💔💘 *SAKACI* 💘💔
2⃣7⃣
© *Fatima A Garba*
Ya na fitowa daga masallaci, kai tsaye d'akin kwanan Ummi ya wuce, ita kawai yake so yasa a ido, sam jiya bacci ya k'auracewa idanunshi, wani irin kewarta ya keji.
Kwance ta ke a kan gadon ta na bacci, duk rabin cinyoyinta a waje kasancewar rigar baccin ta tattare, wani irin shauk'in kaunarta ne ya ke d'ibanshi, a ta ke ya saukar mai da wata kasala.
Kujerar dressing mirrow ya janyo zuwa bakin gadon kafin kuma ya zauna, tallafe ha6arshi yayi da hannu biyu.
Kallonta ya ke tamkar idan ya d'auke idanuwanshi zata 6ace, ji yake tamkar yaje ya kamata ya rungume abarsa, cikin wata irin murya mai cike da shauk'i ya ce.
"Farida ina sonki, ina tsananin k'aunarki ba zan iya rabuwa da ke ba matata, domin kece farincikina"
Cikin bacci ta ke tajiyo maganganu, a hankali ta bud'e idanunta wanda suka sauka akanshi.
Da sauri ta janyo zani gami da rufe jikinta har ma da kanta, ya jima ya na zaune kafin daga bisani ya mik'e had'e da cewa.
"Idan kin gama ki sa meni a d'akina" daga haka ya juya ya tafi cikin tafiyarshi ta k'asaita.
**** ****
Sai da ta yi wanka, wannan karan ma ba ta yi wani kwalliya ba gudun kar a fad'a mata maganganu marasa dad'i, sai da ta feshe jikinta da turare kafin ta fita.
Kai tsaye d'akinshi ta nufa, sallama ta yi, sai da ya bata izini kafin ta shiga, ba ta yi k'ok'arin zama ba domin yau kam baza ta iya jure munanan kalamansa.
Sai dai kuma yanayin da ta ganshi a ciki ya bata mamaki tamkar ba Yayanta ba tagumi yayi da hannuwanshi biyu.
Ya d'an jima ahaka kafin ya d'ago kai ya kalleta, cikin sanyin murya ya ce "Bismillah zauna mana inaso muyi magana ne"
Ba ta re da gaddama ba ta zauna, amma shuru ne ya sa ke biyo baya, ita kam tana mamakinshi mutun tamkar magana na bashi wuya da kyar yake magana, itafa ta fara jin yunwa kuma ma bata so Ummi ta fito bata ganta ba.
"Faridaaa nasan na k'untata miki ba kad'an ba na kasance mutun mara tausayi agareki, ki yafe min"
Ya d'anyi shuru, kafin daga bisani ya cigaba.
"Zuciyata ta kasa mance ranar da naga Faridana da na jima ina tattali a k'irjin wani kazami, Farida why, mai yasa, na jima ina tattalinki, duk wani kariya ina baki, me ya rud'eki da wannan kazamin, wanda har ta kai kina jifata da mugayen kalamai akanshi Farida"
"Dr zargina kakeyi, Mai yasa zaka yi tunanin zan sake yarda wani d'a namijin ya sa ke rud'ana ya 6ata min rayuwa, kasan yadda nake ji a zuciyata kuwa"
Sha re hawayen da ya zubo ma ta ta yi gami da cigaba.
"Wallahi na rantse maka da Allah babu abinda ya ta6a shiga tsakanina da shi, wannan ranar itace rana ta farko da ya fara kamani, kuma a lokacin ina k'ok'arin kwatar kaina kazo, sannan ina rok'onka gafara kayi hakuri da irin munanan kalaman da na fad'a maka"
"No Farida ni nafi cutar dake, na musguna miki na hanaki walwala a karshe na rabaki da masoyinki ta hanyar auranki, ki yafemin, sannan ki bani lokaci insha Allahu komai zai dai-daita"
"Kin amince za ki ci gaba da zaman aure da ni Farida?"
Shuru ta yi gami da sunkuyar da kanta.
