ANA KUKAN TARGADE...
Part 2⃣
Avva omar yaro
(Prince av)
09032724001
...runtse idonta kawai tayi tana jira ta ina zai fara, vocal dake tsaye kamar an dasa sai lokacin ta tattara duk karfinta wajen hankade chuchun ta fadi gefe daya, hakan shiya hana kwalisa karairayatan dayai niyya, amma dukda haka takan clutch bag dinta ya taka ya wuce.
Da sauri md da vocal suka karasa wajen datake kwance dan sunga batada alamar tashi, vocal ce tasa hannu ta dagata tana karkade mata jikinta, hawayen tausayin chuchun nata kara kaina a idanuwanta, md kuwa tsananin tausayi da borin kunyar abinda kwalisa yai ya hanashi magana sai binsu da ido dayake kamar ya samu majigi, dakyar ya hado harufan cewa "meyasa kika hankade ta" ya karashe da dora idonsa akan vocal
"Wallahi dana bari wannan gardin ya karairayata a banza gara nina Hankade ta, dan nasan komai zan mata soyayya ce ta jawo hakan, sabanin wancan mai zuciya kamar ta mutanen farkon" gyada kai yai kawai dan yasan ta fishi gaskiya a duk kalaman data fada.
Ita kuwa chuchu tsananin bacin ran abu biyu ya hanata magana, na farko md daya tsaya 6ata baki baibi kwalisa ya rarrashe shi ba, na biyu kuma Kalmar vocal data kirayi kwalisan da ita wai "gardi" wadannan abubuwan su suka 6ata mata rai mutuka fiye da faduwar datai, ganin shirun nata yai yawa yasa md cewa "kiyi hakuri chuchu....". Bata bari ya karasa ba ta tareshi "dan allah ka tafi, ka tafi ka bashi hakuri kona samu zuciyarsa tai sanyi ya samu yakuma cin wani abincin" daga haka ta tsuke bakinta bata kara cewa komai ba.
What kind of really & true luv ix dat, abinda md keta maimaitawa kenan a ransa "meyasa Abokinsa bazai fuskanci tsananin so da kaunar da chuchu ke masa ba" yakuma raya hakan a ransa, hakika yai alkawarin janyo hankalin kwalisa kan chuchu kodan ya fuskanci irin gangariyar so da kaunar datake masa, wanda yai karanci a wannan duniyar ta yanzu damuke ciki.
"Alfarma na nema bawan allah inba zaka iyamin ba wallahi ni abu mai sauki ne na bishi koda hakan na nufin a bakin raina ne bawai karairayawa ba" chuchun ta kara fada a karo na biyu tana mai kallon kofar da kwalisan ya fita, da salon barkwanci md ya amsa mata "karki damu ranki ya dade zanma aiwatar kodan gudun kar naje gobe a ki siyamin abinci" ita saima kunya ta kamata ta sadda kanta kasa tana kallon tiles din wurin.
Vocal ce ta tareshi da dariya "kasan kuwa hajiyar akan haka ba abinda baxata iya ba, ciki kuwa harda dakawa makaranta barkono" juyawa yai ya fara tafiya da cewa "adai kara hakuri da abokina madam" yana fada ya karasa ficewa daga cafteria.
Saida ya kule sannan chuchu ta dauke ido daga kallonsa tareda dalawa vocal duka a baya "dan iskanci ke kuma wai gardi " vocal ta gantsare jin zafin dukan tareda harararta cikin wasa "kya dakeni mana tunda na rufa miki asiri na rabaki da kwanciyar ORTHOPEDIC (asibitin kashi) ai yasin da yanzu likitoci na can suna kaida kawowa akanki tunda wancan abin ya maidaki kashin miya"
Cikin dariya chuchu tace "ina ruwanki inya karyani ko ke zaki jinya"
"A'a kodai banyi jinya ba amma dai ziyadin zuwa dubiya ya kamani"
"Ke kika sani kuma 'yar banza kawai" suka karashe da dariya su duka kafin vocal tace "ni kinga dan allah tashi muje mu karasa dan wallahi ko koshi banyi ba na taso"
"Muje karki samin kuka"
Koda suka sabuwar oda aka sake yowa vocal dan tace wancan iskar aman kwalisa tabi ta kai ta wuce, chuchu na jinta tai mata banza tasan sarai halin shakiyancin vocal kwarai so take kawai tai mata magana tasamu abinyi, sanin hakan yasa ta biye mata a yadda take so.
* * *
Yauma kamar kullum tayo shirinta cikin yaluwar doguwar riga mai hannun vest, saita saka riga top mai dogon hannu a ciki maroon colour, ta daura roses a kanta shima maroon, gashinta kuwa tai masa dogon kitson nan irin na 'yan indiya (plait) ta sako shi a gefen kafadar ta yana reto, kafarta cikin flat shoe na GUCCI, ta riko jaka post a hannunta fuskarta ba kwalliyar komai banda powder da white lips, haka tsarin kwalliyar chuchu yake duk randa tasa riga da wando ko siket to zatai rolling da karamin mayafi batare data sa dankwali ba, inkuma doguwar riga tasa zata daura dan kwali ammfa ko arzikin karamin mayafin babu, haka zatai ta fama da aran mayafi ko hijabi inzatai sallah a skull, dan vocal tayi rantsuwa bazata kara bata aran mayafinta ba, tace intana so taringa yafowa kota sako a mota inzatai sallar ta ringa daukkowa, amma taiwa zancen kunnen uwar shegu, danma mutuncinta da kirkinta ke hana mutane gajiya da bata aran mayafin.
Ta karasa saukkowa daga step din bene tanata kamshin tsimamman turarensu na bare-bare, da ko wucewa sukai sai sunbar wani a wajen.
Hajiya deejah na zaune tana shan dan itaciyar strawberry chuchu ta karaso da sallamarta ta amsa mata tareda cewa "ayeesher yau baki late ba kuwa, Inban manta bafa lecture 1:00 amma yanzu 1:30 garin ya akai haka"
"Mummy wallahi malamin ne jiya ya hade mana lectures din ta jiya data yau, kasancewar ya bamu uzurin dama bazai zo yau ba" ta karashe fada tana kai hannunta kan bowl din da strawberryn ke ciki, biyu ta dauka tareda mikewa "mummy na tafi ai mani addu'a" da kallon kauna H.deejah ta kalleta "allah ya kiyaye, allah ya kareki daga sharrin duk wani abun ki, ki kula da hanya banda tukin ganganci ayeesher, kuma kiyi addu'ar fita daga gida data hawa abin hawa"
"Nikam mummy kullum saikin maimaita min banda tukin gangancin allah banayi ba, kuma addu'a ma kullum sai nayi nake fita wani inya ji saiya dauka banayi ne" dariya H.deejah tayi "ke dadina dake shirme wata ran wallahi, aikowa yaji wannan yasan tunasarwa nake miki bawai fada bane"
"Yawwa mummy ashe dai na girma" ta fada tana dariya tareda ficewa daga cikin tangamemen falon.
Lumshe ido H.deejah tayi tareda ci gaba da kwararowa 'yarta ta addu'a a cikin zuciyarta, tasan ba tsimi ko dabararta ke kare chuchu ba illa addu'a da kariyar ubangiji kawai.
* * *
Tun daga bakin get ake daga mata itama tana aikin washe hakora (inji vocal) tareda daga musu hannun har taje inda zatai parking ta fito tana gyara zaman glass din data manna a fuskarta....
Daga bakin Y.B hall kuwa kwalisa ne sanye cikin yadi filters fari mai shara shara, kana iya hango farar vest din daya saka a ciki, kansa da hula zanna bukar mai launin zaren da akai aikin kayan dashi, ya dukufa da binciken dayake cikin mini laptop dake kan dakalin dasuke zaune.
A gefensa abokinsa ne md shima cikin tashi kwalliyar ta shadda gezner ruwan kasa, saidai shi sa6anin kwalisa hularsa na gefe a ajiye, da alama ya ajiyeta ne dan zafin da karatun ya hada masa bawai zafin gari ba, "kasan mene abokina"
Da sauri kwalisa ya dubeshi dacewa saika fada, allah yasa dai amsar ka samo mana, danni wallahi dama turata tana neman kaiwa bango" ya karashe da murmushin allah yasa abinda ya fada ne ya faru, amma sa6anin haka sai tsinkayar muryar md yai yana cewa "wai meye hujjar daka rike wajen wulakanta yarinyar nan"
Kwalisan da saida ya ja tsaki kafin ya kalleshi kamar baxai amsa ba sannan kuma yace "wace yarinya kenan" ya fada batare da yabawa zancen kulawa ba.
"Chuchu" kai tsaye md ya amsa, da fusatacciya murya kwalisa ya tareshi "mtsw dan allah yanzu ba lokacin dambe bane, kabari in marmarin naushi kake sai banida aikin yi saika kuma zuwar min da zancen nan" shi md ma abin dariya ya bashi ganin yadda kwalisan ya birkice kamar wani mai aljanu, dan haka dayaso kara cusa masa haushi saiya kara karya murya dacewa "nikam ina ma sha'awar kasancewa sirikin babban mutum kamar A.A koba komai...."
A fusace ya kuma dagowa "wallahi md aikin danake inya hanani naushinka, bazai hanani surfa maka ashariya ba" bilhakki yake magana da zuciyarsa daya, kafin md yakuma magana suka ji muryar wasu maza guda biyu da mata biyu dasuke tutorial a gefen "chuchu ba fada meya kawo gaba" harta gifta ta dawo wurinsu "kuyi hakuri wallahi ina saurine bana so nai missing lecture dina nakusa late ne" hannu ta mika musu suna gaisawa su duka akan namijin na karshe kwalisa ya dago kansa da niyyar ce musu sun takura musu sai kawai yaga chuchun na gaisawa da shi, kafa yasa ya hauri md da karfi, dasauri ya mike jin dukan dabai shiryawa ba, kallon kwalisar yake yana karawa yana son hango alamar datai nuni da ta6in hankali a jikinsa, bai gama tunanin ba ya katse jin sallamar chuchu a gunsu kasa amsawa yayi sai binta da ido kawai, ita kuwa hartai niyyar wucewa ganinsu tsaye yasa ta dawo, hannun ta mikawa md da fara'arta "how pa" bai tsaya shawara ba shima ya mika mata hannun dan da alama zafin hauri har yanzu bai sake shi ba.
Kwalisa ta kuma mikawa hannu da nufin su gaisa, wani wawan mari ya dauketa dashi dasaida ta durkushe a gurin tsabar karfi da zafin marin, wasu taurari tafara gani a idonta tsayin lokaci kafin ji da ganinta su dawo, kwalisa ya dubi md daketa tsimar jiki kamar zai rama mata marin harda dunkule hannun da nannade hannun riga "tur! Da mummuna shawara irin taka, yanzu wannan KARUWAR kake min fatan na aura, matar da musulincinta bai hanata fasikanci ba, wallahi ko mata sun kare a duniya ba abinda zanyi da wannan" ya karasa yana nuna chuchu da dan yatsa .
Chuchu dake durkushe tana hawaye saita dago da sauri, kalaman kwalisa sunfi mata zafi akan marinsa "karuwa! Karuwa!! Karuwa!!!" Taci gabada nanatawa a fili, tunda take a duniya ba'a ta6a kiranta da wannan sunan ba sai yau, yau dinma kawai danta nuna abinda ba ita ta dorawa kanta ba, ita kuwa aiko san kwalisa zai kasheta tabarshi kenan, ta mike tsaye da kumburarriyar fuskarta "in takamarka ina sonka to a yau inai maka albishir dacewa na daina, ba wanda na tsana yanzu a fadin duniyata Irinka, wallahi da dama yanzu tun kafin ka nakastani zan nakasa ka, amma yanzuma ka tsaya jiran tsammani" tana gama fada ta juya da gudunta tana kuka bata ko tsaya ta saurari kiran da md ke kwala mata ba....
😳 tofa laifin dadi karewa
Amma shin da gasken chuchu ta hakura da soyayyar kwalisa kuwa, inkuma ta hakuran to wane mataki ta ambata zata dauka akansa? Duk wannan amsar na ciki kashi na 3.
Da kai da ke da ku da su duk prince av ke cewa mu hadu a ANA KUKAN TARGADE-3
ngde
09032724001
Prince av
No comments:
Post a Comment