®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
ZUWA GA MASOYA "BINTU 'DIYAR BAYI" INA MAI NEMAN AFUWAN KU NA JINKIRIN SHAFI NA GABA DA ZA A SAMU, HAR ZUWA JUMA'A SABODA WANI UZIRI BABBA DA YA SHAFI WANI KARATUN DA NA KE. MADALLAH DA KU. SIDIYA CE KE MU KU FATAN ALKHAIRI🤝
©Khadija Sidi.....✍🏼
0⃣9⃣
Ranar da su ka gama jarabawa da yammaci, ana gobe za su tafi gida, Gimbiya Binta ta ce da Bintu ta raka ta wajan Aisar, dan ta ga idan su na tare ne kad’ai ya ke d’an sakar mata fuska. Sanye ta ke cikin doguwar riga ta alfarma kalar ja, dake Gimbiyar fara ce ba karamin kar6ar ta kalar ta yi ba, ita kan ta Bintu sai da ta yaba da kyawun Gimbiya cikin ran ta. Bintu kuwa kayan su na bayi ne jikin ta, kan ta tufke da kallabi, jin Gimbiya ta ce za su gun Aisar ya ta ware kallabin dan ya dan rufe mata jiki, amma duk da haka iya ka wuyar ta ya ya tsaya, gashi ita ba mayafi gare ta ba.
Gimbiya tafe Bintu na biye da ita ba su zame koina ba sai ofishin malamai. Malaman duka ba sa nan, daga Aisar sai wani malami da su ke kira Malam Sunusi, shi ma d’in su na shiga ya na fita. Malam Aisar da ke zaune bisa kujera ga teburi gaban sa ya na rubuce rubuce, sanye cikin wannan shigar ta sa dai, ko da ya d’aga ido ya ga su Bintu sai ya dakatar da rubutun da ya ke ya na mai aikawa Bintu murmushi. Ita kuwa ta kau da kai karda Gimbiya ta gani ta shiga uku.
‘’assalama’alaikum warahamatullah’’ sallamar Gimbiya kenan gare shi, ya amsa da ‘’wa’alaikum salam’’ Bintu kamar munafuka sai 6uya ta ke bayan Gimbiya ma sallamar ta masa a tak’aice, ya amsa ya na mai k’arawa da ‘’Bintun Sa’ayrasa, ya ki ke 6uya ne, fito sarari mana’’ Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Jiki a sanyaye, kan ta sunkuye Bintu ta fito sarari. A sannan Malam Aisar ya lura da shigar da ta yi, sai dai duk sanda ya ke ganin ta da irin shigar be tab’a ganin ta sa riga k’arama wacce ta kama ta kamar ta yau ba, gashi zani ne d’aure jikin ta kuma ya fi fitar da surar mace, dad’in dad’awa kuma gashi Bintu ba kad’an ba duk da dai yarinya ce.
Nan da nan su ka nemi fara’ar da ke fuskar Aisar su ka rasa, har sai da Bintu ta tsargu ta d’an ja da baya, Aisar na mai d’auke kai da barin kallan ta ya ce ‘’dole ki 6uya mana, tin da kin hito(fito) yawo ba mayafi da irin wanga shigar!’’ Bintu ta sunkuyar da kai ta na mai tunanin ko dai ya manta da tsayuwar Gimbiya a wajan ne ko me? Allah ya sa kar ya ja mata jaraba. Gimbiya na kallan ikon Allah cikin ran ta fad’i ta ke ‘’aikin banza kyaramuwa tsaftar yaye!’’, Aisar be gushe ba ya k’ara da ‘’kul kar ki k’ara hita(fita) haka ko da a masarautar ku ne!’’ Bintu ta amsa da ‘’toh’’
Gimbiya ya ce ta ce "Monsieur Ina wuni’’ ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’lafiya’’ ganin haka ta ce da Bintu ‘’Gide hita (fita) waje ki yi jira na....’’ be jira amsar Bintu ba yayi saurin katse Gimbiya ta hanyar fad’in ‘’idan kin hita ki wuce d’aki kar ki tsaya waje da wanga shiga ta ki, idan kin gama kya same ta ca’’
Cikin sauri Bintu ta bar wajan ta na mai hamdalar ceton ta da Allah yayi. Bayan fitar Bintu maimakon ya tsaya ya saurari Gimbiya sai ya cigaba da rubuce rubucen sa, kamar be ma san ta na wajan ba. Kamar za ta juya sai dai ta d’aure ta ce ‘’Malam gobe za mu koma gida’’ ba tare da ya d’ago ya kalle ta ba amsa mata ‘’sai aka yi yaya?’’ Gimbiya ta d’an cije le6e kafin ta ce ‘’dama zuwa na yi na maka sallama, na kuma gayyace ka zuwa masarautar mu idan da hali’
‘’na gode da sallamar, sai dai masarautar ta ku ce ban da lokaci’’ amsar da ya bata kenan. Kana Gimbiya ta dad’a gwada sa’ar ta ta hanyar fad’in ‘’dama wai ina nufin in ka sami lokaci.....’’
