Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) 6

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


Khadija Sidi..✍🏼

6⃣

Ko  da Gimbiya K’amariyya ta koma d'akin ta, sai ta sallami bayin ta gaba d’aya sannan ta kulle d’akin ta haye tsakiyar gado ta na rusa kuka. Bintu kuwa d’akin Hajja Kilishi bayi ke jera kaya da aka d’inka ma ta na alfarma, yayinda Hajja Kilishi ta sa ta gaba sai bayani iri-iri ta ke mata akan kayan da kuma yanda za ta na amfani  da su, da yanda ake son zaman na ta ya kasance  a fadar Fabarusa kasancewar Sarki ya janye makwanin biyun da ya kamata a kai Bintu ga Masarautar Fabarusa.

Bintu da ba cikin hayyacin ta ta ke ba, babu abun da ta gane kawai dai amsa ma ta ‘’um’’ ta ke. Da wuri Hajja Kilishi ta bawa Bintu umarnin kwanciya saboda sammakon da za su yi a washagari. Yanda ta ga rana haka ta ga dare, haka ta kwana cikin zulumi sai da asuba wani bacci mai nauyi ya sace ta.

Ba ta jima ta na bacci ba, Hajja Kilishi ta aiko d’aya daga cikin Bayin da aka bawa Bintu, wato Ladiyo ta tada ita gudun kada su makara.  Nan ta ke tseguntawa Bintu cewar Gimbiya Binta har ta wuce Nigeria makaranta bisa ga umarnin Takawa. Kuka Bintu ta saka ta na mai fad’in

‘’Na shiga uku ni Bintu, wallahi ni Bintu na ke ba Binta ba, d’iyar bayi na ke ba d’iyar Sarki ba, ashe dai ba zan kammala makaranta ta ba, wayyo Inna ki zo ki taimake ni na shiga uku na lalace!’’

Da ladiyo ta ga haka, kawai sai ta fice, jim kad’an sai ga ta dawo biye da ita Hajja Kilishi ce rai 6ace. Tuni ta hau Bintu da fad’a, ta na fad’in

‘’Wai ashe ba ki da tawassali Fatima? Ba ki yarda da k’addara ba? Idan ba ki fasa kuka ba ba ba ki nuna mana ba a isa da ke ba’’

Jin wanna kalame na Hajja Kilishi tuni Bintu ta shiga taitayin ta, sai ajiyar zuciya ta ke kawai. Hajja Kilishi ba ta gushe ba ta cigaba da maganar ta kamar haka

‘’Ki d’au kaddara ki yi fata Allah ya sa hakan shi an alhairi gare ki, yoto ai alkhairin ne ma. Ina ke ladiyo ?’’
Ladiyo ta matso kusa tare da fad’in

‘’Ran ki shi dad’e’’

‘’Maza ku shiga bayan gida ku had’o mata ruwan wankan amare’’

Cewar Hajja Kilishi.
‘’An gama ran ki shi dad’e’’

‘’Ke kuma Hansai maza shirya kayan Gimbiyar ta ku, Ina Maman Cangwai ne? maza ku sheda mata ta ta kawo maganin d’ar nan da lalle domin yiwa amarya wankan lalle’’

Hansai na mai duk’ar da kai ta ce

‘’Ranki shi dad’e ai tuni Maman Cangwai na can rariya, fitowar Bintu kawai ake jira......’’

‘’Bintu ki ka ce!!’’

Hajja Kilishi ta daka ma sa tsawa. Hansai ta zube k’asa jiki na 6ari ta ke fad’in

‘’Tuba na ke ranki shi dad’e, na tuba ran ki shi dad’e ki min rai aradu na tuba’’

‘’Kwarankwatsi ki na rasa ran ki muddi ki ka kuskure asirin Masarautar ga tonu sanadiyar kuskure irin wang, shasha kawai, me an sunan Gimbiyar ga?’’

Hajja Kilishi na magana ne a hasala kamar mai shirin bugun Hansai. Ita kuwa Hansai idanun ta ke kawo ruwa.

‘’Gimbiya Bintu.....’’

