®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
7⃣
Sidiya ce...✍🏼
Jakadiya ta bud’e kofar motar ta in da Bintu ta ke. Bayi mata guda goma shabiyu, wanda su ka kasu gida biyu sahu su ma jere kan sa sunkuye gaban motar su na jiran fitowar Bintu domin taka mata baya. Idan Bintu ta motsa toh dutse ma ya motsa, sai da Gwaggo Munri ta fito sannan ta zagayo gare ta, hannun Bintu ta lalabu cikin alkyabba, sannu a hankali, cikin azanci kai ka ce Gimbiyar ce da gaske ta fito da Bintu. Tuni bayin nan su ka zube gwiwowin su biyu a k’asa cike da girmamawa. Mata da yara masu waka ba su fasa ba. Cewa su ke
‘’Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!
Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!!’’
Jakadiya kuwa ba ta fasa gud’a ba. Tuni hayaniya da sowar jama’a ya rud’a Bintu, har sai da Gwaggo Munari ta fahimta ganin yanda ta cize waje d’aya ta kasa tafiya. Cikin rad’a Gwaggo Munari ta ce da Bintu
‘’yo to ki ka cize nan Gimbiya kya iya wad’uwa ba ki sani ba, gide rufa mana asiri mu tai, ke kawai ki ta salati, hallo ka da ki kuskura ki kai kallan ki ga jama’a, hakan ka iya rud’a ki, maza soma ambaton Allah’’
Nan da nan Bintu ta tsinci kan ta ta na mai ambaton Ubangiji. Tsakiyar Uwanlenze da Gwaggo Munari, Jakadiya daga baya, biye da ita bayi goma shabiyu ne, su ka kutsa ta hanyar da aka tanada na musammam domin wucewar Gimbiya. Ba su zame koina ba sai cikin fadar Fabarusa.
Kansencewar Masarautar Fabarusa ta yi biyun ta Sa’ayrasa a girma da tsari, ba su Ladiyo ba, hatta Gwaggo Munari sai da ta yi da gaske wajan 6oye shawa’an ta ga Masarautar domin kuwa lokacin da su saka k'afar su a katafariyar fadar Fabarusa, sun ga abin mamakin gaske, wato bayan girman fadar na da ban al’ajabi, kuma yadda aka fasalta ko tsara ginin ta shi ma abin mamaki ne. A tak’aice sai da su ka zamo tankamar k’auyawan da su ka shigo birni. Gini ne irin na gargajiya wanda aka kafa harsashin ginin da manyan duwatsu ma su tsada, wad'an su kamu takwas wasu goma. Tsakanin kowace katanga akwai duwatsu masu tsada wad’anda aka yanka su bisa ga ma’auni san’annan aka dasa itacen al’ul daga gefan su. Tsuntsayen fada iri iri ke shawagi, musammam d’awisu da jin su ne su ka fi yawa.
Sai da su kusta sauro gomasha biyu kan su kai ga shiga cikin gidan Sarki, kowanne da na sa irin adon da kayan k’awa, wanda idan su ka shiga wannan su ka shiga na gaban sa sai su ka ashe na baya ba komai ba ne idan aka had’a sa da na gaban sa. 'Bangarn uwar gidan Sarki Abdulrahman, wacce ake kira Goggon nan aka sauke su. In da aka zaunar da Bintu bisa shimfid’a na musammam da aka ta na dar mata daga tsakiyar falo, yayinda su Ladiyo, Hansai, Lanta da Maman Cangwai su ka yi zaune daga gefe matsayin su na bayin Gimbiya.
Tuni Barori da Bayi su ka shiga kai kawo da hidima domin tarbar baki cikin aminci ta hanyar tabbatar da ba su bawa Masarautar su kunya ba. Kayan marmari na daga ‘ya’yan itace ne, nama na k’arama da babban dabba kai har da ma na d’awisu, su dubulan ne, caccabe, alkaki da nakiya komai bajau sai wanda jama'ar Sa’ayrasa su ka za6a. Gwaggo Munari na mai jinjina kai cikin ran ta take fad’in
‘’ma su abu da abun sa, gaskiya dukiya cikin wanga masarauta ba a cewa komai! D’iyar bayi ke kuwa Allah ya yankewa kakar saka, amre cikin wanga Masarauta shi an baiwa’’
Ciki su ka bud'e su ka ci su ka yi nak. Amma ita ko Bintu ruwa ma kasa sha ta yi bare ta kai ga cin abinci duk da kuwa azababban yunwa ne ya addabi cikin ta. Bayan an tabbatar su huta ne wata baiwa ta zo ta ce da su idan sun shirya za ta kai su ga masauk’in su domin Gimbiya Fatima ta shirya ta sami fitowa zuwa taron wankan amarya wanda za a yi nan ba da jimawa ba.
🐫🐪🐫🐪🐫🐫
No comments:
Post a Comment