Saturday, 16 September 2017

Ina ze kai mu 6

INA ZE KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul
safiyyahjibril@gmail.com

            6.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ka mik'a kanka kawai ya yanke maka haddi, shi ne kawai mafita a gare ka. Taɓ ta'addanci, oh ni ya rabbi kuma sai a ta fakewa da sunnan manzo SAW, duk da shi ɗin ya kasance mai kyakkyawar mu'amala da wa'inda su ka kafurce masa ma ballantana musulmi. Allah dai ya shiryar da masu wannan mugun halin" cewar Afreen tana mai cike da mamaki.

"Toh tun da ba'a same shi a lokacin da yake aikatawa ba kuma in ya tuba mai inganci ai ban tsammanin wani cikinmu zai shiga hurumin Allah. Don shi ɗin mai amsar tuba ne" cewar Ustaz

"Wayyo cikina wai duk da ban ji naku ba ai na san ku ɗin ma wasu tantiran masu zunubi ne amma sun kanannaɗe sai wa'azi kuke antayowa, Wayyo hahahaha!  Ta karasa tana dariya har da kwanciya a benci.

" Toh mara zunubi faɗi naki muji, kin zauna sai zuba cikin ki guba kike, Mtsw!" inji Sufyan

"Ai duk abinka malam sai na aure ka mun ci kuɗin nan a tare" Ta amsa tana fari da ido

"Lallai codeine na faɗa miki k'arya kenan. Ke muke saurare"

***

"Suna na Zulfaa Zakari. Iyaye na ba za'a kira su talakawa ba duk da kuwa sun yi gadon ta. Abin nufi anan shi ne Sana'ar gidanmu ɗaya ce tun kaka da kakanni kuma har yanzu in kuka cire mahaifi na ba wanda bai ɗauke hakan a sana'a ba.

Sana'ar kuwa ita ce gyaran keke. Shi kuma mahaifi na tun da ya buɗe ido ya ga irin rayuwar da su ke sai ya samfe ya koma kauyen su ya samu fili ya fara noma, tun yana yi kaɗan kaɗan har Allah ya haɗa shi da wani ɗan boko ya ɗaura shi akan hanyar noma ta zamani shike nan ya samu wadata.

"Kun ga ni da na ki yarda na gaji wannan talauci ai na nema ma kaina wani Sana'ar daban. Ku zo in ba ku jari mu fadada sanaoinmu ko zamu samu yalwan arziki a zuriar mu" Ya ce da yan uwansa wata rana

"Toh zaka yi yaki da ikon rabbi kenan, ya qaddaro mu talakawa ya kake so mu yi. Ni dai ba zan kashe kaina ba in ya so in yi kuɗi da faci zan fi dangote kuɗi" cewar babban yayansu kuma take ya samu mabiya.

Jiki a sanyaye mahaifi na ya koma kauyen da muke zaune.

***
Da Sana'ar noma yayyi na huɗu su kayi karatu a Kasar Ingila, ni kuma na haɗa digiri a jami'ar Bayero. Nan ne hankalin dangin mahaifi na ido ya raina fata. Ba su da aiki sai jifan mu da muggan kalamai da muguwar fata kala kala.

Ina kammala jami'a nayi aure, na auri Mustapha. Mun haɗu da Mustapha ta hanyar Facebook ne, abin da ya ja ra'ayina gare shi yanda yake dagewa ya zage gwamnatin kasarmu, yana faɗin zaluncin da suke ma kasarmu ni kuma na kasance maabociyar son siyasa.

In Mustapha ya yi rubutu akan samu comments fiye da dubu, abokansa kuwa sun fi dubu shida.  Hakan yasa da ya furta min kalmar so na ji babu wanda ya kai ni dace.

***
Sanin da mahaifi na yayi masa a Facebook ya sa bai wani yi dogon bincike ba ya bashi aure na don ya san yana tare da manya kuma shafin sa na nuna yayi karatu har digirgir a California. Duk yanda yayyi na suka so yin bincike Abbanmu ya hana.
Haka aka yi aure aka kai ni gida na da ke Jan bulo. Gida mai hawa biyu da kuma wani a kasa (underground).

Kasar Amerika mu ka yi amarcin mu sai daga baya mu ka dawo a nan ne na san wanene Musty.

Mustapha Bukar ba kowa bane face kawali ga yan siyasa, sannan ɗan Koren boka ne. Yayi karatu har matakin sakandire a nan ne ya goge a turanci. Ba a nan gizo ke saka ba Mustapha shi ya koya min shan duk wani nau'i na kayan maye... "

" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, da ga raya sunna" faɗin Ustaz a mamakance

"Hmmmmn ai duniya ka ji tsoron mutum, balle wanda ka ci karo da shi a social media da yake gaibu" Ta ce tana karkada kai..

No comments:

Post a Comment