Sunday, 25 December 2016

Sakaci 12

  💔💘 *SAKACI* 💘💔
    

                      1⃣2⃣

© *Fatima A Garba*

Har yau bazan manta halin da muka iske Ya Hamid ba, halin da muka iskeshi yayi mugun d'aga mana hankali, yana kofar station akwance cikin jini dak'yar nunfashinshi yake fita, ga k'uda sai binshi suke da alama ya jima a haka, mutane na tsaye akanshi, ba wanda yaje kusa dashi ballantana asamu mai taimaka mishi.

Rungumar shi Mama ta yi, cikin kuka  ta ke cewa "kaga halin da ka jefa kanka ko" yafiyar Mama kawai ya ke nema cikin mawiyacin hali, ya ke cewa.

"Mama ki yafemin, ki nema min yafiyar ubangijina, na tuba Mama"

Ya Umar ne ya d'aukeshi Ummi ta taimaka mishi suka saka shi a mota, hanyar asibiti Ya Umar yayi muna bakin asibitin kafin mukai ga shiga ciki, Allah yayi ikonshi akan Ya Hamid.

Munga tashin hankali ranar, haka aka shirya Ya Hamid aka mik'ashi gidanshi na gaskiya, duk hakuri irin na Ya Abdallah ranar sai ya baka tausayi.

Haka muka cigaba da k'ar6an gaisuwa, ni da Mama da Ummi sai Ya Umar da Ya Abdallah a waje ba wani cika akayi ba tunda ansan ba wani k'arfi ne damu ba.

Baba kan bashi da masaniya domin ba wani d'an aiken da Mama zata tura ya sanar dashi, shi kuwa Alhajin su Ya Umar baya gari, kuma koda yana gari ma basa magana da Baban tun wani lokacin da Alhajin ya kira Baba ya na mai nasiha akan irin ruk'on da yake yiwa iyalinshi.

Shi kuwa Baba ya rufe ido yayita fad'an maganganu na rashin kunya, k'arshe ma ya d'au gaba mai zafi tsakanin shi da Alhajin.

                   *****

Ranar da Ya Hamid ya cika kwana hud'u da rasuwa, muna zaune da daddare bayan sallah magriba ni da Mama, ni ina ninke kaya, Mama kuma na zaune.

Hassan ya shigo d'akin mu, na yi niyar guduwa don bana so ko ganinshi nayi, zuwa wannan lokacin na tsane shi, tsana kuwa mai tsanani.

kasancewar ina ninkewa Mama kayanta wanda na wanke mata a yammacin ranar, ba yadda na iya haka na tsaya, domin nasan idan nace zan shige dole Mama zata yimin magana.

Bayan sun gaisa, Mama ta d'au buta ta ce ta na zuwa, Mama na fita yazo kusa dani ya zauna, ya cigaba da yimin kallon nan nashi na yaudara kafin kuma yace.

"Tunda bazaki gaishe ni ba, ba damuwa dama ba wannan ne ya kawo ni ba"

Wata harara na aika mishi da ita, amma ya kau da kai tamkar bai gani ba, ya kuma cigaba da cewa.

" ina jiranki anjima" hawaye tab cikin idona nace mai "kayi hakuri rasuwa aka mana fa"

Ware hannayenshi duka biyun yayi had'e da cewa "lalle gobe za'a sake zaman makoki" cikin tsoro na kalleshi, kad'a kanshi yayi alamar tabbatarwa.

Shigowar Mama shi ya hanani cewa komai, amma idona tab da hawaye, ina tausayin kaina, shin wannan wace irin rayuwa ce, k'arshe kasa cigaba da ninke kayan na yi saboda fargaba, shikuwa cikin kwanciyar hankali suka cigaba da hiransu da Mama.

Banyi bacci ba har wajen shabiyu na dare, sai share hawaye kawai na keyi, sai da na bari Mama bacci ya d'auketa, na lek'a falo naga shima Ya Abdallah yayi bacci tukunnan na fita cikin sand'a.

Ashe abinda ban sa ni ba shi ne, Ya Abdallah idonshi biyu baiyi bacci ba koda yaga fitana yayi mamaki domin yasan ni matsoraciya ce sam bana iya fita ko'ina da zaran dare yayi.

Tashi shima yayi yace bari yayi alwala yayi nafila ko yasamu bacci ya d'aukeshi, sai dai yana fita sai yaga nayi harya waje, lokaci guda hankalinshi ya tashi sai ya fara tunanin ko cikin bacci ne na fita, bina yayi amma ga mamakinsa sai yaga na tura k'ofar d'akin Hassan na shiga.

Mamakin abin ya bashi amma sai yace bari ya jira fitowa ta sai ya tambayeni, ya d'an jima a tsaye a wurin.

Lokaci guda yaji hankalinshi bai kwanta ba, bud'e kofar yayi a hankali abinda ya gani yayi mugun tayar mai da hankali.

Cikin gudu-gudu yaje ya taso Mama wacce tunda Ya Hamid ya rasu sai lokacin ta d'an samu bacci.

Cikin rashin fahimta Mama take tambayarshi mene ne, shikuma yana cewa ta yi shuru yana jan hannunta, bai saketa ba sai a d'akin Hassan.

Salatin Mama ne ya ankarar da mu, kafin kace meye Mama ta yi k'asa ta fad'i, cikin tashin hankali mukayi kanta nida Ya Abdallah, ganin Mama bata nunfashi nasa ihu ina cewa

"nashiga uku wayyo Mama kitashi"

Kafin kace meye wannan har matan gida sun fara fitowa,tsawa Ya Abdallah ya daka min had'e da cewa " ki wuce kisa kaya tunda hankalinki ya kwanta kin tonawa kanki asiri"

Komawa nayi nasa kaya ina kuka shi kuwa ruwa yake ta sawa Mama amma sam bata farfad'o ba, mijin Ladiyon gidan mu ne yace "dole fa sai an kai ta asibiti"

Ba tare da 6ata lokaci ba Ya Abdallah ya fita su Ummi ya bugawa k'ofa Allah yasa Ya Umar bai tafi aiki ba shi ya d'auko motar Alhajinsu.

Ya Umar ya na shigowa kan Hassan yayi gami da kamo ya shak'e shi, mazan gidan sunyi iya k'ok'arinsu amma ba wanda ya iya k'watan Hassan a hannunshi, idonshi ya kad'a yayi jazir, yana cewa.

"Saina kasheka maciyin amana azzalumi mazinaci, yau saika gane kurenka"

Ummi ce ta rik'eshi ta na kuka ta ke cewa "ba wannan zaka tsaya ba kazo ka taimaki Mama don Allah" 

cikin wani irin 6acin rai ya tunkud'e Hassan har sai da ya bugu kafin kuma ya d'auki Mama cikin zafin zuciya.

Ya kuma juyo ya cewa Hassan "kai kuma zandawo gareka"

~Ummu Hanan~

No comments:

Post a Comment