A zahirin gaskiya bata da za6i, idan har tace lalle ta na so ta rabu da Dr, toh wazai aureta, sannan kuma ta yi musu budulci.
Sannan bata kyauta mai ba, shi da ya yarda ya aureta duk da irin nakasar da ke ta re da ita, bai gujeta ba, dole ne ta jure duk irin abinda za ta fuskanta arayuwar aurenta, tabbas sun mata karamci.
"Please Farida karki ce a'a, karki guji yayanki, ki amince za ki bini ki cigaba da zaman aure da ni kinji" Dr ya katse ma ta tunani.
Tashi ta yi da zummar barin d'akin, cikin hanzari ya tashi ya sha gabanta gami da rik'e hannayenta a ta ke suka ji wani irin shock, k'ok'arin zame hannunta ta ke daga nashi, amma ya sa ke rikewa gam, gami da cewa.
"Noo karki tafi ba ta re da kin ban ansa ba, nasan bakya so na amma please ki bani lokaci"
Wannan magana tashi ji ta ke tamkar a mafarki, wai yau yayanta ne yake mata magiya akan karta rabu dashi, "Allah nagode maka" abinda ta ke fad'a kenan azuciyarta.
"Za ki cigaba da zama dani" ya tambayeta, d'aga mai kai ta yi alamar "eh" gami da barin d'akin da gudu domin bata so ya cigaba da bata kunya.
Da sauri ta fito daga d'akin, da Ummi ta ci karo, kunya ne ya rufeta, a take ta hau kame-kame, murmushi Ummi ta yi gami da barin wurin.
A zuciyarta ta na yan bad'on yara, suna so suna kaiwa kasuwa.
Ranar lahadi sukayi shirin komawa, sosai Ummi ta yi musu fad'a gami da nasiha mai shiga jiki.
Ummi ta k'ara da cewa "yanzu zakuje ku d'auki Mariya Ku wuce ko" cike da rashin jin dadi Dr ya ce
"Ummi wallahi bansan me yake damun yarinyar nan ba, na fad'a mata lokacin da zamu tafi akan tazo kuyi sallama sai mu wuce amma kina ganin har yanzu, tana wasa dani, ta biyo motar haya kuwa"
Ummi tace "a'a baza ayi haka ba kaga komai d'an hakuri ne, kuma kai babba ne karka biye ma ta, idan zaku wuce kaje ka d'auketa karka ce ma ta komai, nan gaba ko ance ta yi hakan baza ta yi ba"
Daga gidan Ummi kai tsaye gidan Auntyn Mariya sukaje Dr kam bai shiga ba waya ya mata ta fito.
Ta na zuwa ta bud'e kofar gaba wurin da Farida ta ke zaune gami da cewa Farida
"malama fita anan kin dai san wurin zama na ne"
Dr ne ya fito ya zagayo inda ta ke gami da cewa "haba Mariya ba kiga nan kan hanya bane, please karki jawo mana idon mutane tunda da zamu zo kekika zauna a gaba yanzu kiyi hakuri ki zauna a bayan please"
Cike da tsiwa ta ce "wallahi wannan yarinyar ba ta isa na bar mata wurin zama na ba, akwace min miji sannan gaban ma ahana ni zama"
Tabbas ta fara kai shi bango, sam baya son ya ma ta abun da zata ga kamar ya fifita Farida akanta, shi baiga wani abun fad'a akan zaman gaba ba.
Lek'awa yayi ta widowo motar ya ce wa Farida "Faridana za kiyi hakuri ki bar mata gaba ki koma baya, amma karki ga hakan a matsayin tursasawa kiyi abinda zuciyarki ta amince da shi"
Murmushi ta yi gami da cewa "zan koma yayana ai da bayan da gaban duk d'aya ne"
Wannan abu ya 6atawa Mariya rai, don haka koda suka fara tafiyar ma habaici ta diga yi wanda duk Farida ta ke jefawa magana, Dr sam bai gane mai ta ke nufi ba amma ita Farida ta gane, banza ta bawa ajiyarta har suka iso bauchi .
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment