Tuesday, 19 September 2017

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) 16

®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


1⃣6⃣

Sidiya ce...✍🏼

Ta na tafe ta na hawaye haka ta isa 6angaran Bintu in da ta tadda Ladiyo zaune gaban Bintu ta sha kuka ta k'oshi, daga gefan Bintu kuwa Maman Cangwai ce zaune a k’asa, d'ayan 6angaran Hansai da lantana ne zaune. Bintu ta sallami dukkanin bayin Fabarusa domin samarwa Ladiyo masalaha.

A gaban Bintu baiwa ta aje fanteka ta na mai rawan jiki, tun gaisuwar da ta kai ga Bintu, bakin ta na motsi amma tsoro da kwarjinin Bintu ya sa ta kasa furta komai. Maman Cangwai na me duban ta ta furta
‘’ke mu ke sauraro ya ke d’iyar Fabarusa....’’
Maimakon Baiwa ta fad’i dalilin zuwan ta da kuma sak’on Barde, sai gani su ka yi ta fashe da kuka ta na mai fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e, ki min rai na tuba ki rufa min asiri, tuba na ke’’
Nan fa su Ladiyo da lantana su ka shiga kallan kallo cike da mamaki. Bintu ma mamaki ya ne ya lullu6e ta, cikin ba da umarni ta ce da Maman Cangwai ta bud’e fantekar ta ga abun da baiwar ke tafe da shi. Ko da Maman Cangwai ta bud’e fanteka sai da gaban ta ya fad’i ganin turaruka iri daban daban masu yawa ciki. A hankali ta kai kallan ta ga Bintu wacce ita ma ta hango me ke cikin fantekar kafin ta maida kallan ta ga baiwar, kana ta furta
‘’wannan kuma daga ina?’’
Baiwa ba ta fasa hawaye ba ta furta

‘’gide sak’o ne daga Yarima Barde zuwa ga Gimbiya Fatima, hallo ya na mai sheda mata cewar Yarima Barde ma’abocin k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta sauya gimshikin kusurwar ta.......’’

Ta k’arasa furucin na ta ne cikin rawan murya. Shiru kake ji babu mahalukin da ya furta komai tsabagen bazata da kalamin baiwar ya mu su, babu shakka Barde na me shedawa Bintu wani abu daga 6angaran ta ya na wari duk da dai be fayyace mata ko menene ba, wanda turo fantekar turaren da yayi ba k'aramin cin fuska a gare ta ba ne, ba dan ma an riga an d’aura mu su aure ba da hakan daidai ya ke da ya ce ya fasa auren ta saboda wari da ya ji na daga wani 6angare da ya shafe ta.
Sai a sannan Maman Cangwai ta gane kukan da baiwa ta ke, dan kuwa a k’aida ya zama dole Bintu ta hukunta ta bisa ga sak’on cin fuska da ta iya duban tsabar idanun Bintu ta sheda mata, in kuwa ta yi sake ta rabu da ita salin alin, toh tabbas ta siyawa kan ta raini daga kan jama’ar fada har izuwa sauran bayin na fada babu wanda za ta k’ara yiwa kwarjini bare a ji shakkar ta.
Jin Bintu ba ta furta komai ba Maman Cangwai ta dawo daga gefan ta, in da ta zauna kamar me jiran umarni daga Bintu, a kaikaice yanda baiwar ba za ta fahimta ba ta ce da Bintu
‘’hattara Gimbiya, wanga batu ba na sassauci ba ne, dan haka zan ari bakin ki in ci albasa, ina mai neman alfarma rashin maganar ki bisa hukumcin da zan aiwatar kan wagga baiwa ta fabarusa’’
Ba tare da ta jira amsar Bintu ba ta mayar da kallan ta ga baiwa, sannan ta ce
‘’bisa ga umarnin Gimbiya, ta yaba da kyautar Yarima a gare ta, sa'annan wagga baiwa da ta kawo sak’o gare ta, zaki amshi bulala hamsin na daga tsimagiyan Gimbiya Fatima’’
Da sauri Bintu ta kai kallan ta ga Maman Cangwai cike da 6acin ran jin furucin na ta ta yi k’ok’arin dakatar da ita, wanda hakan ya sa Maman Cangwai saurin fad’in
‘’na yi kuskure Gimbiya, bulala sittin Gimbiya ta ke nufi, maza Lanta tashi ku fitar da ita zuwa d’akin horo, ki kuma sheda ma su umarnin Gimbiya kowa ya ji ya gani ya kuma sheda!’’

