®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
©Khadija Sidi.....✍🏼
1⃣7⃣
Inna na mai rafka salati gami da dafe k’irji ta ce
‘’lahaila haillallahu mahammada rasulilahi! Bintu kuma Malam? Me ya had’a Bintu da masarautar Fabarusa saboda Allah da manzan sa? Yo to da haka a d’au wuk’a a da6a mana sai mu san kashe mu ake son yi da hujja!’’
Baba na mai nuna Bintu da d’an yatsa wacce ta ke hawaye d’aya na bin d’aya ya ce
‘’ga ta ga ki nan dai shegen biko’’
Kuka Inna ta sa yayinda ta rungumo Bintu ta na fad’in
‘’bar kuka Bintu, bar kuka d’iyar arziki, addua shi ya kamata mu yi, innalillahi wainna ilaihiraji’un’’
Ganin haka Baba ya sa kai ya fice ya na mai fad’in
‘’kwa dai k’araci munahuncin ku, bakin alk’alami ya bushe’’
Ranar sam Bintu ba ta sami bacci ba, kwana ta yi ta na kuka. Shi kan shi yayan ta Habibu ya tausayawa Bintu, zai ji dad’in zama yayan matar sarki, amma kasancewar auren hatsari ne ya sa shi girgiza da juyayin abun.
Washagari da ciwan mara Bintu ta tashi, kasancewa al’adar ta ta sake dawowa, ga kuncin zuci da ya addabi rayuwar ta ya sa gaba d’aya ta fita daga hayyacin ta. Ji ta ke dama motar bayi sun tafi sun bar ta a makaranta, in ya so Aisar ya tafi da ita ta huta da wannan rayuwa mara ‘yanci. In kuwa ta tuna shikenan fa ba ita ba komawa makaranta, ita da Aisar sai dai ta hange shi a akwaitin talabijin idan Allah ya sa an nuna shi sai ta k’ara saka wani kukan har da shasshek’a. Ko damar shiga babban gida ba ta samu ba, haka kuma daga Gimbiya K’amariyya har Gimbiya Binta babu wanda ya bi ta kan ta. Musamma Gimbiya da buri ya cika.
Ranar sarki ya tara iyalen sa a turaka bayan Jakadiya ta tabbatar ma sa da inganci da ilimin Bintu akan sarauta kasencewar ta tashi gidan sarauta, wanda su ke da yak’inin lamarin da aka k’ulla zai daidaita ba tare da an sami akasi ba.
Zaune suke gaban Sarki, Hajja Kilishi ce zaune ta 6arin dama, kusa da ita Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ne zaune. Sai Uwar fada da kuma Inna Salti, kusa da ita autan ta Yarima Nadir ne zaune daga 6arin hagu. Gaban su kuma ‘ya’yan Sarki ne maza, ciki har da babban d’an sa, dokajin Sa’ayra sa wato Yarima Inuwa, kusa da shi Yarima Nuhu ne. Sai kuma daga can gefe Yarima Hassan da Yarima Hussaini, Yarima Hamza, Yarima Abdallah da kuma Yarima Ahmadu su ka yi na su dairar.
Jin batun na Sarki, idan aka d’auke Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta da dama ita ta kulla k’ulalliyar babu wanda be girgiza ba. Yarima Inuwa ne ya duk'ar da kai kana ya ce
‘’Allah shi ja da ran Sarki, shin an zatar da hukunci ne ko kuwa ana buk'atar shawara daga iyalan Mai Martaba?’’
