®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
Na gaishe ki aminyar arziki Ummi Aysha, ina alfahari da ke. Allah ya bar zuminci🤝
©Khadija Sidi.....✍🏼
2⃣6⃣
Da yammaci Inna ta zo mata sallama d’auke da su langar tuwo da miya, da humra da turaren wuta. Tun zuwanta Bintu ta ke kuka, har yanzu da Inna ta ke mata jawabi kamar haka
‘’Bintu kar ki damu, wani hani ga Allah baiwa Bintu. Ki yi addu'a Allah Ya sa hakan da ya zo mana shi an alkahiri, ina so ki sani Allah ne ya za6a miki wagga rayuwa da za ki shiga, ki sa Allah a ranki shi kad’ai zai miki gata.’’
Bintu ta gyad’a kai alamar toh.
‘’Duk da amren ga ba a san ranmu za a yi ba, ki na jinin barebari ba zan bari ki tafi haka ba, wagga(ta nuna kwalaban turarukan da ke aje gaban Bintu da yatsa) tun kina shekara biyar a duniya na had’a mi ki su na binne da niyyar sai amrenki ya tashi na hak’o, wannan kuma langar tuwo da miya da cokali da ludiya wanda na fara miki taro ne, duk da dai na san ba lalle ba ne a bari ki tahi da su ba, gashinan dai na baki a matsayin uwa, na hita hakkinki.’’
Bintu na kuka ta ce
‘’Wallahi ba na so! Ba na so Inna! Inna makaranta na ka so, dan Allah Inna ki taimaka kin ga dai sati uku ya rage mu koma....’’
Rungumeta Inna ta yi cike da tausayawa, Allah kad’ai yasan iya adadin lokacin da su ka d’auka a haka, kafin Bintu ta zame jikinta daga na Inna, kayanta ta nufa ta na mai bincikawa, nan ta fito da turarikan da Aisar ya bata, ta dawo ta durkusa gaban Inna, ta na mai mik’a mata ta ce
‘’Inna ga wagga, dan Allah ki kar6a ko da kuwa ba za ki yi amfani da su ba, wannan kyauta ne tsakanin uwa da d’iyarta, dan Allah Innata, wagga shi ne kad’ai abunda na mallaka nawa na kaina’’
Hannun Inna na rawa ta kar6a ta na mai fad’in
‘’Allah Ya sadamu da alkhairinsa d'iyar arziki, Allah ya sada mu ko da a darussalamu ne, saduwa ta alkahairi......’’
Kuka ne ya su6ucewa Inna, nan su ka yi mai isarsu, har dai Inna ta ga abin ba na k’arau ba ne, dakyar ta janye jikinta ta fice ta na jiwo kukan Bintu.
Yarima Nuhu kuwa har da jinya don kuwa babu yanda baiyi ba na ganin an fasa aurennan amma abu sai dad'a kankama ya ke, haka kuma ya so k’ara ganin Bintu amma Jakadiya ta k’i. Ta wannan dalili ya sa ko ganin Gimbiya Binta ba ya san yi, don kuwa ba zai manta da asarar da ta jawo masa da kuma halin da ta sanyashi ciki ba. Haka kuma bai fasa zayyanawa amintacciyar baiwarsa yanda ya ke san ta kula da al’amuran Bintu yanda zai kasance ba zai cutu ba har ya samu ta dawo gare shi.
Ana gobe d’aurin aure da daddare aka yiwa Bintu k’unshi irin na amare. Yanda ta ga dare haka ta ga rana, haka ma Yarima Nuhu wanda zazza6i ya rufe har da k’arin ruwa. Aisar kuwa farin cikin zai ga Bintu ne ya hana shi bacci, don da an bi ta tashi da tun aranar zai d’au hanyar Sa’ayrasa, sa idon Junaidu da gudun sharrinshi ya sa ya hakura. Haka ma Yarima Barde wanda farin cikin zai had'u da Gimbiya K'amariyya ya hana shi bacci, da ita kanta Gimbiyar.
******* ******
Washegari tun da sassafe Jakadiya ta sa Bintu wanka da wani ruwan magani gudun kar bak'in da su ka zo daga Fabarusa d’aurin aure su buk'aci ganin amarya, ko kuma Sarki Abdulrahman da kansa ya buk’aci hakan bayan an d’aura masa aure da Bintu ba tare da an shiryawa hakan ba. Leshi fari kyal mai adon koren duwatsu ta ce ta sanya. Farar alkyabba Jakadiya ta d’aura mata bisa, da wani takalmi kore. Kai da ka ga Bintu ka ce d’iyar Sarkin ce, ita kanta Gimbiya Binta da ta shigo ta gan ta sai da ta girgiza, ta kasa zama bare kuma dama tunda Allah ya wayi gari ta ke fama da fad’uwar gaba na ba gaira ba dalili.
‘Bangaran d’aurin aure kuwa, misalin sha biyu na rana tuni babban masallacin fada ya cika mak’il da jama’a, mutan Fabarusa, Mai Martaba Sarki Abdulrahman ya iso tare da tawagarsa, hakimai da dogarai, har da ‘ya’yansa biyu, Sadauki da na shi abokan, haka ma Barde da abokansa biyu, d’aya taubashinsa(cousin) wanda ake kira da Yarima Jafar, sai kuma d’ayan mai suna Khalil wanda ya ke babansa hakimi ne a Masarautar Fabarusa.
Haka ma su Aisar tare da Ministocin da su ka taho wakiltar mai girma shugaban k’asa, sun sami isowa, inda aka musu mazauni daga cikin Masallacin. Ba k’aramin kyau Aisar yayi ba, dan kuwa ado ya sha na burgewa musammam saboda Bintu. Dokakkiyar shadda ce jikinsa, ruwan toka, ya sha d’inki da aiki irin na manya, ga hularsa da takalminsa kalar zaran da aka masa aiki da shi, wato ruwan toka mai turuwa, da ka gansa ka ga d’an manya masu ji da mulki. Allah Allah ya ke ayi d’aurin auren a gama ya nemi Bintu don shi ita kad’ai ta kawo shi cikin wannan taro, yak’i jinin taro saboda yanayin aikinsa.
Yarima Barde kuwa daga waje yayi zamansa, gudun kar ya shiga ciki taro da turnak’in jama’a su hana shi ya fito da wuri don zuwa ga sahibibar ta shi wato Gimbiya K’amariyya. Sanye ya ke cikin farar shadda d’inkin babbar riga, ga rawani ya sha kai, ka ce za a kira shi Sarki ya amsa. Ango kuwa Sarki Abdulrahman tare da hakiman sa da kuma su Sadauki suna daga cikin masallaci.
Dake taro ne na manya da Sarakuna, shaddodi kala-kala tsadaddu ki d'aukar ido da kukama kalar kayan dogarai daga Masarautu iri-iri, abun dai ba a cewa komai, don kuwa wuri ya yi wuri, taro ya yi taro sai kamshi da kid’an algaita, kirari da kiran lafiya na dogarai da marok’a ke tashi. Sarakunan yanki da sassa na cikin jamhuriyyar Nijar babu wanda be sami halarta wajan ba, Sarkin Agadaz ne, Diffa, Marad’i, Zindar da dai sauran su.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
No comments:
Post a Comment