Thursday, 12 January 2017

Abin da ake gudu 14

ABINDA AKE GUDU🙆🏽14

Batul Mamman💖



Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji uku a jami'a sannan ansa bikinta wata hudu masu zuwa. Asmau tayi murna don lokacin ta gama jarabawa.  Karatu take yi sosai saboda don cika burinta na zama likita. Har gidan su Abubakar yaje da laptop dinsa yayi mata registration din JAMB. Anan ne ya cike mata medicine a matsayin zabin farko sai pharmacy a zabi na biyu.

Duk abinda ya shige mata gaba tana tambayarsa ya koya mata.

Gab da fara jarabar  tasu ne posting din su Abubakar ya fito an tura shi jihar Ebonyi bautar kasa. Da yaje fadawa Umma yana kula da yadda fuskar Asmau ta nuna rashin jindadi sosai. Shi kuwa hakan yayi masa don yanzu ya tabbatar ba shi kadai ne zuciyarsa ta kamu da sonta ba. Jira yake yi ta kammala makaranta sannan ya fada mata.

Watansa biyu da tafiya watarana tana dawowa daga makaranta sun gama practical din food and nutrition yamma tayi sosai wani saurayi ya tareta a hanya. Tunda ta fito daga makaranta bayan sunyi sallama da Walida kawarta yake binta a baya. Tsoro ne ya cika mata zuciya bare da yayi mata sallama ya bukaci ta tsaya. Yana bayyana mata soyayyarsa tace yayi hakuri tana da mijin aure  har ansa mata rana. Saurayin ya gamsu ya tafi. Ita kuwa a ranta gani takeyi kamar taci amanar Abubakar ne ma idan ta tsaya da wani duk da bai taba cewa yana sonta ba.

Alhamdulillah sun gama jarabawarsu lafiya sai jiran sakamako. Ranar da ta gama tana dawowa gida Umma na kitchen ta kwala mata kira. Ko kayan makaranta bata cire ba taje amsa kiran.

Umma na murmushi tace "Asmau yau an gama jarabawa ko? To ki dage da addu'a kamar yadda kullum nake yi muku. Allah Ya bada sa'a Yasa ku gama lafiya."

"Amin Ummana".

"Kije dakina akan gado duk abinda kika gani naki ne na tayin murnar gama exams. Sauran kyauta sai naga result mai kyau."

Dadi ya kama Asmau tana ta godiya ta ruga dakin Umman.

Kwalin waya ta gani akan gadon hannunta har yana rawa ta dauka tare da yin ihun murna.

Daga kitchen Umma tace "Asmau babu hamdala sai ihu ko? Kin kyauta."

Dena ihun tayi ta fara godiya ga Allah sannan ta fito falo wurinsu Jafar. Sun tayata murna Yassar yana rokonta ta rinka bashi yana yin game. Shema'u da Jafar kayansu baya tabuwa.

Jafar ya bude kwalin harda sabon sim na mtn. To dama Umma yanzu ta kara samun matsayi don har mota ta siya. Masu abu da abinsu. Duk wanda ta sayawa waya dole yayi sim din mtn.

Suna gama murnarsu ta saka hijab ta fadawa Umma zata je ta nunawa Mama. Umma tace "babu inda zaki sai kinyi wanka kin canja kaya. Kin yini da uniform kuma kice dasu zaki fita?"

Komawa tayi ciki tayi wanka ta canja kaya ta. Tare da Aina'u da Yassar suka tafi. Umma ta girgiza kai kawai tana dariya.

Da sallama ta shiga ganin Nasiba tayi a falon da danta Amir. Asmau ta karasa ta rungume Nasiba tana murna sannan ta karbi Amir.

"Tun dazu nazo fa, naje munsha hira da Umma tace kina makaranta. To ya exams din?"

Maimakon amsa wayar ta mikowa Nasiba bakin nan yaki rufuwa. Ta tayata murna suna duba wayar Mama ta fito "yau Idon kuka ce take ta murna haka kamar an baki takardar karatun likita."

"Haba Mama na dena fa. Kinga wayar da Umma ta bani."

"Masha Allah, Allah Ya tsare. A kula sosai don Allah banda yin abinda bai dace ba kinji ko. Ni zaki fara bawa numbar kuma" .

Dariya suka yi Umar yazo shima yana nacin a bashi ya gani. Kamar daga sama aka ziro hannu aka karbe wayar a hannun Umar. Da sauri tabi hannun da kallo.

Abubakar ne tsaye yana mata wannan murmushin. Yayi kyau wata uku da rabi da bata ganshi ba har kiba yayi. Ga gemu dan madaidaici ya tara shi. Fuskarsa sai tayi mata kyau.

Nasiba ce tayi dan tarin gulma wanda yasa Asmau tayi firgigit ta dauke idonta daga kansa. Mama sai ta basar kamar bata gani ba ta tashi ta bar falon.

"Bazaki gaisheni bane?" Ya fada yana zama kusa da yar uwarsa.

Kunya ta kama Asmau tace "ina wuni?"

"Tunda sai da na roka na yafe. Ni da na taho musamman saboda tayaki murnar gama makaranta ".

Nasiba ta soma dariya ganin yadda Asmau tayi kamar ace kyat ta tashi a guje. Mikewa tayi "bari naje na fara shiri ana magriba Baban Amir yace zai zo daukana."

Aina'u ta kinkimi Amir tabi bayanta. Yassar da Umar ne suka rage. Abubakar ya dan kallesu "baku da abinyi ne a ciki kuka tsaya a nan?"

Ba shiri suka tashi suka bi bayan Nasiba. Itama Asmau tashin tayi zata bisu taji muryar Abubakar yana mata magana a hankali
"not so fast Mrs A.A Matawalle. Zance zamuyi. Ko kinfi so nazo gida anjima?"

A kidime take sosai. Tana dago kai ya kashe mata ido daya.

Yau kuma me ya sami Yaya Abubakar tayi tambayar a zuciyarta.

"Soyayyarki ce ta sameni Asmy. Kuma nayi missing dinki da yawa."

Hannu tasa ta rufe bakinta don bata san maganar ta fito ba. Shi kuwa dariya ta bashi ma. Bata saba ganinsa yana nishadi kamar haka ba, sai take ganinsa kamar ba wanda ta sani ba. Duk ya canza.

Ya kula duk bata da nutsuwa kuma shima dai bazai sake ba a falon gidansu inda ake ta shige da fice.
"Ki koma gida anjima zan zo in sha Allah."

Kanta a kasa tace to ta juya zata fita. A takure take dama kamar wadda tayiwa sarki karya.

"Asmy..." sabon sunan da ya rada mata taji ya fada. A hankali ta juyo amma bata iya daga kai ta kalle shi ba.

A tsaye yake shima "dama fuskarki nake son kara gani. Sai na shigo anjima".

Bata iya yiwa kowa sallama ba ta fita da sauri. Ko wayarta bata nema ba wadda tana kallo yasa a aljihun wandonsa.

Har taje gida ta kasa gaskata maganganun Abubakar. Wai ita ya kira Mrs A.A Matawalle. Murmushi ta saki saboda sunan yayi dadi. Kai tsaye daki ta shige ta tarar Shema'u ta dawo daga makaranta.

Itama murna ta fara taya kanwarta ta sannan tace ina sabuwar wayar ta gani.

Asmau ta danyi yake "Yaya Abubakar ne ya karba zai duba amma yace zai kawo min anjima."

Shema'u tace to Allah Ya kaimu. Daga nan hira suka cigaba wadda duk akan shirye shiryen bikin Shema'un ne.

Sai bayan sallar Isha Abubakar yazo. Dayake  ranar babu karatun dare saboda Malam Hadi ya danyi tafiya.

A falo ya same su suna cin tuwo ita da Aina'u a plate daya. Yana sallama Asmau ta tsame hannunta don yadda take jin kunyarsa yanzu ko kallon inda yake ta kasa. Binta yayi da ido yana murmushi har ta shige kitchen.

Shema'u da Yassar suka yi masa sannu da zuwa ya tambayi ina Umma. Yassar ne ya kirata suka gaisa tana tambayarsa ya Ebonyi. Sun sha hira har yake fada mata bazai koma ba sai bayan bikin Shema'u. Makarantar secondary aka tura shi service kuma sun yi hutu.

Asmau tunda ta shiga kitchen ta kasa fitowa. Yana ta kallon hanya yaji shiru. Gajiya yayi ya tashi yayi musu sallama sannan yace Shema'u tazo zaiyu mata magana.

Wurin da Umma ke ajiye mota suka tsaya ya dan shafi fuska "nifa wurin Asmau nazo amma na kasa sanarwa Umma kamar yadda nayi niyya tun a gida."

Dariya Shemau tayi cike da jindadi "Allah Yayi lokaci yayi. Mun dade muna jiran lokacin nan da zaku dena satar kallon juna ayi kowa ya sani".

Ya dan daure fuska yana harararta "Ke nifa yayanki ne kike min dariya. Amma seriously ke da waye 'yan sa idon?"

"Tabdi, Yaya Abubakar kowa fa ya gano ka tuntuni. Su Umma ma duk jira suke hasashensu ya zama gaskiya. Yanzu ma da ka kalli kofar kitchen sai Umma tayi murmushi."

Kunya yaji sosai "kice kawai na dena zuwa gidan nan. Ga wayarta ki bata, ni yanzu kunyar ganin Umma nake yi ma."

Shema'u dai dariya tayi ta masa da tsokana har ya tafi. Tana shiga gida ta bawa Asmau wayarta sannan ta sanar da Umma yadda suka yi da shi. Kasa boye farincikinta tayi saboda sun jima suna jiran hakan ita da Mama. Asmau ta kira ta bata izinin zata iya tsayawa da Abubakar tunda ko yanzu za'a iya aurar da ita a shekara shabakwai. Sannan  ta ja mata kunne sosai game da kare mutumci duk da dai ta yaba da tarbiyar Abubakar.

Asmau kamar ta shige kasa don kunya wai ita Umma ke yiwa nasihar fara zance. Bayan ta koma daki missed calls ta gani da numba an sa _Mine_. Duk tunaninta tasan batayi saving numbar kowa da wannan sunan ba. Tana kallon wayar aka sake bugowa ta dauka. Muryarsa taji mai dadin sauraro musamman idan yana karatu. Ya ce
"My Asmy"

A hankali tayi magana "Yaya Abubakar?"

"Sunan da kika gani kenan da aka kira ki?"

"A'a" ta amsa tana dan murmushi

"Wane suna kika gani?"

Lallai ma Yaya Abubakar so yake ta fadi sunan da ta gani yaji dadin cewa tayi rashin kunya. Shiru tayi har kusan minti biyu babu wanda yayi magana.

Ya numfasa har tana jin sautin "idan na dameki ne bari na ajiye wayar."

Da sauri ta ce ba damunta yayi ba.
"To ki fadi sunan da kika gani don shi kadai zan rinka amsawa daga gareki idan har kin yarda nan gaba kadan ki zama matata."

Wani irin dadi taji yana ratsa zuciyarta. Bata taba sanin soyayya ba sai akansa. Muryarta kamar mai rada yaji ta ja kalmar
"Mine"

Ji yayi kamar yafi kowa nishadi a wannan lokacin. Bai ja ta da hira sosai ba sai dai duk abinda ya fada mai tsayawa ne a rai. Da suka yi sallama wata hirarsu ta tuna da Walida inda take ce mata babu wanda ya kai ustazai wadanda suka koshi da boko kuma suka dauki koyarwar Al'Qurani da hadisi a matsayin jagoran rayuwarsu iya soyayya. Kafin tayi bacci yayi mata text ya kai biyar duk na kalamai masu ratsa zuciya.

Cikin dan lokaci kowa ya san soyayyar Abubakar da Asmau. Mama ta kara nuna mata so tamkar 'yar cikinta. Duka gidajen biyu babu wanda alakarsu bata burge shi. Ya zauna a Kano har akayi bikin Shema'u da sati daya sannan ya koma Ebonyi. Waya kam shi da Asmau kullum ne sai sunyi. Soyayya suke yi mai tsafta saboda dukkansu sun fito daga gidan tarbiya. A can garin ma shine Amir din Muslim Students' Society (MSS) dinsu suna kiransa Young Ustaz.

*****
Admission ya fito Asmau bata sami medicine ba sai pharmacy. Abubakar yace ta karba ta godewa Allah domin zabinSa a kodayaushe shine alkhairi. Haka kowa tayi registaration dinta tayi sa'a Walida ma shi aka bata saboda haka kullum suna tare.

Yana dawowa Abdulhalim yayi aure Mama tace gidan nata duk ya daye saura su biyu shi da Umar. Shima aiki yake nema ido rufe saboda a fara maganar aurensa da Asmau. Baba yayi musu gini duk su uku mazan a wuri daya gate ne ya rabasu. Amma yace daga nan kuma mutum ya nemi aiki ko sana'a sannan a fara batun aure.

Itama Umma a nata bangaren sai siyan kaya take tana ajiyewa kada biki ya tashi batayi tanadi sosai ba. Da bikin Shema'u dangin babansu na nesa sune suka bata gudummawa. Hajjo da 'ya'yanta da suke makusantansu babu abinda sukayi mata. Daurin aure dai Alh Rabe ne ya karbi sadaki...su Rabe an zama Alhaji sakamakon  kujerar Makkah da shugabar kamfanin da yake aiki Haj Rufaida ta biya masa. Shiyasa wannan karon Umma ta kara dagewa don fita kunya.

No comments:

Post a Comment