Sarki na mai duban sa ya ce
‘’mun gama yanke hukunci, amma jin ta bakin ku ba laifi ba ne’’
Jin haka sai Yarima ya ce
‘’Allah shi kyautata lamarin Babban biji, komai ku ka zartar daidai ya ke, ina ga zai fi kyau a duba lamarin nan saboda gaba, ran Mai Martaba ya dad’e’’
‘’Allah ya ja zamanin Takawa, ni ma dai hakan zance, dan kuwa gaban ya fi baya yawa, muddin ba za mu iya yin yanda su ka tambaya ba, zai fi kyau a yi watsi da maganar gaba d’aya in ya so sai mu nemi taimako wani wajan daban ko kuwa a amra masa K’amariyya yanda ya buk’ata’’
Inna Salti ce ta ara ta yafa, dan kuwa kusan ta fi kowa jin d’acin maganar cikin matan Sarki, hakan ya sa ta kasa yin shiru. Tun da ta fara maganar Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ke hararar ta ta wutsiyar ido. Shi kuwa Yarima Nuhu tun da aka fara maganar ya ke son furta abun da ke ran sa, jin Yarima Inuwa tare da Inna Salti sun share masa fage be yi k’asa a gwuiwa ba ya ce
‘’Ran ka shi dad’e, ka gafarce ni, amma ni a nawa wautar wannan lamari ba shi ne mafita ba, shin ya za mu yi a warware wannan sak’ar idan har aka kulla? Menene makomar wannan baiwa idan Allah ya sa Masarautar Fabarusa su ka gano wannan lamarin? Menene mazaunin wannan Masarauta ta mu? Shin gaba ake san kawarwa ko kuwa wata gabar ake san kullawa? Wannan tunani ya sa na yarda da Inna Salti, mu yi yanda Masarautar Fabarusa ta buk’ata ba tare da wani sark’akk’iya ba, ko kuwa zai fi kawai mu hakura da batun gaba d’aya in ya so mu nemi taimako a wata Masarautar ko ma Gwamnatin tarayya duk da dai shugaban k’asa be da lafiya, da lafiya ya ke na san da ba a kai ga haka ba, kuma ba za a rasa wanda zai duba wanga lamari ba’’
Ko da Yarima Nuhu ya dasa aya, Gimbiya Binta ji ta yi kamar ta kurma ihu, ita kuwa Gimbiya K’amariyya har ta fara kwalla ganin Yarima Nuhu na neman dawo da gaba baya. Shiru ya biyo baya. Har sun fitar da rai da k'ara jin maganar Sarki, daga bisani ya numfasa ya na mai duban Hajja Kilishi ya ce
‘’wani shawara za mu ji daga gare ki? Shin kin amince mu aurar da d’iyar mu ga abokan gaba ko kuwa mu sake neman taimako wanda hakan jinkiri ne wanda ya ke barazana ga rayukan talakawan mu?’’
Hajja Kilishi na mai nusar da kai cike da kissa ta ce
‘’lafiya toya matsafa, lafiya waliyin Allah, lafiya baya goya marayu, lafiya adali! Hukuncin ka daida ta Saka Takura, mun ji mun kuma amince’’
Sarki na mai nuna jin dad’i da batun Hajja Kilishi, haka ya bi sauran iyalan sa kowa na fad’in na shi albarkacin bakin. Duk da Sarki ya san Su Inna Salti, Yarima Inuwa da Yarima Nuhu sun fi gaskiya, sai ya bi san ran sa tare da kafa hujjar an rinjaye su, dan haka maganar ta tsaya. Da wannan su ka watse kowa da abun da ya ke sak’awa cikin ran sa. Musammam Yarima Nuhu wanda ba tun yau ya ke da k’udirin mallakar Bintu ba, ko da kuwa a matsayin sad’aka ce, tin da wata baiwa ta kawo masu tsirkun abun da ta ji Gimbiya Binta da Jakadiya su na kullawa ya kasa sukuni. Ya had’a goma na arziki ya nemi amintacciyar baiwar sa, ya ce ta kaiwa Jakadiya, wato na sharan fage kenan kafin ya je mata da buk'atar sa.
