ABINDA AKE GUDU🙆🏽21
Batul Mamman💖
Sunyi tafiya ta kusan rabin awa kafin su isa gidan. Dan matsakaicin gida ne mai kofa daya. Idan ka shiga siririn soron akwai kofar daki a wurin sai kuma daga gaba ainihin kofar gidan. Tsakar gida ce mai dan fadi da dakuna uku, bandaki da kitchen.
Daya daga cikin kofofin Rashida ta bude suka shiga tana nishi da kyar. Asmau dake tsaya tana jiran su bata izinin shiga taji Rashida na cewa mijinta " gaskiya Baban Abba kana kokari yin tafiyar nan kullum. Kodayake kiba kake son ragewa" ta kare tana dariya.
Labulen kofar ta makale a jikin kofa sannan tace Asmau ta shigo falon. Da sallama ta shiga tana ta addua a zuciyarta ta sami wuri akan ledar falon ta zauna.
Sada ya zauna kusa da matarsa a kan kujera yana dubanta.
"Nan shine gidana kuma kamar yadda na fada miki wannan matata ce. Muna da yara hudu duk maza suna makaranta yanzu. Abba, Abdul, Ahmad da Amir. Mu dai har ga Allah bamu da niyyar cutar dake ina fata kema haka abin yake a zuciyarki. Yanzu al'amarin Dan Adam sai addua. Da mai taimako da mai neman taimako kowa yana tsoron dan uwansa. Idan kin amince zamu zauna dake har ki haihu in Allah Ya yarda sai muyi miki jagora zuwa wurin iyayenki. Na tabbata a lokacin zasu hakura tunda kin haihu babu mai zubar miki da ciki."
Asmau tayi musu godiya sosai tana share hawaye. Bazata taba mantawa da mutanen nan ba a rayuwarta. Dakin soron Rashida ta kaita tace ta jira tana zuwa.
Wurin mijinta ta koma ta kai masa ruwa da abincin da baici a shago ba sannan ta koma bakin rijiyarsu ta janyo ruwa har bokiti uku. Katuwar tukunya ta dorawa Asmau ruwan wanka sannan ta kai mata abinci. Ta karba tana ci Rashida ta dauko tsintsiya ta share dakin tas ta dauko daya daga cikin karifar yaranta ta shimfida mata. Asmau dai sai godiya.
Bayan Sada ya koma kemis dinsa Rashida ta kira Asmau ta bata sabulu da soso tace taje tayi wanka. Sai da ta fara wanke kayanta wanda suka kusa karar da ruwan sannan tayi wanka da wankin kai. A take taji ta zama kamar wata sabuwar mutum. Da ta fito Rashida ta bata riga da zani ta saka. Da kuka ta rinka yiwa Rashidan godiya.
Da yaran suka dawo daga makaranta aka gabatar musu da ita a matsayin 'yar uwarsu. Abba ya kare mata kallo ya dubi mamansa "Mama wannan tayi kama da almajirar da Baba ya siyawa awara rannan."
"Kul na sake jin kalmar almajirar nan Abba. Sunanta Anti Asmau kunji ko" yaran suka amsa sannan duk suka gaisheta cike da ladabi.
Da daddare bayan Sada ya dawo ta fada musu tana son dauko kayanta daga gidan Uwargida. Yace bai amince ba, tunda Allah Ya rabata da gidan kin komawarta shine mafi alkhairi.
Rashida tace "zan duba miki wasu cikin nawa kayan sai kiyi amfani dasu zuwa lokacin da zamu ga abinda Allah Ya nufa."
Washegari Sada da kansa yaje gidan Uwargida don tabbatar da zancen Asmau ya nuna kamar haduwa yayi da ita kuma yana sonta. Daga kwatancen da yayi Uwargida ta gane wa yake nufi tace masa ya dawo washegari tun jiya bata ga 'Yar Da6as ba. A ransa yace kuma bazaki kara ganinta ba.
Cikin kwanaki kadan Asmau ta saba dasu Abba sosai ta dan murmure. Tana fitowa ta taya Rashida ayyukan gida musamman wanke wanke da shara. Da ta gama take komawa daki don kunya take ji ace ta saki jiki sosai ita da ake yiwa alfarma. A nata bangaren Rashida kullum kokarin jan Asmau take yi a jiki saboda nutsuwarta. Har mamaki take yi yadda irin wannan azal ta fada mata. Sai kuma ta tuna babu abin mamaki a rayuwar duniya.
*****
Haka rayuwar Asmau ta cigaba da tafiya tare da wadannan bayin Allah. Zama suke yi na amana kullum tana addua Allah Yasa kada su gaji da ita su koreta wata rana.
Tsakaninta da Sada baya wuce sannu da zuwa, ina kwana ko ina wuni. Wannan yasa Rashida take kara janta a jiki. Don kuwa babu wadda zata so daga taimako taga ana shigewa mijinta. Shima da yake mutum ne mara hayaniya ba shiga sabgarta yake yi ba.
Tayi kimanin sati uku a gidan rannan an kawo wuta Rashida ta tura Amir ya kirawo Asmau tazo suyi kallo. Tana daki tana aikin tunanin rayuwarta taji sakon ta tashi.
Sallama tayi Rashida ta amsa tana murmushi.
"Asmau wai ke haka kike ne da wuyar sabo, uhmm? Kullum sai na aika an kiraki zaki fito muyi hira. Zaman dakin da tunani sai ya haifar miki da matsala ko da babu ciki kuwa."
Ita ma Asmaun murmushi tayi kanta a kasa "kiyi hakuri Antina, in sha Allah zan dena."
"Zaki dena, ba ki dena din ba kenan".
Suka yi dariya su biyun sannan Abba ya kunna tv din suna kallon fim din Zinaru suna dariya.
Sai da fim din ya kare Asmau ta dan karkata tana kallon Rashida.
"Anti dama wata alfarma nake nema amma don Allah idan kinji abin baiyi miki ba kiyi hakuri."
Rashida ta juya ta kalli yaranta. Ba tare da tayi magana ba duk suka fice sannan ta mayar da hankalinta ga Asmau.
"Ina jinki kanwata"
"Anti dama shawara nake da ita idan babu damuwa. Na kula Kawu Sada yana zuwa wani aikin bayan ya taso daga kemis dinsa. Kamar yadda na fada muku na kusa gama aji uku a jamia kuma pharmacy (hada magunguna a kimiyance) nake karantawa. Nayi tunanin ko zai nuna min yadda yake a kemis din na rinka taimakawa da zaman wurin idan yana wani aikin."
Shiru Rashida tayi na dan lokaci tana tunani. Ban da kemis Sada yana 'yan buge buge irin na maza don dai a cigaba da samu. Hakan yasa baya samun zama a kemis sosai. Wani lokacin tun karfe takwas yake rufewa. Tayi masa magana akan ya koyawa Abba yace so yake suyi karatu tukunna. Ta numfasa "bari ya dawo muji ta bakinsa. Amma kin kawo shawara mai kyau. Sai dai ya zakiyi ga ciki ya fara girma?"
Asmau tayi farinciki da Rashida bata yi mata mummunar fahimta ba tace "zama wuri dayan ma yana da illa. Idan na samu ina fita sai naji dadin jikina".
Yau tun bayan magariba Sada ya dawo. Ya ci abinci yake sanar da Rashida ya samu za'a rinka bashi hayar adaidaita sahu daga karfe shida zuwa shadayan dare. Saboda haka yanzu da wuri zai rinka dawowa.
Tana jin haka ta fada masa yadda suka yi da Asmau. Yace ta kirawota suyi magana.
A kasa ta zauna ta gaishe shi yace "Yanzu nake jin shawarar da kuka yi da Rashida. Kina ganin babu matsala ga ciki?"
"In sha Allah babu in dai kun amince".
Ya dubi Rashida "ina ganin hakan wani taimako ne daga Allah. Zan nemi a canja tsarin hayar dan sahun. Yadda ita sai taje da safe zuwa shidan ni kuma naje zuwa shadayan dare."
Asmau tayi musu godiya har zata tashi Sada ya dakatar da ita ya tambayeta nawa zai rinka bata a wata.
Zaro ido tayi "Allah Ya kiyaye na karbi kudi. Matsayinku a gareni ya wuce hakan. Kun bani wurin kwana da abinci duk da ina halin da duniya zata kyamace ni. Irin tawa gudummawar kenan gareku ba don na biya kyautatawarku ba. Wannan Allah ne kadai Yasan ladanku" da kuka ta karashe maganar.
Sada yaji dadi yace ta tafi zasuyi shawara da Rashida amma dole a bata wani abin.
Bayan fitarta Rashida tace "kaga ikon Allah ko. Sai Ya kawo maka taimako idan ka taimaki bawanSa. Yanzu sai kayi aikin cikin kwanciyar hankali kafin ta haihu."
"Haka ne amma ya kamata kafin ta fara zuwa kuje asibiti a duba ta duk da naga bata damu da cikin ba."
Dariya Rashida tayi "da kenan Baban Abba. Yanzu idan muna hira zance kadan sai ta sako abinda ke cikinta. Har hira nake ji tana yi a daki da shi tana fada masa tana sonsa."
Sada yayi murmushi "gara ta so shi domin da yawa matan dake yin ciki a waje idan sun haihu sai tsanar dan ta biyo baya ko su yar. Karshe yaro ya tashi babu tausayi ko imani a zuciyarsa."
*****
Bayan kwana uku Asmau ta fara bin Sada kemis dinsa. Sunje asibiti an bata magunguna irin na masu ciki sannan ance ta rage tunani saboda jininta ya dan hau.
Cikin ikon Allah bata dade ba ta gane kan aikin ta rike kudin kayan shagon, magungunan da lemo. Allura ce kawai bata yi sai tace mutum ya dawo karfe bakwai lokacin Sada ne a wurin.
Duk iya bincikensa ya duba bai samu tana ha'intarsa ba. Komai aka siya sai ta rubuta sannan kafin ta tashi zata yi lissafi ta ajiye masa kudin. A wannan lokacin kam sun sami budi sosai ga kemis ga adaidaida sahu.
*****
Mama da Umma kamar basu sami sabani ba don tuni Mama ta amince da zancen Qasim na cikin Asmau. Su biyu ke kai kawo a asibiti suna jiran Shemau ta haihu. Mijinta ya tafi dauko kayan haihuwar da suka manta a gida saboda sun fito a gigice.
Nurse ta fito ta sanar dasu ta sauka lafiya an sami da namiji. Bakin Umma da Mama yaki rufuwa don tsabar farinciki sai yiwa juna barka suke yi.
Suna dakin maijegon Zubair mijinta ya dawo. Yana ta murmushi ya dauki dansa yayi masa huduba sannan ya mikawa Mama yace "Allah Ya raya mana Abubakar Saddiq".
A take hawaye ya sauko mata ta kalle shi ta kalli Umma. Ita ma Umman har Shemau hawayen suke yi tace "Allah Ya raya shi bisa sunnah. Mungode sosai Zubair."
Mama ta share hawaye "A lokacin da ko 'yan uwansa babu lallai su sakawa 'ya'yansu sunansa saboda ya mutu ya bar baya da kura shine kayi mana wannan karamcin. Me zance maka Zubairu."
"Mama so nake ku dena tada hankulanku. A rayuwa kowane mutum da irin kaddararsa. Kuma haka ke sawa mu kara imani da sanin cewa ba wayonmu ko ilimi ne yake karemu ba. Rahma ce kawai daga Allah da ibada da kuma tawakkali ."
Shemau tace "mungode Abban Mimi. Allah Ya jikan Yaya Abubakar".
Duk suka ce Amin.
*****
Da taimakon Alh Adamu, Qasim ya tura hotunan Asmau ofisoshin 'yan sanda da yawa ana cigiyarta ko wanda ya ganta.
Abdulhalim kuma ya baza a gidajen rediyo da talabijin. Duk inda suka ji kishin kishin da gaggawa suke zuwa ko za'a dace. DPO din division din da Qasim yake a Zamfara shima ya taimaka ta hanyar dagawa Qasim din kafa a duk inda suke tunanin za'a sameta yana bashi izinin zuwa.
*****
Watanni sun shude cikin Asmau ya kusa kaiwa lokacin haihuwa. Dan kudin da Sada yake bata duk da yace ba albashi bane dashi take siyan dan abinda ba'a rasa ba na jarirai. Kunya tasa take boyesu kada ace tana yiwa dan da bashi da uba siyayya. Sada yace ta dena zuwa kemis din haka tace zata iya tare da alkawarin duk ranar da taji alamun ciwo zata hakura.
No comments:
Post a Comment