‘’ban da wannan lokacin’’ ya katseta ya na mai kafe ta ido. Ganin haka Gimbiya ta cije le6e ta na mai hamdalar korar Bintu da ta yi da yanzu gaban ta Aisar zai mata wannan cin fuskar. Fuuu ta juya ta fice ba tare da ta sake tankawa ba. Sai da ya ga ta fita ya aja rubutun ya na mai jan tsaki, takaicin sa na ganin ta na masa yawo da Bintu haka babu mayafi, ko wani kare da biri ya kalla! ‘’ba dan karancin shekarun wangad’iya ba, wallahi ba d’iyar bayi, ko d’iyar bola ce sai na aure ta! Amma ba komai lokaci ne ni Aisar mai hakurin jira ne’’ furicin Aisar kenan azahiri ya na mai jadda batun kawo kanwar sa Maryam makarantar ko ba komai ta ke saka Bintu a hanya. Tsaki ya sake ja ya na mai tura rubutun da ya ke gefe dan kuwa lamari in dai akan Bintu ne ya na jagula masa lissafi.
Komawar Gimbiya Binta d’aki kan Bintu ta sauke takaicin ta, laifukan na Bintu da yawa ciki har da ta na sane ta bita gun Aisar babu mayafi tsabagen ta na so ta yi masa tallar jikin ta, an fad’a mata shi d’an iska ne? Ta ji dad’in yanda ya yiwa Bintu kurar kare, da kuma ta ce ta jira ta waje shi ne ta bi umarnin uban ta ta koma d’aki.
Aiki tuk’uru ta saka ta wanda tun da Bintu ta zo duniya ba ta tab’a yin irin shi ba, hatta kayan ta da ke wanke a goge sai da ta sa Bintu dad’a wankewa da guga, dare yayi kuma ta tura ta lungu cikin sauro, nan Bintu ta kwana ta na mai adduar Allah ya sa iya haka hukuncin Gimbiya ya tsaya, ba za ta aiwatar da alkawarin sakawa a cire ta daga makarantar ba.
Washagari da ruwan sama aka tashi, motocin Sa’ayrasa na d’aya daga cikin motocin da su fara isowa. Sai da ruwa ya d’an tsaya sannan bayi da fadawa su ka taimakawa Bintu wajan kwasar kayan Gimbiya, har ya rage akwaitin karfen Bintu kad’ai ya rage a d’akin. Ita kuwa Gimbiya yar sarki mai dole kuma ta na jira a take mata baya zuwa mota, haka Bintu ta na ji ta na gani ta bar akwatin na ta su ka takawa Gimbiya.
