Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 25

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

DA BAZARKU NI NA KE TAKA RAWA ​FIKRA WRITERS ✌🏽

Ummuabdoul
Ummu Hannan
Rashida Kardam
Sanah Matazu
Aysha Kura
Batul Maman
Bingel
Farida Abdullahi
Da uwa uba Rufaida Umar, ba zan mance da ke ba. Allah ya bar zumunci.




©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣5⃣

Kai tsaye 6angaran Jakadiya da ya zame mata sabon wajan kwana ta shige, ta tsallake bayi biyu wanda ke ta faman had’e sababbin kayan da aka d’inko mata, ta shige d’akin Jakadiya ta na mai doka k’ofar gudun kar Yarima Nuhu ya biyota.  K’uryar d’akin ta shige ta k'udundune ta na mai mayar da numfashi. Ba ta yi minti biyar da shiga ba bayin su ka biyo ta su na mai tambayar lafiya? Ko ta yi gamo ne?

Baki na rawa Bintu ta ba su amsa da ‘’Don mai sama ku rabu da ni, ko shakka babu na kusa rasa raina, na shiga uku ni Bintu na lalace, wayyo Allah Inna ta!’’

Kallon junansu su ka yi, su na mai gyad’a kai cikin jaddada zatonsu na Bintu ta yi gamo, har an fara jifanta daga Masarautar Fabarusa tun kan ta shiga Masarautar, su ka juya jiki a sanyaye su ka fito suna mai rufo mata k’ofa.
Daga waje baiwa ta dubi ‘yar uwarta ta ce
‘’Gide k'ak'a kenan, kinga har an fara yiwa wagga d’iya ture ko? Babu mamaki wani bakin aljanin aka fara mata ture da shi don ta fita hayyacinta ta ce ta fasa amran ga, wagga sharri sai kishiyoyi, maza je ki shedawa Jakadiya tun kafin abu yayi tsamari.’’
Cike da jimamin abun baiwar ta amsa mata da
‘’Wagga batu gaskiya ta, aradu wagga d’iya gamo ta yi, inda kin lura har launin idanunta ya sauya, bara dai na je ga Jakadiya, mutum hege ne, mutum ba imani.’’

Tana mai ta6a kafad’arta, ta ce
‘’Maza Ladiyo, ni bara na tsaya daga rariya ko da wani abun zai faru.'’
Jikin baiwar na rawa ta fara tafiya, tana fad’in
‘’Eh tsaya Kyallu, bara na ruga na dawo, Allah shi fisshemu daga sharrin mahassada.’’
Ta fice, inda ta bar Ladiyo da tsaron k’ofar Bintu. Ita kuwa Bintu ita kad’ai tasan abinda ke damunta, yau ta ji ta kuma ga abinda ba ta ta6a tsammani ba, ko shakka babu tasan rayuwarta ce ta zo k’arshe, ko kuwa dai Yarima Nuhu ya soma shaye-shaye kamar yanda wasu samari daga cikin bayi su ke yi. Abinda ke d'agawa Bintu hankali shi ne sake rike hannunta da Yarima Nuhu ya yi, ita tasan rayuwarta ce ta zo k'arshe.

Jin Bintu ta fara yin gamo tun ba aje ko'ina ba, nan da nan Jakadiya ita ma ta had’o kayan tsubbuce tsubbucenta, haka ma Hajja Kilishi, wacce dama ita aka damk’awa Bintu a hannu. Suna mai jan kunnan bayinnan biyu, Ladiyo da Kyallu, akan kar su sake aji maganar a waje.

A gaba Jakadiya da Hajja Kilishi su ka sa Bintu, tambayar duniyarnan sun mata akan gamon da aka ce ta yi, amma shiru Bintu ta kasa ce musu komai don kuwa muddin ta fad’i gaskiya to kashinta ya bushe. Ganin haka su ka yanke hukuncin fara kare ta tun daga yanzu don babu mamakin sammu da aka fara mata har da na d’aure baki. Bintu na ji ta na gani aka fara mata lalas da siracen magunguna, har da na sha da wanka, kan ka ce me tuni ta fita hayyacinta in banda attishawa babu abinda ta ke yi, ko iya haka aka barta ta san ba k’aramin masifa ganin Yarima Nuhu ya jaza mata ba.
Bayan siracen da ta sha, sai da Jakadiya ta bi duka ga6o6in jikin Bintu ta na d’aura mata laya, wai gudun kar a zo mata cikin dare, nan ko ba su san in ma akwai aljanin ba zai wuce Yarima Nuhu ba, kai Allah shi fisshe mu aikin jahilci.

Saida su ka tabbatar sun gama kafe Bintu kaf, Hajja Kilishi na mai duban Bintu da gaba d’aya ta jigata saboda siracen da ta sha, gashi cikinta har juyawa ya ke tsabagen had’aka na magunguna da Jakadiya ta afka mata duk da sunan makarin sammu da kafiya, Hajja Kilishi ta ce

‘’Ni ko Jakadiya d’iyarnan na shan maganin da’a kuwa(maganin mata)?’’

Jakadiya na mai susa k’eya ta amsa da
‘’Yo to wani maganin da’a za a bawa wagga d’iya za a amran da ita ga tsoho ank’i rami? Ai ni a tunanina tunda dai Sarkin Fabarusa an tsufe ban ji zai damu da abubuwa irin wagga, ko k’ak’a kin ka gani?’’
Hajja Kilishi na mai murmushi ta ce
‘’Tsoho ba mutum ba Jakadiya, yo to maza ma ai ba sa tsufa, kar ki so ki ga yanda Takawa ke ji dani duk farin gemun nan nasa, yauwa tun da magana ta kawo magana, Jakadiya ina mai buk’atar zuwan Takawa gare ni a yau ma, hallo zannuwa da kallabi har guda goma na nan tafe izuwa ga d’akin Jakadiya nan ba da dad’ewa ba’’
Dama dai maganar kenan, ta 6ige da Bintu gudun kar Jakadiya ta ga kamar ta cika naci, don kwana hud’u kenan ita Jakadiya ta ke kai wa Sarki, kasancewar hatta kwanan matan Sarki sai wacce Jakadiya ta za6a tsabagen matsayi irin na Jakadai a fada.
Jakadiya kuwa mai idon cin naira, jin zannuwa na tafe tuni ta kada baki ta ce
‘’Yo to menene, in ma sau goma ki ke san zuwan Babban Bijimi aradu gun ki ya ka kwana, an gama ranki shi dad’e, sai kin ga zuwan mu.''

Hajja Kilishi na mai jindad’in yanda Jakadiya ke damawa da ita, duk da dai ta san na d’an k’ank’anin lokaci ne, in dai Jakadiya ce bakin ganga ta ke, arzikinka shagalinka. Ta mata sallama in da ta barta da Bintu ta mai mata jawabin yanda za ta yi ta kare kanta a Masarautar Fabarusa. Ita dai Bintu jinta kawai ta ke, amma ko yaya ta rufe idanunta fuskar Yarima Nuhu ta ke gani yayinda ya ke furta kalmar so a gareta, haka zalik’a maganganunsa ke mata yawo cikin kwakwalwarta. Ko shakka babu Bintu ta yi gamo, amma fa da Yarima Nuhu, mutuwarta kad'ai ta ke jira kamar yanda Iya Dije ta ce muddin namiji ya ta6a ta.

Zoben Aisar kuwa d’aya daga cikin bayi ne, wanda saurayi ne, mai kula da lambu ya tsinta yayinda ya ke shara. Ganin zobe mai matuk’ar tsada yayi saurin 6oyewa cikin aljihunshi, don jira ya ji ko mai shi zai nema, idan kuma ba a yi cigiya ba ya kai kasuwa ya siyar ya sami kud’i.


********
Kwanaki uku ya rage auren Bintu. Da hantsi Inna Salti ta kawo ziyararta ga Bintu. Daga ita sai Bintu da ke d'urkushe gabanta ne a d'akin. A sannu cikin lallami Inna Salti ke mata magana, in da ta ce
‘’Bintu ki sani wannan lamari jarabawa ce daga Allah, saboda haka ki kasance mai biyayya sai ki ga kin ci jarabawar. Wagga amre za a yi shi ne cikin surri, duk wanda ki ga ya san wani abu na game da gaskiyar wagga amre to amintaccen fada ne, hallo sai sun rantse ake ba su amanar ga, dan haka kema wagga al'amari ya kasance amana a naki 6angaren, idan ki ka kuskura gaskiyar al’amari ya hito, rayuwarki za ta kasance cikin hatsari Bintu, wanda ba na fata. Daga sanda aka amra miki amre za ki tashi daga Bintu, za ki fara amsa Gimbiya Binta.’’

