Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 13

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣3⃣

Kai Gimbiya Binta ta girgiza, tana mai fad’in ‘’Ba ki san makircin wanga d’iya ba ne Didi, bari dai na baki labarin kad’an daga cikin halin ta.’’ Nan fa ta saka Bintu a faifai, k’arya da gaskiya haka ta had’a ta shedawa Gimbiya K’amariyya, ba don komai ba ko don ta samu mai taya ta saka baki a hana Bintu komawa makaranta.

Jiki na kyarma Bintu ta fito, Allah ya sa shigowar Inna kenan su ka had’u a rariya. Inna na ganin Bintu ta san akwai abin da ke damunta, tambayar duniyar nan Inna ta yi mata, amma ta k’i fad’a mata, sai k’arya ba ta jin dad’i ta yi mata. Ta na mai mata Allah ya sauwake ta ja ta gefe ta bata fatan dusan da ta taho mata da shi dan karin kumallo kafin ta yi na ta wajan, tabar Bintu ta na zabga loma.

              ***      ***      ***

Da yammaci, sati guda kenan da dawowa su Bintu.
Bintu kwance tare da Inna da Habibu zaune bisa tabarma a tsakar gida su na shan iska dan kuwa zafi ake na gaske ma kuwa. Inna da ya Habibu ke hirar halin da ake ciki na fari a yanki, su na muhawarar yanda za a sami mafita, in da Bintu ta yi kwance can gefe, gaba d’aya tunanin Aisar ne ya addabi rayuwar ta, dan ko yanzu ma tunanin na shi ta ke yayinda ta ke murza zobensa da ke sanye cikin yatsunta.

Baba ne ya shigo kamar an jefoshi, fad’i ya ke ‘’An dai wad’i(fad’i) ba nauyi!'’ Tashi su ka yi tsaye a tare, Inna na mai tambayar ‘’Malam lafiya kuwa?’’ 
Baba ya ce ‘’Yo to tunda aka fara fari ina mu ka ga lafiya? Yau fa kur’ia aka doka a fada, kuma sakamakon shi ne za mu nemi sulhu da kuma taimako daga wajan mak’iya abokan gaba, eh masarautar Fabarusa!’’

Babu wanda bai girgiza ba jin kalamin na Baba. Habibu ne ya ce "Gide a rasa in da za a k’ask’antar da kai sai wajan abokan gaba?’’ Baba na mai d’aga kafad’a ya ce "Ta dai faru ta k’are an yiwa mai damo d’aya sata, don kuwa magatakarda ya tura wasik’a zuwa Fabarusa, idan an amsa gobe da sassahe za a d’auki hanya  tare da Uban Gabasawa(Sarki) da kansa zuwa wajan abokan gaba nema sulhu’’

Ya na gama fad’in haka ya shige ciki Inna na mai bin bayansa. Shi kuwa Habibu silifa d’insa ya ja ya saka sannan ya fice, wato ya fita yad’a zancen kenan. Bintu kuwa komawa ta yi zaune abin ta, duk da dai itama ta yi tunanin neman taimako daga Fabarusa, jin za a je d’in da gaske sai ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba.

********
Washegari da sassafe Mai Martaba da tawagarsa su ka d’auki hanyar Faburusa. Babban gida sam babu armashi kowa cikin fargaba ya ke. Gimbiya K’amariyya tafi kowa shiga tashin hankali, gashi tun jiya ta ke kiran wayar Yerima Barde amma wayar ba ta shiga. Gani ta ke kamar alakarsu ce ta zo k’arshe. Ita kuwa Gimbiya Binta damuwarta daban ne, tun dawowar su ta ke ta sak’e-sak’e akan abinda za ta ce da Takawa(sarki) ya canza mata baiwa, dan ita aradu ba za ta koma makaranta da Bintu ba.

Ranar Allah ya taimaki Bintu ta yi aiki da hidimarta cikin Babban gida ba tare da ta sami matsala daga wajan Gimbiya Binta ba. Da yammacin ranar ta raka Yerima Nadir Lambu, nan su ka ta tad’in su kamar ta sami babban mutum. Labarin makarantar su ya ce ta bashi, nan fa Bintu tai ta bashi, har da labarin Aisar. Bata san ta na kewan sa sosai ba sai da take maganar sa a zahiri ba a zuci ba, wata k’ila ma ya manta da wata Bintu, abun da take fad’awa kan ta kenan. Shi kuwa Yerima Nadir kallon ta kawai ya ke ba tare da ya fahimci in da ta dosa ba, ballantana ya gane halin da ta ke ciki.

