INA ZE KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul
3.
Dukkansu huɗun na zaune ne a farfajiyar ofishin ba da shawarwari da tallafi don inganta rayuwa wato ofishin SCCvolunteers reshen su na jihar Kano. Karfe goma na safe ya kamata su ga wacce zata basu shawaran amma tun karfe bakwai suka hallara. Kukan da Afreen Aliyu ke yi ne ya ja hankalinsu zuwa gare ta.
"kinga ko wanenmu a nan cike yake da matsalar sa, ban ga dalilin da za ki zo ki kara mana damuwa ba, mtswwwe" faɗin mutumin da tun zuwan su wajen ya ke zaune a gefe yayi tagumi da duka hannayensa biyu.
"don ba ka san damuwar da ke tattare da ni ba ko" Ta faɗi a fusace kamar za ta nushe shi a baki.
"se ki faɗa mana Kinga mun samu abin da zai cinye lokacin mu, ko ba haka ba kawas" Ya karasa zancen sa zuwa ga budurwar da ke balla musu harara tun da suka fara magana. Kamar tana jira sai ta fara basu labari kafin Ustaz ya katse ta.
"Kun wani aje mu a cliff hanger, ni ban ga abin zuwa neman mafita ba, su de wa'innan counseling su ke yi sai in ya kama a taya ka shigar da kara haɗe da tsaya maka ne su ke yi. Ku kuwa ai duk soyewa kuka yi, don Allah ku bamu waje" faɗin yar kwayar cikin murya da ke tabbatar da maye ya bi jinin ta.
"Ni bari ku ji abin da nayi gamo da shi, amma sai mun bar wajen nan zuwa can firamaren da ke tsallake, sai ku ji labarin kowa Allah barshi gobe ma dawo" Ya ce yana mai Mike wa, nan ba musu suka bishi zuwa wani aji da babu kowa amma sun same shi buɗe.
***
"Ni sunana Sufyan Zakariyya, shekaru na talatin da uku, na taso cikin gata daga iyaye na har yayyi na mata kasancewa na auta. A shekaran 2009 na yi rajista da 2go, na kan shiga nayi chatting da wa'inda na sa a shafi na, daga baya sai na fara shiga zauren tattaunawa na addini mu yi ta gardama.
A nan na haɗu da wani wanda ba ya wasa wajen kare musulunci da sukar wanda ba musulmi ba wai shi Abu Zaid. Tun ina sha'awar sa daga nesa har ya kai ga na masa magana kuma na faɗa masa ina sha'awar kasancewa abokinsa saboda ilimin sa. Bai gardama ba, nan na faɗa masa sunana da garinmu shi kuma ya ce yana Damaturu ne amma asalin sa ɗan Jigawa ne.
Sannu a hankali ya ja ra'ayi na na buɗe shafi a Facebook nan ya sa ni a zaurukan musulunci in da ake watsa madaran karatu. Hakan ya kara masa matsayi a waje na har na fara sha'awar kai masa ziyara. Ko da na faɗa masa a lokacin sai bai Musa min ba.
***
Ba'a rufa sati biyu ba na shirya jaka ta nayi sallama da mahaifana akan zan je intabiyu na neman aiki saboda in na ce ga inda za ni tabbas ba za'a bar ni ba.
Mun haɗu da Abu zayd, ya kai ni gidan su inda ya sa da ni da iyayensa da iyalinsa. Na yi farin cikin karramawar da na samu har bayan kwana uku, anan na fahimci duk addinin da su ke yi iya fatan baki ne amma ayyukan su da dama sun saɓa ma shari'a.
***
Kwatsam ranar da na kwana huɗu a gidan sai aka yi bak'i, da fari ban da ra'ayin zuwa amma ganin irin girke girken da ake yi ya sa na san ko su waye bak'i toh ba kananan mutane bane. Mamaki ya cika ni da na ga manyan shugabannin Kasar ne wa'inda suka haɗa addini mabambanta.
"Sannunku da zuwa" Na ce in rusunawa.
"Ameer ka yi sabon ɗa ne bamu sani ba. Da fatan imaninsa ya kai na mai son lahiransa fiye da duniya" Wani ya faɗi, ɗaga kan da zan yi sai naga ai shugaba ne ga wani addini can daban ba musulunci ba.
"Kwarai kuwa wa ya ki Aljanna, ni ban ma wanke shi ba Tukuna, abokin Abu zayd ne amma da gani zai kyau ma aiki, inaga zan tura shi shugabancin yankin gabas" da haka suka cigaba da magana ta a cikin zaurance inda su kaɗai ke fahimtar junansu.
Ban wani damu ba har zuwa da dare wani babban ɗan siyasa ya kira ni ya bani zobe, sannan ya kara da cewa
"ni tun da na ganka kayi min, kada ka yarda su ɓata rayuwarka. Ka rabu da su lafiya kuma kada ka sake dawowa" Ya ce yana min kyautan azurfan.
Kamar yanda ya bani shawara haka kuwa aka yi, na haɗa kayana nace zan tafi mahaifi na ya kira ni. Nan Ameer ya min kyautan daloli na tafi ina godiya.
Na dawo garinmu da sati biyu kenan wasu kuɗin suka sake shigo min daga Ameer, haka dai ya cigaba da turo kuɗaɗe sannan suna cigaba da da'awa a shafinsu na kyamatar wanda ba musulmi ba sannan da maida su dabbobi ma sun fi su daraja. Sannu a hankali akidar ta fara shiga na balle kuma ganin irin kyautatawan da su ke min.
" Umma ki dena kula wancan banzar arniyar, jininta fa ya halatta Tom yanzu sai ta kafirta ki" Na ce ma umma na da ta raka kawarta inyamira Ezinne.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Sufyan, kana da hankali kuwa, ko annabi bai yi mu'amala da wa'inda ba musulmai bane aka ce maka. Ina zaka kai kafiran amana da hukuncin su a musulunci" Ta ce min ranta a ɓace, amma inaa kallon ta nake sak wacce ta ɓata, takaici ya ishe ni da ta cigaba da fade-fade se kawai na ga anya ma umma ta ba ta kafirta ba, kawai rigar musulunci take sanye da?
No comments:
Post a Comment