ABINDA AKE GUDU🙆🏽16
Batul Mamman💖
Wannan karshen satin tun alhamis Abubakar yazo. Kullum sai yaje wurin Asmau sunyi hirarsu yadda suka saba. Ranar asabar ya wuce Shanono wurin Qasim suka je daurin auren wani dan uwan Qasim din. Daga nan suka koma gidansu sai zuwa yamma yayi niyar komawa cikin Kano.
Zaune suke a dakin Qasim suna kallon ball wayar abokin nasa tayi kara. Rage sautin TV din yayi ya amsa wayar. Ya dan jima suna hira d wadda Abubakar ya fuskanci mace ce sai daga baya yaji akalar hirar ta canja. Qasim yana tambayar yarinyar wane irin kaya ta saka.
Murmushi yayi bayan ta bashi amsa "me kika saka a ciki?"
"Ni kwance nake a daki da shorts(gajeren wando) ina shan iska ina tunaninki" (karya yakeyi. Kufta da wando ya saka).
Irin wannan hirar ya kusa rabin awa suna yi da budurwarsa. Abubakar sai kada kai yake don takaicin wannan hali na Qasim. Yayi fadan da nasihar har ya gaji gashi ya kasa rabuwa dashi saboda shakuwarsu. In dai hirar banza ce a waya to Qasim ya ciri tuta. Sai ance ya fidda matar aure yace duk mata babu tagari.
Mugun kallon da Abubakar yake jifansa dashi yasa ya katse wayar yana dariya.
"Ya Ustaz irin wannan harara haka. Ni fa bance ka tsaya jin hirar ba duk ka wane hade rai."
"Yanzu bazaka dena wannan muguwar dabi'ar ba? Ina jiye maka tsoron kada watarana kayi me gabadaya. Kasan zuciya bata da kashi".
Kujerar kusa da Abubakar ya dawo ya zauna.
"Kaima kasan duk abuna bazan yarda nayi lalata da 'yar mutane ba. Irin wannan hirar dai da dan abinda ba'a rasa ba shi muke yi don mu rage yawa.
Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma matan suna so. Sai a taimaki juna".
Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA SAA'A SABILA*
(ISRA' 32)
Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_
Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu azo ana cizon yatsa."
Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai shaidan bai barshi ba.
"Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take. Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse."
Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka".
Qasim ya dubi abokinsa. Tabbas Abubakar ba tun yau ba baya cikin maza masu kallon mata. Shiyasa ake masa kallon mai kunya sosai shi kuwa yana yi ne don ya kare zuciyarsa.
"In Allah Yaso zanyi kokarin denawa sai dai fa abin sai a hankali. Bazan maka karya ba wallahi na saba sosai. Allah mun tuba."
Da haka hirar ta kare bayan la'asar Abubakar ya koma gida.
*****
Washegari lahadi Umma ta tafi da Aina'u yinin 'yar wata kawarta sai Asmau da Yassar a gida Abubakar ya kirata a waya zai zo suyi sallama don yau da wuri yake son tafiya.
Sauri tayi ta karasa girki sannan tayi wanka ta canza kaya. Kwalliya tayi sosai irin yadda take karantawa 'yan matan littafi na yiwa samarinsu. Ta saka wata doguwar rigar atampa maimakon ta daura dankwali tasa hijab ko mayafi mai mutumci yadda ta saba sai ta dauko wani karami a kayan Aina'u ta yafa rabin kanta da yasha sabon kitso duk a bude ta gaba. Falo ta koma ta zauna sai taji kunyar ya ganta a haka. Ta tashi ta koma zata canza wata zuciyar tace tayi zamanta abinda sun kusa aure kuma dai haka ake yi yanzu don ita duk abinda ta karanta har ranta gani take yi daidai ne saboda a yadda ta dauki marubuta masu buga littafi da online komai suka rubuta basa kuskure.
Sake shafa hoda tayi ta dawo falon. Tana zama Abubakar yayi sallama tare da neman izinin shigowa ta amsa masa.
Gabansa ne ya fadi da yaga Asmau. Tayi kyau sosai gashi tana da 'yar kiba sai rigar ta kamata a kirji da kugunta. Ba wai bai taba ganin yanayin jikinta ba saboda yau da gobe yakan ganta babu mayafi amma sai bisa kuskure. Yau kuwa shigar ta tsaya masa a kokon rai har ya kasa dauke idonsa daga gareta.
Murmushi tayi na nasara saboda yadda taga yanayinsa ya canza. Tunda ta fara karance karance da hirarsu da Walida taji ta matsu ko hannunta ne ya dan rike itama taji yadda ake ji.
Wani juya ido tayi duk sauran kunyar suka bace "Mine ka zauna mana."
Wani jan numfashi yayi "Asmy kinyi kyau"
Tayi masa murmushi "nagode"
"Kaci abinci ko na kawo maka? Bana son ka tafi da yunwa".
Abincin ya bukaci ta kawo masa. Ta tashi tana tafiya mai daukar hankali. Har ta shige kitchen ya kasa dena kallonta. Sai da ta bace yace _Astagfirullah_ tare da kudurta niyyar zaice ta suturta jikinta sosai.
Tana dawowa kujerar gefensa ta zauna kamshin turarenta ya bugi hancinsa sai ya fasa cewa ta rufe jikin. Yana matukar son Asmau amma yau harda wata muguwar sha'awarta ce ta taso masa. Yana cin abinci suna hira kadan kadan domin duk hankalinsa ya koma kan halittar jikinta.
A nata bangaren ta lura da canjawarsa kuma taji dadi a ranta. Da ya tashi zai tafi dubu biyu ya miko mata kudin motar makaranta. A da sai ya bata sau uku bata karba ba har suyi fada wani lokacin. Amma yau kawai don taji hannunsa a nata ta mika hannun a kunyace tana kallon kasa. Tana sane tayi hakan hannunta ya kai kan nasa maimakon kudin.
Saurin dauke hannun tayi saboda wani yanayi na daban da taji (dama shaidan komai kankantar haram dada mata dadi yake fiye da yadda take don kawai a cigaba da aikata ta)
"yi hakuri ban kula ba"
Abubakar yaji dadi fiye da yadda taji domin tana taba hannunsa ji yayi kamar ya janyota jikinsa. "Dama ina zaki kula kina wani sunkuyar da kai kasa. Ni zan tafi sai friday in sha Allah. Ki kular min da Asmy na".
Tana murmushi tace
" nima ka kular min da Yayana. Allah Ya tsare Ya kaika lafiya."
Haka Abubakar ya tafi surar Asmau tana yi masa gizo. Sawa yayi a ransa idan sunyi waya zai fada mata ta dena irin shigar nan har sai sunyi aure. Sai dai yana isa bayan sallar magriba wasu hotunanta suka shigo wayarsa. Duk babu wanda tasa dankwali kanta wasu ma rigunan sun dameta fiye da rigar dazu.
Bai iya yi mata maganar da yayi niyya ba ya rasa dalili.
A haka suka kwashi wajen wata biyu. Asmau ta dena jin kunyar fita gabansa da shigar bayyana jiki indai tayi sa'a yazo Umma bata gida. Mayafin nan kullum a kafada an baza gashi ta kasan dankwali. Tun yana tsanar kansa idan suka rabu har ya saki rai yana jindadin hakan tunda yasan aurensu yana kusa. Kusa da juna suke zama yanzu ana hira sai su rinka neman hanyoyin taba hannun juna kowa yana nuna kamar ba hakan bane a ransa.
Sai yanzu Asmau ta yarda suna soyayya domin tafi jindadin alakarsu. A zuciyarta ta kwantar da hankali tunda tana da yakinin aure zasuyi kuma dai ana aure komai ya wuce. Ita yanzu babban burinta yayi kissing dinta ko sau daya ne yadda take karantawa. Ayi kiss amma sai a nuna kamar bisa kuskure ne ko kuma a nuna na komai yin hakan a addini da al'adarmu.
A nasa bangaren shima ya dena damuwa. Kullum sha'awarta karuwa take yi a ransa hakan yasa ya soma rasa nutsuwarsa. Bashi da aiki sai azumi kamar mai kaffara amma wasu ranakun shi kansa yasan a irin tunanin Asmau da yake yi na tsantsar sha'awa azumin nan baya kaiwa ko ina.
*****
Su Asmau an gama jarabawa kuma wannan karon suna dawowa makaranta idan aka sake hutu za'ayi bikinta.
Ko sati ba suyi ba da fara hutu Anti Bintu tazo Kano ziyara. Kwananta biyu mijinta yazo da zasu koma tace da Asmau zata tafi. Umma bata musa mata ba ta umarceta da hada kaya. Murna tayi sosai Aina'u kuwa ansha kuka gashi ba'ayi hutu ba.
Abubakar yaji dadin komawar Asmau Zariya wani satin da ya zagayo ko Kano bai je ba. Mama Yalwa tace ta gane dama zuwan ba nasu bane na Asmau ne.
A gidan Anti Bintu yake zuwa su sha hira wadda a hankali ya fara rungumarta da sunan zaiyi kewarta idan ya tafi. Su biyun duk sun san haramcin abinda suke yi amma sunyi nisa. Suna haduwa duk yakin da suka shirya da wannan sabuwar dabi'ar tasu sai ya rushe.
Anti Bintu ko kadan bata san me suke yi ba. Falonta take bar musu idan yazo. Nutsuwa da tarbiya irin ta Asmau da Abubakar babu wanda zai taba zargin haka tsakaninsu.
Wata rana bayan asuba karamin dan Anti Bintu Haidar yana toilet bayan ya gama ya fara kiran Asmau tazo tayi masa tsarki. Lokacin ko bakwai na safe bata yi ba duk baccin da take ji taki komawa saboda an turo cigaban wani labari da take karantawa. Ko yunkurin tashi bata yi ba tace masa tana zuwa.
Haidar ya kirata yafi sau biyar tana cewa gata nan har Anti Bintu ta fito daga kitchen tayi masa tsarkin lokacin har ya fara kuka. Duk abinda suke yi da Asmau ta ji.
Dakin nasu ta shiga Asmau tayi nisa a duniyar labari sai ganin Antin tayi a tsaye a gabanta. Da sauri ta tashi a tsorace zata fita.
"Dawo indai tsarki zaki yiwa Haidar nayi masa"
Duk sai taji kunya sannan ta gaisheta. Anti Bintu ta dauki wayar da ta ajiye akan gado ta bude ta dan karanta wani bangare na labarin. Tayi scrolling sama kuma irin sakon nan ne na kwanciyar aure.
Jikin Asmau kamar mazari don tsoro ta gama rudewa. Anti Bintu ta kama hannunta ta zaunar da ita a bakin gado sannan taja kujerar gaban mudubi ta zauna.
"Kin bani mamaki Asmau. Wannan wane irin text ne kike karantawa? Yanzu kwanciyar aure har sai wata can da baki sani ba ta koya miki? Wannan abu halitta ce wadda idan lokacin yinta yayi baka bukatar malami. Idan kuma har akayi rashin sa'a mace ko miji suka matsala ta fannin gamsar da juna to ba duniya zaki fadawa matsalarki ba. Mutum daya zaki samu cikin 'yan uwa ko abokan arziki wanda zaki iya bawa amanar sirrinki sai ki fadi matsalar a baki shawara. Amma me ya kaiki karanta irin wannan post din wanda ko matar aure ce ta karanta da wuya idan bai karya mata alwala ba saboda yadda ake bayani 6aro-6aro. Kada ki bari kawayen banza suce ya kamata a koya miki irin wannan tunda kin kusa aure. Komai yana da lokaci. Kodayake masu rubutawa sunfi kowa laifi tunda kayi rubutu ne baka san iya idanunwan da zasu karanta ba. Wayar nan yarinyar da bata fara jini ba ma tana da ita kuma akan same su a groups din manya suyi ta sakin baki a gaban 'ya'yan cikinsu. Wani lokacin sai su tura yara masu karfin sha'awa su karanta a tayar musu da hankali su fara neman mafita. Ki rufawa kanki asiri ki dena karanta abinda bazai amfaneki ba.
Abu na biyu wannan novels din da kike karantawa. Nima babarki ina karantawa amma ki sani akwai wanda har ki gama babu wani darasi da zaki dauka sai bata lokaci da tabarbarewar tarbiya. Uwa uba kuma wannan mugun son da muke yiwa labaran yana sawa mu manta da al'amuran da suka fi bukatar hankulanmu.
Tun zuwanki gidan nan na fuskanci kin canja sosai. Kina idar da sallah ko azkar baki gama ba sai ki janyo waya. Har akwai wani labari da zaisa ki kasa hakurin minti biyar ki bautawa Allah cikin nutsuwa? Mata irinki da yawa gasu nan. Sau nawa girki yake konewa ko mace ta yini cikin kazanta saboda karatun labari wanda a ciki tsafta da kula da miji ake koyarwa? Wata ma bata girkin akan lokaci sai taji mijinta ya kama kofar gida zai shigo ta ruga kicin. Wata ta bar yaro da kazanta har sai ta gama karatu. Wata kuwa da wayar zata shigo bandaki tana biyan bukatarta tana karanta labari. Idan hakane karatun labaran masu dauke da darussa bai amfanemu da komai ba sai kasala, ganda da kazanta.
Ki zama mace mai tsari a rayuwa komai kiyi shi a lokacin da ya dace. Babu abin takaici sai kinga mace da tsakar dare ko asubar fari tana cigiyar novel ga mijinta a gefe bawan Allah kila yaso ta bashi hakkinsa na aure ma amma ya hakura don kada ya takurata. Idan mara hakuri ne ayi ta samun sabani.
Asmau nasan Yaya Bara tana kokarinta a kanku. Gashi aiki yayi mata yawa duk don biya muku bukatu. Kada ki watsa mata kasa a ido da dabi'u marasa kyau kinji ko".
An tuno da Idon kuka ana mata fada tana sana'arta. A take tayi nadamar daukar shawarar Walida wanda yasa take yin abubuwan da a da can tasan basu dace ba. Kukanta ya tsananta da ta tuna tabbas irin yadda suke gudanar da soyayyarsu yanzu yana da alaka da canjin da ya fara tasowa daga gareta. Wai ita ce suke rungumar juna da Abubakar. Abubakar dinta mai riko da addini ta zama sanadiyar da suke munafuntar kawunansu da iyayensu.
Anti Bintu ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta tashi. A ranar ta ga canji sosai a wurin 'yar tata. Asmaunta ta da ta dawo.
*****
Abubakar na kwance a daki yana kallon wasu hotunan Asmau. Tun daren jiya da ta turo ko baccin kirki ya kasa yi. Yau da ciwon mara ya tashi irin wanda ake samu idan sha'awa tayiwa mutum yawa. Ya rasa abinda yake masa dadi ko office ya kasa zuwa. Shawara ya yanke zaije Zariya a ranar ko dan yaya yayi dan abinda zai kwantar da kwadayinsa. A yadda yake sonta bazai iya neman wata matar a waje ba. Ita dinma bashi da niyar ayi mai gabadaya ta bakin Qasim. Dan dai abinda ba'a rasa ba yadda sai samu yaji dadi. Da wannan shawarar ya tashi yayi wanka ya hau shirin zuwa Zariya.
No comments:
Post a Comment