Su Gimbiya kuwa ko da su ka koma na su 6angaran mamakin yanda Yarima Inuwa, Nuhu da Inna Salti su ka nuna k’iyayyar su k’iri k’iri ta hanyar k’in amincewa da wannan lamarin, a nasu tun da su ne su ke ciki d’aya su ya fi dacewa ace sun yi na’am da lamarin, amma ga mamakin su waccan da su ke kira yan bakin gida su ne su ka fi nuna kauna gare su.
Yarema Nuhu kuwa kai tsaye 6angaran sa ya nufa rai 6ace, babban takaicin sa shi ne a rasa baiwar da za a sa cikin wannan hatsari sai Bintun shi ta arziki, Bintu da ya dad’e ya na saka buri akan ta, gaskiya dole ya san yanda zai yi wannan maganar a rusa ta. Bakin kofa ya ci karo da Baiwar da ya tura gun Jakadiya, hannun ta nik’i nik’i da kayan da ya bata ta kaiwa Jakadiya. Da ganin sa ta zube k’asa ta na mai gaishe shi. Cike da mamaki ya ce
‘’ba ki kai mata sak’on ba ne?’’
Kai duk’e Baiwa ta ce
‘’Allah shi taimaki Yarima, Uwar baka ta sake hali, da na kalle ta sai dak'uwa ta min, kasan Jakadiya gara ce, ga tsiya ga rana, tsiyar ta ya fi ranar ta yawa’’
Jin haka ya gane me ya faru, ma’ana dai Jakadiya ta yi tsiyar ta, ta kuma k'i kar6ar tsarabar sa wanda hakan ya na nufin ba zai sami kowani taimako daga gare ta ba. Cikin zafin rai Yarima ya ce ‘’kya iya tafiya da kayan’’
Sannan ya tsallake ta ya shige ciki ya na mai bugo k’ofar. Yayinda baiwa ta had’e kaya ta yi gaba, Allah ya kashe ya bata.
A wuni guda Bintu ta rame ta lalace kamar wacce ta shekara ta na ciwo. Da Baba ya dawo da daddare ya ke sheda mu su an fa aika Fabarusa, zance ya tabbata nan da wata d’aya za a amrawa Sark’i Abdulrahman aure da Binta d’iyar Sarki Sule na Sa’ayrasa. Inna na mai d’aure fuska ta ce
‘’yo to tun da ba da Bintu aka ce ba ai can da su gada, ni dai d’iya ta ba sunan ta Binta ba, Bintu an sunan ta, haka kuma ba d’iyar sarki ba ce d’iya ta ce’’
Baba na mai duban ta ya saki murmushin takaici, kana ya ce
‘’ke kuma d’iyar wacece? Ko in ce ke wacece a Masarautar nan da ga ke har d’iyar ta ki?’’
Inna ta yi shiru, ganin haka Baba ya k'ara
'’shirun da ki ka yi ya tabbatar min da kin tuna ashefa ku bayi ne, dan haka ba ku da ‘yanci, ki ma godewa Allah da ya sa amrar da ita ya ce zai yi ba bada ita zai yi sadaka ko sad’aka ba, gide ke dai kin cika butulu. Toh ki saurare ni da kyau gobenan za a zo a tafi da Bintu ga babban gida, hallo dangin ki d’aya ba a yarda kin shedawa ba, yo to ina bayi ina wasu dangi ma in ban da ba'a"
Kuka Inna ta saka ta na fad’in ‘’wannan zalinci da ke shirin aikata min da wanga yarinya Allah shi isar mana’’
Ciki Baba ya shige kafin ya lek’o da kan sa ta assabari ya furta ‘’je ki tari Magajin Gabasawa ki sheda masa, yo to ba ni na kar zoman ba, rataya aka bani’’
Ita kuwa Bintu da ke jiyo su daga d'aki zuciya ne kad'ai ba ta had'iya ba, tunani ta ke ina ma Aisar ya na kusa ya kawo ma ta d'oki yanda ya [truncated by WhatsApp]
No comments:
Post a Comment