®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣2⃣
Sidiya ce.....✍🏼
6angarn Bintu kuwa kamar yanda ta saba, yau ma ta sallami dukkanin bayin ta, ya rage daga ita sai Ladiyo, wacce ita dama d’aki d'aya su ke kwana idan ta tabbatar kowa ya d’auke k’afa, tsabagen tsoro da rashin sabon kwana ita kadai. Bintu na kwance bisa gadon ta, tunanin Innar ta ta take da rayuwar ta na da wanda shi ya fi mata dad’i akan wannan daula da ta tsinci kan ta a ciki. Ladiyo da ke tsaye bisa taga idanun ta kan hanyar lambun da ke kyetare da 6angaran Bintu, sai ajiyar zuciya ta ke ba tare da ta san ta na yi ba saboda tsabagen muradin sake zuwa lambum da ya addabi zuciyar ta, ba dan komai ba ko dan ta ga wannan buzun da ta gani ciki mai irin sifar aljanu tsabagen kyauwu.
Gashi ran da ta fara shiga lambun satar hanya ta yi bayan Bintu ta yi bacci ta ga wucewar sa, kasancewar shi kad’ai ne ya sa ta yi tunanin kila talakan Sarki ne, wanda su ke da daurin gindi wajan fadawan Sarki ko kuwa d’aya daga cikin ‘ya’yan hakiman masarautar nan. Nan ta gan shi zaune bisa kan dutse ya na sakar zuci, har ta k’are masa kallo be san ta na yi ba tajuya tana tasbihi ga Allah bisa tsarin halitta da yayiwa bawan Allah nan.
A hankali ta kai kallan ta ga Bintu, kana ta ce
‘’gide Gimbiya ba ki da muradin ganin farin wata ne? aradu zaman cikin kurya ya ishe ni’’
Jin haka Bintu ta yi farat ta tashi zaune ta na fad’in
‘’yo to Ladiyo mu tai mana, ba tun yau na ke da muradin mik’e k’afa, kwankwatsi ni ma na gaji da zaman nan, hallo ki na ga babu matsala aka gan ni a rariya?’’
Abun da Ladiyo ke so ta samu duk da kuwa ba ta yi tsammanin haka daga wajan Bintu, ko da shike dama ai d’iyar bayi ce Ladiyo din ce ke sha’afa. Ta yi saurin dawowa gaban Bintu jiki na rawa ta ce da ita
‘’gide ai da yawa ba su san fuskar ki ba, ba na jin za su waye ki, kai in ki na son badda kama ma zai fi na ara mi ki d’aya daga cikin kaya na na bayi......idan fa Gimbiya za ta iya sanyawa’’
Ta k’arasa ne cikin d’ard’ar kada Bintu ta ce ta raina ta, duk dai ita kan ta ta san babu laifi Bintu ba ta canza mata ba, in har ba wai akwai mutane gun ba yanda ta saba mata tun tana baiwar ta hakan ta ke ma ta. Ga mamakin Ladiyo sai gani ta yi Bintu ta tashi cikin hanzari ta na mai fad’in
‘’kayya ku ji mu da Ladiyo da yasasshen zance, tuwo ne towo ba a sake masa suna, maza d’auko mu tai ko ba komai na sha iska’’
Cike da farin ciki Ladiyo ta da’aukowa Bintu d’aya daga cikin kayan ta na bayi, kan kace me sai ga Bintu ta koma gidan ta na da, wato shigar kayan bayin Sa’ayrasa, Ladiyo har ta na mata tsiyan ya ta ga kayan sun kar6e ta sun zauna jikin ta sosai, ko da shike daga jikin ne.
