Monday, 19 December 2016

Yar Ajinmu 3rd

'YAR AJINMU CE

PART 7 to 8

"Zaidu Ibrahim Barmo MrZaid"


7==
Tun sa'adda nabar kofar gidansu
bintu ban sake dawowa ko
unguwarsu ba, haka ma ban kara
samun labarin wanda inda yasan
inda suke ba, shikenan na tattara
tunaninsu na aje gefe na fuskanci
rayuwa. Bamu daðe garin abuja ba
muka koma kaduna da zama nida
dukkan 'yan gidanmu Mahaifina ya
samu aiki a wani kamfanin Siminti
yana aiki, a hankali A hankali Allah ya
daukaka sana'ar har ya samu motar
kansa ta kamfanin DANGOTE
karkashin jagorancin SADA IBN
SULEIMAN USMAN Shine mai gidansa.
Shikenan mu ma muka dawo
munajin dadin rayuwarmu bamuda
matsalar komai, kuma a wannan
lokacin ne jarabawarmu ta fito waec
da neco naci duka, wannan yasa anan
take naci gaba da karatu na a
makarantar ABU Zaria akan fannin
Girke-Girke food and nutrition da
farko ban so Course ðin ba amma
mahaifina ya taushe ni akan na tsaya
a hakan idan na gama NCE Sai na
Dawo abinda nake so. Da wannan
shawarar nayi amfani naci gaba da
karatuna ABU ZARIA SAMARU Kamar
yadda wasu suke kiranta, Shekarata
uku acan na kammala ban fuskanci
wani kalubale ba game da karatuna.
Bayan na gama ABU ZARIA Ne na fito
da takardu masu kyau Ban dade gida
ba na koma makarantar BAYERO
UNIVERSITY A BIRNIN KANO inda na
karanci Language Hausa/English
Wannan shine matakin da ya taimaka
man sosai na gane lallai karantar
language ba karamin dace bane,
musamman ma da ya kasance
Yarukan gida ne nijeriya. Can ðin ma
shekarata uku na kammala shikenan
na dawo gida ina taya mahaifina aiki
kafin na samu aiki bayan services da
nayi, Yau ðin nan da na fito yawon
shakatawa cikin gari ne, na haðu da
bintu rabon da nayi yawo kamar haka
tun shekaru hudu baya, sa'adda na
muka fito nida wasu abokaina da
sukazo wajena ziyara ABUBAKAR AUYO
da SANI HAMZA FUNTUA wadanda
makaranta ce ta hada mu da juna.

8===
Ta matso kusa dani lokacin dana
karasa tunanin da nakeyi idanuwanta
sharkaf da hawaye ta kalleni tace,
Jamilu rayuwa ta sauya man kaga
yadda na koma ko? Kamar bazan
kalleta ba saboda tausayi amma nayi
ta maza nace nagani bintu ta yaya
garin haka ya faru? Ta dukar da kanta
kasa tace, labarin bamai dadin ji
bane babu komai a ciki sai tarin
bakin ciki da jimami! Bana son na
tuna labarin nan kwata- kwata
jamilu, ta dukar da kanta idanuwanta
sun kaða sunyi jawur tace, Idan zan
baka labarin bayan rabuwa ya zama
dole na koma baya sa'adda kazo
gidanmu baka tarar damu ba, Nasan
kazo shiyasa nace maka haka, Na
daga kaina sama alamar hakane,
gaba daya hankalina na tattara na aje
shi waje daya ina dubanta. Transfer
ce ta gaggawa akai ma mahaifina
wanda akace ana so daga ranar zuwa
washe gari ya hada kayansa za'a turo
motar gwamnati daukarmu, Tun
ranar nake son zuwanka muyi
bankwana amma baka zo ba!. Washe
gari tunda safe mukabar garin washe
garin ranar gama makarantarmu
kenan, dalilin rashin ganinmu kenan
Banida waya balantana na kiraka har
wasika na rubuta naba da a baka
amma nasan baka same ta ba daka
neme mu. Rayuwarmu a kaduna tai
mana daði sosai kamar yadda muke a
abuja bamuda matsalar komai,
rannan sai mahaifinmu ya samu
mamarmu akan wani case da suke
gabatarwa a kotu akan wata yarinya
da'a kai ma raping kuma ake son a
danne gaskiya, inda wani babban
mutum ya kawo ma mahaifinmu kudi
akan yana son a bar maganar kwata-
kwata, ma'ana ya kare marar gaskiya.
Nan mahaifina yaki amincewa har ya
dauki alwashin idan aka koma kotu
zama na gaba zai fallasa komai,
Wannan ne ta jefa mahaifiyarmu
cikin tashin hankali domin tasan
halin mahaifinmu idan ya aikata
wannan abun tabbas wani abu zai
biyo baya. Haka kau akayi ana zuwa
kotu zama na gaba mahaifina ya
bayyana gaskiya shikenan zaman
kotu ya kare aka ðaure dan gidan mai
kudin nan a gidan maza. Tana
kawowa nan ta fashe da kuka tace,
Labarin da ya biyo baya bamai dadin
ji bane, Na shiga uku ina zansa
rayuwata.

No comments:

Post a Comment