******
Bayan magrib ta koma gida, shiru har lokacin sarki be dawo ba. Bayan sun ci abinci suna kwance a falo ita da Inna, sun ci sa’a akwai wutar lantakarki, fanka ke kad’awa ta na mai fitar da k’ara alamar ta fara gazawa.Akwatin radiyon Inna su ke sauraro in da ake labaran duniya.

Jin mai karanto labarai ya ce ‘’Jikin shugaban k’asa Gaddafi Nur ya tashi, za'a fitar da shi zuwa k’asar waje domin ba shi taimako’’ Ya sa Bintu tashi zaune da sauri ta na mai tambayar ‘’Inna daman shugaban K’asa be da lafiya?’’
‘’Eh Allah sarki ai be da lafiya, yo to da k’alau ya ke ai da tuni ya magance wanga fari da mu ke ciki, dan ba kya sauraran labarai ne shi ya sa ba ki ji ba’’ Inna ta amsa mata.

Bintu na mai dafe kai ta ce  "innalillahi wa innailaihirrajiun, Allah sarki Monsieur Aisar, suna cikin tashin hankali’’ 
Inna ta dubeta, ‘’Waye shi kuma Bintu?’’

Nan Bintu ta kwashe labarin Aisar ta fad’awa Innar ta. Fuskarta na nuna rashin jin dad’in labarin, Inna ta had’e fuska. ‘’Ai da walakin goro a miya, shi ya sa mana na ga kin dawo wata wuri wuri da ke, d’an shugaban k’asa Bintu?’’

Bintu na mai tura baki ta ce ‘’Yo to Inna minene ciki? Ba fa wani abu ba ne taimako gareshi kawai........’’

‘’Wani taimako? Chiim zanne la nya bangin! (rufa min baki ko na buge ki)’’ Inna ta katse ta, ta k’ara da ‘’Taimako ne har da siya miki turare ma su tsada haka Bintu? Binta sudan? Kafin kafin? Danduala? Turaren da sai Saraki kad’ai ke sawa? Kuma ki na dai ganin yanda Gimbiya ta yi mi ki saboda shi? ngoy awo gulgin d3! (ai ga abinda nake fada), yanzu ba za ta bari ko koma maranta (makaranta) da ke ba!"

Komawa Bintu ta yi ta kwanta, ta na mai lumshe idanu. Kana ta ce ‘’Allah ya ba shi lafiya’’
"Wa fa?’’ Inna ta tambaya. Bintu na mai bud’e idanunta ta ce ‘’Mahaifin Monsieur’’

Tsaki Inna ta ja, kafin ta amsa da ‘’Yo to amin, amma kanki ya kamata ki yiwa addu’a fero (yarinya) a halin da ki ke ciki, ki ma cire wannan mutumin daga ranki, can ga su gada zomo ya ji kid’an farau ta’’

‘’Inna Allah na sa a raina." Cewar Bintu. Kamar daga sama su ka jiyo Habibu daga tsakar gida ya ce 
"Kin gama komai kauna(kanwa) ta?''

Ashe duk maganar da su ke ya na can zaune tsakar gida ya na jiyo su ba su sani ba. Murmushi Bintu ta saka, ita kuwa Inna cewa ta yi ‘’Ala sakaa (Allah ya kare)"

Washegari da asubar fari Bintu na tashi daga barci Baba ne ya fad’o ranta, don kuwa har su ka yi bacci be dawo ba. A tsakar gida ta tadda Inna ta na alwala, ka na ta ce ‘’Inna barka da asuba’’

‘’Barka dai Bintu, kin tashi k’alau?’’ Inna ta amsa mata.

"Lafiya lumi, shin Baba kuwa an dawo?’’ Bintu ta sake tambayarta, inda Inna ta amsa mata da sun dawo lafiya lumi kan ta shige d’akin ta bayan ta gama alwala, ita ma Bintun buta ta d’auka ta shige band’aki.

