Saturday, 14 January 2017

Silar Ajali

Silar Ajali
Alkalamin SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

BABI  NA DAYA

Kwance ta ke kan gadon karfen ta, zuciyarta na bugu fiye da bugun sa, cikinta na murɗa mata tamkar mai shirin  gudawa, duk da haka kwakkwaran juyi ma kasa yin shi ta yi,  tsoro ne fal a cikin ranta Kasancewar ba ta san abinda daren yau zai zo mata da shi ba .

Da ya ke wata ya kai ashirin da shida, duhun daren ya wuce misali,  gari yayi baki kirin ko ganin tafin hannunta bata yi. Sassanyar iskar bazara da ke kaɗawa,da kuma kugin iska da ke tashi daga rassa da bishiyoyin kankarar bai hana zufa keto mata ta koina daga jikin ta ba, sai ma tsoron da ya ke daɗa shiga cikin ran ta don har ganin kamar gilmawar inuwar mutum take hakan ya sa ta kara gimtse idanunta gam, don bata ma son tsautsayi ya sa ta buɗe su. Duk da dai ba ta san takamamman lokaci a yanzu ba, ta san dai akalla karfe ɗaya na dare zai yi.

"Ba shakka ya kusa zuwa, yanzun kuwa zai zo"

Ta faɗa a ranta don kuwa kusan sati daya kenan a jere ya kan zo mata Idan ta na bacci sai dai kawai ta ji hannaye na bin kafar ta ko ma jikin ta, da fari ta yi zaton ko tunanin ta ne ko kuma aikin aljanu ne, sai da ta kama hannu ta rike kamin ta tabbatar da mutum ne ba aljani ba.

Ko da ta fadawa Yagana, wato babbar ɗiyar kanwar mahaifiyar ta wacce ta ke hannun ta, ita kuma ta ba ta shawarar ɗaukar mataki.

Jin kamar an tura kyauran ɗakin, gaban ta ya faɗi , ta yi karfin halin daɗa jawo goran da ta ajiye kusa da ita hannu na rawa, sannan ta yi lamo kamar mai bacci. Kusan minti goma ne ya shuɗe ba tare da ta ji wani abu ba, har ta fara tunanin tsoronta ne kawai, ilai kuwa sai hannu ta ji yana shafar kafar ta, daskarewa tayi a nan wajen don kasa numfashi tayi tsabar firgita, ji ta ke rayuwarta ta zo karshe don duk tattalinta wani na shirin wargaza mata rayuwa duk da karancin shekarunta.

Ta na jin hannun na shafa ta, har aka zo ga cinyarta, ganin hannun na yin gaba-gaba fiye da kullum ya sa ta yi saurin ɗaga sandar ta rantama dai-dai saitin da take tunanin mai hannun na wajan.

Ta ko ci sa'a dan kuwa ihu ta ji an saki, hannun na rawa ta ɗauki fitilar toci ɗin da ta b'oye karkashin matashin kai ta  kunna don ta tabbatar da muryar da kunnuwanta suka jiyo mata. Kunnawar da tayi yasa hasken ya garwaya  ɓangaren da ta haska cikin ɗakin.

Nan take idanun ta suka sauka a kansa in da ya ke kwance ya na burgima, jini ya wanke fuskar sa sanadiyar fasa masa kai da ta yi. Ganin hasken ya sa shi tashi zai fice a guje.....kan ya kai ga bakin kofa,  ya ji muryar ta da ke kakkarwa, cike da mamaki ta ke furta

"Baba.....Baba...Baaaaba"

Dakatawa yayi, sai da yai jim na wasu dakiku kana ya juyo ya na mai watsa ma ta wani irin mugun kallo, nan ta kara tsorata ganin irin raunin da ta ji masa, sannan ya fice da sauri.

   Cike da tsoro, ta kasa ko motsa yatsanta balle ta nemi tashi daga inda ta ke dan kuwa sam ba ta yi zato ba, ba ta taɓa tunani ko kawo abin cikin zucuyar ta ba

"Baba!  Baba!!!!! Baba fa......."

Abin da ta ke ta maimaitawa cikin zuciyar ta kenan amma kwakwalwarta ta kasa ɗauka, don kuwa idan har Baba zai iya aikata mata wannan mugun aiki haka, toh wa za ta yarda a duniyar nan?
  
                         ***

   Washagari da asubar fari ta ji hayaniyar Baba da Inna, wacce ke cikin ɗanyen jego, hayaniya ce ke  tashi daga tsakar gida wanda ya sa Sauran mutanen gidan firfitowa don jin ba'asi da samun rahoton kai wa gaba,  abinka da gida ba su kadai ba, gida na haya mai ɗauke da ɓangare ɓangare har goma.

Hakan bai sa Baba ya sassauta ko ma ya dai na kururuwar da kumfar bakin da ya ke ba, Jin ana buga qyauren ɗakin da ta ke, ya sa ta tashi da sauri ta na mai raba idanu.

   "Za ki fito kokuwa sai na shigo na fito da ke yar nema gantalalliya"

Faɗin Baba kenan ya na mai kumfar baki da haki kamar in ta qara wasu mintoci zai ɓalle kofar ne ko ma fushi ya kai shi ga rusa ginin  gaba xaya. Jin haka ya sa ta fitowa da sauri zani a hannu ko ɗankwali bata tsaya ɗaurawa ba.

Baba ta gani tsaye bakin kofa, Inna rike da jinjirinta ɗan sati biyu tsaye ta na zubda hawaye, ga kuma sauran yaran Inna biyar,suma ɗin kuka su ke, duk da dai kananun ba wani fahimtar abin da ke faruwa su ka yi ba, ganin hawayen Inna ya sa su kuka. Sai kuma sauran jama'ar gidan da su ka fito jin kwakwaf.

   Ba kunya ba tsoran Allah Baba ya dube ta yana mai mazurai tare da faɗin

"Faɗa mu su da bakin ki, abin da ya faru jiya"

Da sauri ta ɗaga ido ta kalleshi, duk da dai yarinya ce qarama ta san a iya tunanin ta wannan ba magana ba ce da za'a yi ta gaban jama'a ba, dan haka sai ta yi saurin yin qasa da idanun ta,ta ba tare da tayi magana ba. Shi kuwa Baba dama abin da ya ke so kenan, dan ya san a zahiri ba za ta iya buɗe baki a cikin jama'a haka ta tona masa asiri ba, dama da gangan ya tambaye ta dan ya samu ya ɗaure ta da hakan.

Tun da hakan sa ya cimma ruwa, buɗar bakin sa sai cewa yayi

"shegiyar kaya, dama ai ba kya iya magana ba! Toh ke Amina (Inna) ga ta nan, dama na faɗa mi ki in dai wannan hatsabibiyar yarinyar ce sai ta sa ki kuka da idanun ki, gashi tun ba'a je ko ina ba ta nuna halin ta, yanzu sai ki tasa ta a gaba ta miki bayanin gun wa take zuwa duk tsakar dare na duniya, sati guda kenan ina ganin ta, jiya da daddare ko da na bi ta a baya, saɗaf saɗaf na ga ta buɗe kofa  ta fice. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayanta, don ni a gani na yarinyar nan amana ce gun mu, ko ma menene ya same ta mu mu za mu ji a jiki, ashe yarinyar nan fako na ta ke, ta haɗa baki da kwarton da ta ke gani, ban ankara ba sai saukar gora na ji bisa kai na, ku duba ku gani ya fasa min kai........"
Ya qarasa yana mai fashewa da kuka.

Gaba ɗaya wajen ya kaure da hayaniya, kowa na faɗan albarkarcin bakin sa, wasu na faɗin za ta aikata, wasu kuwa faɗi suke abin da mamaki, dan kuwa yarinya dai natsattsiya ce, kuma dai mutum babba kamar Baba ba zai yiyu ya yi karya ba.

Ita kuwa don mamaki kasa magana ta yi, baki na rawa ta ke duban Baba da ke ta faman kukan munafunci. Inna ce wacce ta kasa gane komai, ta ce da ita ta shiga ɗakin ta, yanzu za ta biyo ta. Ta juya za ta shiga kenan Baba ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar tare hanyar da za ta kai ta ga ɗakin ya na faɗin

"Lillahi warasulihi yarinyar nan sai ta bar min gida a yau! ke ba ma ita ba, har sauran shegun yan uwan na ta!"

Jin haka Inna na fidda kwalla ta ce
"Shegu fa ka ce Malam! yanzu yaran yar uwar tawa ce kake kira da shegu, wani asiri naka ne bata rufe ba?"

Ya shiga kif-kifta idanu ya ce

"Su kuwa, na ce wanene uban su? ko kin taɓa ganin sa bayan ga labarin kanzan kurege da ta aiko mi ki na ta yi aure a Saudiyya, ta auri ɗan Sudan, sai kuma bayan shekaru biyar ta turo miki yara har uku, wai saboda tsada da wahalar rayuwa ki rike mata su,  ina ki ke da tabbacin da gaske auren ta yi? idan auren ne uban su ko dangin sa su riqe mata su mana! wallahi sai sun bar min gida! su je can idan ma hali irin na uwar ta ta za ta yi ba dai a gida na ba!" ya na faɗin haka ya rufo kofar ɗakin Inna.
    Kuka Inna ta sa, dan kuwa ya kwance mata zani a kasuwa, haka ma yarinyar da tabbas ko Baba bai ce su bar masa gida ba ta san zaman gidan dai ya kare musu, ba ma gidan ba garin kano gaba ɗaya, dan kuwa dai ta san kafin gari ya waye tuni sunan su da aka san su da shi zai ɓata a koma kiran su da shegu. Da wannan ɗacin a ran ta juya a guje ta shige ɗakin ta, ta shiga haɗe yan kayan ta cikin Ghana must go, ta na yi ne ta na kuka har ta gama haɗa kayan,  ta zauna a saman jakan kenan sai ga yan uwanta maza biyu sun shigo, babban wanda kallo ɗaya zaka masa ka san ya girme mata,  shi ke dauke da jakan kayan su, karamin da ko gama watsakewa bai yi ba fuskar sa duk  yawun bacci ko ina ya ce da ita

"Didi wai Baba ya ce mu bar masa gida, ina zamu Didi? Ko wajen su Mama za mu?yaushe za mu ga Mama Didi?"

Ya fashe da wani sabon  kuka mai. Karya zukata. Hannun sa ta ja ta na mai faɗin

"Kar ka damu autan, Allah shi ne gatan mu"

Babban kuwa bai iya furta komai ba, jakan hannun ta ya karɓa su ka fito tsakar gida in da Baba ke tsimayen su, haka ma sauran yan gulma. Ga shi dai an tada sallar asuba amma gulma ya hana su zuwa masallaci.

     Gaban Inna ta je ta durkusa, ta na mai neman gafara. Ganin haka shima karamin yayi hakan yayin da babban ya kara rike hannun jakan tare da sunkuyar da kanshi  don baya so kowannen su ya ga rauninsa. Inna na kuka ta rungume ta,kana ta ce da Baba

"Malam ka yi wa Allah ka yi hakuri ka bar yaran nan"

Baba ya gyara tsayuwa sannan ya ce

"Kin san Allah,wallahi sai sun tafi,yanzun nan ma kuwa!"

Nan fa mokota su ka yi yunkurin sa baki, amma Malam yayi kyememe ya hana. Inna ta kwance gefan zanin ta,ta fiddo da kuɗin cinikin ta na daddawa ta mik'a masa , kana ta ce

"Gashi kuyi kuɗin mota zuwa Katsina sai ku je MARKE,  ku je wajen salame  kun san ko da ace kowa zai guje ku salame ba za ta taɓa guje muku ba don ita ta haifi uwar ku, akwai wasu dangin mu a nan unguwar Gwammaja, amma ban san tak'amamman in da su ke ba, da can zan ce ku je ku neme su, Allah ya fishe ku alkahairi"

Hannu biyu ya sa ta karɓa, nan fa kowa ya shiga ba su abin da ba'a rasa ba, mai Ashirin, hamsin har naira ɗari. Inna ta k'ara rokon Baba da ya bari gari ya k'ara wayewa sa tafi,tun da yanzun asubahi ne. Maimakon ya amsa mata, sai ma tasa su gaba da yayi, Inna da yaran ta na kuka, haka ma yarinya da yan uwanta ta,har su ka fice daga gidan.
Sai da ya tabbatar ya raka su har bakin titi kafin ya juya ya bar su cikin halin ko in kula. Babban ne ya dubi yarinya ya kira sunan ta da
"Salma"

Ta na me goge hawaye,ta amsa da

"Na'am, Ya Salman, wallahi Baba sharri ya ke min, shi ne fa duk dare sai ya shigo min ɗaki....."

"Yi shiru da maganar nan Salma, za mu yi ta amma ba yanzu ba, tun da kin tsira da mutuncin ki shikenan ai,kan sa ya yiwa. Yanzu ɗaura kayan ki bisa kan ki, bari na goya Suhayl, dan mu yi sauri, kin ga mik'ak'k'iyar tafiya ce a gaban mu, Allah ya taimake mu, mu sami mota tashin farko a tasha" Da wannan Salma ta aza kayan ta bisa kan ta, Suhayl a bayan Salman, ga kuma sauran kayan na su a hannun shi, su ka sa hanyar tasha a gaba. Tun gari na da sauran duhu har gari ya waye tangararan.

    Ba k'aramin tafiya su ka yi ba kafin su k'arasa tasha. Duk da safiya ce tashar ba laifi akwai mutane da dan dama, ga motoci jere direbobi sai ihun neman passenger su ke, ga kuma yan kabu-kabu da dako, wanda da sun ga mutum ɗauke da kaya sai su yi kan sa da sauri su na mai riga-rigen karɓan kayan domin yin dako. Haka kuma yan tallan abubuwa Iri-iri kamar su koko, gyad'a da dai sauran su, da kuma mai tuyan kosai.

  Ganin su Salman ɗauke da kaya yan dako su ka yi kan su da sauri. Salman ya dakatar da su ta hanyar ɗaga musu hannu ya na mai faɗin

"ku bar mana kayan za mu iya d'auka"

Jin haka su ka bar su da kayan su suna masu faɗin

"Dan bakin ciki sai ku rike tsiyar ku ai!"
   Wani ne ya k'araso gare su ganin sun yi cirko-cirko tsakiyar tasha, ya na duban Salman ya ce yaro ina kuka nufa ne? Buɗarbakin Salman sai cewa yayi "MARKE aka ce mu je, cikin garin Katsina" kai mutum ya gyad'a ya ce motar Katsina  za ku hau kenan, golf za ku hau ko bus?golf dai dubu ɗaya ne ko wani mutum ɗaya , bus kuma ɗari biyar.

Ba tare da wani dogon tunani ba Salman ya bashi amsa da

"Bus din zai fi"

Dan kuwa ya san nauyin aljihun su ba lalle kuɗin da ke hannun su ya kai su ga hawa bus din ba. Mutumin ne ya kai su har bakin bus ɗin, in da ya umarci Salman da ya kawo kuɗin motar na su. Ko da ya haɗa ɗan kuɗin da ke hannun su sai ya ga dubu ɗaya ce cis. Ya nemi a musu ragi mutumin nan yak'i, dan kuwa haka su ke karbar kudin kowa. A k'arshe dai sai kuɗin maneji ya biya mu su ɗari uku-uku, sannan su ka sami matsuguni cikin motar.

Ɗarin da ta rage a dole ya siya mu su k'osai da pure water, dan kuwa yunwa su ke ji, bare Suhayl da tuni ya fara mu su kukan yunwa dan kuwa ba ya jure yunwa.

   Sai da motar ta yi awa ɗaya har da ɗoriya kafin su gama lodi a ɗau hanya. Zaman na su Salma sam ba daɗi sun takura kwarai, jere su ke kan maneji, kafafun su a takure ga wani turiri da ke tashi ta tankin motar, ga shi mai motar ya kwashi mutane da kaya da ya fi karfin motar. Ga haniya da kukan yara da ke tashi ciki, amma hakan bai hana Suhayl gyangyad'awa, shi kuwa Salman gaba ɗaya tunanin sa ya ta'allaka ne kan yanda za su yi su je MARKE neman dangin mahaifiyar su, idan suna da rai kenan,  ko da yake baba salame na nan a raye.

Tafiyar awa biyu sai da su ka yi ta awa uku, saboda lodi da rashin gwabi na motar, ga kuma hanyar ba kyau. Isar su Katsina a babban  tashar garin aka sauke su. Tashar cike ta ke fam da jama'a, matafiya da wanda su ka iso, yan talla da yan dako, jami'ai ma su kula da tashar, almajirai da kuma yan zaman banza. Hayaniya da cikowa na jamar tashar ba karamin firgita Suhayl ya  yi ba, tuni ya kudunnune rigar Salman idanun sa na shirin kawo ruwa. Su kan su Salman da Salma hankalin su ba kwance ya ke ba, musammam ganin yanda yan dako ke ta kawo mu su harin daukar kayan su, Salman na hanawa, haka kuma masu abin hawa na ta mu su tayin hawa babur din su, wanda  ke kira "Adaidaita Sahu" amma su ma din sun ki yi.

   Sai da ya ga jama'ar sun dan sarara, tukun ya tsada wani dan saurayi ya na mai tambayar hanyar da za su bi ya kai su ga unguwar Marke.

Saurayin ya na mai duban sa ya ce
"da gani dai ku baki ne,  MARKE ai gari ne chan a karamar hukumar Dan Musa,  ko daga nan zuwa chan ai awa biyu ne, ba motar Katsina ya kamata ku shigo ba ai don kuwa da ta hanyar Gwarzo zaku bi sai Dayi junction daga nan sai ku biyo ta Gora zuwa kankara daga Kankara sai Yan tumaki,  sai Danmusa,  yanzu kun san inda zaku shiga motar?" ya tambaya yana mai kallonsa

Salman ya girgiza kai sannan ya ce "Ah ah,a kasa za mu je ai,hanya kawai mu ke so a nuna mana"

Dariya saurayin yayi, har da kyakyacewa kafin ya ce "Gaskiya ne mutumin kauye, ka tabbata bako a garin nan shi ya sa ba ka san girma da fad'i irin na jihar Katsina  ba, kai idan ka ce za ka silafa har MARKE da k'afa kai kaɗai ma ba tare da yan uwan nan na ka da kayan nan ba, ace ka fita tun safe ba ka isa ka kai marke  ba sai ka wuni  ka kwana a hanya, bare kuma da su, ai sai kun yi kwanaki! Kai ni ina da abin yi, in da za ka rage ciki ka biya a kai ku toh, ni ka ga tafiya ta!"

Su na ji suna gani saurayi ya wuce su ya na mu su dariyar kyeta. Salman ya yi jigum ya zubawa sarautar Allah ido. Ga wata rana da ake zubawa wanda ta haddasa mu su azababban k'ishin ruwa. Ga shi kuma ko karyawar kirki ba su yi ba, shi kan shi Salman bakar yunwa ce ta sa cikin shi a gaba, bare Suhayl da Salma. Ilai kuwa nan take Suhaly ya sa mu su kukan yunwa. Salma ce mai iya rarrashin sa, shi kuwa Salman wajen ɗaya daga cikin masu yunifon ɗin yuniyo ya isa, ya nemi da ya taimaka  ya kai su marke, amma fa fisabilillahi, dan kuwa kwandala ba sa magani. Cike da takaici ɗan yuniyi ya fatattake shi, ya na mai zargin sa da mutuwar zuciya, matashin yaro kamar shi ya ce a kai shi har marke a kyauta!

Da dai Salman ya ga babu sarki sai Allah, inuwa ya ja su Salma da Suhaly din da har lokacin be daina kukan yunwa ba, ya ce su zauna su jira shi, kada Salma ta yarda ta kula kowa, ta kula da Suhaly, bara ya je ko dako ne ya yi, sai ya samo mu su na abinci da ma na mota gaba ɗaya. Da haka ya bar su zaune, ya kutsa cikin tasha. Ya ci sa'ar samin dako har sau biyu, ana ba shi naira hamsin,domin kuwa tashar cike take da yan dako ko ta ina. Da ya sake gwada sa'ar sa be samu ba, sai kawai ya k'arasa wajan mai abinci ya siya mu su shinkafa da wake, wajen mai abuncin ya tsinci gorar ruwa mai tambarin faro,ya d'auka ya d'auraye. Ciki ya taro mu su ruwan sha.
  Ganin abincin ba karamin murna Salma da Suhayl su ka yi ba, kan kace mai tuni sun far ma abinci. Ganin ba zai ishe su ba Salman ya bar musu su ci su biyu, ya sake kutsawa cikin tasha, ya na mai fatar barin tashar kafin la'asar, azahar har ta kawo kai, gashi zaman Salma cikin tashar ke ɗaga masa hankali, dan kuwa mutane ne iri iri ciki, ba ka san waye mugu, waye na gari ba.

   Lokaci lokaci ya ke samin dako,ya na yi ya na duba su Salma, a haka har azahar ta yi, ya sa su ka yi sallah. Kan la'asar ta k'arasa kuwa Allah ya taimaki Salman ya had'a kud'in sa har d'ari biyar da hamsin. Ya na mai share zufar da ya haɗa ya ke tsadancewa da ɗan yuniyo din Ɗazu don a ɗauke su a maneji, wanda shi kuma ya dage a lalle sai dai Salman ya biya shi d'ari uku, a hakan ma wai sauki ya masa. Da kyar da magiya, Salman ya masa bayanin halin da su ke ciki, sannan ya yarda za'a kai su din a d'ari biyu. Su ka jera kayan su a baya, Salma ta fara shiga, Sahayl ya bita sai Salman a kusa da kwansasta. Nan direba ya tayar da mota kasancewa motar ta cika, Salman na mai sauke ajiyar zuciya.

No comments:

Post a Comment