Friday, 15 September 2017

Ina zai kai mu 5

INA ZE KAI MU
Safiyyah Ummu-Abdoul

        5.

Mutuwar Ameer ya sa na gudo garinmu. Yanda ban ma kowa sallama ba haka ban faɗa ma kowa zan dawo ba. Gani na kawai su ka yi kwatsam

"Safiyanu ashe za ka dawo, Allah ya shirye ka amma in dai ka san wani laifin ka yi ka gudo nan ni da kai na zan mik'a ka ga jami'an tsaro" faɗin Abba na lokacin da ya dawo ya iske ni  gida. Ban ce da shi kala ba haka na cigaba da hidima na ba tare da n musu bayanin in da na fito ba su ma ba su tambaye ni ba.

Dan zaman da na yi a gida ne na kalli kasussukan yaki da haɗe haɗen makamai da na samu tun zamanmu wajen Ameer. Bani da aiki sai kallace kallace, ba abin da ke tada ni sai sallah shi ɗin ma a gida nake yi don ban yarda da musuluncin mutan Anguwan mu ba.

"Safiyanu wai me kake tsinta a kasussukan nan ne, ni bana fahimtar komai" Umma ta ce min haka da ta ga kallon ba na karewa bane.

"Ina shirya ma jihadi ne, don sai Kasar nan ta koma daular musulunci" Na faɗa mata kai tsaye, shanye zancen ta yi sai ta sake jefo ni da wata tambayar

"Sallan da kake yi a cikin gida kuma mai zaka ce game da hakan"

"Umma! In dai ba ni za su ba limanci ba toh ba zan yi aikin baban giwa ba, don ko silin din masallacin sallan bai wucewa balle a amsa" Na amsa mata. Shiru tayi tana kallo na.

"Wahayi aka yi maka ko an baka anabta ne da ka san haka, gani nayi kaf Layin nan babu coci, kuma sallah su ke kamar yanda manzo SAW ya ce SALLU KAMA RA'ITA MUNIE USALLI ko kana da ja ne akai" maimakon in ba ta amsa sai kawai na kwashe da dariya sannan na ce

"Umma Allah ya shirye ki" Na tashi na ɓata waje.

***
Na cigaba da rayuwa ta ba tare da shayin kowa ba. Babu abin da na sauya na daga halayen da na dawo da su sai ma abin da ya karu. Na na siya kwamfuta karama da na kuma ɗosana ma gidan yanar gizo ta wifi. Sai ya zama ban da aiki sai bincike da karance karance abin da ake karantar da mu na game da yaki da sauransu.

Ana cikin haka aka kira ni, ban yi sallama ba na sake zura kai na tafi, muna isa camp dinmu wato gidan Ameer aka rarraba mu, nan wasu kusoshin gwamnati suka sama mana makamai sannan aka faɗa mana inda za mu dinga sa wa.

"Za'a fitar da wasu kuɗaɗe masu tsoka ba ma so yan kasan nan su kai ga sani, akwai wajen wasan yara da gwamnatin jiha zai kaddamar shi ne na ke so a tarwatsa wajen duk wani mai kararren kwana ya sallami duniya" faɗin quasar.

"Abul Hussain kai nake son ka jagoranci shirin" Ya faɗi yana kallo na. Ba Musa ba na amsa. Cikin dare na je na sa duk abin makalawa, na haɗa da waya ta na fito. Washe gari na kwashi mota na isa wajen dai dai da saura mintuna ashirin lokacin da na sa ya yi. Fakin nayi saitin bishiyar da na sa makamai na, ina zaune har saura binti biyu na fakaice ido na fice daga wajen lokacin tawagar gwamnati na tsaka da kaddamar wa.

Kara mai firgitarwa ya tashi na fita daga gate din kenan, ban tsallaka titin ba na biyu ya tashi nan na bi ayarin ma su neman ransu mu ka dinga gudu har na samfe.

***
"Aikin ka ya yi kyau, ban taɓa tunanin zaka fita da ranka ba, har ina bakin ciki zaka yi shahada don na fi so ka yi ta a gaba in ka. Ajiye magaji" faɗin wanda ya bani kwangilar

"Kai ne shugabanmu, ba zamu yarda ayi mana wani mulkin gado ba, ABU Dayyib ya ce tun da mahaifinsa ne Ameer shi zai zama ameer" faɗin wasu daga cikin mu. Nan wannan shawara yayi karfi aka mika ni a shugaba sannan na fitar da faifai na bidiyo ina faɗin mu ke alhakin wannan tashin bomb din don an bude hanyar da sheɗan zai shigo jihar sannan an kashe mana Ameer. Daga nan na ɗaura da wa'azi ga sauran al'umma su tuba su ba mu haɗin kai wajen kafa daular islama.

***
A cikin shekara biyu mun yi karfi sosai, muna samun tallafi daga wasu yan kasuwa, yan siyasa da ma wani ɓangare na gwamnatin kasan. Mun yi nasaran kawar da wasu kauyuka da ma birane saboda in mun tashi kona komai mu ke yi. Mata kuwa a rana sai na kwanta da yara budare fiye da goma. Kuɗin akawun ɗina kuwa ya tasar ma biliyan ɗari biyu. Don duk wani ran da aka kashe cikin mu sai gwamnati ta biya ni kuɗi makudai.

***
Ina cikin haka ne wata rana barci ya kwashe ni ina cikin tura wani sa'ko cikin barci na yi mafarki an yi tashin alkiyama. Maimakon mu ganmu a Aljanna tare da alkawuran da aka karanta mana in mun yi jihadi za'a bamu sai ga mu tsundum a cikin wuta. Ihu muke jikinmu na zagwanyewa saboda azaba amma Sam ba'a rage ba sai ma kara zafi da wutan ke yi. A firgice na farka ina zufa. Nan na tashi na figi mota sai cikin lambunan mu.

Haka na jera sati biyu kullum na kwanta abin da nake gani kenan, azaba nau'i nau'i ake min tun bana jin hakan har na fara damuwa, bana iya barci don ban san abin da zan gani ba. Cikin ruwan sanyi na samfe aka neman aka rasa, na je wani kauye a matsayin ɗan ci rani. Ko wayata ban yarda na tsira da ita ba sai kuɗin da na ke tarawa a wani akawun na daban.

***
Sai da na yi wata shida a kauyen ban da istigfari ba abin da nake yi sannan na samu saukin damuwar da ke ci na. Nan na cigaba da sanar siyar da rake a kauyen da damina ta faɗa suka bani gona na nome, bayan an samu sauyi shugaban kasa ne na fito na je na nemi gafaran iyaye na, na zama wani salihin karfi da yaji, kana na nemi aikin gwamnati shi ne na samu na Npower dinnan. Rashin sanin me zan yi da kuɗin ne ya sa na zo nan wajen SCCvolunteers ko za su bani shawarar yanda zanyi" Ya kare yana mai share hawayen da ya zubo masa.

"Taɓ ba cin kisan kai ai da zan ce duk ka fi mu morewa. Kuɗi! Kuma zaka salwantar, Tab ai ka zo kawai mu yi aurenmu in zama matar mai kuɗi" faɗin yar maye. Da ma tun da ya fara labarin ta kd ɗura ma cikinta codeine

No comments:

Post a Comment