Babban gida kuwa a yau rashin armashin sa ya fi na kullum, babban abin da ya bawa Bintu tsoro da ta shiga gidan da rana shi ne ganin Gimbiya K’amariyya cikin tashin hankali. An hana kowa shiga d’akin ta, Bintu ma dan ita ta takawa Gimbiya Binta baya zuwa wajan Gimbiya K’amariyya ya sa ta d’au haske, duk da dai ita ma iyakacin ta bakin kofa ne. Duk yanda Bintu za ta yi domin binciko abinda ke faruwa ta yi, amma abun ya ci tara, babu wanda ya iya bud’ar baki ya ce komai, dan kuwa kowa tsoran ace shi ya fad’a ya ke.

Haka dai Bintu ta koma gida jiki a sanyaye. Ta tadda Inna zaune tsakar gida, kusa da ita ta zauna a gajiye ta na mai fad’in ‘’Inna barka da yammaci, ashe kin taho’’

Bud’ar bakin Inna sai cewa ta yi "Barka dai d’iyarnan, ba dole na taho gida ba, Babban gida yau ba dad’i, fada babu kwanciyar hankali.......’’

‘’Yo to ina fada ina kwanciyar hankali!’’ Baba ne ya katseta, wanda ya fito daga b’and’aki hannun sa ruk'e da buta, sanye cikin shigar bayin Sa’ayrasa. Kujerar tsakar gida ya ja ya zauna kafin ya k’ara da "ai da ni mai fad’a aji ne a wanga masarauta, da aradu ba a je Fabarusa ba, yo to ina bawa d’an bayi, ina ni ina bada shawara?’’

Cikin k’aguwa ta ji abinda ke faruwa Inna ta ce ‘’Shin ya ta kasance ne Malam? K’ak’a an ka yi ne?’’

Murmushin takaici Baba ya saki kan ya fara ba su labarin yanda ta kasance a masarautar Fabarusa. Wato ba k’aramin fad'uwar gaba Bintu  ta ji ba jin Baba ya ce ‘’Da bud'ar bakin Sarki Abdulrahman sai cewa yayi za mu kawar da gaba, za kuma mu ba ku bashin damun hatsai da dabino yanda aka buk’ata daga gare mu dan ceto rayuwar alumma, amma fa da sharad’i.."

"Sharad’in me?’’ Inna da Bintu su ka tambaya a tare.
Baba na mai girgiza kai ya ce ‘’Ku dai tsaya ku ji furucin tsohon banza, sharad’in shi ne, Uban Gabasawa(sarki) ya amra(d’aura) masa d’aya daga cikin d’iyoyinsa mata....’’

Gaban Bintu ne ya yanke ya fad’i. ‘’A amra masa d’aya daga cikin d’iyoyin Uban Gabasa?’’ Inna ta maimaita.

Kai baba ya gyad’a mata, ya k’ara da ‘’Acewarsa, ba zai ba da zallar dukiya har haka ga tsohon abokin gaba ba, ba tare da ya sami madogara ba, kenan amren d’aya daga cikin Gimbiyoyin Sa’ayrasa shi zai sa dole Uban Gabasawa ba zai yi wasa da dukiyar ta su ba, a fad’ar sarkin Fabarusa fa’’

Hannu bisa ha6a Inna ta ce ‘’Hallo ta nan ya hito?  Ba ya taimako sabida da Allah sai an bashi d’iya? Na ji ance sarkin ga ya bawa shekara tamanin baya, tsufa dai ta yi gardama’’

Gaba d’aya hankalin Bintu a tashe ya ke, musamman da tasan alakar Gimbiya K’amriyya da d’an sarkin Fabarusa, wato Yerima Barde, kuma ta san babu shakka Gimbiya K'amariyya za a za6a ba dai Gimbiya Binta ba.

‘’Shin yanzu ina aka kwan?’’ Muryar Inna ta dawo da Bintu daga kogin tunanin da ta fad’a. Baba ya amsa mata da ‘’Tununna dai, an dai ce za a yi shawara, amma gaskiyar lamarin da kyar za mu kiya , jama’a ana cikin wani hali’’

Ya karkata buta ya fara alwala. Jin haka Bintu ta d’aura kai bisa gwiwa cike da tausayin Gimbiya K’amariyya, duk da dai ba kukan ta ba, mutuwar uwar kishiya.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment