Tuesday, 10 January 2017

Abin da ake gudu 12

ABINDA AKE GUDU🙆🏽12

Batul Mamman💖

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta gama da abinda yafi mahimmanci.
Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya.

Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta yasa ta hade rai.

Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri jin kwaf.

Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace
" Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu tashi"

Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar ma zai saki Sagira.

"Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan."

"Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na kammala gini na."

Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....."

Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara.
"Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa cikinsa wuta ne."

Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki sani babu ni babu su."

"Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa gaisheki tunda ba nisa mukayi ba."

Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta.
*****

*Sabuwar Rayuwa*

Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba.

Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi. Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da 'ya'yanta.

Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim, Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma sunyi kokarin jansu a jiki.

Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara.
Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba.

_Asmau S. Yahya_

Ranar farko da zasu je makarantar kowa yana doki banda Asmau. Haka take da tsoron mutane. Duk gidansu ita ce ta kasa sakewa da yaran Mama.

Kowa ya shirya ta kwanta ciwon cikin karya saboda taji ance kowa karatunsa shi kadai malam zai biyawa. Yadda zata yi karatu a gaban su Suwaiba ne yake kara tsorata ta. Umma na ganinta tasan ciwon karya ne. Da rarrashi ta lallabata suka tafi suna idar da sallar magriba.

Cikin gidan suka fara zuwa suka gaishe da Mama sannan suka fito waje. Suwaiba 'yar Mama ta hudu ita ce kusan sa'ar Shema'u amma duka ita da Sadiya sun zama kawaye da Shema'un. Tare suka fito zuwa masallacin Asmau na bin bayansu rike da hannun  Aina'u.

Malam Hadi yana zaune tare da Abdulhalim, Abubakar da Umar. Suna zuwa gaishe shi suka yi kowa ya sami wurin zama. Sai da ya gama da manyan sannan yaji karatun su Suwaiba. Daga nan ya fara jin inda su Asmau suka tsaya yace kowa sai ya biya surar karshe inda ya tsaya.

A nan ake yinta ana zuwa kan Asmau da ta fuskanci idanu sun dawo kanta tana yin Bismillah sai hawaye. Malam yace ta barshi ya gama da sauran .Shema'u tayi tsaki tace " malam wallahi ko a islamiyya haka take yi sai taji bulala take kawo hadda."

Murmushi yayi "ni bana duka kinji Ma'u. Bari na gama da kannenki sai ki biya min."

Hatta Aina'u sai da ta karanta suratul Ikhlas amma ana dawowa kan Asmau sai kuka. Jafar yace Ummansu tace a zaneta idan bata yi karatu ba.

Tunda ta fara kukan farko Abubakar yake kallonta. Dariya abin ya bashi sai da yaga taki denawa ta soma bashi tausayi.

Malam Hadi yayi har ya gaji taki karatu sai kuka da rawar murya. Yace  kowa ya fita banda manyan yayye. Suna tafiya ya nuna mata Abdulhalim da Abubakar
"Waye a cikinsu kika yarda zakiyi karatun a gabansa tunda kin kasa a wurina."

Tana daga kai suka hada ido da Abdulhalim ya hade rai. Da shine malamin zaneta zaiyi fes baya daukar rainin hankali. Da sauri ta nuna Abubakar. Malam Hadi yace "to Sadiq ka kwatanta gaskiya ka ji karatun. Ke kuma gobe ki tabbatar zakiyi a gabana ko na samo bulala".

Da haka suka fita saura ita da Abubakar.
Fuskarsa a sake ya fara tambayarta "shekarunki nawa Asmau?"

"Shahudu"

"Ashe ma kin girmeni da shekara takwas"

Ta dan saki fuska amma muryarta bata dena rawa ba "so kake kace ka girmeni da shekara takwas dai"

Yayi murmushi  dama so yake ta saki jikinta "Haka ne,  ni yanzu ina level two a BUK ina karanta computer science. Ke fa?"

"SS1 nake a science class. Likita nake son zama" yadda take maganar yasan ba karamin son hakan take ba.

"Very good, sai dai bakiyi kama da likita ba saboda tsoro yayi miki yawa. Likitoci kuma basu da tsoro".

Yana kallon  bata ji dadin maganarsa ba ya sake yin murmushi.
"Kada ki damu akwai maganin tsoro. Shine ki daure ki rinka magana a cikin mutane. Babu mai yanka ki. Iyaka idan kinyi kuskure a gyara miki. Karatun Qur'ani karfin zuciya yake sawa ba ragwanta ba."

Shiru tayi tana sauraronsa yana ta janta da zance. Sai karshe yace ta biya masa yaji.

Da kyar ta daure hawaye wani na bin wani ta karanta. Kafin tayi rabi kukan ya dauke sai karatun ake ji.

Tana kaiwa karshen surar yayi kabbara sannan ya sake karfafa mata gwiwa wurin bude baki a gaban jamaa.

Da murmushi ta fito suka tafi gida ran Shema'u a bace saboda tasa sun dade.

Tun daga wannan lokacin ko ta fara kukan idan Abubakar yana masallacin sai ta daure. Karshe dai sunanta ya koma Idon kuka saboda kullum sai tayi. Gashi ta tsani sunan.

Haka rayuwa ta cigabar musu har lokacin bikin Nasiba. Gidajen biyu suna ta shiri duk da su Umma basu fi shekara daya a unguwar ba. Haka suka yi bikinsu lafiya kalau kamar dangin juna.

Su Asmau an  kara zama 'yan mata. Yanzu tana dan sakewa har ayi hira da ita. Wani lokaci da Umma zata Wushishi  gashi basu yi hutu ba a nan gidan Mama Yalwa ta barsu.

Abdulhalim ya tafi bautar kasa Jos yanzu Abubakar ne babba a gidan. Duk da yanayin karatunsa bai hana shi cigaba da zama daukar karatu a wurin malam Hadi ba. Duk cikinsu yafi kowa mayar da hankali akan karatun  addini shiyasa Baba yake matukar ji dashi.

Watarana an gama karatu kowa ya fita daga masallacin sai Asmau dake zaune tana kokarin kammala aikin da malam ya bata na fitar da hukuncin (NUUN saakina) a thumunin da ya biya mata ranar saboda washegari test gareta a makaranta karatu take son yi. Abubakar yana can wurin zaman liman yana tilawa aka soma iska mai karfi alamun ruwa zai iya sakkowa a kowane lokaci.
Da dan gudunta ta tashi zata rufe tagogi kafin ta fita saboda kurar dake shigowa. Har ta gama rufewa Abubakar baiyi yunkurin tashi ba. A take kuma aka dauke wuta saboda wata tsawa da akayi mai karfi. A dan tsorace tace
"Yaya Abubakar kazo mu fita kafin ruwan nan ya sauko"

Shiru taji sai numfashinsa da ya kara karfi. Gabansa ta karasa sai dai duhu yasa bata ganinsa sosai. Wayarsa da ta taka ta dauka ta haska shi. Kwance yake numfashinsa yana sama-sama da kyar yake fita. Hannunsa daya kuma yana nuna mata aljihun wandonsa.

Asmau duk ta rikice ta kuma fahimci abu yake so ta miko masa daga aljihunsa. To kuma Umma tayi musu gargadi sosai akan taba maza wannan yasa ta kasa tabashi ta fita da gudu a cikin ruwan ta shiga gidansu ta fadawa Mama Yalwa.

Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?"
Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi masa sannu.

Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru.

No comments:

Post a Comment