Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 5

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

0⃣5⃣

Bayan an tashi daga makaranta, ko kallan ta Gimbiya Binta ba ta yi ba ta ta wuce gaba ita da Ruqayya, Bintu na rawar jiki rik’e da jakar Gimbiya ta bi bayan su. Ba su zame koina ba sai d’akin su in da su ka tadda Zahira na jiran su dan gasawa Bintu gurasa danya a hannu.

Zagaye Bintu su ka yi tsakiyar d’aki,   sai ta fad’a musu yanda aka yi Aisar ya san ta yasan sunanta da har ya ci mutuncin Zahira saboda ita. Bintu na raba idanu ta ce ‘’Dan Allah Gimbiya ki min afuwa, aradu shi da kan sa ya tambayi sunana........’’

Ji ka kake tas! Gimbiya ta kwashe ta da marin da sai da Bintu ta ga wuta a idonta, a gigice ta sa hannu bisa kuncin ta na mai fashewa da kuka. Gimbiya ba ta gushe ba ta ce " Yar iska! A shekarun ki har kin iya karuwanci?!!!’’ Ta sa k'afa ta shure Bintu. "Yo dama ana raba bayi da karuwanci ne Gimbiya?’’ Rukayya ce ta ara ta yafa. Zahira ta k’ara da,   "Wallahi tunda ki ka sa mutum kamar Aisar ya ci mutuncina sai kin yabawa aya zak’inta."

Ita dai Bintu ta kasa magana, kanta durk’ushe, sautin kuka kad’ai ke iya fita daga bakinta. Gimbiya ta ce ko dai ta fad’a mu su yanda aka yi ya san ta har ya tambayi sunan ta ko ta kira waya fada a zo a mayar da ita Sa’ayrasa. Jin haka haka nan da nan Bintu ta shaida musu komai. Duka da mari babu wanda ba ta sha ba. A fad’ar Gimbiya don tasan tana da k’udirin auren Aisar ya sa ta ke masa shisshigi dan ta 6ata ta wajan shi, toh wallahi ta yi kad’an, duk randa ta yarda wani abu ya k’ara shiga tsakanin su ta tabbatar ranar zaman ta a wannan makarantar ya k’are. "Godiya nake Gimbiya’’ a
Abinda ke fita daga bakin Bintu kenan har su ka k’araci masifar su, su ka tafi d’akin Zahira.

Bintu na zaune inda suka bar ta, ta had’e kai da gwiwa in ban da ajiyar zuciya babu abun da ta ke, sai ga Iya Dije ta shigo da sallamar ta. Ganinta Bintu ta yi saurin gyara zama ta na mai k’ok’arin goge hawayen da ke fuskar ta gudan kar Iye Dije ta gani. Cike da mamaki Iye Dije ta ce "Bintu lafiya? Me ya sa ki kuka haka? Ya na ga idonki d’aya ya kumbura?’’  "Ba na jin dad’i ne Iya Dije, ciwon kai da ido na ke’’ Bintu ta yiwa Iya Dije k’arya gudun abun da zai je ya dawo. Cikin nuna tausayawa Iya Dije ta ce " Ayya Allah ya sauwake, na ce dai kin je kilinik (clinique, karamin asibitin makarantar) an duba ki ko?’’ Kai Bintu ta girgiza alamar ah ah, sannan ta k’ara da ‘’Ba sai na je ba, ina da magani, idan na sha shikenan."

Kallan ta Iya Dije ta ke kamar mai nazarin wani abu, kafin daga bisani ta ce ‘’Toh Allah ya sauke.’’ Ta ja wata yar kujera ta zauna sai a sannan Bintu ta lura da ledar hannunta, a gaban Bintu ta aje ledar kan ta tambaya "Shin al’adar ta ki ta d’auke ne?’’ Cikin nuna jin kunya Bintu ta girgiza kai alamar ah ah. Iya Dije ta ce "Ai bakomai, dama daga kwana d’aya har zuwa kwanaki goma sha biyar yakan iya kai wa. Dama batun turaren ne, Malam Aisar ya ba ni kud’i, sanin ba a bari dalibai su fita daga makaranta yasa na yi karambani na siyo miki’’ Ta sa hannu cikin ledar sai gashi ta fito da kwalaban turare har guda uku, ta aje gaban Bintu ta na fad’in ‘’Kinga wannan Danduwala ne, ga kuma Kafin-kafin, ga Binta Sudan duka na ki ne." Ta k’arasa maganar tana mai washe hak'ora don tasan ba k'aramin gwanin ta ta yiwa Bintu ba, duk da dai rabin kud’in da Aisar ya bata a aljihun ta ya k'are.

Bud’ar bakin Bintu sai cewa ta yi "Iye Dije na gode amma dan Allah ki mayar masa, aradu ba zan iya karb'a ba, ba na so’’ ‘’La'ilaha illallahu!" Fad’in Iye Dije ta na mai tafa hannu "Ku ga yarinya za ta watsan k'asa a ido! Ba kya so a na wani dalili? Iyye?!!!’’ Ta yi tambayar ta na mai fidda idanu ganin Bintu na shirin kwance mata zani a kasuwa, don kuwa karya da gaskiya ta had’a ta fad’awa Aisar kan buk’atun Bintu, haka ya bata kud’i CFA na gugan CFA har (10000 CFA), fiye da rabin kud’in ta kashe. Bintu ta rasa amsar da za ta bata, ta tsinci kanta tana mai fad’in ‘’Na ga ba na buk’ata ne Iya Dije.’’

Ba ta ankara ba sai ganin Iya Dije ta yi ta d’aga hannunta tana mai k’ok’arin cusa hancin ta k’ark’ashin hammatar Bintu. Da sauri Bintu ta ja da baya ta na k’ok’arin kwatar kanta, fad’i ta ke ‘’Iye Dije ya haka?” Iya Dije kuwa duk da babu abinda ta shak’a na wari daga jikin Bintu don kuwa Bintu irin mutanen nan ne wanda sam ba su da warin jiki, sai ga ta ta yi baya da sauri ta na mai toshe hanci ‘’Kin ji yanda ki ke bugawa ki na hamami kuwa? Har ki ce ba kya buk’ata? Shi kan shi Malam Aisar d’in wannan hamamin na ki ya ji shi ya sa ya ce na tambaya ko ki na da buk’atar turaren.’’

Jin haka kunya ta rufe Bintu, kamar k’asa ta bud’e ta shige. Ta na mai yin k’asa da ido ta ce ‘’Ai idan Gimbiya ta gani ko ta ji ina kamshin turare ma su k’amshi haka Iya Dije kashi na ya bushe’’ Sai a sannan hankalin Iya Dije ya fara kwanciya, ta ce ‘’Yo ba sai ki 6oye yanda ba za ta gani ba, sai ki na sawa kad’an haka, ni dai ba zan mayar da wanga turare ba’’ Ajiyar zuci Bintu ta saki ganin babu yanda za ta yi dole ta hakura ta kar6a ta na mai godiya. Ita kuwa Iya Dije ko da ta samu ta cusawa Bintu turare sai ta sami kwanciyar hankali, dan da ba ta san yanda za ta yi ta biya da kud’in Aisar da ta ci ba.

Aisar kuwa sai da ya tabbatar ya kaiwa Malam Hamisu k’orafinsa kan rashin tarbiyar d’alibai da kuma zaman wata d’aliba a waje lokacin cin abinci ba tare da ya ambaci sunan Bintu ba. Malam Hamisu ya nuna rashin saninshi kan maganar yanayin cin abincin d’aliban, kuma ya yi masa alk’awarin d’aukar mataki. Saidai batun rashin tarbiyar d’aliban ya ce su ma hakuri su ke da su kasancewar kowani tsuntsu kukan gidansu ya ke, amma In sha Allahu za su k’ara tsauri kan lamarin.

Washagari da safe wajan taron d’alibai (Assembly), Mallam Hamisu ya ja kunnan d’alibai akan bin duka, musammam wanda ba sa halartar wajan cin abinci idan lokacin yayi, ya kuma tsawatar da hukunci mai tsanani muddin aka ga d’aya daga cikin d’aliban na aikata hakan. Da wannan Bintu ta sami saukin samin cin abinci tare da yan uwan ta d’alibai duk da kuwa sai da ta sha tuhuma gun Gimbiya akan zargin ko ita ta kai k’arar ta.

Kwanci tashi haka rayuwa ta kasancewa Bintu cikin makaranta. Gaba d’aya gudun Aisar ta ke, tun shi ma bai gane ba har ya zo ya gane ya daina nemanta. Ita kuwa Zahira hakuri ta je ta bashi tare da sa bakin Malam Hamisu ya hak’ura ya bari ta koma ajin na shi. Gimbiya Binta babu irin cusa kai da ba ta yiwa Aisar, amma sam ba ta gabansa bare ya san ta na yi, manyanta ma yan aji biyar da shida fama su ke bare ita karan kad’a miya acikin jerin ‘yan mata.

Da yammacin ranar lahadi, ana saura sati biyu su Bintu su fara jarabawa. Yanda garin yayi wasai, gajimare yayi lub-lub, ciyawa da bishin da ke cikin lambun sun yi kore shar, ga wani ni’imatacciyar iskar da ked’awa wanda sanya rassa da ganyayyakin bishiyun da ke cikin lambun rausayawa suna mai fuzar da feshin ruwa sanadiyar ruwan sama da ya sauka ya kuma tsaya mintina talatin da su  ka wuce ne ya sanya Aisar da ke kwance kan kujerar hutun da ke k'ark’ashin d’aya daga cikin rumfunan lambun, in banda kukan tsuntsaye da kuma k’arar saukar sauran ruwan sama da yayi ragowa bisa kwanan rumfar lambun babu abun da ke tashi.

Sanye ya ke cikin bakar riga mai k’aramin hannu, da wando wanda ya ke shi ba gajere ba bai kuma kai masa har k’asa ba. Idanunsa lumshe tamkar mai bacci, ko da yake da zai sami bacci da hakan zai fi so dan kuwa tunanin da ya dad’e ya na damun sa yanzun ma shi ya sa shi gaba. Ba kuma tunanin kowa bane, face na Bintu, musammam yanzu da aikin binciken su ya k’are, Bintun ce ta zaunar da shi a makarantar da tuni ma ya dakatar da koyarwa, dan kuwa dai hakin su ya riga ya cimma ruwa a game da aikin su. Abin takaicin shi ne tsakanin sa da Bintu sai dai a aji, duk yanda zai yi ya ganta bayan aji ya gwada amma abu ya faskara, don kuwa dai Bintu gudun sa ta ke k’iri k’iri. Shi kan shi bai san meyasa ya kasa cire yarinyar daga ransa ba, amma dai yau idan har bai sa ta a idanunsa ba zai iya shiga damuwa. Gashi kuma yau lahadi  ko makarantar bai shiga ba bare ya ganta a aji. Nan fa wata dabara ta fad’o masa, ya tsinci kansa ya na mai murmusawa.

Ajiyar zuci ya saki yayin da ya bud’e idanu a hankali jin d’igar ruwa bisa fuskarsa sanadiyar iska da ta kad’o wani reshe zuwa cikin rumfar. Tashi ya yi zaune ya na mai duba lokaci, k’arfe biyar daidai, ya aje hannu inda ya tashi cikin azama ya na mai k’ok’arin zura takalmi cikin k’afafunsa. Kai tsaye ya  fice daga cikin lambun, ya bi ta farfajiyar gidan ya shige falonsa wanda zai sada sa da d’akin baccinsa. Cikin k’ank’anin lokaci ya sauya kaya izuwa farar jamfa da hula tare da farin takalmi. Ya gama fesa turaren sa mai kamshin gaske ya wuce cikin motarsa. Hankali kwance ya fito daga gidansa, sai gashi kan titin francophonie, kai tsaye ya nufi makarantar Soverign.

No comments:

Post a Comment