Bintu na duban kan ta cikin madubi, idanun ta cike da kwalla ta ce
‘’Allah Sarki wata rana, aradu Ladiyo na fi san rayuwa ta a da akan wagga sabuwar rayuwar’’
‘’yo to Bintu ina ga cigaba ki ka samu, wani sa’ilin sai na ji dama ni ce ke aradu da kin ga yanda ake tsiya da mulki. Mu tai dan Allah kar wani abun ya zo ya sa mu fasa hita’’
Bintu na me goge kwalla ta bi bayan Ladiyo. Daga waje su ka tadda bayi mata wanda Goggon nan ta bawa Bintu zaune. Ganin su sai da Bintu ta ja da baya gudun kar da su waye ta. Ladiyo ce ta yi maza ta ja hannun ta tana mai fad’in
‘’barkan ku da dare’’
‘’barka dai Ladiyo, an fito shan iska ne?’’
Su ka amsa mata amma idanun su na kan Bintu. Ladiyo ta ce
‘’eh Gimbiya na da muradin a bar ta ita kadai’’
Kai su ka jinjina su na mai musu fatan dawowa lafiya. Har sun yi gaba su tsaida su ta hanyar fad’in
‘’ba ku ji ba’’
Cak su ka tsaya, Bintu na mai rawan jiki, cikin ran ta fad’i ta ke
‘’shikenan sun gane ni’’
Ita kanta Ladiyo mutawar tsaye ta yi ta na jiran tsammani. D’aya daga cikin bayin ce ta matso gare su kana ta ce
‘’Ladiyo wagga baiwar ban waye ta, shin ko ita ce Lantana?’’
Ta na magana ne yayinda ta ke k'ok'arin ganin fuskar Bintu wacce ta 6uya cikin duhu. Ladiyo na mai sosa k’yeya ta ce
‘’ah ah wagga Batula sunan ta’’
‘’Batula?’’
Baiwa ta sake maimaitawa, Ladiyo ta jinjina kai kafin ta ja hannun Bintu su ka yi gaba ta na fad’in
‘’bari dai mu je mu dawo....’’
Ko da su ka k’urewa ganin bayin sannan su ka karya kwanar da za ta sada su ga lambu, har lokacin gaban Bintu be dena fad’uwa ba, haka kuma Ladiyo ba ta fasa mitar gulma irin na bayin Fabarusa ba.
Hankalin Bintu be kyauta ba sai da ta tsinci kan ta cikin lambu. Lambu ne mai ban sha’awa wanda ya sha ado da bishoyin kayin marmari iri daban daban. Hasken wata da yayi fari kal a tare da hasken lantarkin da ke daga cikin kowacce kusurwa na cikin lambun ba k’aramin k’ayata shi yayi ba. In ban da koken tsuntsaye da na kwari babu abun da ke tashi cikin lambun.
Tuni Ladiyo ta shiga raba ido ko Allah ya sa ta ga wannan mutumin, ita kuwa Bintu wani dutse ta samu ta yi zaman ta kai ta na fad’in
‘’kai Ladiyo wagga lambu ba dai ni'ima ba, ni dai na yi wajan zama daga nan’’
Ladiyo na mai raba idanu ta ce da Bintu ita dai za ta d’an taka to, yanzu za ta dawo. Nan bisa dutse ta bar Bintu yayinda ta kutsa cikin lambu domin neman wannan mutumin.
Barde kuwa da daman shi Ladiyo ke nema zaman Lambun ne ya ishe shi, gaba d’aya ya kasa samin nutsuwa. A hankali ya ke shawagi cikin lambu, wani irin wari ya ji yana bak'untar hancin sa sannu a hankali, tun ya na iya jurewa har ya kasa ya yanke hukuncin ficewa daga Lambun gaba d’aya dan kuwa warin ya fi k’arfin na mataccen dabba. Ko da ya d’auki hanyar fita daga Lambun nan ya ji wari na k’ara gabato shi. Nan bisa dutse yayi kaci6us da ita kishingide, idanun ta runtse tamakar mai bacci, hakan nan wani irin wari da tun da yazo duniya be ta6a jin irin sa ba ya daki hancin sa har sai da ya ja baya da sauri wanda k’aran sautin motsin na sa ya sa Bintu bud’e idanun ta yayinda ta kai kallan ta ga kyakkawan buzun da ke tsaye gaban ta, hannayen sa biyu bisa hancin sa da alama yana k’ok’arin kare hancin daga jin wari ne.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪
No comments:
Post a Comment