Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce 24

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


🕊Special shoutout to all the Atikus🙋🏽🙋🏽 onelove💞😘😘


©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣4⃣

Kallon Bintu Yarima Nuhu ya ke cike da so da k’auna, murya can k’asa ya kira sunan ta
‘’Bintun arzki, dama haka ki ke da kyau? Anya kuwa Bintu zan juri rashin ki?’’
Kanta a k’asa ta d’an ja da baya, dan kuwa ganin Yarima Nuhu durkushe gabanta ba k’aramin takura ta yi ba, dad’in dad’awa yau kuma ya zo mata da saban salo na magana. Ai kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Kana ta ce

‘’Allah shi taimaki Yarima, Barka da yammaci, Jakadiya ce ta ce Yarima na da buk’atar gani na’’

Hannunta da ke rawa ya bi da kallo, in da idanunsa suka  sauka bisa zoben hannunta, sai kyalli da shek’i ya ke, ba tare da wani tunani ba ya d'aura hannunsa bisa hannun lta mai d’auke da zoben. Jin sabon salo hannun Yarima Nuhu bisa na ta ya sa Bintu janye hannunta a firgice cikin sauri kamar wacce aka d'aurawa garwashi, nan ta shiga yarce hannun tana ka6ewa kamar wanda wani abu ya mak’ale. Gaba d’aya ta firgice idanunta na shirin kawo ruwa.

Cike da mamaki Yarima Nuhu ya ke dubanta, kana ya ce
‘’Haka ki ke k’yank’yamina Bintu? Duk wannan d’aga hankalin da yarfe hannun dan na ta6a ki ne?’’

Sai a sannan ta farga da abun da ta ke, tuni ta zube hannayen nata a k'asa, idanunta na fidda kwallar da dama su ke mak’ale cikin kwayar idanunta, fad’i ta ke.

‘’Na tuba, kamin rai, na tuba, ba na so na mutu Yarima, aradu ba na san na rasa raina.’’
Ya na mai jinjina maganar cikin ransa, cike da mamaki ya ce da Bintu
‘’Wa ya ce za ki mutu?’’

Zuciyarta d’aya, har ila yau ba ta fasa hawaye ba ta ce
‘’Iya Dije ce’’
‘’Iya Dije?’’
Yarima Nuhu ya maimaita. Bintu na mai gyad’a kai ta ce
‘’Eh Iya Dije, ta ce idan har na sake na bari namiji ya ta6a ni mutuwa zan yi, kwankwatsi ma kuwa.’’

Ga mamakinta sai gani ta yi Yarima Nuhu ya jefa kansa baya ya na mai saka dariya mai sauti. Cikin rashin fahimta Bintu ta duk’ar da kai jiki na rawa.

Tashi ya yi, ya koma wajan zamansa na fari, yayinda  ya zauna ya na mai kishingid’a bisa tintin cike da mulki da sarauta. Har a lokacin idanunsa kanta ya ke, fuskarsa kunshe da murmushi bayan wasu d’an dakik’ai ya ce
‘’Bintu d’ago ki kalle ni.'’
A hankali ta d’ago kanta, cikin bin umarni ta kai kallonta gareshi, fuskarta cike da hawaye. Gefansa ya mata nuni da shi sannan ya ce
‘’Dawo nan ki zauna.’’
Ta na fidda kwayen idanu ta ce
‘’Iye?’’
Kai ya gyad’a mata cikin jaddadawa, bai kuma fasa mata murmushi wanda ke k'ara masa kyau ba. Cike da shakku Bintu ta tashi a hankali, inda ya mata nuni nan ta je ta zauna, amma can nesa da shi.

Ya na mai jin dad’in maganar Bintu, duk da yayi mamaki ace baiwa kamar Bintu batasan komai ba har haka, sakamakon shaidar rashin kamun kai da ake yiwa matasan bayi irinta. Kana ya nisa tare da fad’in
‘’Iya Dije ki ka ce kowa? Ko shakka babu ta yi gaskiya’’

A tsorace Bintu ta d’ago ta kalleshi ta na mai fad’in
‘’Shikenan ni Bintu mutuwa zan yi, na shiga uku na lalace.’’

Dakyar Yarima ya iya kunshe dariyar da ta kusa cin k’arfinsa, ya na mai k'ok’arin d’aure fuska ya ce
‘’Banda yanzu, ba za ki mutu ba tunda ni ba ta6a ki, hallo na yi ba gangan ba, zoben hannunki na ta6a, amma kar ki yarda wani ya ta6a ki muddin ki na so ki yi tsayin rai, musamman idan aka kai ki wannan Masarauta na Fabarusa, ko da kuwa Sarki Abdulrahman ne da kansa.’’

Ta na mai tunani yo dama me zai sa Sarki Abdulrahman ya ta6a ta, ta yi saurin amsawa da
‘’Aeadun Allah ba zan bari ba, hallo ni ma ba na zuwa kusa da maza, Inna ta ta hana’’

Yarima na mai duban zoben hannun ta wanda hakan nan ya ji ya tsole masa ido, ya ce
‘’Wagga zobe na hannunki, wa ya baki?”

