ABINDA AKE GUDU🙆🏽10
Batul Mamman💖
www.fikrahwriters.blogspot.com
Bara'atu ta gama girkinta tayi wanka sannan tayiwa yaranta. Albishir gareta ga maigidanta idan ya dawo wanda take tunanin zai rage masa bacin rai. Ciki ne da ita har wata biyu. Dayake ranar babu islamiyya su Jafar sai wasansu suke yi a gida.
Sallamar maza taji a kofar gidan ta dauki mayafi ta fita. Ga mamakinta har da 'yan sanda biyu. A tsorace ta gaisa da su sannan guda cikin 'yan sandan ya miko mata ID card ko ta gane wanda yake jiki.
Tana ganin hoton jikinta ya fara rawa "ku fada min abinda ya same shi"
Wani mutum a gefe yace "Hajiya sai dai hakuri a hanyar shiga gari muka ga motarsa yayi hatsari. Allah Yayi masa rasuwa".
Kuka Bara'atu ta saka har yaranta suka fito. Ganin Ummansu na kuka suma suka fara. Bare Shemau da Jafar masu wayo sosai.
Cikin dan kankanin lokaci sauran abokan aikinsa suka zo. Bintu da mijinta ma duk sun zo da makotansu. Karfe uku suka kama hanyar Kano.
Basu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Marigayi Mal Yahaya a unguwar kofar mazugal. Hajjo tayi kuka sosai na rasuwar danta sai fadin irin halinsa na hakuri da kawaici take yi. A nan aka yi masa sutura aka kaishi.
Bara'atu duk ta rame a cikin 'yan kwanakin nan saboda tashin hankali. Saukinta daya shine canjin data gani a tattare da Hajjo. Mutuwar ta daketa sosai shiyasa duk tayi sanyi. Sabanin yadda ta saba yanzu tana jan su Shemau a jiki. A da kuwa sai dai tace su dena kallonta da kwala-kwalan idanunsu na mayu.
Bayan sati biyu da rasuwar gabadaya 'ya'yan Hajjo suka taru da Kawun Bara'atu tare da wani malami da Rabe ya kira akan rabon gado. Kafin malamin ya fara jawabi Bara'atu ta sanar dasu cewa tana da ciki.
Ran Rabe yayi matukar baci ita kuwa Hajjo abin yayi mata dadi. Dole aka hakura da rabon gado sai ta haihu.
Da amincewar Hajjo ta koma Zaria saboda makarantar yara. Tausayin Bara'atu ne kawai ya kamata tun bayan rasuwar Shu'aibu.
Bayan wata shida ta haifi 'yarta mace Hajjo da kanta ta zaba mata suna Aina'u. Yarinyar duk tafi sauran 'yan uwanta kama da mahaifinsu shiyasa ta shiga ran Hajjo sosai. Kano suka dawo lokacin kafin tayi arbain. Kwana goma da haihuwar Bara'atu Rabe ya sake dawowa da Malamin rabon gado. An gabatar masa da dukkan kadarar Shu'aibu wanda ya hada da motarsa guda daya da kuma makeken gida da ya gama ginawa a unguwar Hotoro sai 'yan kudade a banki da kuma wanda wurin aikinsu suka bawa iyalinsa sai kuma wata gona a Zaria. Malam ya gyara zama
"Tunda mamacin yana da 'ya'ya da mata sannan mahaifiyarsa tana da rai duk 'yan uwansa basu da gadon shi."
Rabe yaji kamar an kwada masa guduma "Malam ya zaka ce bamu da gado? Dukkanmu fa uwa da uba daya muke. Ni nan da kake gani shi ya saki nono na kama ko ba haka ba Hajjo?"
Malam yayi murmushi "Alh Rabe ai shi rabon gado ba'a yi masa katsalandan. Allah SWT da Kansa Ya raba saboda haka babu wani son zuciya a nan. Zan nemi 'yan uwana malamai kamar mutum biyu sai muyi abinda ya dace. Allah Ya jikan Alh Shu'aibu".
Malamin na fita Rabe ya soma fada ya dubi 'yan uwansa. Babu wanda yace masa komai. Dama Garzali karamin cikinsu baya shiga sabgarsu sosai shaye shayensa ne a gabansa. Yaya Abu da Lami ma basuyi magana ba ganin Hajjo tayi shiru. A haka taron ya watse Bara'atu na mamakin wannan hali na Rabe.
Har daki Rabe yabi Hajjo tana daga kwance akan gado ta tashi zaune.
Ya numfasa yace "Hajjo kina jin malamin nan. Yanzu banda sharri yace bamu da gado. Nufinsa wannan gidan da Yaya yake ta shirin komawa Bara'atu da 'ya'yanta ne kadai zasu tare?"
Hajjo tace "banda abinka Rabe ai haka rabon gado yake. Da so kake ace kaima ka shiga gidan ko yaya? Dubi fa yadda ya sake gyara gidan nan. Ni bana son tashin hankali. Kada na sake jin zancen nan ya taso". Da haka ta kashe maganar.
Kwanaki biyu a tsakani Malamin ya dawo aka zo akayi rabo daidai da sharia. Gida da mota duk sun fada rabon Bara'atu da 'ya'yanta. Gonar Zaria an sayar aka fitarwa Hajjo nata sauran duk na 'ya'yansa ne. Bakin cikin Rabe baya misaltuwa. Ya kwallafa rai sosai akan gidan. Bara'atu ta koma Zaria suka fara shirin dawowa Kano gabadaya.
*****
Rabe zaune gaban wani malamin tsibbu ya gabatar masa da bukatarsa ta son a toshe bakin Hajjo duk abinda ya fada ta amince.
Dariya Malamin yayi sannan ya karbi kudin aikinsa. "Indai wannan ne matsalarka an gama."
*****
Bayan sati daya Hajjo ta zaunar da Rabe fuskarta cike da damuwa " idan baka fada min matsalarka ba wa kake dashi wanda ya fini?"
Kansa a kasa yayi dan murmushin takaici "Hajjo ko na fada bazaki amince ba. Gani kike yi kamar cutar da iyalin dan uwana nake son yi".
"Ko kadan Rabe, fada min abinda ke ranka".
"Dama nayi tunani ne bai kamata na bar zuri'ar Yaya ta wulakanta ba. Kinga matarsa tana da sauran kuruciya. Idan tace zatayi aure waye muka sani da zai kula da ita da 'ya'yan da zuciya daya? Ni a tunanina ta bani su tunda mun rabo da Laraba sai na kara aure na rikesu gabadaya. Ko kuma....."
"Ina jinka, ko kuma me?"
Dan murmushi yayi mai nuna yana jin kunyar abinda zai fada "nace ko zaki yi mata magana ta amince na aureta. Kinga sai mu zauna tare gabadaya da yaran. Babu zancen a rabata da 'ya'yanta."
Shiru Hajjo tayi yana tunani.."yanzu matar da ko wata uku batayi da haihuwa ba kana ganin ba'ayi wauta ba idan aka bijiro mata da zancen aure?"
Dadi yaji batayi fada ba "nima ba wai yanzu yanzu zan ce ayi auren ba. Kawai dai tasan da maganar ne".
Hajjo ta kada kai "shawararka tayi kyau , ranar asabar zata zo su fara kawo kayansu sai kayi mata magana a lokacin.
Asabar da yamma Bara'atu na shayar da Aina'u a tsohon dakinsu Rabe ya shigo babu ko sallama.
Da sauri taja rigarta ta suturta jikinta rai a bace. Wani kallon kasa kasa yake mata yana murmushi.
"Mutum da kayansa meye kike wani rufe jiki"?
Maganarsa ta bata mata rai tayi yunkurin tashi yace ta zauna magana zasuyi. Zama tayi a nan ya sanar da ita bukatarsa. Hade rai tayi tana kallonsa a wulakance.
"Rabe bahaushe yace in maye ya manta uwar da bazata manta ba. Duk irin cin kashin da kukayi min a gidan nan don rashin kunya zaka ce kana son aurena. To ni ba shashasha bace, nasan sarai abinda kake nema a gareni. Gida ne ya tsokale maka ido kake son mu koma daga nan dani da yaran da abinda kake ganin sun samu mu koma mallakinka. To wallahi kayi kadan. Ko mazan duniya sun kare bazan aureka ba."
Hajjo ta shigo tana kallon yadda Bara'atu take fadawa danta magana. Tuni ta rufe ido ta fara fada.
" yanzu saboda yana son rufa miki asiri kike masa wannan rashin mutumcin? Idan har baki aure shi ba to ki sani dole ki bashi yaran nan."
Fada sosai Hajjo tayi Bara'atu bata tanka ba. Washegari ta koma Zaria suka karasa hada kayansu wata mai zuwa zasu taho idan sun karbi takardun yara na makaranta.
*****
A nasa bangaren Rabe yayi ta zuga Hajjo akan ta bari ba sai ya auri Bara'atu ba kawai ta amince ya zauna a gidan da nasa yaran sai ya hada duka ya kula dasu. Itama Hajjon ta zo a tare da ita tunda gidan akwai dakuna.
Yaci galaba domin Hajjo ta amince. Sannan tace ya nemi mata yayi aure. Ita ya barwa zabi ta hadashi da 'yar kanwarta. Bayan sati uku aka daura aure amarya ta tare a sabon gida a Hotoro. Ba ayi mata kaya da yawa ba saboda kusan komai na amfani Shu'aibu da Bara'atu sun saka.
Kwanan amarya biyu su Bara'atu suka iso Kano. Kayansu ta kwatantawa masu mota aka kai hotoro ta wuce kofar mazugal. Makota ke sanar da ita su Hajjo sun tashi. Tayi mamaki sosai to ina suka koma? hotoro ta wuce da sa ran zata je gidan Lami a kwatanta mata inda suka koma.
Suna isa gate din gidan Jafar ya fita ya budewa mijin Anti Bintu da ya tuko su a motar da yanzu ta zama ta Bara'atu ya shiga. Yaran Rabe su biyu ta gani suna wasa a waje ga Hajjo zaune karkashin bishiyar goba tana shan iska.
A sanyaye Bara'atu ta karasa kirjinta na dukan uku uku. Hajjo ta washe baki tana yiwa jikokinta maraba. Bara'atu ta gaisheta tana kallon kofar gidan a bude.
Hajjo tayi tsaki "ya naga duk jikinki yayi sanyi ne? Ki kwantar da hankalinki nayi tunanin bai kamata na matsa miki ki auri Rabe ba shine muka dawo gabadaya a taro a kula da marayu. Kuka ne ya tasowa Bara'atu sai dai kafin ya kai ga fitowa ta ga Sagira yar kanwar Hajjo ta fito Garzali yana binta a baya yana tsokanarta.
Hajjo ta saki murmushi "ga amaryar Rabe fa shekaranjiya ta tare. Bari tazo ta nuna miki dakunanku ke da yara. Daki har biyu Rabe yace a baku. Su Jafaru dakinsu yana nan kusa da na kawunsu Garzali"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Bara'atu ke fada saboda tsananin bacin ran da take ji a wannan lokacin.
No comments:
Post a Comment