KARNINMU...
©FIKRA WRITERS ASSOCIATION
Ga masu bukatar labarin daga farko, za'a samu a www.fikrawriters.blogspot.com ko kuma a Wattpad (Ummu-Abdoul).
BABI NA GOMA SHA DAYA
A guje suka bar wajen babu wanda zai ce ko su waye, ganin suna gudu wasu suka bi sawun su tunanin su ma yan gudun neman tsira ne, wasu kalilan ne suka yi karfin halin zuwa wajen Lado,
"Sun kashe shi, na shiga uku sun kashe shi" faɗin Larai tana mai kuka wiwiwi.
"su wanene? Kinga fuskokinsu? " faɗin sajen ɗin ɗan sanda da ya kara so wajen.
" eh na sansu, chan hayin suke Lanto ya ma sunansu? " ta ce tana mai juyawa saitin da lanto take zaune amma se wayam ta gani ba ko burbushinta.
" Anya ma ba ita ce mai kisan ba, don ni ina zaune nan ban ga alamun su ba, ihunta ya ankarar da mutane duk ta ruɗa kasuwa. " cewar wani dattijo da ya kasance Kawun Mahaifiyar Baaba, dama tun da ya ga ɗan sandan yake rokon Allah ya rufe bakinta, don ba zai so a rufe masa jikansa ba.
"Wallahi ba ni na kashe shi ba, muna zaune suka zo wai ya basu kuɗin aikinsu, Lanto ta sansu a kira ta a tambaye ta." ta faɗi tana mai kara fashewa da kuka.
"wai wace Lanto? " faɗin mutanen wajen. Kuka kawai take yi ba tare da ta amsa musu ba
A haka har motar yan sanda ta kara so aka sa su har Larai da komatsen tallanta zuwa Charji ofis. Chan yamma yan uwan lado suka zo, aka saki gawarsu. Yayin da Larai a ka tura ta bayan kanta ana jiran wani dangi nata ya zo.
***
Fitar da suka yi ba su zame ko ina ba sai gidan su Rabs, cikin ikon Allah ba su iske kowa a hanyar shigan su ba, nan suka chanza kaya suka ɓoye wukar sannan suka kwanta.
Ko da Rabs ya dawo bayan jana'izar Lado ya iske abokansa na barci, nan mamaki ya ishe shi don ya je har gidajensu ba sa nan, "Toh yaushe suka zo nan" ya tambayi kansa sannan ya zauna yana mai nannaɗe musu ragowar wiwin da suke da.
***
"Gafaranku dai", cewar Baba dije.
"Yauwa lale marhabin. Dije ke ce da magariba haka shigo" cewar mama Hanne tana mai kuskuren baki.
"na biyo sawun yarinyar nan ne, ace ka haifi ɗa amma yana maka bakin ciki, tun tallan Ɗazu bata dawo ba, dambu na yayi kwantai fa kenan" ta faɗi rai a ɓace.
"aiko ba nan ta zo ba, ni tun Ɗazu Lanto ta dawo kamar wacce tayi gamo, nayi tambayar duniyar nan bata amsa ni ba, ga ta chan kwance zazzaɓi ya rufe ta" ka fin Dije ta bata amsa sani ya shigo fuska cike da alhini.
"kai kuma lafiya?" Mama Hanne tayi saurin tambayarsa.
"daga Janaza nake Allah yayi ma lado rasuwa, wai an kashe shi a kasuwa " ya faɗi a hankali.
" ko can Larai ta tafi, da yake mutuminta ne sosai, bari in koma in jira toh" ta faɗi tana mai juyawa amma ta tsaya chak sakamakon abinda ya fito bakin sani.
"Mai unguwar hayin magarya na nemanku, don an sanar bayan jana'iza cewa tana hannun yan sanda.
"inna ninnahi wa inna alaihin rajium" faɗin mama Dije tana mai ɗaura hannu aka.
"mtswww! In an ce suje islamiyya su ki suna kasa kayan talla, yanzu istirja'in ma basu iya ba" ya faɗi a ransa
Haka suka bar gidan afujajan basu tsaya ko ina ba sai gidan mai unguwa.
***
" Sadisu ! " ta kira sunan sa a kausashe, ita kanta tayi mamakin jarumtarta, haka shima mai girma Minista ya tsaya chak, a iya saninsa bata taɓa kiransa da sunansa ba, yau da tayi ba karamin abu ya sa hakan ba. Ita kuma ganin ya yi mutuwar tsaye ya sa ta cigaba
" kai yanzu fisabillahi baka jin kunyar kanka, tun da ka nuna ma duniya cewa ka riga ka kyankyashe kwayakwan kunyar da aka san mumini dashi ba ni ina da shi" ta karasa zuciyar ta cike da kuna.
"me kuma nayi Sarah, a iya sani na ina iya kokari na wajen kare miki mutunci, amma ke duk ba kya gani" ya ce yana mai marairaicewa, ya san zancen bai wuce na Lubah shi kuma yanda ya ke ji game da ita se dai fa Saratu tayi hakuri.
"An fara biyo ni har gida a ci min mutunci akan karuwan da kake bi, in har Bilkis zata goranta min ka goya karuwa Allah kaɗai ya san abinda makiya suke faɗi akaina" ta karasa tana sakin kukan da yafi jini ciwo.
"ka auro su mana, ka auro su duka in ba ka da space ma zan ba ka waje" ta faɗi cikin gunjin kuka.
"Haba Sarah, ya zaki dinga haɗa kanki da kazanta, ni kai na tun zancen goyon nan na tuba don duk da ba wanda ya tunkare ni amma tabbas na muzanta. Sarah ke tsarkakka ce yayin da sauran kazanta ne, najasa yafi dacewa a kira su, wallahi da na haɗa ki tarayya da su a gidan aurenki gara in mutu. Ni Sadisu da auran karuwa Allah ya tsare ni"
"kuna da bambanci ne wajen rubuta zunubi, nasu ya fi naka kenan duk da kasancewar ka bazawari " ta katse shi
" amma a Al'adance fa, duk duniyar nan babu inda za'a kalli abinda na aikata a matsayin najasa kuma ko yar waye na so Zan aura, su fa? Mace da zina, Toh me zata ce ma Yaranta wani tarbiyya zata ba su? " ya faɗi a fusace
Dariya Haj Saratu tayi don maganar sa ya sa ta nemi rabin bakin cikin ta ta rasa, ta kara kyalkyalewa da dariya ta ce
" Meye abin ɓacin rai Toh? Ai Naga abinda zaka faɗa ma si Afreen shi zasu faɗa ma nasu yaran. Ita mace ko da yaushe ita ce yar wuta, ai ko da manzo SAW ya ce mata zasu fi yawa a wuta bai ce a maida ita mai kwasan zunubin laifin maza ba, ita mace ko mijin ta zai bi duk matan duniya yayi zina da su za'a ce ta zauna tayi hakuri amma su masu cewa ta zauna da mazinaci su zasu zuga mijin ya sake ta ranar da kaddara ta hau kanta ta aikata zina. Kaico da wannan KARNI namu. Shin ka taɓa bincikar dalilinsu na shiga karuwanci a matsayinka na mai kiwon mutanen Dunotsi? Ta karasa tana karasowa gaban shi. Ta Tabbatar da ya kasance mai saurin hannu da sai ya nakaɗa mata duka.
"Kinga Saratu fitar min a ɗaki, haka ake mata? Ace in Kwaso fitanar mutanen da nake mulki ki rasa kwantar min da hankali, mstwww" ya karasa yana fitowa da wayarsa.
Dariya tayi sannan tace "A dai ji tsoron ranar da za'a biya bashi akan yaranka mata" ta fice ta barshi zuciyar sa na masa tukuki sai da ya ji an ta hello hello ya tuna ya kira waya.
"Ahmad ka ja kunnen matarka, kada ko da wasa ta sake zuwa min gida, ya za'a yi ta zo tana faɗa ma Sarah na goya Lubah, nine yau Sarah ke ma yara na fatan kasancewa karuwai, Ahmad Wallahi ba don kai ba da na sa a kulle Bilkis ko in sa a ɓatar min da ita. Na faɗa maka ka kwaɓa mata ko inyi abinda zakuyi mamaki na, babu ruwan ka da Lubah balle wata matarka". Ya katse ba tare da ya ji amsar shi ba..
Muna jiran raayinku akan KARNINMU ta fikrawriters@gmail.com...
No comments:
Post a Comment