Monday, 11 September 2017

Ina ze kai mu 2

INA ZAI KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com

             2.

"Kinga kenan naki duk da sauki" faɗin matashin da take faɗa ma labarin ta.

"Ai ka katse ni ne, da ka ɗan saurare ni na kai aya" Ta ce tana share hawayen ta..

"Kin san ni menene Mafarin nawa Fitinar, kamar dai ke ɗin ce, sai dai ni nawa in da ya fi naki shi ne nayi karatu har matakin digiri na biyu a fannin Tafsiri a jami'ar islamiyya da ke madina.

Bayan dawowa ta na buɗe shafin karantarwa a Facebook da WhatsApp. Tambayoyin da mata kan aiko min da akan hirar da ake a shafukan su na mata zalla ya sa na sauya suna zuwa mace nayi amfani da sunan 'ya ta Rabiatu Aliyu na bud' e da shi. Take na bi ɗaya daga cikin ɗalibai na mata nace ta sa ni a shafukansu.

Ba musu ta sa aka jefa ni saboda tabbacin da take da duk wanda ke zauren karatun mu na addini jinsi ɗaya su ke da don ina da takatsantsan duk don kar a shiga hurumin da bai kamata ba.

Ana shigar da ni aka ce in gabatar da kaina, nan na tura hoton da na samu a kafar sadarwa ta Instagram na wata balarabiya da Yaranta.

'Sunana Rabiatu, mahaifiyata yar Kasar Masar ce amma mahaifi na ɗan riruwai ne a jihar Kano na taso a garin Kano ina aure a Kano ga wani ɗan uwan mahaifiyata'. Tun daga gabatarwa ban iya cewa komai ba ganin yanda in dare yayi ake bajewa masu tallan magungunan mata su kafa cafta da sunan koyar da mata.

"Ai jiya umma Albarka ta dinga shi min don tace haɗin Hajiya mai gyara ya haɗu" cewar wata da ta sa sunan baby

Nan labari ya koma kanta tana faɗin  mahaifinta yayi lattin asuba shi kuma uku da rabi yake tashi kullum.

"Taɓ baby kin isa aure, gara a aurar da ke mu huta" faɗin lubbatu tare da turo ɗan aljanin nan mai nuna kyafta ido ɗaya.

Anan na gane ashe budurwa ce ba ta da aure, take zuciyata ta ce na bi ta na yi mata wa'azi, ban yi tunani biyu ba ganin an ce AMRU BIL MA'ARUF WAL NAHYU ANIL MUNKAR.

"Baby yar Abba" Na aika mata

"Laa balarabiya matar balarabe oh ni baby" Ta maido martani haɗe da aljanu masu rawa. Murmushi na maida mata nan cikin dabara na mata wa'azi kuma babu gardama ta nuna ta amshi gyaran.

Tun da ga wannan  lokacin muka fara gaisawa sama sama kafin na ankara mun yi Shakuwar da ni kai na ban san yaushe mu ka yi ba.

***
Bayan shekara ɗaya mun shak'u sosai har ta kai ga na faɗa mata ni namiji ne bayan na bar zauren su ma mata zalla. Sam ba ta nuna damuwa ba, nan sai kuma soyayya ta Gitto a tsakanin mu.

"sheikh za ka iya aure na kuwa, ni wallahi ba auren Ustaz ba hijjabi da niqabi" Ta ce dani wata rana muna waya

"Toh ba sai ki koma sa Jalbab ba irin na Larabawa. Sam ba zai bayyana surar ki ba, amma ba zan haɗa ki da umm Rabiatu ba, sunna zamu yi sak, kowace mace da gidanta" Na faɗa mata duk da ina shakkan yiwuwan hakan kasancewa na mai matsakaicin karfi, amma son ta ya bi jini har tsoka na jiki na duk da ba mu yi haɗuwar ga da ga ba sai dai hotunan junanmu da mu ke turawa kusan kullum sai mun sabonta shi.

"Yaushe zaka zo, ina Kano ina Jos, ga yan jami'ar ku da dama cikin jasawa. Masauki ba zai gagara ba" Ta karasa da rufe min kofar korafi.

"Gimbiya faɗi yaushe kike so in zo, daga nan zan ga abba ko" ba musu ta amince min da haka muka tsaida sati mai kamawa.

***
Ranar tafiya ta iso na shirya haɗe da yi ma iyali da iyaye na sallama da sunan zani gaida abokin karatu. Duk nayi karya akan baby sai na ji bugun zuciyata ta karu don rabon da na yi karya tun zamanin kuruciya.

Mun yi ban kwana suna min fatan dawowa cikin aminci, ni kuma na tafi ina murnar ganin masoyiyata ashe ban sani ba tafiyar ba abinda zata jawo min sai... " bai iya karasawa ba saboda kukan da ya saki.

***
" ikon Rabbi daga soyayya sai kuka, kai baka bari ta karasa mana ba, ka zauna kana kukan daɗi. Ni a dalilin shafukan sada zumunta sai da na zama shugaban wani sashi na yan ta'adda mai suna "Al mujahidoon" don dai kawai na arce ne amma lahira na kuma fa" Ya ce yana murmushin da gani an san iya lebansa ne kawai.

"Garin yaya" sauran suka tambaya a firgice

"Kace gara ni da iya ka ta codeine se wani sa'in in shaqa" wata yar firit da ke zaune a gefe ta ce tana dariyar mugunta.

No comments:

Post a Comment