‘’Gimbiya Fatima, ban yarda kin kira ta Bintu ko Binta ba!’’

‘’An gama ran ki shi dad’e, godiya na ke’’

Cewar Hansai. Allah Allah ta ke Hajja Kilishi ta sallame ta ko ta sami sarari. Jin Hajja Kilishi ta ce ta yi maza ta idda umarnin da aka ba ta, Hansai ta tashi da sauri ta fice. Kan ace me? Tuni aka shiga hidimar shirya Bintu, sai ga ta ta fito tsaf da ita cikin fararan tufa tun daga sama har k’asa. Hajja Kilishi ce ta d’auko wani dank'areriyar sark’a na gwal tare da yari da warwaro ta ce a sanyawa Bintu na ta gudunmawar kenan. Haka ma Inna Salti ta turowa Bintu goma ta arziki, ciki har da farrar god'iya. Sauran matan Sarkin ma suma ba a bar su baya ma, sai da su ka yi tattaki domin
nuna bacintar su dan kuwa abu na kishiyoyi sai da ya so ya zama gasa.

Rana ba ta k’arya, sai ga shi ana fitar da kayan Bintu zuwa motocin da ke jere domin kai amarya ga Masarautar Fabarusa, yayinda dattijiwar da ta zo amsar amarya, me suna Uwalanze ke zaune ta na jira. Wasu dattijai mata guda biyu, wanda su ke tamkar kakanni wajan su Gimbiya K'amariyya ne bisa ga al’ada su ka zo raka Bintu wajan Sarki domin su yi sallama a matsayin Mahaifin ta, sannan su damk’a ta ga mutan Fabarusa.

Bintu na ji ta na gani su ka sa ta tsakiya, gud’a ke tashi su kuwa tsofi fad’i su ke

‘’Allah Ya ba da sa’ar tafiya Gimbiya Binta, Allah ya sa a dace d’iyar arziki’’

Ba su zame ko ina ba sai turakar Sarki, in da su ka tadda Jakadiya tsaye bakin k’ofa ta na jira. Da isar su ta mu su iso zuwa gaban Sarki da ke daman abun da ta ke jira kenan. Gaban Sarki su ka aje Bintu dan idan aka d'auke dattijiya mai suna Gwaggo Munari cikin su, duk a na su zatan Gimbiya Binta ce. Sai da su ka kai gaisuwar su ga Sarki sannan su ka juya su ka bawa Sarki waje domin su gana da d’iyar sa.

Murya na rawa Bintu ta furta

‘’Barka da safiya ran ka shi dad’e’’

Shiru be iya amsawa ba, tsabagen tausayin Bintu da ya ji ya lullu6e shi, gami da nadamar hukuncin da ya aikata bisa ga san zuciya. Daga bisani ya nisa tare da fad’in

‘’Da wata murya za mu amsa mi ki Fatima? Da wata murya za mu amsa mi ki d’iyar arziki? Da wani baki za mu amsa mi ki wanga d’iya da ke gaban mu? Yau mun yi kad’an mu amsa gaisuwar wagga d’iya, wacca jama’a su ka ku6uta da ga yunwa saboda ita. Sanadiyyar wagga d’iya, mutan Sa’ayrasa na godiya gare mu, mu kuma godiyar mu gare ki ya ke, Allah ya saka mi ki da alkhairi sa’’

Shiru ya yi na d’an wani lokaci sannan ya cigaba

‘’Mungode kwarai hak’ik’a mun yi dana sanin abin da ya wakana a Masarautar mu, hallo mu na fatan hakan ya zama alkhairi a gare ki. Ki tsaya tsayin daka domin tabbatar da rufin asirin mu, shakka babu kin mana abin da ‘ya’yan mu ba su ma na ba. Tashi ki tafi d’iyar arziki, mu na addu’a albarkar Allah ya bi ki duk in da za ki kasance’’

Jiki na rawa, amma Bintu ta kasa tashi ta kuma kasa magana. Jakadiya ce ta lek’o, ganin yanayin da Bintu ta ke ya sa ta yiwa Dattijan nan magana su shigo su tafi da Bintu Sarki ya gama ganawa da ita.

A 6angaran Hajja Kilishi su ka tadda Dattijiwar Fabarusa wato Uwalanze. Nan aka damk'a hannun Bintu gare ta bisa alada da amana. Bintu fuska k’udundune cikin alkyabba kuka har da majina, Uwalanze ta ja hannun ta, biye da su d’aya daga cikin wannan dattijan ne da su ka kai ta ga Sarki, dama kuma ita d’in ce cikin su ta san gaskiyar lamarin wato Gwaggo Munari. Kai tsaye motocin Fabarusa su ka numfa.

Motoci ne na gani na fad’a wanda ke tashe wannan k’arnin. Mota ta farki cike fal da dogaran Fabarusa, sai ta biyu wacce ke rufe ruf da bakin gilashi, ita ce motar da su Yarima Barde ke ciki. A ta ukun Bintu ke zaune tsakiyar Uwalanze da Gwaggo Munari. Sai ta hud'in kuma bayin da aka bawa Bintu ne, wanda idan ka d'auke Maman Cangwi ko wacce daga cikin su tafe ta ke da na ta kullalliyar akan Bintu. Mota ta biyar ma dogaran Fabarusa ne ciki. Nan su ka d'auki hanyar Fabarusa.

A  hankali Bintu ta ji ana ta6a kafad'ar ta, maimakon ta tashi sai ma dad'a lumshe idanu ta yi ta na mai murmushi, kasancewar mafarkin da ta ke mai dad'i, wai ga ta a makarantar su, tare da Aisar su na zantawa ya sa ta ji sam ba ta so ta farka. Gwaggo Munari ce ta katse mata jin dad'i ta hanyar jijjaga kafad'ar ta, wannan karan da d'an karfi domin kuwa sun jima da isa Masarautar Fabarusa, yanzun haka kofar fada su ke, Uwalanze har ta fice daga motar amma Bintu na nan ta na baccin asara.

A firgice Bintu ta tashi jin jijjigar ta wuce hankali, ga busar algaita da ke tashi, har da hayaniya da wak'e dake  tashi daga bakin mutan Fabarusa da su ka cika kofar fada domin ganin isowar amaryar Yerima Barde.

Ganin alamar Bintu ta tashi, Gwaggo Munari ta shiga gyara ma ta alkyabba yanda fuskar ta zai rufu da kyau, ta na fad'in

"Ko ke fa Gimbiya d'iyar Sarki mai dole, ai ke kuwa bacci be same ki ba"

Kalmar nan ta Gimbiya da jama'a ke kiran Bintu da shi sam ba ya mata dad'i, gani ta ke tamkar ana raina mata iyayen ta, ya ga wanda su ka haife ta amma fin k'arfi zai sa a raba ta da su? In dai haka zama Gimbiya ya ke Allah wadar da irin na Sa'ayrasa.

Ta na kan wannan tunani ne gilashin motar ya sauka, yayinda Jakadiyar Fabarusa ta bayyana a gare su, kana ta ce

"Gide mutan Fabarusa, na cikin gari hallo da na fada, kwan mu da kwarkwatar mu, mun hito domin tarbar amaryar zaki, Yariman mu abin alfaharin mu. Mu na neman alfarmar bayyanar wagga Gimbiya ta Sa'ayarasa, da ta kasance Gimbiyar Fabarusa da ga ranar jiya har illa MashaAllahu"

Gwaggo Munari na mai murmushi ta amsa mata da

"Gimbiyar ta mu, wacce ta kasance fure a gare mu, wacce babu shakka za ta wadata ku da kyawu gami da kamshi da ke tattare da ita, Gimbiya Fatima ta Sa'ayrasa ta amsa kiran mutan Fabarusa"

Jakadiya ta rangwad'a gud'a, tuni waje ya kaure da hayaniya,yayinda mata da yara su ka hau wak'a su na tafi, fad'i su ke

"Mun nema! An ba mu! Mun k'aru!
Mun nema!  An ba mu! Mun k'aru!"
🐪🐫🐪🐫🐪🐫

No comments:

Post a Comment