Ta na shiga mota ta juya da niyar komawa ta d’auk akwaitin na ta, Gimbiya ta tsiyar da ita ta hanyar daka mata tsawa ‘’gide ina kuma za ki?’’ dan a zatan ta wajan Aisar Bintu za ta. Ko da Bintu ta fad’a mata cewar akwatin ta za ta d’auko, minti gama kacal Gimbiya ta bata idan ba haka ba za ta taka zuwa Sa’ayrasa da k’afar ta. Hanyar da za ta kai ta ga d’akin na su Bintu ta kalla, ko zuwa bakin kofar b’angarn sai ya fi minti goma bare kuma ga hawa bene ga nauyin kaya. ‘’ki nan tsaye ne? idan kin fasa ma iya tafiya’’ furucin Gimbiya cike da tak’ama.
Cikin hanzari Bintu ta ce ‘ tuba na ke ran Gimbiya shi dad’e’’ kafin ta tafi da sauri, sai da ta tabbata ta wuce ganin su Gimbiya sannan ta arta a na kare. Ta na ji wasu na ‘’fad’in ku kauce ta fara gudun na ta na masifa’’ har dariya ake mata ita kuwa ba ta san suna yi ba. Haurawa ta yi ta d’auki akwaitin ta bisa kan ta. Ta fito daga sashin kwanan na su kenan kamar daga sama ta ji an d’auke ma ta akwatin daga kayin ta.
A tsorace ta juya sai ga Aisar sanye dai da shigar nan nasa, amma yau fara ya sa, idanun sa rufe da gilashi, hannun sa ruk’e da wata leda mai d’an girma cikin nuna damuwa ya ce ‘’wanga ya yiwa d’iya mace nauyi’’ cikin kokawa Bintu ta ce ‘’dan Allah ka yi min rai ka bani na tafi, aradun Allah minti goma kacal Gimbiya ta ba ni’’ maimakon ya bata, sai ma dad’a ruk’e akwaitin yayi kafin ya ce ‘’idan kuma ki ka k’ara fa? K’ak’a za ta yi?’
Idanun Bintu na mai kawo ruwa ta ce ‘’aradu tahiyar su za su yi su bar ni a nanniya (wallahi tafiya za su yi su bar ni a nan)’’ Aisar na mai murmushi ya ce ‘’idan su ka tahi shikenan sai na tahi da ke gidan mu hankali kwance’’ ganin za ta sa masa kuka ya ce ‘’shhh..wasa na ke mi ki’’ akwatin ya aje k’asa sannan ya ciro zoben hannun sa ya mik’a mata ya na mai fad’in ‘’kan ki tafi ga ajiya ta Bintu, ina so ki aje min duk sanda mu ka sake had’uwa zan kar6a’’
Cikin saurin ya bar ta tafi, ba tare da ta kawo komai cikin ran ta ba ta sa hannu ta karb’a ta na mai k’ok’arin cusa zuben cikin zanin ta,ya ce ‘’ah ah a yatsar ki na ke so ki saka, nan ya na iya fad’uwa’’ ba musu ta fara k’ok’arin zira zuben, duk da ya so ya mata yawa ta samu ya shiga yatsar tsakiyar hannun ta na dama. Ta yunk’ura za ta d’au akwatin kenan Aisar ya riga ta cikin zafin nama, ya wuce gaba abun sa, da sauri ta bi bayan sa ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ka bani akwatin dan Allah’’ shiru ya mata, dake Aisar mutum ne mai kuzari, nan da nan su ka isa ga motocin Sa’ayrasa. Bintu sai karanto adduoin da ta koyo makarantar allo ta ke dan neman tsari daga masifar Gimbiya, dan ba ita kad’ai ba ma kallo da zund’e da ta sha wajan sauran d’alibai ma sai Allah, musammam yan aji shida da dama sun gama tsanar ta, yau ga Aisar Gaddafi Nur yayi dakon akwaitin d’yar bayi. Shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa wai an mintsli kakkausa.
Suna isa ya sakar mata murmushin da ita kan ta Bintu ba ta san na menene ba, ita dai ta na ganin sabon salo kiran sallah da husir, kana ya ce ‘’wata motar Gimbiya za ta shiga’’ Bintu ta amsa da ‘’ai Gimbiya ta na cikin waccar motar’’ ta masa nuni ga motar da Gimbiya ke ce. Aisar ya kai kallan sa ga motar, ko da yayi ido hud’u da Gimbiya, duk da 6acin ran da ta shiga ganin Aisar d’auke da akwatin Bintu, sai da ta tsinci kan ta ta na mai sakarwa Aisar sakon murmushi. Yayi saurin maido da kallan sa ga Bintu ya na mai fad’in ‘’ba Gimbiyar ki na ke magana akai ba, Gimbiyar Aisar na ke nufi, wata motar za ki shiga?’’
