Sunday, 25 December 2016

Sakaci 33

           💔💘 *SAKACI* 💘💔

                     3⃣3⃣

© *Fatima A Garba*.

"Please ka sanar dani Dr, ban gane ba" abinda Dr Umar yake fad'a kenan.

Dr Shamsudeen yace "Matarka nada ciki, Dr Umar, matarka nada juna biyu"

Kamar a mafarki yakejin maganar, cikin wani irin yanayi Dr Umar yace "anya kasan abinda kake fad'a kuwa, na fad'a maka matsalar matata, amma naji kana fad'a min abinda hankalina baze d'auka ba"

Sa ke kamo hannunshi yayi akaro na biyu yana mai nuni da na'urar da ake scanny kafin kuma yace "zoka gani, ba karya nake maka ba Dr umar, bama haka da kai"

Tabbas abinda ya fad'a hakan ne, gudan jininsa yake gani a marar matarshi, tabbas shi ne, wata biyar da kwana goma gashi har abun ya fara motsi, wannan ya nuna a watan da ya fara tarawa da ita a watan Allah ya azurtasu.

" *Allahu Akbar* " shi d'inma yake fad'a, kafin kuma yafad'i k'asa yana sujjada ga mahaliccinsa.

Farida suman kwance ta yi, tabbas da bata gani da idanunta ba da zata k'aryata, lalle ni'imar Allah ta buwaya, godiya ta ke ga mahiliccinta ta na hawaya, lalle Allah ya mata kyautar da ba wanda ya isa ya yayi irinta.

Ya azurtata alokacin da ta fitar da rai, "Allah na gode maka" abinda ta ke fad'a kenan ba adadi.

Kan kace meye Dr yayi waya yanata sanar da jama'a, ana fad'awa Ummi itama fad'uwa k'asa ta yi ta na sujja domin godiya ga ubangiji.

Shi kuwa Baba baza ka iya tan-tance tsakanin shi da Dr wanda yafi farinciki ba.

Tabbas duk wani masoyinsu sai ya tayasu murna, Alhaji ne yayiwa Ummi biza akan ta taho India domin kulawa da Farida.

Kasancewar likita yace mahaifarta ba karfi don haka bazata juri zirga-zirga ba, sa'annan idan lokacin haihuwarta yayi baza abari ta yi nak'uda ba za'a mata aikin acire abinda ke cikin.

Dakyar Dr ya hakura ya dawo Nigeria bakin aikinsa, sai da Ummi ta nuna 6acin ranta sosai tukunna ya tafi, amma kuma tun da ya tafi kullun yana ta re da Faridarshi a waya kuma duk bayan wata biyu yake zuwa.

Dr yayi k'ok'arin kama musu hotel amma Dr Shamsudeen yace yabari akwai d'akuna a gidanshi su zauna, mutumin sam bai mance irin karamci da Dr yamai ba.

Yadda Mariya taga ana d'okin cikin taso ta sawa kanta damuwa, toh amma daga baya sai ta cire komai aranta ganin ba dainawa za'ayi ba, sannan kuma hakan da sukeyi bai tauyeta da komai ba kona k'ank'anin lokaci.

         ****            ****

Ummi ce da Dr sun saka Farida a tsakiya sai rarrashinta sukeyi, ita kuma sai kuka ta ke wai ta na tsoro.

Haka dai dak'yar suka lalla6ata.

Allah mai kyauta da kari, Allah mai azurta wanda yaso alokacin da yaso.

Anfito da Farida lafiya ta re da yaranta y'anbiyu mata, yara kam sai godiyar Allah, idan kaga Dr da Ummi aranar zaka d'auka a ranar aka fara yimusu haihuwa.

Haka fannin Baba, bayyana irin farincikin da ya tsinci kanshi bazai yuwu ba amma kam yayi kuka yayi dariya, Allah kenan.

                  *******

Ummi na zaune ta na ninke kayan Ummi da Mama (sunan 'yan biyun kenan) kasancewar a washegari zasu dawo gida Nigeria.

Dr baya nan yana can yana cuku-cuku.

"Farida kinga ribar hakuri ko, Allah ya jarrabeki da jarabawa kala-kala kinyi hakuri ba ta re da kin butulce ba, alokacin da akace bazaki ta6a haihuwa ba nasan kin shiga wani irin hali, amma kika jure "

"Sannan ya jarrabeki da jinkiri, daga 'karshe kika fara samun manema amma daga 'karshe sai su gujeki"

"Wanda kika amince dashi amma ana gobe d'aurin auranku suka fasa, nan ma kin jure ba ta re da kin butulce ba, haka a zamanta kewar auranki"

"Tabbas ke d'in me juriyace, da ma matan da suka samu kansu a hali na jarrabawa zasu zama masu juriya kamarki da tabbas zasu zamto masu sa'a"

"Domin ke kinga riba kuma riba ma har biyu kenan, kinada lada awurin Allah gashi kuma aduniya ya azurtaki da miji irin wanda ake cewa mijin marainiya, akarshe kuma ya azurtaki da yara biyu alokaci guda, Allah ya albarkaci rayuwarki Farida"

Zuwa ta yi ta tsuguna agaban Ummi ta na hawaye tace

"Ummi kun bada gudunmawa mai yawa arayuwata, wallahi bani da abinda zan saka muku dashi sai addu'a, Ummina nagode Allah...."

"Shhhhhh" Ummi tace mata, kafin kuma tace "bana son wannan hawayan naki, yanzu lokacinsa yawuce Farida, sannan ki rike godiyarki bana so"

Rungume Ummi ta yi ta na fitar da hawayen farinciki, rayuwa kenan.

                   *****

Zaune suke a reception 'din filin jirgin sama, suna jiran lokaci ya cika akirasu, Ummi na rik'e da Mama, Dr kuma na rungume da Ummita a hannunshi na hagu, hannunshi na dama kuwa yana rungume da Faridanshi .

Mutane biyu ne suka nufo inda suke, yar dattijuwan mace da kuma wani a gefenta da alama d'anta ne.

"Ina wuninku" cewar mutane biyun, Ummi ce ta iya ansawa itakuwa Farida mamaki ya hanata magana, tabbas Ahmad idanunta yake gani.

Dr kanshi mamaki ya hanashi magana.

"Farida karde wannan jariran naki ne" "Nata ne yau satinsu uku" Ummi ta bashi ansa.

"Amma da kince likitoci sun ce baza ki sa ke haihuwa ba, ya akayin hakan ya faru" wannan karan Dr ne yayi magana da cewa "Allah"

Juyawa yayi ga dattijuwan nan yace "Hajiya kin gani ko, Allah ya azurta Farida da haihuwa ni d'in da kika hana na aureta har yanzu shuru kingani ko"

Wannan dattijuwar da Ahmad ya kira da Hajiya ita tazo kusa da Farida had'e da kama hannunta ta na cewa

"kiyafe min, na hana ya aureki saboda ina tunanin bazaki ta6a haifamin jikoki ba ashe na yi kuskure, Allah shi ne mai azurtawa, ga Ahmad nan har yanzu shuru, ko 6atan wata matarshi bata ta6a yiba kuma angwada lafiyanta kalau, kiyafemin don Allah"

"Ba komai na yafemuku Allah ya yafemana baki d'aya" cewar Farida

Karshe sukayi rabuwar arzik'i gami da jinjina halin karamci da yawan yafiya irin na Farida.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a tsakanin masoyan nan cikin farinciki da kwanciyar hankali.

        *ALHAMDULILLAH*

Anan na kawo 'karshen wannan littafi na *SAKACI* kuskuren da na yi aciki ina neman gafarar Allah.

Gareku makaranta ina nemar afuwanku abisa tak'aita rubutun da na yi wanda wasu abubuwa ban fito dasu ba.

Wannan ya faru ne bisa ga 'karancin lokacin da na samu kaina aciki, sannan nasan makaranta zasu ce mai yasa ban nuna makomar "Hassan* ba, toh agaskiya *Hassan* da masu hali irin nashi Allah ne yasan makomarsu da irin azabar da ya tanadar musu.

Ba abinda zance muku sai Nagode, Nagode, *I LOVE YOU ALL* .

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment