ABINDA AKE GUDU 🙆🏽6
Batul Mamman💖
Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci. Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma titi ta tare dan sahu.
Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi magana
"Hajiya ina zuwa?"
"Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume jakarta da akwati.
"Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda zaki je"
Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya
" kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?"
Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace "kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai"
Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe fuskarta da hijabinta.
Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin labarin komai, idan taje wurinsu ba ta tsira ba. Tana cikin wannan tunanin taji ana cewa,
"Azare mutum daya
Azare mutum daya"
Ko dogon tunani batayi ba ta nufi motar da sauri. 'Yan kamasho har sun fara baibayeta ana tambayarta ina zata je. Da shigarta motar dreban yazo suka gama surutansu da 'yan uwansu drebobi ya tada mota suka harbi titi.
*****
Har karfe tara babu motsin Asmau. Anti Bintu da Jafar ne zasu kaita asibitin duk sun shirya. Umma tace aje a tashe ta idan batayi wanka ba su tafi a haka ta yi idan sun dawo.
Aina'u aka tura taje ta dawo tace bata ganta ba. Shema'u tace kila tana bandaki kije kice mata tayi sauri ita ake jira.
Da gudu Aina'u ta dawo tace "Anti na duba bata daki kuma bandakin a bude yake".
Umma na jin haka tace a tashi a dubota karshenta buya tayi saboda kada aje asibitin. Da farko Yassar da Aina'u kadai ne suka duba dakunan da bayan gidan suka dawo basu ganta ba. Hakan ya soma tsorata Umma kowa ya tashi a rude suka shiga nemanta. Ganin babu alamun za'a sameta a gida Shema'u ta kira wayarta. Tayi mamaki jin muryar Walida. Bayan sun gaisa Walida tace wayar na hannunta. Tun ranar da abin ya faru zance ya fara bazuwa mahaifinta har gidan yazo ya dauketa da kansa lokacin da aka sake mayar da Asma'u asibiti kuma ya haramta mata sake zuwa gidan.
Shema'u tayi kasake har Walida ta gama bayani sannan tace zata turo Yassar ya karbi wayar. Tana juyowa Umma ta kalleta a tsorace
"Kada kice min an sace wayar ne".
"A'a Umma tana wurin Walida."
"To ina Asmau ta shiga, ni Bara'atu daga wannan sai wannan".
Da gudu Jafar ya dawo falon da takarda a hannunsa wadda ya gani a tsakiyar gadon dakin su Asmau. Jiki babu kwari ya mikawa Umma ta karba hannu na rawa.
_Umma ina mai rokon gafararki a lokacin da kike karanta wannan takardar nayi nisa da gida. Nayi nadama da bakincikin halin da na saka ku na kuma jefa kaina. Sai dai na dauki komai a matsayin kaddara. Na tafi ne saboda bana son ku daukarwa kanku zunubin kashe rai. Zan haifi abinda ke cikina da izinin Allah zan kula dashi batare da na fada mummunar rayuwa ba. Ki yafe min kuma ki cigaba da yimin addu'a. Allah Ya hadamu cikin aminci. Sannan ina mai kar tabbatar muku cikin nan na Abubakar ne. Ku yafe mana._
_Asmau_
Kuka mai sauti Umma ta saka wanda yasa Shema'u saurin karbar takardar ta karanta. A take itama ta fashe da kukan. Umma sai sumbatu take saboda tsabar tashin hankali.
"Asma'u ki dawo wallahi babu mai cire miki cikin. Ki dawo na yafe miki. Ina zaki je ke kadai a wannan duniyar da amana tayi mana karanci?"
Duk wanda yake wurin sai ya tausayawa Umma. Dama da mayafi a jikinta tace Jafar ya dauko mukullin motarta yazo su fita neman Asma'u. Nan da nan kowa ya fita suka fara karade unguwar. Daga nan sune gidajen kawayenta da tashoshin mota tare da hoton Asmau suna tambayar ko an ganta.
*****
Karfe goma na safe tayiwa Qasim a kofar shagon mai gyaran waya. Mai shagon a wurin ya sameshi a ransa yace dan anace ya iso. Allah Ya taimake shi ya gama gyaran shiyasa da fara'arsa yace "ranka ya dade ai yanzu nake shirin kiranka idan na bude shagon."
"Baka da abin da zaka fada min. Gyaran waya sati guda kuma na biyaka. Kawai sai ka zauna kana ja min rai."
Gefe ya matsa mai shagon ya bude. A cikin wata drawer ya dauko wayar Qasim wadda screen dinta ya fashe tun ranar alhamis da ya iso garin Zamfara. Duba wayar yayi ya tabbatar tayi sannan yayi sallama da mutumin ya fita.
Bakin titi ya koma inda ya ajiye motarsa. Yana shiga ya kira mahaifiyarsa bayan sun gaisa ya sanar da ita wayar ta gyaru zata rinka samunsa. Dama ta wani yake ara a ofishinsu ya saka sim dinsa ya kira. Karamar wayarsa tana wurin kanwarsa da ya bawa kafin ya taho.
Bayan yayi sallama da ita ya kira numbar Abubakar. Kullum idan ya ari waya sai ya gwada amma a kashe yake samunta. Dariya kawai yake yi yace ango ya dau hutun waya kenan. Sai da aka fi kwana uku a haka ya fara damuwa ko sace wayar aka yi. To da yake data aro yake amfani shiyasa bai matsa ba sosai. Yau kuwa yayi sa'a gwaji daya ta shiga. Sai da ta kusa tsinkewa yaji an dauka. Ko magana bai jira anyi ba yace
"Haba mutumina, daga aure sai ka yar dani. Nayi ta kira bana samu gashi tawa wayar ta lalace. Ya madam? Ina fata duk kuna lafiya."
Shiru yayi saboda yaji ba'ayi magana ba.
"Hello, Abubakar ko baka jina ne?" Ya dan cire wayar yana dubawa ko gyaran ne baiyi ba.
Daga daya bangaren yaji ance "Qasim".
Muryar tayi kama da ta Abubakar sai dai ya tabbatar bashi din bane.
Rike wayar yayi yaji an sake kiran sunansa sannan ya amsa
"Ango me ya sameka ne? Naji muryar taka taso ta canja min."
Abdulhalim ya hadiyi yawu sannan ya shafa kansa yana tunanin da yadda zai fadawa Qasim abinda ya faru.
"Qasim nine Abdulhalim, dama Abubakar ya fada min anyi maka transfer a wurin aiki da karin girma".
Sai a lokacin Qasim yayi ajiyar zuciya da ya gane mai maganar
"Wallahi kuwa baban Yaya. Kuma da yake ko wata ba'ayi da bani query ba shiyasa dole na tafi kada nayi laifin da za'a koreni. Daga karin girma ace na fara wasa da aiki" Yana dariya yake maganar sannan ya tambayi ina amininsa ango Abubakar.
Shiru Abdulhalim yayi na dan lokaci sannan yayi ajiyar zuciya yace
"Qasim Allah Yayiwa Abubakar rasuwa a ranar daurin aurensa".
Wani duhu-duhu Qasim ya fara gani da kyar ya iya cewa "kai, karya ne Wallahi. Abubakar din? Abubakar fa nake nema kaninka mai wannan layin".
Abdulhalim yasan za'a rina. Abubakar da Qasim abokai ne tun aji daya a firamare. Cikin nutsuwa ya labartawa Qasim abinda ya faru.
Tamkar karamin yaro haka Qasim ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace "ina Asmau?"
"Tana gidansu" Abdulhalim ya bashi amsa a takaice. Qasim yayi alkawarin zuwa Kano a satin idan ogansa ya bashi dama. Mahaifiyarsa bata sami zuwa bikin ba saboda ciwon kafa kuma kanwarsa wadda su biyu ne dama ita take jinyarta. Kila shiyasa basu ji zancen rasuwar ba tunda a Shanono suke.
Daga nan suka ajiye wayar Qasim ya tafi office. Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. Koda yaje wurin ogansu da hawaye a fuskarsa ya fadi bukatarsa. Labarin ya taba zuciyar ogan ya bashi damar tafiya a ranar ya dawo wata lahadin.
Gidan da aka bashi yaje ya canja kaya cikin kankanin lokaci ya kama hanyar Kano.
*****
A can Kano an bazama neman Asmau. Umma tayi kuka har ta gaji. Hajjo da 'ya'yanta suka zo har gidan suka yi mata abinda suka saba. Har cewa sukayi ita ta turata yawon karuwanci.
Da zance ya kai kunnen Mama Yalwa ko kadan bata ji dadi ba haka ma Baba da sauran 'ya'yan gidan. Sun tausayawa Umma sosai Baba yace zai sa a bada cigiya a kafafen yada labarai.
*****
Shiru Asmau na zaune a cikin mota banda addu'a babu abinda bakinta yake ambato. Tana daga gefe ta ja hijab dinta ta rufe rabin fuskarta. Sunyi nisa sosai taji wani daga gaba yana tsaki da zage-zage. Na kusa dashi wanda da alama abokinsa ne yace "ya dai kake tsaki kai kadai Bala?"
Wanda aka kira Bala ya nuna masa wani hoto a wayarsa "ka duba don Allah yadda ake rashin imani a duniyar nan. Dubi fuskar yarinyar nan kai kace idan aka saka mata hannu bazata ciza ba...."
Hankalin sauran 'yan motar ya koma jin jawabin Bala. Shi kuwa ya cigaba da magana cikin bacin rai "....wai yarinyar nan ce ranar aurenta ta kashe mijin saboda ya gano tana da ciki kuma yace ba nasa bane. A cikin gidansu fa aka tsinci gawar tasa a bandaki ta buga masa guduma a keyarsa bayan an kai ta, ance a halin yanzu tana hannun hukuma. Shegiya Allah Yasa su harbeta ma"
A hankali Asmau ta daga kai ta kallo hoton da duk 'yan motar sai da suka karbi wayar suka gani. Gabanta ne ya fadi sosai da taga hotonta ne. Cikin dan lokaci an canja labarin gabadaya. Ba karamin mamaki tayi ba da taga hoton da ita kanta yanzu bata dashi a wayarta. Mutane kamar jira sukeyi abu ya faru sai ayita yayatawa ana ta kara gishiri da maggi a zancen. Kafin ka ankara zancen ya sauya daga ainihin yadda yake. Shiyasa ake so mutum ya kiyaye me yake saurin turawa mutane a kafafen sada zumunta (social media).
Sake rufe fuskarta tayi don kada su ganeta. Wani daga kujerar baya yace "nima ina da wani hoton nata daban da wannan harda mijin" wayar tasa ya miko shima da hotonsu na dinner ita da Abubakar.
Mutumin ya cigaba da cewa "ni a yadda aka turo cewa akayi kafin a daura auren aka tsinci gawarsa a bandakin hotel shine aka kalawa yarinyar. Ana tunanin wata yayiwa ciki ta kashe shi."
Har zuciyarta zancen yayi mata daci sai dai kafin a gama ganin hoton wata tace itama taji labari amma cewa akayi rasuwa yayi a gidansu kuma a ranar aka gane amarya nada ciki. An rasa gane ko cikin waye nasa ne ko na yayansa don amaryar tana bin maza.
Duk masu bayani na matar ne yayi kama da gaskiya. Duniya kenan, kowa da abinda zai ce ba tare da yasan gaskiyar lamari ba. Asmau tana ji motar ta kaure da tsine mata ita da Abubakar ga wadanda suka yarda ciki yayiwa wata. Rufe ido tayi kamar mai bacci tana kukan zuci har suka shiga tashar Azare ta jihar Bauchin Yakubu.
No comments:
Post a Comment