ABINDA AKE GUDU🙆🏽15
Batul Mamman💖
Asmau da Walida sun shiga aji uku karatu ya fara zafi. Abubakar ya kusa gama hada lefe domin ya sami aiki a Kaduna. Duk juma'a yake tahowa Kano ya koma lahadi da yamma. Wasu lokutan kuma sai bayan sati biyu yake iya zuwa. Iyaye maza sun shiga maganar auren har an kai kudi sannan an sa rana wata bakwai saboda wanda yake haya a gidan Abubakar din ya nemi alfarmar a kara masa lokaci ya kusa gama gininsa. Idan ya tashi sai anyi 'yan gyare gyare a gidan.
Dubu hamsin dangin Abubakar suka bayar kudin aure amma ko kwandala Alh Rabe bai aikawa Umma ba kamar yadda yayi a na Shema'u. Shiru tayi kawai ta barsu da halinsu. Cin haram ba komai bane a wurinsa.
*****
Lecture akeyi ta Chemistry hankalin Asmau yana wurin malamin tana jindadin bayanin da yake yi musu. Daga gefenta Walida hankalinta gabadaya yana kan wayarta. Sau biyu Asmau na tabata idan ta kula kamar ita malamin yake kallo sai ta doke mata hannu.
Takowa yayi har wurin zamansu ya tsaya gaban Walida amma ko motsinsa bata ji ba. Murmushi ne a fuskarta mai nuni da tana jindadin abinda take yi. Hankalin Asmau duk ya tashi ta sake zungurinta da hannu. Walida na dago kai zata yi mata fadan ta dameta suka hada ido da malamin yace ta bashi wayar.
A take ta rude ta fara bashi hakuri. Gani yayi zata bata mishi lokaci yace ta zabi ko wayar ko kuma ta kawo ID card dinta. Ba yadda ta iya dole ta bashi wayar tana ta turo baki.
Bayan minti arba'in da biyar suka fito Walida sai tsaki take yi. Asmau ta gyara jakarta tana kallon kawarta.
"Ni kina bani mamaki Walida, sai ki kafawa waya ido ko sassautawa bakya yi. Ace ana lecture ma bazaki hakura ba. Da wa kike chatting haka?"
Tsayawa Walida ta yi tana jiran fitowar malamin "nifa ba chatting nake yi ba. Wani novel nake karantawa mai dan karen dadi. Don bakiji yadda ake soyewa bane a labarin" ta fada tana lumshe ido.
"Tunda har an turo miki ba sai ki hakura mu fito ba sannan ki karanta. Yanzu gashi kin rasa wayar ai."
Idanun Walida na duban ta inda Malamin nasu zai fito tace "bazaki gane irin dadin labarin ba sai kin karanta. Kuma naga idan an fito lokacin sallah yayi bazan nutsu a sallar ba bayan nasan an turo shiyasa na karanta a aji. Bari na samu ya bani zan turo miki."
"Nima ina karantawa kinsani amma gaskiya ba ko wanne ba. Kuma bana bari karatun novel yaci karo da abubuwa masu mahimmanci na rayuwata. Komai idan kika bashi lokacinsa yafi."
Fitowar malamin ta katse musu hira nan fa Walida ta hau magiya. Da kyar ya bata wayar tare da gargadi sosai. Ita dai ta karba tayi masa godiya sannan suka nufi masallaci. Kafadar Asmau ta dafa cikin zumudi ta cigaba da karatun duk da ranar da akeyi bata ganin rubutun sosai. Ko inda take ajiye kafa bata damu ba ta mayar da Asmau tamkar 'yar jagora.
Har Asmau ta idar da sallah Walida tana karatu ko alwala bata yi ba.
Tsaki Asmau tayi "dama bai baki wayar ba muga tsiya. Dazu kinki sauraron lecture yanzu kuma sallah ta gagara. Wallahi kiji tsoron Allah. Ina mamakin yadda mata yanzu suke matsuwa da labarai irin haka har ya hanasu gabatar da abubuwan da suka fisu mahimmanci."
Mitar Asmau ce ta ishi Walida ta tashi tayi sallah. Daga nan suka sayi awara da kunun aya suna ci Walida tace
"Asmau anya kina karanta novels din da nake turo miki?"
"Eh amma ba duka ba. Sai na duba mai amfani kuma mara rashin kunya. Akwai wani da kika turo ana soyayya amma harda taba jikin juna. Har na kai karshe banji inda marubuciyar ta kawo illar abinda masoyan sukayi ba. Abu kadan fa sai kiss kamar wasu mata da miji. Daren amarcinsu kuwa kamar akan idona akayi. Amma akwai wasu da nagani komai cikin nutsuwa da tsarin addini. Irin dai yadda ni da Mine muke yi" ta kare maganar da murmushi.
"Gulmar banza, yanzu duk wasu masoya ba'a rabasu da irin wannan abubuwan shiyasa marubutan suke sakawa a labaransu. Kuma ina amfanin soyayyar babu wani dan abu da zai kara mata armashi? In kin lura wani abin ana sawa sunyi saboda shaukin so ne"
"Masu yi zasu ga shaukin so kuwa a lahira. Ni dai wallahi ina miki rantsuwa idan har hannun Yaya Abubakar ya kai jikina sai dai bisa kuskure. Ko kyauta zaiyi min sai kiga yayi yadda hannuwanmu bazasu hadu ba. Kuma hakan bai rage komai a irin yadda muke ji game da juna ba."
Walida dai bata yarda ba. Karshe tace "anya yana sonki kuwa? Yanzu fa duk budurwa da saurayi ko da yana da mata kuwa a gida ba'a rabasu da rungume juna ko kiss. Ni kwatakwata na dena daukarsa komai tunda kowa yana yi. Kuma dai ba iskanci aka yi ba. Don dai bani da wanda na tsayar ne har yanzu da ko yaya dai..." shiru tayi bata karasa maganar ba.
Asmau kallon mamaki take yiwa kawarta. Tabbas Walida idonta yafi nata budewa saboda rashin kula daga wurin matar uba. Amma bata zata abin ya kai haka ba. Walidar ce ta katse mata tunani "shi Abubakar da yake aiki a Kaduna yana ganin 'yan gayun mata tuni wata zata ja ra'ayinsa. Da nice ke duk sati kafin ya koma idan kika ga kamar yana son ko dan hug ne sai ki bada fuska yadda zai tafi yana tunaninki. Amma tunda kika ji shiru ina mai tabbatar miki akwai wadda take deba masa kewarki a can. Yadda mazan yanzu suke kaunar irin wannan romance din. Abu kadan suke jira kiji hannunsu a jikinki"
"Ni dai bama yi Walida, idan kinayi ma ki dena don wallahi babu kyau."
"To naji amma zan bada numbarki asa a wani group na novels irin masu dadin gasken da kuma wani na matan aure"
Asmau ta girgiza kai. "Walida kin shiga tara bama uku ba. Me kike yi a group din matan aure?"
"Ke irin groups dinnan ne fa na taimakon juna. Zaki ga mace mai experience a gidan miji zata turo abubawa irin yadda zaman aure yake don taimakon wasu. Kinsan iyayenmu da kunya. Gara ma ke kuna tare da Umma ni kuwa idan naje gidan Ummanmu bata koya min komai saboda irin kunyar 'ya'yan fari take yi min. Ni yanzu a harkar aure ai sai dai mu jira shafa fatiha."
Asmau shiru tayi Walida tana ta fada mata amfanin irin groups din ko posts makamantansu. Ga kuma irin yadda zata kara gogewa ta fannin soyayya idan ta rabu da tsamayen novels ta kama na soyayyar gaske. Har suka tashi a taxi hirar kenan. Basu hakura ba har Walida ta sauka a Gandun Albasa aka wuce ta Asmau Hotoro.
*****
Kwanaki uku a tsakani Walida ta fara turowa Asmau wani novel. Abinda take gudu ne a ciki. Saurayi da budurwa suna sumbatar juna duk a cikin love kuma an nuna suna da tarbiya. A hankali suka fara shigar Asmau duk da bata bari karatun ya hanata sallah da wuri ko wasu ayyukan sai dai ta fara tantamar kwarewar Abubakar a fagen soyayya wanda a da take ganin babu kamarsa. Abun bai tsaya nan ba sai da Walida ta bada numbarta a wani group inda yininta na farko aka turo wani zungureren text mai dauke da bayanin wani salon kwanciyar aure tun daga farko har karshe. Har wata a group din tana cewa ta taba gani sun gwada da mijinta. Nan mata suka rinka tambayarta game da hakan tana ta bayani. Asmau dama bata yi magana ba a group din amma cikin hirararrakin wanda suka tafi duk akan harkar tsakanin miji da mata sun tsaya mata a rai. A take taji inama tana da aure saboda tasirin da abin yayi a zuciyarta.
Tun daga lokacin karatun novels ya sarketa sosai. Abinda ya kamata muyi don nishadi lokaci zuwa lokaci sai ya zama idan bata ga cigaban labari ba tamkar mara lafiya take zama. A karkashin zuciyarta tana tunanin meyasa bata jin haka game da al'amuran addini sai novels. Novels din ma tafi jindadin irin wanda bata karantawa a da. Wato na soyayyar taba jiki. Dama kuma zuciyar *dan Adam* tana karkata ne ga abinda yawanci bashi da amfani a garemu.
Texts kuwa na kwanciyar aure saboda tsabar yawansu da irin na kayan mata sai da ta kai itama tana iya tsarawa a kanta tace sai anyi aure.
Allah Sarki Umma Bara'atu. Tana nata kokarin wurin bawa 'ya'yanta tarbiya amma wasu can da ba'a ma san ko su waye ba suna turo abubuwan da suke gurbata tarbiyar yara kanana da sunan ilimantarwa.
Saura Abubakar.
www.fikrawriters.blogspot.com
No comments:
Post a Comment