Thursday, 1 December 2016

KARNINMU 1


KARNINMU... 
© FIKRA WRITERS ASSOCIATION
              
Shimfiɗa...
   Kasar Haurobiya  tana da ga cikin manyan kasashe a nahiyarsu ta Turubu,  ƙasa ce kunshe da manyan birane da aka san da zaman su a duniya.  Kasa ce wacce ta ke yarurruka da dama  ciki kuwa har da Hausa wacce ta kwashe kashi sittin cikin ɗari na yarikan da ake yi a Kasar.
    Duk da kasancewar ta kasa mai cike da arziki da albarkatu hakan bai hana ta shiga halin ha'ulai  a KARNINMU ta ashirin da ɗaya.
     Birnin Dunotsi babban gari ne a Kasar Haurobiya,  Haurobiyawan da ke wannan gari mafi akasarinsu Hausawa ne sai Fulani masu bin Addinin musulunci ,  akwai wasu yarurruka da kasuwanci ya kawo su garin ko karatu ko aikin gwamnati.
          BABI NA  ƊAYA
Zaune take a harabar ginin da kallo ɗaya zaka masa ka san cewa otal ne, 
kas!  Kas!  Kawai ake ji na cingam ɗin  da take taunawa. Hankalinta kwance,  gabanta ɗan karamin tebur ne mai kunshe da farantin toka (ash tray)  yayin da kwalin taba ke gefen sa.
   Lubabatu Musa kenan wanda aka fi sani da Gimbiya.  Sanye take da jallabiyya baki, ta yane kanta da bakin gyale wanda ya taso sama kamar tozo,  saboda nannaɗa kitson attachment dinta da tayi ya ba da abinda ake kira da acuci maza.
     Fara ce doguwa kyakkyawa, kyawunta kan ruɗar da mata ma ballantana maza musamman in tayi murmushi wushiryanta ya bayyana.
A zahirance wando ne kasan jallabiyanta amma ita a rayuwarta wando in ya wuce kamfai to bata ɗaura masa komi a kai ko da kuwa bai wuce katarenta ba.  Wani kalan leggings gare ta da tsawonsu daga idon sahu ne zuwa guiwa,  su ta tara kala-kala  don amfani dashi wajen yaudaran wainda ba su Santa ba da shigan mutunci.
    Ɗan Zaman da tayi a farfajiyar otal din ya karo musu kwastamomi don wasu sun shiga sashin saida abinci na Otal din don kawai su kare mata kallo sa'ilin da zasu wuce.
    "Ranki shi daɗe oga ya iso"
wani daga cikin ma'aikatan otal ɗin ya faɗi yayin da ya karaso wajenta yana mai rusuna mata.
Yi tayi kamar bata san da zamansa a wajen ba illa ma jawo karan sigarinta  da tayi  ta kunna.
Sai da ta tabbatar da ta busa masa hayaƙin a fuskarsa sannan tayi fari da idanunta ta kalle shi tace
   "Bazan iya tafiya ba,  ya barni nan zaune ina jira kafafuwana sun yi tsami"
  Ta faɗi tana kawar da fuskanta zuwa wani ɓarin.
    "Ranki shi daɗe his mai girma Ministan Dunotsi  ne fa, kiyi hakuri bana tsammanin zai miki abinda kike so"  Ya ce yana mai kara rusuna mata kamar zai mata sujjada.
  "kasan doka ta ai,  bana son ɓata lokaci in ba zai iya ba zan bar wajen nan ne,  kuma kada ku sa ran zaku sake samun service ɗina nan kusa... "  bai jira ta kai aya ba  ya juya da saurinsa,  ya isar ma da mai girma Ministan  Dunotsi sakonta shi ma bai gardama ba ya biyo bayan ɗan sako.
Mai girma Ministan Dunotsi kenan,  Alhaji Sadisu  Jamilu Dunotsi,  ɗan shekara hamsin da shida, kyawun jikinshi na Fulani ya sa ake masa kallon ɗan shekara arba'in ko kasa. Fari ne kyakkyawa, iliminsa da wayewarsa kan kara haska shi.
Yayi karatunsa tun daga farko har karshe a Birnin Dunotsi, amma arzikin mahaifinsa  yasa shi leka kasashe da dama na kusa da nesa.
   Yana da yawan ibada tare da kiyaye hakokkin Allah amma yana da rauni ta fannin  mace, duk da Kasancewar sa mai ra'ayin zama mijin mace ɗaya ne kacal.  Ya daɗe yana taɓa bariki har zuwa lokacin da aka zaɓe shi Ministan birnin Dunotsi.
A yanda  aka bashi labarin Gimbiya luby ba zai so ya rasa lagwadan da ake samu ba. Ba cin wuyar da ya sha kafin ta amince ma sa a wannan rana.
"hmmmm!  Ita dai komi nata mai kyau ne" ya faɗi a ransa yayin da ya karaso wajen da ta ke zaune.
     Yana isa zuwa gareta ya fara mata watsi da kuɗi a jiki duk a tunaninsa zai burge ta amma ga mamakinsa ko ɗaga kai batayi ta kalle shi ba har sai da ya rusuna a gaban ta sannan tace
  "Ina ga duk wanda yayi maka tallan lagwadan da ake samu a tare da ni ya manta bai faɗa maka ko ni wacece ba, 
    Nice Luba yar gidan Juma da Musa, wacce ke tafe da nasara,  nasaranta  ba ita kaɗai yake amfana ba har duk wanda ya tara da ita. 
Ni ba karuwa bace face yar rakiya ko in ce sakatariya ga mafi akasarin masu kuɗi.  Gimbiya ce mai mulkin nan" Ta karasa tana nuna masa tsakanin cinyoyinta.
Yanda take magana da muryanta haɗe da rausayan da takeyi ne ya tafi da ɗaukacin tunanin sa.  Da kyar ya kai ga furta.
    "yanzu me kike so ayi ranki shi daɗe"  ya sunkuyar da kansa tamkar bawan da ke gaban ubangidansa.
   "ka goya ni zuwa ɗakin tukuna,  daga nan sai mu san hukuncin da za'a maka na zuwa latti." 
   Bai yi wani tunani ba,  sam ya manta yana tare da tawaga ciki kuwa har da yan jarida, hakan ya goya ta har cikin otal ɗin.
   Ai kuwa kamar jiran su ake Idanuwan ɗarurruwan mazauna wajan suka rakasu, nan da nan masu ɗaukar rahotanni suka soma aikinsu ba tare da ya ankare ba wasu suka fara ɗaukan sa hoto.
Bai tsaya ko ina ba sai kan gado.
Wayarsa  da makusantarsa ke kiran sa da shi ne ta fara kuka.
    "Ana kiran ka ne fa gwarzona"  Ta ce tana mai cire rigarta.
    "Bana so a shiga lokacin mu,  kinga ina da taro karfe shida na maraicen nan,  taimaka min da zuwa ɗaya kacal."  Ya faɗi yana kashe mata idanu.
    Cikin awa ɗaya suka kintsa jikinsu,  kuɗi ya bata dalloli bata ko iya kirgawa  ba,  ya fita tare da mata alkawarin rakiya zuwa Kasar Nurato da zasuyi da shugaban kasa.
    Wayarsa ya ɗauka don kiran amininsa  da yai ta kira sanda yake tare da luby.
"Kasan kuwa abinda kayi Sadisu,  wani irin rashin hankali ne ka aikata haka a matsayinka na Minista, to ga hotunan ka nan goye da wata yana ta yawo a kafafen sada zumunta..,"
Gummm....  ya bige kanshi saboda tsananin firgici yana kokarin mikewa, cikin sarkakakkiyar murya yace
ka bari dan Allah abokina.  Kasan shegiyar yarinyar  nan ce gimbi  ta sa na goya ta,  wallahi halin da nake ciki dole na bi abinda ta ke so, bara na fito meeting sai mu je wajen malam a rufe musu baki" 
Gaban shi bai dena faɗi ba duk da ya dan ji sauki da ya tuna malam bai taɓa saɓa Alkawari ba.
             ***
Samari ne su uku zaune a cikin wani kango da ke cikin makarantar gwamnati da ke hayin magarya a cikin birnin Dunotsi, Dukkansu sanye suke da kayan makaranta,  sai dai guda ɗaya ne kawai sanye da cikakken  kayan makaranta,  kallo ɗaya zaka musu kasan basu wuce shekara goma sha shida ba,  ledar  da bakin cikinsu ya ciko tsakankanin wasu bulo  ne ya baje musu...
     "Za mu yi yawo a gajimare"  ɗaya cikin su ya faɗi yana lailayi  kamar zai faɗi daga zaune.
   "Baaba!  Wato kaji daɗin garin, tun yaushe muke son ɗaura ka a network kaki,  ai ka daɗe cikin ɓata billahillazi"  faɗin wanda ya ɗauko ledar.
    "Manta dashi Rabs,  tsoron mai dattin hula yake, kasan wai shi ɗan malam"  Na ukun ya faɗi yana dariya.
     "kaga Messi! Duk iskanci na ba'a  taɓa min su in yi shiru,  ina da abin biyansu ne,  wallahi  mutum in ya raina ubansa  ya zo zai raina nawa zan masa rotsi ne"  Ya karasa yana ɗaukan kwalban mirinda da ke yashe a wajen.
   "Afuwan shukran inji Larabawa, kasan kai mera dosti ne inji Shahrukh khan"  Ya faɗi yana mika masa nannaɗaɗɗen takardar da suka kyasta ma ashana. 
   Nan sukai zaune suna zuka suna cin gyaɗa,  sun shagala don hankulansu ya soma gushewa su ka ji motsin mutum. Ɗaga  kan da za su yi su kayi  ido huɗu da shugaban makarantar.  Haba mai suka ci basu bashi ba,  nan suka ari na kare suka shige cikin yara da suka fito tara.
    Saukar ajiyar zuciya kawai suke yi.  Sai su kalli juna su fara dariya
"Kai Baaba Allah ya tarfawa garinmu nono".
Cewar Rabs kenan yana ciccije leɓe tare da lumshe idanu alamu mayen ya soma ɗaukarsa.
"Kaifa ɗan jagaliyane Rabs, saime dan wannan ɗan tsamungen (principle) ɗin shugaban makarantar ya gamu?"
. "Babu komai amma babbar illa ce kukewa kanku da iyayyenku."
Muryar wani matashi tsaransu ta karaɗe kunnuwansu. Suka juya tare da shekewa da dariya da alamu mammalakin fuskar sannanene a wajansu.
     "Ga masu samana najiyamu nan"
wani ɗan tsamurmuri mai kirar karan sigari ya furta a cikinsu yana ɗaga baki kamar bindin   saniya. Take wajan ya kwashe da shewa, ya kaɗa kai kawai ya bar musu wajan ransa yana takaicin gurbacewar tarbiyar abokan nasa.
"Na rasa yaushe Nuhu zai waye ya fara zaga gajimare Rabs? Koda yake ai irin su o'o ne sai ana nuna musu hanya zasu gane"
Ya karasa yana satar kallon abokin nasa.
"Dan uban mutum ya daina kumbiya-kumbiya ya fito filli ya bayyana abinda yake kasan ransa"
ya faɗa cikin ci da zuci. Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗar
"haba Baaba manta kawai kuzo mu shafce an wuce wajan"
"A to nidai an san halina yanzu na burma wuka, maganar fatar baki bata gamsheni, ni ba mace bace da zan zauna cecce kuce".
"Wo! Mazaje"
suka haɗa baki suna yi masa kirari.
                           ***
"Maza Lanto ki ɗauki tallar nan ki kaimin makarantar su Amarun mai gari, kinga anfi ciniki a can sossai da alamu ana gab da tashi"
"Mama ki dinga ɗorawa da wuri saboda nima nafi san inyi ciniki da yawa in samo kuɗin da zaki sani makarantar" lanto ta faɗi tana mai murmushi
"Kedai Lanto burinki makaranta, bama kya tunanin kuɗin da zamu tara dan fiddake kunyar aure komai karatu kamar ɗiyar Malam Liman?"
Cikin takaici ta karasa furucin tana karewa yarinyar kallo yar kimanin shekaru goma sha huɗu amma girman jikinta wasu ma sha bakwai suke kaita.
"Mama ki daina yimin zancen aure kaleni fa yar karama baki ga ɗiyar maigariba katuwa amma karatu take?"
"Gidanku Lanto rabani da wannan yahudancin wallahi sam ba a gidana ba a wannan KARNINMU da muke ciki abinci ma na son gaggarar bawa ki wani kwasomin kwataragin da zaifi karfina?"
Zumɓuro baki lanto tayi har  zata yi magana mamanta ta korata da kayan tallan,
"maza mai kan albarka ba kan kwantai ba nasan tsaf zaki said harma da kari yauwa mai farin jinin jeki ɗan dara maka giwar mata"
Lanto ta kyalkkyale da dariya ta yi waje.
HANYAR KASUWA....
Tafe take tana wake-wakenta a kan kwanar unguwar Madugu ta yi kiciɓus da Laraba tana ɗauke da alalanta fall botiki,
"Lanton Baba an fito?" faɗin Laraba cikin sakin fuska
"Eh! Na fito yau awarar taso yin dare mu hanzarta kar in yi kwantai danke kina da me yimiki juye"
"Kema dan kin ki yadda ne, amma tsaf za ayi miki juye haba Lanto kalleki fa kina kyau" ta faɗi tana nuna lanto daga sama har kasa.
Sanye take da batik riga da zani,  tayi ɗammara da bakin gyale. Duk da kwalliyan  da ta ɓata fuskanta da shi bai hana bayyana kyawunta ba.  Baka ce kyakkyawa ga diri, karancin shekarunta bai hana bayyana zubinta a matsayin wanda ake kira da coca cola.
"Taf! Wallahi Laraba ba zan iya shiga shagon wannan kazamin Buban ba bale in tsaya ya jagwal-gwalani akan zaimin juye, kullum Babana yana min nasiha kan ko hannu kar mu yadda maza su taɓa mana. Ke banda sauyin rayuwa da KARNINMU na wahala da muke ciki ai Babanmu bazai barmu talle ba" lanto ta faɗi tana mai murtuke fuska.
"Ashe da Limammiya nake makotaka ban saniba?"Muryar Laraba ta katsewa Lanto maganganunta.
Ta cigaba
"wallahi Lanto ki sake ɗamara domin a wannan KARNIN NAMU bani gishiri in baka manda ake!". Ta karashe furucin taka buga cinya dai-dai lokacin suka karasa cikin kasuwar.
CIKIN KASUWA......
®
✏📖
*FIKRA WRITER'S ASSOCIATION*

No comments:

Post a Comment