Baiwa na kuka ta na fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e’’

yayinda Lantana ta tasa ta gaba, ta na mai fad’in
‘’godiya ta ke Allah shi taimaki Gimbiya’’
Su na fita hawayen da ya ciki idanun Bintu tuni ya gangaro bisa kuncin ta tsabagen tausayin baiwa da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba an k'ak’aba mata horo tsabagen rashin adalci. Cike da 6acin ran da ita kan ta Maman Cangwai ba ta san Bintu na da irin wannan fushin ba, ta furta

‘’akan wani dalili za a yiwa baiwa horo? Gide ita na ta ba sak’o ba ne? idan adalci ne na lalle sai kin nuna an min ba daidai ba ki hukunta shi Barde wanda ya aiko ta mana? Saboda ita baiwa ce? Su bayi ba su ‘yanci? Bayi su an bola?’’
Jiki a sanyaye Maman Cangwau ta furta
‘’hakan da na yi kad’ai zai nuna matsayin ki na d’iyar sarki, dan kuwa babu d’iyar sarakin da za a yiwa wanga cin fuska ta kasa aikata yanda na aikata, in ba dai so ki ke asiri ya tonu ba. Na san yanda ki ke ji, amma fa kada ki manta ko nima baiwar ce, ina fatan za ki fahimce ni.....’’
A fusace Bintu ta tashi tsaye, ta na mai girgiza kai ta ce da Maman Cangwai
‘’ba zan ta6a fahimtar ki ba in dai bisa zalinci ne, ba da yawuna ki ka aiwatar da hukuncin ga ba, umarni na anan shi ne ki gaggauta dagatar da shi!’’
A fusace ta wuce d’akin ta, wanda kan ta kai ga shiga sallamar wata baiwa ya tsaida ita. Ta na ji baiwar na gaishe ta amma 6acin ya sa ta kasa amsawa ta d’aga k’afa za ta shige kenan amma jin furucin na baiwar ne ya tsada ta. Jin ta na fad’in

‘’Yarima Sadauki ya na da murad’in ganin dukkanin bayin Sa’ayrasa!’’

A hankali Bintu ta juyo, wato 6acin ran da take ciki ya sanya ta rikidewa hatta Maman Cangwai, bare kuma su Ladiyo, tashi guda ta tashi daga Bintun da su ka sani ta zame mu su wata daban mai wuyan fasaltuwa. Ta na mai duban baiwar ta furta

‘’wa an Sadauki? A matsayin sa nawa ya ke da muradin ganin bayin Sa’ayrasa gide? Akan wani dalili?

Baiwa ta yi jim  dan kuwa ta tsorata da yanayin da ta ga fuskar Bintu, cike da 6acin rai da kwarjini ga kuma tambayoyi na gadara da ta mata akan Yarima Sadauki. Nisawa ta yi kafin ta amsa mata da

‘’Allah huci zuciyar Gimbiya, Yarima Sadauki shi an Yaya ga Yarima Barde wanda ya ke maigida a gare ki, dalilin sa na murad’in ganin bayin Sa'ayrasa shi kad’ai ya barwa kan sa sani’’
Bintu na mai jinjina kai ta ce da baiwa
‘’ki koma ki shedawa Sadauki ni Fatima na ce bayin Sa’ayrasa ba za su isa gare shi ba muddin be zo mana da gamshashshiyar dalilin sa na murad’in hakan ba!’’

🐫🐪🐫🐪🐫🐪

No comments:

Post a Comment