Cike da mamaki Bintu ta amsa masa da ‘’iyye? Na’am? Ni Bintu?’’ kai ya girgiza mata, jiki a sanyaye ta masa nuni dai ga motar da Gimbiya ke ciki, kana ya ce da direba(driver) ya ce ‘’Aboki na bud’e min bayan motar na aje kayan ko’’ jin haka Bintu ta yi saurin fad’in ‘’waccar motar ta baya za a aje kayan’’
Aisar ya ce ‘’toh gidan gaba ko baya ina ki ke zama?’’ ta na hango Gimbiya ta na girgiza kai har da kwafa, ta na mai duban Bintu ta ce ‘’a juri kai zuga gabas, wataran ta zo da ruwa’’ maimakon Bintu ta bashi amsar sai kawai ta kai hannun ta ga murfin motar da niyar bud’ewa, yayi saurin tsaiyar da ita, ya b’ud’e da kan sa, Bintu ta shiga, ita kan ta ta san ta wuce gona da iri. Ledar ya aje bisa cinyar ta, ba tare da ya rufe motar ba ya ce da direban ya fito kai akwaitin Bintu cikin motar da ake ajewa. Direban ya so yi masa musu, amma ko da suka had’a ido da Aisar ya ga waye gaban shi tini ya fito yayi yanda aka saka shi.
Aisar ya ce ‘’ki gaida gida ki gaida yan gidan Bintu, sai kin ji daga gare ni’’ kai kawai Bintu ta iya gyad’a masa, yayin da ya mayar da murfin mota ya rufe. Direba ya dawo ya tada mota har su ka fita be dena kallan motar da Bintu ke ciki ba, ji ya ke kamar ya bi bayan su.
Da fitar su, ta baya ta ji Gimbiya ta kifa mata mari, ta na mai fad’in ‘’shegiyar kaya!dama wajan shi ki ke san zuwa sai da jiki na ya ban!’’ kuka Bintu ta saka, fad’i ta ke ‘’ki yi min rai Gimbiya, tuba na ke, ba wajen shi na je ba a hanya mu ka had’u, idan karya na kai arratta kashe ni’’
Tas! Ta dad’a kwashe ta da mari ‘’shi ne har da d’aukar d’an akurkin ki ko? Kai direba tsayar motan nan! Direba ya ja ya tsaya, sauran motocin ma tuni suka faka gefe guda ganin na Gimbiya ma ya faka. Ledar hannu Bintu ta fizge ta na bud’e, mayafai ne manya masu kyan gaske har guda goma. Tsaki Gimbiya Binta ta ja yayinda ta sauke gilashin motar ta na ji ta na gani ta wulga mayafan waje, kan idanun Bintu haka su ka sauka cikin ruwan sama da ya kwanta a gefen titi, sannan ta ce ‘’Direba mayar da d’iyar bayin nan cikin bayi sa’annin iyayen ta’’ Direba ya dubi Bintu da ke faman kuka ya ce ‘’yo to ai sai ki hito ko?’’
Bintu na k’ok’arin fitowa ta ji Gimbiya ta ce ‘’ke da wanga ecole har abada! aradu ma kuwa!’’ da ma dai ko ba ta fad’a ba Bintu ta san ta faru ta k’are ramamme ya zagi maye. Haka ta na mai fad’in ‘’ina tuba’’ amma Gimbiya ta mata kunne uwar shegu, yayinda direba ya raka Bintu izuwa motar bayi a wulak’ance. Nan su ka d’auki hanyar masarauta Bintu na mai bakin ciki da fad’uwar gaba.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪🐫
No comments:
Post a Comment