Zuciyar Bintu d’aya ta amsa masa da
‘’Monsieur Aisar ne ya bani ajiya.’’

Wani bakin kishi ne ya ta so masa jin sunan namiji bakin Bintu, nan da nan ya sha mur ya na mai kausasa murya ya ce
‘’Akan wani dalili zai baki zobe ajiya? Shi waye d’in ki? Ashe dama ki na soyayya?’’

Cikin k’ok’arin kare kai ta ce
‘’Wallahi ba na soyayya, ban ta6a yi ba, idan k’arya na ke aratta kashe ni,  Monsieur ne a École ya ce na ajiye masa.’’
‘’Ciro zoben ki bani’’

Ya ba ta umarni. Har ga Allah ba ta son cire zoben, idanunta na fidda kwalla yayinda ta ciro zoben daga yatsanta, maimakon ta bashi sai ta dunk’ule shi cikin tafin hannunta. Ganin bata da niyar mik’a masa, ya mik’o hannunsa gare ta, a hankali ta d’aga ido ta kalle shi, ya na mai gyad'a mata kai ya mata nuni da hannunshi. Hannunta na rawa, ta aje zoben bisa tafin hannunsa, ba ta ankara ba sai gani ta yi yayi wulgi da shi gefe. Da sauri ta bi inda ya jefa da kallo yayinda ta ji zuciyarta na mata rad’ad’i, sai a sannan  tasan ashe zafin da zuciyarta ke mata ba na rabata da iyayen ta kad’ai ba ne, har da na rashin Aisar har abada, gashi idan aka d’auke turarukan da ya bata, zobenshi ne kad’ai ya rage mallakin sa a gunta, ta na ji ta na gani Yarima Nuhu ya raba ta da shi kamar yarda ‘yar uwarsa ta rabata da shi, idan ita dan ta na son Aisar ne, shi kuwa Yarima Nuhu menene na shi azancin? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wanda nan ta ke kuwa ta ji amsarta, Yarima Nuhu na mai duban ta ya kira sunan ta da kakkausar murya
‘’Bintu’’
Hakan yasa Bintu dawowa da kallonta gareshi. Bai gushe ba ya cigaba

‘’Soyayya gaskiya ce, soyayya halal ce muddin ba a tsallake iyakokin Ubangiji ba, ba laifi ba ne don kinyi soyayya, amma ki sani duk duniyar nan da ni ya dace ki yi, Bintu ni mai kaunarki ne, ni Nuhu ni masoyinki ne da ni ya dace ki yi soyayya ba da wani tsoho da ake shirin amra mi ki ba, ko kuwa wancan sokon Monsieur da ya bawa d’alibarsa ajiyar zobe!’’

A tsorace Bintu ta fara ja da baya, ta na mai girgiza masa kai, tsabagen firgici ta kasa magana. Da sauri ya rik’o hannunta, ya na fad’in

‘’Karki guje ni Bintu, ni mai k’aunarki ne, kimin alkawarin za ki aje min kanki amana, ah ah kawai ki shirya mu gudu, duk k’asar da ki ke so aradu zan kai ki Bintu, kar ki yarda a amra mi ki wannan tsohon.’’

Cikin sauri Bintu ta fizge hannunta daga nashi, har lokacin ba ta fasa girgiza kanta ba, yayinda ta ke hawaye d’aya na bin d’aya, tunda ta ke a rayuwarta babu wanda ya ta6a furta kalmar so a gareta, kuma ba ta ta6a zaton zata ji shi daga bakin ko da ‘yantaccan d’an adam ba ne, bare kuma Yarima, Yariman ma na Sa'ayrasa. Hankalin Bintu bai dad’a tashi ba, sai da ta ga kwalla cikin idanun Yarima Nuhu na gangara a hankali bisa kuncinsa, nan ta mik’e tsaye da sauri yayinda kuka ya ci k'arfinta tana mai tattare kasan doguwar rigarta, ta juya da niyyar tafiya, hakan yasa Yarima Nuhu tashi da sauri, ya na mai rik’o kallabinta ya ke fad’in.

‘’Karki tafi ki barni Bintu, aradu zan iya rasa raina, ki tausayamin.’’
Sakar masa kallabin ta yi, gashin kan ta lub lub ya sauko har bisa wuyanta maimakon gadon bayanta da ya saba saukar sakamakon askin da ta sha gun Marry, tana mai tafiya cikin gudu gudu, sauri sauri, ta d’au hanyar fita daga lambun.

Yarima Nuhu rik’e da kallabinta ya shiga doka mata kira
‘’Bintu! Bintu!! Bintu!!!’’
Ina ko waige ba ta yi ba bare ta tsaya har ta fice daga cikin lambu, in da ta bar Yarima Nuhu rungume da kallabin na ta bisa k’irjin sa, ya zube gwiwowi biyu k’asa zuciyarsa na bugawa kamar za ta tsage ta fito.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment