ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 2
Batul Mamman💖
Lokaci guda Umar ya gigice jikinsa ya hau bari. Da sauri ya shiga bandakin ya zauna cikin ruwan kusa da Abubakar sannan ya daga kansa ya dora a kan cinyarsa. Da kyar ya iya cewa "Yaya".
Babu wata alamar motsi a tare da Abubakar. Umar ya shiga jijjiga shi yana kiran sunansa. Duk da haka Abubakar bai motsa ba. Iyakar tsorata Umar yayi don ji yake kamar zuciyarsa zata buga. Wasu zafafan hawaye ya soma yi a hankali yace "Yaya Abubakar ka tashi an daura auren."
Nan ma dai shiru yaji. Tunaninsa gabadaya ya kulle ya rasa me zaiyi ya taimakawa dan uwansa. Da sauri ya tashi ya fara kokarin daga shi ya fitar dashi daga cikin ruwan, amma yayi masa nauyi domin duk jikinsa a sake yake. Ya sake gwadawa yaji tabbas bazai iya ba sai ya tashi ya fita tare da rufe dakin da mukulli.
Duk wanda ya ganshi da kaya a jike ga alamun jini a gaban sabuwar shaddarsa da tasha dinki sai ya tambaye shi ko lafiya. Babu wanda ya bawa amsa ya wuce dakin Mama.
A tsaye ya ganta a gaban mudubi tana saka sarka. Kafin yayi magana ta juyo da sauri saboda ganinshi da tayi ta mudubin. Gaban rigarsa ta nuna tare da zuwa gabansa ta tsaya "Umar me ya faru? Ciwo kaji garin gyaran bandakin? "
Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeta yana kuka mai tsuma zuciya.
*****
Duk akwatunan kayan Asmau an gama hadasu a wuri guda. Daya daga ciki ta bude ta dauko wata atampa zata saka Aina'u ta shigo dakin da gudu sai haki take yi.
"An daura auren. Daga yau dakin nan ya zama nawa ni kadai" ta fada iyakar karfinta tana murna. Tana gama fadar abinda ya kawota ta sake ficewa da gudu.
Su Walida suka soma guda suna yiwa Asmau tsiya. Harda masu yi mata wakar ta zama dauko riga....ta zama dauko hula....ta zama dauko wando....
Duk baki irin nata jikinta sai da yayi sanyi ta kasa biye musu kamar yadda ta saba. Ji tayi zuciyarta tana bugawa da karfi har abin ya bata tsoro kawai sai ta soma kuka. Hankalinsu ya fara tashi. Walida ce ta rungumeta maimakon ta bata hakuri itama sai ta fara kukan. Wata 'yar kanin baban su Asmau ce tace "haba Walida maimakon ki bata hakuri sai ki biye mata. Yau ai ranar farinciki ce ba kuka zakiyi ba. Ki tashi kiyi nafila ki godewa Allah da Ya nuna miki wannan rana."
Jiki a sanyaye Asmau ta saka kayanta ta dora hijab ta tayar da sallah.
*****
Gaban Mama ya fadi ta dan ture Umar daga jikinta. Ta soma kokarin daga masa riga ta ga ko ciwo yaji ya zubar da jini da yawa haka.
"Mama jinin Yaya Abubakar ne".
Jin maganar tayi har tsakiyar kanta. Jinin Abubakar kuma? Abubakar din da ta tabbatar yana tare da abokansa yanzu suna shirin zuwa wurin reception din da zasuyi. Cikin rashin fahimta tace "wane irin jini? A ina kaga Abubakar din?"
Umar yace "yana toilet dina ya suma".
Mama bata jira ya sake magana ba ta fita daga dakin da sauri yana binta a baya. Matan dake cikin gidan suna ta tambayar abinda ke faruwa. Ganin basu tsaya basu amsa ba suka bi bayansu.
A kofar dakin Umar suka tsaya ya saka mukulli zai bude kofar Abdulhalim ya shigo yana fadan Abubakar ya bar mutane suna ta cigiyarsa har Baba sai da yayi ta fada. Umar dai bai kula shi ba ya bude kofar Mama ta ture shi ta shiga da gudu. Inda ya barshi a kwance suka sake samunsa.
Abdulhalim ya karasa gabansa da sauri yana tambayar Umar me ya faru. Da taimakon Umar suka dora shi a kan gado daga shi sai dogon wando a jikinsa. Mama ta fada kanshi tana jijjiga shi tana kuka.
Matan dake kofar dakin suma suka soma kukan. Nan da nan aka kirawo 'yan uwansa mata. Abdulhalim ya kira wani abokinsa likita da yazo wurin daurin auren ya bukaci ya karaso gidansu da gaggawa. Dakin duk ya rude da kuka duk da har yanzu basu san ainihin me ya same shi ba. Sai da Abdulhalim yayi da gaske ya iya sawa suka fita.
Cikin mintuna kadan likitan ya karaso. Yayi mamakin ganin angon kwance jini har ya soma jika zanin gadon. Umar ne yayi masa bayanin yanayin da ya tsince shi a ciki. Abdulhalim yace "bari mu saka shi a mota mu tafi asibiti. Bana so mutane su ganmu. Zanyi kokarin kawo motata baya sai a fita dashi." yana gama magana ya fita.
Kabiru ya duba kan Abubakar inda ya fashe sannan ya taba kirjinsa da tsintsiyar hannunsa. A razane ya dago kai Mama ta kalle shi da jajayen idanu tace "ya cika ko?"
Yadda ta tsare shi da idanu bai isa yayi mata karya ba. Sunkuyawa yayi ya sake bincika shi sosai sannan cikin murya mai rauni yace "Mama sai dai muyi hakuri....".
A take ta zube a jikin Abubakar a sume. Su Suwaiba sai kuka suke yi suka dagata. Kabiru ya fara kokarin taimaka mata. Kuka kowa na dakin yake yi sosai. Tun kafin Abdulhalim ya karaso yaji sautin kukan ya shigo a guje. Umar ya fara hangowa durkushe yana kuka ya shigo ya tarar Kabiru yana danna kirjin Mama. Wani irin numfashi taja sannan ta bude ido da kyar.
Mikewa tayi tana kuka ta koma bakin gadon inda har ansa gefen zanin gadon an rufe Abubakar. "Allah Ya jikanka Abubakar. Na yafe maka duniya da lahira. Allah Ya sa mutuwa hutu ce gareka."
Ana amsawa da amin kuka yana karuwa.
Duk dauriya irin ta Abdulhalim shima kukan yake yi ya kama hannun Kabiru suka fita. Suna fitowa ya fara hango kawunansa da sauran abokansa da na Abubakar. Wurinsa suka taho suna tambayarsa ina ango. Bai iya cewa komai ba sai hawayen da yake zubarwa. Kabiru ne ya iya basu amsa ya sanar dasu halin da ake ciki. Gabadaya farfajiyar gidan ta rude da addu'a. Tashin hankali mara misaltuwa aka tashi dashi. Abubakar ya rasu daidai lokacin daurin aurensa.
Maza sai kai kawo suke yi cikin dan kankanin lokaci labari ya isa kunnem Alh Adamu wanda dama suna hanyar shigowa gidan da abokansa. A gigice ya shigo ya wuce dakin Umar inda su Yalwa suke da sauran 'ya'yansu. Suna ganinsa kuwa su Nasiba suka rungume shi suna kuka. Duk wanda yake gidan sai ya tausaya musu wannan tashin hankali da suke ciki. Shi kanshi Alh Adamun da kyar yayi ta maza da taimakon dattijai abokansa suka sa duka matan suka fita domin a yiwa Abubakar wanka idan sun sauko daga sallar Juma'a sai a kai shi.
*****
Jafar shine wanda yake bin Shema'u ita kuma Asmau take binsa. A gabansa Kabiru yake fadar rasuwar Abubakar. Saboda firgice bai san da yadda kafafunsa suka kawo shi gida ba.
Masu kidan kwarya ya hango suna ta jera kayan kidansu. Zuciyarsa ta sake tsinkewa da ya tuna halin da kanwarsa zata shiga. Dama tun a bakin gate ya goge hawayensa saboda gudun tambaya. Yana shiga falo aka fara tambayarsa ko 'yan daurin auren sun watse ana son kai Asmau wurin kakarta tayi mata nasiha kafin 'yan yini su kara cika gidan. Jafar yace akwai sauran mutane sannan ya nemi jin inda Umma take.
A bayan gida ya ganta suna magana da kanwarta Anti Bintu. Umma na ganinshi tace "baban Yaya har kun dawo? Ka ce zaku reception ko kaya ka dawo canzawa?"
Jafar ya ji kamar ya fasa fada sai dai kuma babu yadda zaiyi. Idanunsa suka kada sukayi jazur yace "Umma Allah Yayiwa Abubakar rasuwa".
Daga ita har Anti Bintu a tare suka ce "Me?"
Jafar yace "yanzu muka dawo daga wurin daurin aure Yaya Abdulhalim yake fada...." maganar tasa makalewa tayi saboda kukan da ya zo masa.
Suma kukan suka fara. Wannan tashin hankali da yawa yake. Fuska sharbe da hawaye tana salati Umma ta shiga ciki ta tafi daki. Anti Bintu ta daure ta leka dakinsu Asmau ta kirata.
Tun da ta taso gabanta ke matsanancin faduwa tana ta karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil.
Kafin ta shiga dakin Umman taji muryoyi suna cewa Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....a razane ta shiga Shema'u ta taso ta rungumeta. Kokarin ture yayarta tayi bakinta har rawa yake yi tace "waye ya rasu?"
Bazata iya tuna muryar wadda tace "sai dai hakuri Abubakar ya rigamu gidan gaskiya" ba.
Kamar saukar aradu haka Asmau taji zancen sannan numfashinta ya fara kokarin daukewa. Daga nan bata sake sanin inda take ba sai farkawa tayi a gadon asibiti.
No comments:
Post a Comment