Numfashi ta ja, sa’annan ta cigaba
‘’Kin dai ga yanda sarauta ta ke, a fada aka haife ki ciki ki tashi har rana ita yau da ake shirin amrar da ke. Hallo sai kin yi takatsantsan da rayuwar da za ki shiga, zaki shiga rayuwar amre hallo a fada, akwai wuyar ganewa. A fada ba kowa ne zai 6ud’i hak’ora ya miki dariya ya kasance masoyi gareki ba, wani sa'in ma mak’iyinki ka iya nunawa kin fi kowa soyuwa a gareshi, haka zalika ba kowani mai 6ata miki ba ne mak’iyi a gareki, ta iya yiyuwa kauna ke kawo 6acin ran, don haka ki nutsu ki gane.’’

Bintu na mai share hawaye sai gyad'a kai kawai ta ke. Inna Salti na mai nisawa ta k’ara da
‘’Ki ji ki k’i ji, ki gani ki k’i gani, ki iya harshenki, hatta bangon fada kunne gareshi, ki kyautata dangantakarki da kowa, ki sa Allah a ranki, ki yawaita addu'a da zikiri, ki kasance mai yawan zama da alwala, shin kin iya azkar?’’

Bintu ta girgiza kai alamar ah ah,
Inna Salti na mai gyad’a kai ta ce
‘’Zan yi k’ok’arin sawa a koya miki kan a kai ki ga Fabarusa, ki na yi safe da yamma, ni ma da kika ganni anan addu'a ce da tawassali ga Allah kad’ai ke zaunar da ni a wagga Masarauta bare kuma Masarauta mai girman gaske kamar Fabarusa.’’

Jakadiya ce ta shigo, yayinda ta zube gaban Inna Salti cike da girmamawa duk da dai ba yin Inna Salti ta ke ba, ba ta yi mata kyauta da cin hanci kamar sauran matan Sarki.
‘’Barka da hantsi ranki shi dad’e.’’

‘’Barka dai Jakadiya, na sameki lahiya?’’
‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e.’’
Kana Inna Salti ta maida dubanta ga Bintu ta ce
‘’Inaso na san adadin bayin da za su bi Bintu Masarautar Fabarusa.’’

Jakadiya na mai gyara zama ta ce
‘’Akwai Ladiyo da Kyallu, wanda Gimbiya Binta ce ta za6esu da kan ta....’’
Jin haka sai da Bintu ta d’ago ta dubi Jakadiya cike da fad’uwar gaba, don kuwa ta san hakannan siddin Gimbiya Binta ba za ta ta6a za6a mata kowani abu ba, muddin ba sharri ba ne. Ita kuwa Jakadiya da ba ta san ma ta na yi ba, ba ta gushe cikin jawabinta ba
‘’Sai kuma Uwanini, amintacciyar baiwar Yarima Nuhu wanda shi da kansa ya buk’aci hakan.....’’

Ihu ne kawai Bintu bata kurma ba jin wannan masifar da ake shirin had’a mata, maganar Inna Salti ne ya d’an kwantar mata da hankali, jin ta ce
‘’Ita fa Bintu? Shin an tambayeta ko ta na da baiwar da ta ke son tafiya da ita?’’
Jin haka Jakadiya ta kai kallanta ga Bintu, ta ce
‘’Bintu shin ko kina da wannan buk'atar gide? Wa ki ka za6a”
Bud’ar Bakin Bintu sai cewa ta yi
‘’Innata, dan Allah a tafi da Innata’’

Jakadiya na mai girgiza kai ta ce
‘’Innar ki gobe goben nan za su yi bulaguro zuwa marad’i bisa ga umarnin Babban Bijimi, har sai an sami lafawar al’amura za su dawo, sai dai fa ki za6i wata baiwar.’’
Nan da nan Bintu ta fashe da kuka jin Innarta za su bar gari, Inna Salti ta fara k’ok’arin rarrashinta Jakadiya ta ce
‘’Ai da kin kyaleta ranki shi dad’e, abun ga ne ya zo ga ma su shi, kukan amre da sallallami '’
Inna Salti ba ta fasa rarrashin Bintu ba, har ta samu ta d’an yi shiru kafin ta k’ara bata za6i, inda ta za6i aminiyar Inna kuma mahaifiyar k'awarta Cangwai, wacce aka fi sani da Maman Cangwai.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment