Friday, 30 December 2016

KARNINMU 10

KARNINMU...

©FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA...

Washagari da hantsi, Muazze zaune rumfar Mallam, ga kwanon tuwo gaban sa ya na shirin fara ci,wani dan almajiri ya zo ya durkusa ya na faɗin

"Muazze irin wannan sanwa haka ba ta yi?"

Tuni Muazze ya ja kwanon gaban sa sannan ya ce

"Wallahi ba za ka ci ba! Rabona da abinci tun na baran jiya !"

"Ko loma ɗaya ka emmin dan Allah!" Faɗin almajirin ya na mai haɗiyar miyau.

"Zancen kake so wai ance da gauro ya iyali!" Ya  faɗi tare da juya masa baya, almajiri na ji ya na gani ya hana masa. Hamze wanda da kyar ya ke takawa dan yunwa ya karaso ya durkusa gaban Muazze.

"Muazze na yi bara ban samu ba, tun safe ban karya ba"

Muazze da ya samu ya kai lomar tuwo bakinsa  sannan ya tura masa abincin, ya ce

"Ga nawa ka ci,bani kwanon na ka sai na sake baran, yunwa ba ta da hankali"

Tuni Hamze ya ja kwanon Muazze ya fara kai loma, hanun baka hanun kwarya. In da shi kuma Muazze ya ɗau kwanan Hamze ya bazama bara.

                    ***

Hajja Bilkis ta bakunci gidan Minister. Zaune ta ke a falon Saratu matar minister, in da su ke tattaunawa akan kungiyarsu na kawaye chan  Hajja Bilkis ta nisa ta na mai gyara zama ta ce

"Kayan nan nawa fa sun iso Saratu, zan  aiko mi ki sabuwar yar aikatau da na ɗauka ta kawo mi ki sample"

Saratu ta murmusa sannan ta ce
"Hajja Bilkis yar kasuwa, ke dai kullum cikin sauya yan aikatau ki ke ba kya ko tsoron ɗauko mugun iri"

"Ya zan yi Saratu, yan aikatau din ne ba su da tabbas, yanzu haka ma Talatu ce ba lafiya ni kuma ba zan iya wahala ba shi ne fa yaya ta aiko min da wannan" Faɗin Hajja Bilkis ta na mai duba wayar ta da ke tsuwa alamar shigowar kira. Karawa ta yi a kunnen bayan ta latsa wajen amsa kiran tace,

"Hello Honourable"

Daga bisani ta k'ara da faɗin,

"Ba na gida fa, amma na kira Iya dudu na sheda mata"

Ta aje wayar ta na mai jan tsaki Hakan ya sa Saratu faɗin

"Lafiya kuwa Hajja Bilkis? wannan tsaki haka kamar tsaka?"

Hajja Bilkis na mai kwafa ta ce

"Wannan mutumin mana! wai da la'asar zai kawo min baki gida, in sa a yi abinci da su! dan ma ya maida ni baiwa kawai sai ya kwaso min tarkace!"

"Baki daga ina? ko dai yan jagaliya?"

Saratu ta tambaya. Buɗar bakin Hajja Bilkis sai cewa ta yi

"Ba gwara yan jaliya da gayyar da zai kawo min ba! Dangin sa ne fa daga kauye, duk sanda su ka zo gidan kumewa ya ke da warin talauci da dauɗa, mstw!" ta kara jan wani tsakin

"Heyyye".

Saratu ta yi shewa har da tafa hanun.

"Dangin nasa ne za su zo shi ne bai faɗa miki ba sai yau, yau ɗin ma da rana, gaskiya dai kin yi sake kawata, kin bari Ahmad ya raina ki!"

Kasake Hajja Bilkis ta yi jin batun Saratu,kafin ta ce.

"Saratu? har kura ta ce da kare maye? ashe ki na da bakin magana ke da yanar gizo ta haskawa duniya mijin ki hajaran majaran ya goyo karuwa? Ke ni fa da ni ce ke ko kallan idon jama'a ba zan iya ba bare ma na iya yiwa wata kauɗin baki, ai Hausawa basu yi karya ba da su ka ce bagiringirin ba Saratu, ta yi mai!"

Tuni Saratu ta tsuke fuska ta na mai ɗagawa Hajja Bilkis hannu

"Dakata Malama! Ke fa matsalata da ke cin fuska Balkis, ba za ki zo har in da na ke kice za ki ci min mutunci ba!"

Hajja Bilkis na mai murmushi ta ce.

"Ai ke ɗin ce Kawata na ga ki na neman ki min iyayi, shi yasa na ce mu gani k'asa wai ance da kare ana biki a gidan su"

Gaba ɗaya fara'a da walwalar Saratu ya ɗauke, ganin haka ya sa Hajja Bilkis jan mayafinta, ta yana sannan ta ɗauki jakar ta tana mai faɗin

"Na bar ki lafiya Kawata......"

Haka ta fice Saratu ko tanka mata ba ta yi, ita kuwa Hajja Bilkis ran ta fari fat, ba ta ma san wutar da ta kunna ta bar Saratu ciki ba. Wacce tun fitar Hajja Bilkis ta ke kai kawo, dan ranta ya sosa kwarai, a da ta gani ta yi shiru, amma tunda ya fara ja mata gori daga wajan kawaye dole ta ma tufkar hanci, wannan a gaban ta kenan waya san wanda aka yi bayan idon ta!

                        ***
Tun jiya da luba ta fara zuwa wajen aikin da Minista ya ba ta, yan hayinsu  suka samu labari daga bakin matar kawu yaro,  wasu sun yi mata fatan Alkhairi wasu sun yi tofin Allah tsine.       Dawowarta  kenan karfe huɗu kamar jiya,  tafiya take kamar mai tausayin kasa,  sanye take da kamfala  ɗin kin bubu,  babu ko alkbarkan gyale illa ɗan kwalin da ta kashe ɗauri dashi.

   "mtswww!  Me aka yi da rashin abin hawa,  bari in kira minista ma kawai"  ta faɗi a bayyane tana mai buɗe jaka alamun zata ɗauki wani abun.

  Ita kanta ta manta yaushe rabon da ta hau motar haya ko achaɓa.  Amma fara aikin ta ya sa ta shiga saboda minista ya sa ta kori duk kwastamominta sai dai ya wadata ta da motoci da direbobinsa don harkokinta,  wanda hakan ba zai yiwu zuwa wajen aikin ta ba saboda gudun tonuwar asiri.

    Bata kara taku uku ba,  wata mota kirar camry XSE V-6 mai ruwan zinari  ce ta tsaya a gabanta.  Tafiyarta ta cigaba ba tare da ta kallo shi ba.  Fitowa yayi  da sauri ya zubewa,  tana shirin magana ya ɗaura yatsa a kan leɓenta  ya ce
" Afuwarki nake nema sarauniyar kyawawa,  don Allah kiyi hakuri ki min izinin zama direbanki na yau kaɗai ki ga ko na cancanci  tuka ki"

Kur, ta ke kallonsa tun da ya fara har ya kai aya don kan shi ya tsaya sannan ta gitta ta gefen shi ta cigaba da tafiya. 

   "Kiyi hakuri  ki bani dama,  kin fi karfin tafiya a kafa"  ya sake faɗi yana binta da yar sassarfa.
   
"oh!  So kake ka kashe min aure ko mene,  don Allah ka ɓace min ko in sa a kulle min kai" ta faɗi a tsiwace.  Kallonta yayi sannan ya kalli kan shi da motar da yake kai,  ya ga ai iya haɗuwa ya kai da babu macen da yake tunanin zata yankuna shi,  amma sai gashi ta masa a tsakiyar titi,  amma ji yake kamar yanda mayen karfe ke jan duk wani abin da ke da karfe a jikin shi haka so da sha'awar Gimbiya ke jan shi.

     "Naji, mu je in sauke ki,  don in har miji ne da ke Toh nine nan mijin.  Haba sarauniyar kyau,  ki taimaka min don Allah"  ya faɗi yana mai kara zubewa a gabanta karo na biyu.

Da kyar dai ya samu ta shiga motar,  zuciyar ta cunkushe da haushinsa don duniya in da wanda ta tsana yana bayan mai naci.  Ganin Shirun yayi yawa ya sa shi gyara murya da faɗin,
"Suna na Yasir,  ni ɗan asalin Kasar nan ne,  na yi karatu na a kasar Raitu,  na karanci tukin jirgin ruwa,  na kan yi wata uku zuwa shida saman ruwa duk da kasancewa na ɗaya daga cikin iyalan da suke lamba ɗaya a kasar nan (first family),  na dawo hutu ne sai mahaifi na ya aiko ni wajen ministan birnin nan.  Ashe da rabo in je masa da labarin da yafi kowanne Daɗi. " ya karasa yana murmushi.

Nan take ta kara haɗe fuska,  gabanta na dukan bakwai- bakwai amma ta ɗaure ba tare da ta bayyana hakan a fuska ba.
   
" yana nufin shi ɗa ne ga shugaban kasa,  zan ja kaya kaya kenan sai dai kuma Minista zai zama matsala,  yanzu ya kenan... "

" Kinyi shiru" ya katse mata tunaninta,  nan take ta ɗago ido ta Kalle shi,  da ganin sa yana fama da kuruciya don ba zai girme ta da shekaru fiye da biyar ba.
    "Kwanan nan zaka sauke ni,  zan karasa gida da kai na"  ta faɗi fuskarta a haɗe kamar ba ta taɓa dariya ba.
   "zan iya samun Numb ki tunda ko sunanki rowansa kike min."  ya faɗi a marairaice.
   "babu hali,  na faɗa maka ni matar aure ce"  ta ce haɗe da buɗe kofa ta fita,  shi kuma ya tsaya ya bi ta da kallo.
   
  Sai da ya ga ɓacewarta sannan ya ja motar a hankali zuwa masaukinsa. Ya rufo ɗauki wayarsa da ledan da ya aje a kujerar da luba ta zauna akai wanda a dalilin shigowarta ya aje a kasa.  Yana ɗauka sai yar posa ta faɗo,  alamun an manta da shi a waje.  Dariya kawai yayi yace
   "Ashe dai yar gari ce" 
Ya kwasa ya wuce ɗakin barcin sa.

No comments:

Post a Comment