®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
ZUWA GA K'AWATA HYK, SAKON KI NA ARZIKI YA ISO GARE NI, NA KUMA CE AMEN HAR DA KE. NA GODE KWARAI, MADALLAH DA KE, SIDIYA CE KE MIKI FATAN ALKHAIRI🤝
©Khadija Sidi.....✍🏼
1⃣0⃣
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
Wanene Sarki Sule Inuwa Magaji?
Shi ne Sarki na ishirin bisa gadan mulkin Sa’ayrasa. Ya hau kujerar mulki a shekara ta (1984), bayan Sarki Inuwa Magaji mai rasuwa, lokacin ya na da shekara arba’in a duniya. Allah ya azurta shi da ‘ya’ya goma sha takwas, ya birne takwas saura goma a raye, maza takwas, mata biyu.
Mata hud’u ya aura, uwargidansa marigayiya Hajja Fatima Abdu, wacce ta rasu bayan shekara d’aya da hawar sa mulki, wajan haihuwar Gimbiya Binta. Haka kuma ita ta haifawa sarki yara takwas, kasancewar auren saurayi da budurwa su ka yi da Mai martaba, ‘ya’yan ta su an manya duk da dai yawanci ba su yi tsahon rai ba dan sai da ta birne hud’u kafin ta samu masu zama guda hud’u. Yerima Inuwa mai shekara talatin, yayi aure har da yara uku, Yerima Nuhu shekara ishirin da biyar, Gimbiya K'amariyya mai shekara ishirin da haihuwa sai kuma Gimbiya Binta .
Sai kuma matar shi ta biyu Hajja Salame wacce ake kira Hajja Kilishi, ita Allah be nufe ta da haihuwa ba. Sai ta uku Hajja Maimunatu ana kiran ta Uwar fada, yaran ta biyu, Hassan da Hussain wanda su ke sa'annin Gimbiya K’amariyya sa kuma amaryar wacce ta ke kanwa ce gun Hajja Fatima Abdu, aka d’aura masa bayan rasuwar sa mai suna Masarriya, ana kiran ta da Inna Salti(wacce za ta haihu da yawa), yaran ta hud’u, duka maza. Sun had'a da Yerima Hamza wanda shi ne babba mai shekara goma sha uku, sai mai bin sa Yerima Abdallah dan shekara goma, na ukun Yerima Ahmadu, shekara takwas sai autan ta Yerima Nadir mai shekara biyar a duniya.
Kasancewar ‘ya’yan sa mata biyu kacal a duniya da kuma soyayyar da ya ke yiwa uwar su, ya d’auki san duniya ya d’aura ma su, musammam K’amariyya wacce kamar ta d’aya da mahaifiyar ta kamar kabo da kabo. Hakan shi ya zame babban rauni ga Sarki Sule.
***** ******
Sai da su ka shige tsaunika da duwatsu, suna mai ketare yankuna da dama ta sahara, kafin su hau mik'ak'k'iyar hanyar da za ta sada su da Sa’ayrsa. Ta babbar kofar wanda ake yiwa lak’ani da kofar Magaji Babba su ka shiga yanki. Rana ne sosai kwallewa a yankin daga gani ka san ruwa be sauka baw, kamar ma ruwan sama be sauka a yankin ba bana. Jama’ar gari kowa sabgar gaban sa ya ke, daga masu zuwa ko dawowa daga kasuwa, sai masu zuwa gona, mata wasu da goyo wasu da yara a hannu su na ta hidimar su, ya yara su ma ba a bar su a baya ba, su ma da na su sabgar irin ta yara.
Babban abun da Bintu ta lura da shi, shine rashin annushuwa da kuzari na jama’ar yankin, ba kamar yanda ta saba ganin jama’ar yankin cikin farin ciki da annashuwa ba.
‘’Shin ko dai akwai wani abu da ke faruwa wanda ba mu da masaniya akai?’’ Tambayar da ta ke yiwa kan ta kenan, amma gudun magana ya sa ta kasa kada baki ta tambayi sauran bayi ‘yan uwan ta, har su ka kai ga kofar fada.
Ta k’ofar gabas su ka shiga fada, wanda dama in dai iyalan sarki ne ta nan su ke shiga.
Nan da nan jama’ar fada su ka fito tarban Gimbiya, ciki har da k’annan Gimbiyar wato Yerima Hassan da Yerima Husaini, Yerima Abdallah da kuma Yerima Hamza. Murna da farin ciki gun su kuwa ba a cewa komai.
Ana cikin wannan yanayin ne Bintu ta fito ta, bayan ta d’au d’an akwatin k'arfen ta, ta ja gefe babu wanda ya lura da ita bare a damu da halin damuwa da ta ke ciki. Ganin Gimbiya ta fito, da sauri ta k’arasa cikin bayi yan uwan ta, in da su ka zube domin kai gaisuwa ga su Yerima, sannan bayi su ka taka mu su baya su ka shege izuwa fada.
Bintu na durk’ushe ba ta tashi ba ta ji an tab’a kafad’ar ta, a hankali ta d’aga ido, tuni murmushi ya maye fuskar ta yayin da ta tashi tsaye ta na mai rungume yayan ta Habibu. Cikin farin ciki ya ce ‘’Kauna(kanwa) mu na ta ke kewan ki, tin ba ma Inna ba, yo kawo akwaitin na ki mu tahi ko?’’
Saboda murna Bintu kasa magana ta yi, sai kawai mik’a masa akwaitin ta yi. Akwaitin ya d’auka, ya na ruke da hannun ta su ka wuce sashin su na bayi. A hanya ya ke tambayar ya yaga idanun ta sun yi jajur haka? Ta ce da shi idanun na ta ke ciwo shi ya sa. Ya ce da ita ta dai sha magani dai ko? Ya kara da Allah ya sauwake.
'Bangaran su na bayi b’angare ne mai d’auke da sashi-sashi na gidajen bayi. Gidan su Bintu wanda ya ke na uku cikin jerin gidajen bayi, gida ne ginin k’asa, mai d’auke da d’akuna uku da falo, sai kuma d’akin dafa abinci da kuma 6and'aki guda d’aya.
"Dakunan biyu a cikin falo su ke, na ukun kuma tsakar gida ya ke kusa da dak’in girki, in da 6and'aki ke daga can gefe daf da soro. Ba wani girma ne da tsakar gidan ba haka zalika d'akunan, idan ana zafi da kyar su ke iya bacci, musammam yanayi irin wanda su ke ciki a yanzu, ruwa be sauka a yankin ba. Falon na su kuma babu komai ciki daga daga ciminti sai tabarma.
A tsakar gida su ka tadda Inna ta na tankad’en hatsi, kasancewar ta bababbariya baka ce wulik, doguwa ta na da dogon hanci, fuskar ta d'auke da zane da fashin goshi irin na al’adar barebari. Duk da Bintu ba ta kama da ita, akan ce tsayi da garin jikin Bintu na Inna ne, haka ma gashin kan ta wanda idan ta ware ya na saukar mata har gadon baya.
Da gudun ta Bintu ta je ta rungume ta, Habibu na mai fad’in ‘’Gide ga autar ta ki na kawo mi ki Inna’’
Cike da farin ciki ita ma ta rungume d'iyar ta ta, fad’i ta ke "Usoo am morantiye, wushe k3shero, is3maa?? Nda zawol?"(sannu yan boko, sannu da zuwa, an dawo? Ya hanya?)
‘’Lahiya limi Alhamdulillah, mun same ku k’alau?’’ Cewar Bintu. Inna na mai duban ta cikin nazari ta amsa da ‘’lahiya limi, Gide ya na gan ki da idanu haka jajur?’’
Bintu na fara'a dan gudun kar Inna ta gane halin da ta ke ciki, ta ce idanun ta ke ciwo. Ita ma sai a sannan ta lura da yanda Inna ta rema ta lalace, d’aga idan da za ta yi ta kalli Habibu sai ta ga ashe gwara Inna ma akan shi. Cike da alamar tambaya ta dawo da kallan ta ga Inna, kana ta ce "lafiya kuwa Inna? Ya na gan ku a rame haka? Ina Baba?’’
"Ya na fada.’’ Amsar da Inna ta bata kenan a takaice. Kana Bintu ta ce ‘’Yo to lafiya na ganku haka?’’
Inna ce ta amsa mata da "Yanzu dai ba lokacin tambaya ba ne, Habibu maza k’arasa mata da kayan d’aka, sai ke kuma ki watsa ruwa ki ci abinci ma yi maganar ko?’’
Cike da fargaba Bintu ta gyad’a mata kai kafin ta shige d’akin ta wanda ya ke d’aya daga cikin na falon, Habibu biye da ita.
Shigar su ta bi d’akin na ta da kallo, d'an karamin d’aki ne mai d’auke da gado na k’arfe mai (spring)na daidai kwanciyar mutum d’aya, sai kuma wani k’atan buhu gefe in da Bintu ke aje kayan sawa. Ko tabarma babu a d'akin, sai siminti da ya bi ya faffashe rugu rugu. Gefe guda Habibu ya aje akwatin sannan ya fice ya bar Bintu ta na mai zubewa bisa gadan ta a gajiye. Lalle kuwa kowa fa ya bar gida gida ya bar shi. Daga waje ta jiyo Inna na fad’in ‘’Ki hito ki watsa ruwa fa ‘yar nan’’
Bintu ta amsa ‘’Gani nan hitowa(fitowa) Inna’’
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
No comments:
Post a Comment