yai gyaran murya danya lura duk tsawon lokacin daya dauka bata san da zuwansa ba, jin gyaran muryar tasa yasata dago da kanta idonnan nata kamar nama abinki da farar bafulatan nan da nan fuskar tai jajir itama, hannunsa ya wara mata alamar ta taho da sauri ta fada kirjinsa taci gaba da rera kukan.
Bayanta ya shiga bubbugawa "relief! relief!! relief!!! Hajiyata" ya dagota tareda zaro hand kerchief yana goge mata hawayen da salon barkwanci yace "yakike min asarar hawayenki, ki tanadar minsu inmunyi aure yadda zanji dadin rarraahin ki iyami" kalaman dayake gaya mata kenan lokacin datake budurwa inta fara kukan kewar beli, yake kawai tayi tareda ci gaba da jejjjera ajiyar zuciya, tunda yaga haka yasan yau abin yakai intaha, dan haka ya zage wajen lallashinta dabata baki, labarai yake mata na ban dariya da sanya nishadi nan da nan kuwa sai gata ta murje tana sheka dariya.
Daga baya take gaya masa labarin rashin lafiyar chuchu ne ya tuna mata da marigayiya, alh nafseen ya gyada kanshi "ni nasan da zancen rashin lafiyar ai tun wajen kwana 8 baya har dubiya na leka nayi"
"Au dan wariyar launin fata shine ni aka kyaleni ba'a gayan ba dan suga bakina" ta fada tana auna masa hararar wasa, da dariya ya tareta "maida wukar ciki hajiyata, nima ranar alh zainudden zain naje dubawa asibitin baida lafiya, saina gansu shida md da wata budurwa zasu shiga wani daki, danai musu magana mukhtar din ke sanar mini 'yar ajinsu ce batada lafiya nace to inna fito daga duba alh zainudden zain din na leko, shinefa bayan na fito na shiga naima iyayenta yamai jiki, kinji yadda akai amma ni bashi ya gayan ba"
H.iyami tai dariya kawai "dan kwal uba bawani 'yar makarantarsu, sirikarka ce yai maka kwangen bayyana maka"
"Kinsan nayi zaton hakan a raina, amma sanin halin miskilanci irin na mukhtar baxai barhi yai budurwa ba, sai nace to ko budurwar md ce, kin san me?"
"A'a saika fada"
"Yarinyar fa 'yar gidan A.A ce tarangahuma irinta mukhtar ko ina zai kaita" ya karashe da salon zolayarta, ta gane sa rai da ita dan lokacin da kaninta abule zai aure yake son wata 'yar mai hamshakin mai kudi ga yarinyar da kiba h.iyamin ta ringa yiwa alh nafseen mita da cewa abule ya daukko wacce tafi karfinshi ko ina zai kaita, bayan aurensu kuwa watanta tara cif-cif ta haihu.
Shikenan alh nafseen yasamu abin tsokana yana ce mata yanzu kinga inda ya kaita ko, inya fada saidai kawai tai shiru dan tasan jan magana ne irin nasa.
Yanzun ma shiru kawai tai masa tana dariya dacewa "kaika san inda zai kaita"
* * *
Sallama yai tareda tura kofar dakin, h.deejah na kan kujera tana juya cornflakes a dan karamin bowl da alama sai lokacin zata karya.
Tsugunawa yai tareda gaisheta yana mata ya mai jiki "alhamdulillahi mukhtar yaka baro mutanen gidan"
Kwalisa ya kuma kasa da kai suna nan sunce ai gaishe daku" da murmushi g.deejah ta amsa "muna amsawa kuwa"
Ya danyi wuri wuri da ido "yau saike kadai suka bari hajiya"
"Wallahi mukhtar ya za'ayi yanzun nan na tura jimmai da hanne (masu yi musu aiki) siyo cotton din gogewa chuchu baki a pharmacy, shikuma dady yau jirgin karfe 9:00 yabi zuwa abuja cewa yai tunda jikin nata yai sauki zaije ya dan duba ma'aikatunsa amma ba kwana zaiba nake jin zuwa yamma dai ka ganshi ya juyo, dama duk wata yake zuwa dubawa to rashin lafiyar nan ce ta damawa kowa lissafi"
"Haka ne" kawai kwalisa yace tareda yunkurin mikewa zai tafi, danya lura kamar nauyinsa ya hanata shan cornflakes din "har zaka tafi" ta tambayeshi dan taga yadda yake kaunar zaman asibitin kamar wanda akewa kyauta inya zo.
Ya dan sosa kai "ammmmm ehhhhh hajiya dama nace inkin gama break kawai saina dawo" ta lura francea ne shi, wato mai fadar gaskiyar ransa kawai batare daya tsaya wani nuku nuku ba, saitaji ya kara burgeta.
Daukar bowl din tai tareda cewa "no kai zamanka kawai mukhtar nidama zan shiga office din dr.fauza ne akwai maganar dazamu tattauna da ita" tana karasa fada ta fice tareda ja mishi kofar.
Komawa yai ya zauna tareda daukar wani littafin addu'o'i daya gani akan fridge din dakin, yana cikin dubawa su hanne suke sallama suka shigo ya amsa musu sukuma suka gaisashi, amsawa yai tareda karbar cotton din dasuka siyo.
Hanne ce ta bude food flask din ta zuba musu soyayyen chips da wainar kwai, sai plantain da aka rufe da naman kaza, a tea flask din kuma kunun gyada ne daketa faman tashin kamshi da gardin madara, bayan ta gama zubawa ta direwa kwalisa wani a gabansa suma suka dauki nasu suna ci, saida ya rufe littafin yake ce mata tazo ta maida kayan saida yai break ya fito, anjima dai inda hali ya sha kunun gyadar tunda shi mutumin shi ne.
First aid box ya daukko tareda fiddo wani jan ruwa a cikin kwalaba, sai wasu tarkacen karafuna daya debo, safar hannu ya fara sawa sannan ya fara amfani da jan ruwan da cotton wajen gogewa chuchu bakinta, kasancewar ya saba gani h.deejah ko vocal na goge mata yas shima baisha wahala ba wajen gogewar, yana dab da gamawa ya lura kamar 'yan yatsun kafarta na motsi a hankali kuma na hannunta suka fara, kafin fatar idonta taringa kokarin budewa, a hankali ta fara bude idanuwan nata kamar mai mayen bacci.
Dakin tafara bi da kallo sannan ta dire idonta a fuskar kwalisa dake zaune gefen gadon datake, ko mafarki take bataso ta farka dan haka ko idonta tana tsoron kiftawa karta rufe ta bude taga baya nan, ta gwammace ko a gizo ne taci gaba da ganinsa, a hankali wata irin kwallar tausauyin kai ta fara saukko mata, da sauri kwalisa yasa hannu yana goge mata shima hawayen yake da cewa "chuchu ki daina kuka, zubar hawayenki kamar digon narkakkiyar dalma yake a raina"
A tare jummai da hanne suka kalleshi danjin yana magana shi kadai, amma ganin chuchu ta farfado yasa suka mike a dokance bakinsu kamar gonar auduga kafin suce wani abu h.deejah tayi sallama ta shigo da "chuchuuuuuu" ta fada da karfi tareda sakin bowl din tangaran din a kasa ya tarwatse, da sauri ta karasa ta rungumeta suna kuka su duka "mummy dan allah mafarkine ko almara abinda ke faruwa dani, tunda surar kwalisa kemin gizo bata ta6ai min magana ba sai yau kuma naga tsayin lokaci taki bacewa daga idanuwa kamar yadda ta saba, mummy ki rokar min daddy alfarma ya barni in rayu a nan dakin indai zan ringa cin karo da gizon mukhtar irin haka"
Kalamanta ba karamin tasiri yai a zuciyar su duka hudun ba, saiga su hanne suda basuyi kuka ba suna sharar kwalla.
Hannun kwalisa h.deejah ta kamo tareda hadawa dana chuchu "ayeesher ba mafarki bane bakuma gizo bane, mukhtar nedai kike gani gashi nan" saida taji hannun kwalisa a nata sannan ta tabbatar shidinne amma farin ciki da mamaki sun hanata furta komai kawai sai hawaye da idon datake bishi dasu.
H.deejah ta kalli hanne "kirawo doctor"
* * *
Yau satin chuchu daya da farfadowa, zuwa lokacin tasan duk wani abu daya kamata ta sani gameda bayyanar sabon kwalisa a duniyarta, wata irin soyayya mai tsayawa a rai suke gabatarwa abin har mamaki yake bawa md da vocal ganin yadda suka dinke cikin kwanaki kadan kamar dama sunyi shekaru da fara soyayyar.
H.iyami taso zuwa duba chuchu bayanda kwalisa ke sanar da ita ta warware, ciwon kafarta ne ya motsa kwana biyu hakan ya katse mata uzurin zuwa dubiyar, ammafa kullum in kwalisa zai taho akwai abinci na musamman datake shirya masa tace ya kaiwa 'yarta, kiran waya kuwa kobata kira ba sai chuchu ta kirata duk safiyar allah ta gaida ita, batasan meyasa take jin so da kaunar chuchu a cikin zuciyarta ba, bata taba ganinta ba amma yanayinta da muryarta dataji a waya ya gamsar da ita irin tarbiyyarta, kwanan chuchu 17 a asibiti bayan farfadowarta aka sallameta.
Sunci gaba da zuwa makaranta itada vocal, saidai wannan karan sun cazawa 'yan skull din hankali itada ogan nata, ganin yadda lokaci daya suka birkide daga tom & jerry zuwa Romeo & Juliet, indai dayansu baida lecture to suna tare susu hudun, shigar riga da wando kuwa ta rage sosai sai dogayen riguna datake yawan amfani dasu kirar oman saitai rolling da karamin mayafi, vocal da md kam yanzu hankalinsu ya kwanta tunda sun tabbatar da samun nutsuwar aminan nasu.
* * *
Kwanci tashi ba wuya a wajen allah zuwa yanzu kwalisa sunata shirye shiryen tafiya bautar kasar su shida md, inda suka ci sa'a duk gari daya aka hullasu jihar edo.
Chuchu kam abin bai mata dadi ba ta tashin hankalinta sosai har ciwonta yaso tashi, duk kan damuwar kwalisa zai mata nisa na wasu watanni, haka kullum yake fama da lallashi dabata baki tayi hakurin kamar yau ne zasu dawo.
Ta sanya damuwar a ranta sosai har tunanin hakan yai mata yawa, zuciya kuwa tace bata san wannan ba, a ranar ne zata fara zuwa gaida h.iyami mahaifiyar dan a lokacin kawai jiran kwalisan za'ai ya dawo daga NYSCE din ai musu engagement.
Yanata magana shi kadai yajita shiru dan haka ya juya yaga ko chat take, amma saiya ganta suguri da alama tunani take, ya gangara gefen titin tareda parking din motarsa a gefe, da sauri ta dago tana kallonsa "my guy mun iso ne"
Ya tsareta da ido "bamu iso ba, ina gaya miki bestie kidaina sa kanki a damuwar tafiyata, bafa wani jimawa bane zanyi, kuma nai miki alkawarin duk sati biyu zan ringa dawowa ki ganni, pls ki daina damuwar nan banaso wlh tana yakushin farin cikina" ya karashe da marairace murya.
Saida ta fara goge kwallar idonta sannan muryarta na rawa tace "my guy kwana biyun nan gabana na faduwa wallahi ji nake kamar zan rasaka ne shi...." Ta kasa karasawa sakamakon tari daya turnuketa, yi take ba kakkautawa kafin daga bisani jini ya fara biyo tarin.
A guje kwalisa yai ribos tareda maidata gida koda yai parking a harabar gidan hannu yasa ya ciccibeta ya shiga da ita, zuwa lokacin ta daina tarin da aman jinin dan haka sai h.deejah kawai ta kira family doctor dinsu.
A.A ma dawowa yai daga office ba shiri, lokacin dayaje bacci take saboda allurar bacci da akai mata, harta rame cikin lokaci kadan, tsananin tausayin tilon 'yarshi ya tsirga mishi ganin yadda tata kaddarar jarrabawar mata tazo akan so.
Sai karfe goman dare kwalisa ya bar gidan, hakanma dandai ba yadda zaiyi ne, dayaje gida ya tadda h.iyami a falo sai safa da marwa take "ya jikin nata" ta tambayeshi, dan tunda abin ya faru ya kirata a waya ya sanar mata cewa bazasu samu damar karasowa ba.
"Hmm da sauki za'ace hajiya nidai harna taho bacci take" ya fada kawai tareda fadawa kan kujera
H.iyami ta kalleshi kawai tareda dauke kai "mukhtar dan allah karka rabu da yarinyar nan koda wasa, banaso kazama namiji mai irin halin su bukhar, aman jini mugun abu ne daga shi beli tai sallama da duniyarta" tana gama fadar haka ta wuce dakinta kawai, ya tabbatar kuka zata je tayi shima saiya sami kansa da muguwar tsanar bukhar dukda baisan shi ba.
* * *
Washe gari h.iyami tace zai kaita ta dubo chuchu, dan haka ya kira md ma a waya ya sanar dashi.
Karfe hudu suka kama hanyar forestry dan zuwa gidan A.A dubo chuchu, md da kwalisa na gaban motar yayinda h.iyami ke baya ita kadai, tunda suka taho kwalisa ya kira wayar h.deejah ya gaya mata, dan haka dasukaje har an shirya musu cima kala kala.
Ba karamin murna h.iyami da h.deejah sukai da ganin juna ba kamar dama cen sun san juna hira suke bawata nuna bakunta h.deejah ce tace "hajiya 'yar taki fa kiyi mata uziri tana toilet wanka take, gata da shegen kakale kakalen kwalliya"
Dariya h.iyami tai "ki barta kawai taci duniyarta da tsinke zamaninta ne kewa ya takuraki lokacin ki"
Dariya sukai su duka kafin md yace "mummy ashe tama warware" h.deejah ta amsa "tun jiyan data farka ta wartsake yau dinma tun dazu hirarsu suke da vocal a ciki, jin zuwanku ne yasata shiga wankan ba shiri"
Tana gama fada sukaji karar saukkowarsu daga saman bene itada vocal din, h.iyami tai tsaiii da ido tana kallon chuchu ganin muguwar kamarta da wanda ta tsana a duniya, to kodai..... Da sauri ta kawar da tunanin domin tasan kamace irinta kanuri kawai, dukkansu kusan kamarsu daya, dan haka ba abin mamaki bane dan wani yai kama da wani.
A tare suka gaida ita, cikin yake da tsananin faduwar gaba ta amsa gaisuwar tasu, kafin h.deejah tace barita kirawo A.A su gaisa.
Hankalin h.iyami na can tunanin wani abu dan haka bataji karasowarsu ba, sai muryarsa dataji ta sauka a dodon kunnenta "inaiwa manyan bakinmu sannu da zuwa" bazata taba mantawa da mai wannan muryar ba dan haka a rikice ta dago tana kallonsa, aisai gata ta mike tsaye tana nunashi da dan yatsa kafin tace da karfi "BUKHAR !!!" duka su biyar din juya sukai suna kallon A.A, dan harta chuchu, vocal da h.deejah sun san labarin bukhar da beli a bakin kwalisa.
A firgice shima yace "IYAMI"
H.iyami ta kalli kwalisa "mukhtar waye wannan?"
Ta fada tana nuna A.A cikin tsananin bacin rai, da rawar baki yace "hajiya shine dadyn chuchu"
Wani irin murmushi tai mai ciwo tareda kare masa kallo "bukhar ba aman jini ba ko 'yarka mutuwa zata ringayi tana dawowa wallahi dana bazai aureta ba..........."
Hmmmm tofa wannan shine ANA KUKAN TARGADE... SAIGA KARAYA, chuchu na zullumin kwalisa zai tafi nysc ya barta, saigashi zai barta bari na har abada, ko yaya zata kaya?
Mu hadu a part 8 a nan rigimar take
Prince av
09032724001
No comments:
Post a Comment