Sunday, 25 December 2016

Sakaci 24

          💔💘 *SAKACI* 💘💔

                      2⃣4⃣

© *Fatima A Garba*

Aikuwa da safe da ta bud'e fridge d'in ba farfesu ba alamarsa, tasan ba kowa ne ya d'auka ba sai Dr.

Toh kuma ita ai har zuwan wannan lokacin bata bud'e kofa ba, toh ta yaya ya shigo har ya d'auka.

"yana da wani key ne a hannunshi" zuciyarta ta ba ta ansa, haka ta cigaba da aikace-aikacents da mamakin Dr fal cikin zuciyarta.

Tun daga wannan ranar Dr bai sake yarda sun had'u ba, sai dai ya tura ma ta sak'o ta waya ya tambayeta lafiyarta.

Idan kuwa ranar girkinta ne, toh nan fa zai shiga kitchen ya samawa kansa abin ta6awa.

Lura da ta yi yana zuwa cin abincin cikin dare bayan ta kwanta yasa ita kuma ta dage da dafa duk wani abinci da ta tabbatar yana so, ta ajiye mai.

                   ****

Yau ne hutun ta ya k'are, don haka murna ta keyi sosai, dama ta gaji da zaman wuri d'aya, ko ba komai yau zata samu canjin wuri.

Ta sha mamaki lokacin da Dr ya tura mata sak'o ta waya yana tambayarta k'arfe nawa zata tafi aiki, domin ta yi tunanin ya manta.

Karfe takwas ya turo da driver yazo ya d'auke ta.

Farida mace ce da kowa yake sonta saboda kyawun halayenta, da son mutane gami da kyauta, shiyasa duk inda ta shiga a fad'in asibitin nan ake martabata da bata girma.

                    ****

Ta na daf da shiga ICU ta hangota, cike da farinciki Dr Jidda ta k'araso wurinta, rumgume juna sukayi cikin kewa.

Dr Jidda ce ta saketa gami da d'an ja baya kad'an, rike baki ta yi alamar mamaki kafin kuma ta ce.

"Kawata kinganki yadda kikayi fresh kuwa, fatarki sai wani shek'i ta keyi, gaskiya aure ya k'ar6eki kawata kuma da alama ubangidan nawa ya iya kiyo"

Ta6e baki Farida ta yi gami da cewa "nifa banga wani dad'i a wannan auren ba Jidda"

"Wai kina nufin Dr har yanzu bai bada kai ba" Jidda ta fad'a.

" Hmm, idan ya ta6a kwana d'aki d'aya dani kenan, nifa....."

Ganinshi a gabansu yasa maganar ta tsaya a mak'oshints ba ta re da ta iya k'arasawa ba, cikin k'ank'anin lokaci ta shiga rud'ani.

Bai sa ke kallon inda suke ba, yayi wucewarshi, cikinsu ba wacce ta iya magana, sai daga bisani ne Jidda ta ce.

"Alllah dai yasa bai ji abinda muke fad'a ba"

"Ma had'u anjima Jidda" abinda Farida ta iya fad'a kenan, kafin kuma suyiwa juna sallama ko wacce ta kama gabanta.

                   ****

Yau gaba d'aya ta yi wuninta ne cikin fargaba, ganin har lokacin tashi daga aikinta yayi har wannan lokacin bata samu kiran Dr ba yasa hankalinta ya d'an kwanta, kad'an.

Indomie ne a gabanta ta naci lokaci zuwa lokaci hankalinta yana kan film d'in da ta ke kallon a TV, Sallama yayi had'e da shugowa, kasancewar hankalinta na kan film d'in da ta ke kallo yasa bata ji sallamar da yayi ba, balle kuma ta san da shigowar shi.

Gyaran muryarshi ce ta ankarar da ita, a ta ke zuciyarta ta bada ras, lokaci guda kuwa ta tsahi tsaye cikin fargaba, wani kallo ya ke jifanta da shi, kallo ne wanda ta riga tasan na 6acin rai ne.

Lokaci guda fargabanta ya dad'u fiye da baya, k'arasawa yayi ya zauna akan kujera.

Cikin yanayi na 6acin rai ya ce "ai bansan rashin mutuncinki ya zarce tunanina ba, ban kuma san cewa Islamiyar da najima ina kaiki na dawo dake duk runtsi bana miki wasa da ita ashe duk abanza ne, babu abinda kike fahimta"

Wani irin murd'awa cikinta yayi har saida taji tamkar gudawa zai fito, "magana nake miki" ya fad'a cikin tsawa.

Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da ta tanka mai ba.

" Na gode kinje kin tona min asiri awaje, tunda ke baki san laifin tona sirrin aure ba"

"Ba ma haka ba, ke don Allah ba abin kunya ba ne a gareki ace auren fari amma kinje kina fad'awa jama'a mijinki ba ya had'a gado da ke"

"Wallahi ban ta6a ganin jarababbiyar mace irinki ba, wacce ba kunya a idanunta"

Ya cigaba da cewa.

"Toh inaso ki bud'e kunnuwanki kiji ni da kyau, bazan ta6a iya had'a jiki da ke ba, ko kina tunanin zan manta da irin kazantar da kuka aikata ke da wancan kazamin da kika gama cimun mutunci akanshi ne"

"Allah ya sauwak'a, turrr da halinki wallahi"

Wani kuka mai zafi ta fashe da shi, cikin wani irin yanayi Farida ta ce! 

"mai yasa ka aureni"

Cike da masifa ya ce "shak'eni sai na baki ansa, kuma zan miki gargad'i idan kin d'auka kinsamawa kanki lafiya, wallahi kika sake zuwa kika bud'e min sirrin gidana a waje, saina nuna miki other side of me"

Ya na gama fad'an haka yasa kanshi yayi ficewarshi, kwanciya Farida ta yi ta na kuka mai ban tausayi gami da cewa.

Mama aure bai kar6emu ba, nima kinga yadda rayuwata ta dawo, duniyar ta yimin zafi Mama, nima nasan nakusan zuwa gareki, Ya Umar ba masoyinmu ba ne, Mama ya yaudaremu ne"

Kuka sosai ta keyi ta cigaba da surutai tamkar wacce ta zare.

Yana tsaye a k'ofar falonta ya na sauraran maganganunta, wani irin zafi zuciyarshi ta keyi, ya rasa dalilin da yasa ya kasa manta laifin da Faridanshi ta aikata mai.

Dukan bakinshi ya ke da hannunshi ya na cewa "banyi ba mai yasa na kasance mai k'untatawa wacce nafi so fiye da rayuwata, why why?"

Juyawa yayi da nufin yaje ya rungumeta ya rarrasheta, amma lokaci guda hoton ta ya hango ta na rungume a jikin Adamu, a take zuciyarshi ta yi mai zafi, juyawa yayi gami da tafiya shashinsa.

Ko da ya koma shashinsa rasa abinda yake mai dad'i yayi, wani irin tausayinta ya keji, mafita yake nema amma sam k'wak'alwarshi ta kasa hasko mai komai.

Yana bukatar ya mance wannan rana daga cikin tarihin rayuwarsu amma ya kasa, to wai shi ya zai yi ne, wa zai tunkara " *ALLAH* " zuciyarshi ta bashi ansa.

Toilet ya shiga gami da d'auro alwala, sai dai lokacin da ya idar da sallah sai ya rasa wace addu'a zaiyi me ma zai rok'i Allah, komai ya tsaya mai, k'arshe hakura kawai yayi.

                     ***   ***

Farida ma kwana ta yi ta na kuka gami da yiwa mutumin da ya 6ata ma ta rayuwarta Allah ya isa, domin tasan da badan hakan ba, ba wani namijin da ya isa ya zageta, tabbas wata shari'ar sai a lahira.

Ranar dai duk cikinsu ba wanda ya runtsa har sai bayan sallar asuba.

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment