💔💘 *SAKACI* 💘💔
2⃣9⃣
© *Fatima A Garba*
D'agata yayi ajikinshi gami da cewa "kibar damun kanki Farida yi musu addu'a, ki kwanta sai da safe"
Wani abu ne ya tsaya mata a mak'ogwaro wanda har ta kasa yin magana.
Wai me yake faruwa da ita ne, "wayyo nashiga ukuna" fad'a ta ke cikin kururuwa.
Ga baki d'aya duniyar ta ma ta zafi wani irin shauk'i da kasala ne yake d'ibanta, ita kam da badan ta najin tsoron Allah ba, babu abinda zai hanata fita yawon bariki, ita kad'ai tasan yadda ta keji.
Bacci ya k'aurace wa idanunta, ta rasa tudun dafawa, ta na buk'atar mafita.
Toilet ta shiga da zummar ta yi wanka gami da d'auro alwala ta kai kukanta ga mahaliccinta sai dai ta na shiga ruwan zafi ta fara hamma alamar bacci.
Alwalar da bata yi ba kenan ta dawo ta kwanta.
Washegari haka ta wuni da ciwon kai, kuma ta kasa ta6uka komai a wurin aiki har sai dai Jidda ta lura kawarta ta na cikin damuwa.
Bayan aiki ya mata sauk'i ta sameta ta na tambayarta abinda yake damunta, ba taso ta sanar da ita, sai dai ta na bukatar mafita saboda hakurinta ya gama k'arewa.
"Jidda ban san me yake damun mu ba nida Dr bansani ba jidda" ta k'arshe hawaye na zuba daga idanuwanta.
Cikin rashin fahimta Jidda ta ce " kawata bangane me kike nufi ba kiyi min gwari-gwari"
"Kinsan na fad'a miki zuwan mu Jos komai ya dai-daita ko" Jidda ta ce "tabbas anyi haka, toh yanzu wani abun ne ya sa ke faruwa"
"Jidda, Dr kwata-kwata yak'i had'a gado dani, ni kuma nakasa hakuri, ni ban san me yake faruwa ba, wallahi ni nasan yadda nakeji, har takai yanzu idan naga namiji a waje inaji tamkar naje na rungumeshi"
"Na rasa gane kan wannan abun wallahi" Jidda ta fad'a cike da tausayi.
"Wallahi bariki zan shiga" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Farida karna sakejin wannan kalmar a bakinki, karki sake aikata wani sa6on da yafi na baya girma"
Farida tace "Jidda ya zanyi wallahi hakurina ya k'are ina bukatarshi, na rasa me yake damuna, kikaini asibitin mahaukata a dubani Jidda"
Wani irin tausayin kawarta ne ya tsirga mata, wannan wace irin jaraba ce take tunkaro su, asaninta da Farida bata ta6a yi mata maganar da ta dangacin hakan ba, balle ta yi tunanin ta na daga cikin jinsin da suke da yawan buk'ata.
Cikin sanyi murya Jidda tace "kawata karna sakejin kin fad'i wannan maganar, dole mu samu mafita amma kafin nan yau kwananki ne ko na Mariya?"
Farida tace "na Mariya ne" Jidda tace "yanzu sai zuwa jibi kenan zai dawo gareki ko"
"Eh" Farida tace, Jidda ta k'ara da cewa "yanzu abinda nakeso dake shi ne ki yi azumi a wannan kwana biyun kinga na farko ga lada sannan zai rage miki yadda kike ji"
Cike da damuwa Farida tace "wallahi Jidda yanzu bana iya yin azumi bansan ya zanyi a watan Ramadan ba, mubar wannan maganar kawo wata shawara"
"Farida abun yakai haka" Jidda ta fad'a cike da mamakin kawarta, domin asanin da ta yiwa Farida ada mace ce mai rik'o da ibada, yanzu me ke faruwa da kawarta ne.
"Toh karki damu yanzu dai kiyi hakuri zuwa ranar da girki zai dawo hannunki, zo na fad'a miki yadda zakiyi na tabbata Dr bazai ta6a tsira da wannan tarkon ba"
**** ****
A kwana biyun nan idan ka kalli masoya biyun nan zaka ga suna cikin damuwa, baram ma Farida da ta rame ta dawo wata iri da ita.
Lokaci guda ta dawo mara walwala.
Ranar da ta kar6i girki bayan ta tashi daga aiki ta aika mai sak'o ta waya tana sanar dashi zata je ta duba Baba.
Kasancewar kwana biyu ta kasa samunshi a waya, kuma idan ta kira number Aunty sai tace mata baya kusa, hankalinta sam yaki kwanciya.
Cewa yayi ta jirashi yazo suje tare, ba'a jima ba kuwa yazo, don haka a motarshi suka tafi tabar tata a asibitin.
Koda sukaje kofar gidan ya ajiyeta akan idan yazo d'aukanta bayan magriba ya shiga su gaisa da su Baba.
Da sallama ta shiga gidan amma ba kowa a falo, kitchen ta fara dubawa, Babanta ta gani ya nad'e hannun rigarshi yana zuba abinci a wormer abun ya bata mamaki.
"A'a Farida kece da yamman nan" Baba ya fad'a fuska a sa ke.
"Eh Baba, kai ne da kanka a kitchen" " eh wallahi Auntyn taki ce ba lafiya shi ne nake temakawa"
Cikin damuwa Farida tace "toh Baba kai da ba lafiya ba ina Iya ta ke"
Murmushi yayi gami da cewa " Iya ta tafi garinsu, kingan ni nan jikina yayi sauki sosai"
"Baba amma mai yasa ba'a nemo wata ba" farida ta fad'a gami da kar6an cokalin kwasar abincin.
"Farida naga kin rame, ko akwai abinda ke damunki ne" ya tambayeta ba ta re da ya bata ansar ta ta tambayar ba.
"Ba komai Baba, gaskiya yakamata asamo wata, dan wannan aiki ai banaka bane" farida ta fad'a cikin tausasawa.
"A'a Farida yaushe kika shigo" Aunty ce ta fad'a yayin da ta shigo kitchen d'in, "ban jima da shugowa ba" ta bata ansa.
Ita sam bata ga alamar rashin lafiya a tare da ita ba, Allah sarki Baba yanzu yana k'ok'arin kyautatawa iyalanshi, bata mantawa lokacin ta na karama ta na yawan ganin Alhaji na taya Ummi dafa abinci.
Amma ita yanzu sanin irin yanayin da yake ciki baza taso ya wahala ba.
**** ****
Bayan magriba Dr yazo d'aukwanta, kayan arzik'i sosai ya kawo gidan, sosai ta yi farinciki, wannan ne ya goge kashi 80% na haushinsa da ta keji.
Kafin su tafi Aunty ta sake kawo mata wani jik'o akan tasha.
"Aunty nikam abar wannan abun" " akan me za'a bari Farida, wayace miki yanzu ana zama" Aunty ta fad'a.
"Aunty nikam abarshi kawai ba yanzu ba, wallahi damuna yake nikuma ba wani abinda ke shiga tsakanin mu"
Murmushi Aunty ta yi gami da cewa" oh yaro man kaza, kar6i nan wannan shi zai juyo da hankalinshi zuwa gareki"
Ba dan taso ba haka ta k'ar6a ta shanye, amma tunkafin tabar gidan ta ke da tasanin sha.
Kwanciyar hankalinta d'aya irin yadda taga yana mata a motar nan, nan ne tasan yaufa ba ita kad'ai bace abun ya motsa.
Suna zuwa gida ta bud'e jakarta cikin wani irin salo tace "ka ganka ko"
"Me na yi " ya fad'a yana kashe mata ido, "ba kai bane kasa na manta key d'akina a asibiti cikin motata"
"Yau awaje za ki kwana kenan" "ni gaskiya a'a kazo mu koma na d'auko" ta fad'a cikin shagwa6a.
"No ba inda zan koma,kuma kema bazaki koma ba" ya sake fad'a, bubbuga kafarta take gami da cuno baki alamar shagwa6a.
Fita yayi ya zagaya ta inda ta ke. Batayi aune ba taji ya d'auketa tamkar yarinya k'arama, sa ke lafewa ta yi a k'irjinshi tana shak'ar kamshin shi.
"Farida na gaskiya ba haka ake ba, you're a doctor kina ba mutane shawara akan su rage k'iba but ke kinata hawa"
Turo baki ta yi gami da cewa " Allah ni sharri kakemin, ba haka bane" murmushi yayi ba ta re da ya sa ke magana ba.
Bai ajiyeta a ko ina ba sai akan gadonshi ya fad'i yana mai da nunfashi waishi ya gaji, muntsininshi ta yi.
"Faridana mugunta ne kuma, oya tashi kije kiyi wanka daganan ki d'auro alwala"
"Ni Allah nagaji sai da safe zanyi" ta fad'a cikin kasala, "ko kitashi kije kiyi kona d'auko ruwan cikin fridge na miki dashi"
Tashi ta yi tana dariya.
Bayan sun idar da sallah ita da kanta ta fad'a jikinshi, d'aukanta yayi ya d'aurata akan gadon.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment