Thursday, 12 January 2017

KARNINMU 13

KARNINMU...

BABI NA GOMA SHA UKU

Jim kaɗan Maryam ta dawo ta ce

"Ban gan ta ba"

"Mtsw ita ɗin fita ta yi kenan, wai ma ina Hanif? ba a ɗauko shi daga makaranta ba! Mantawa ta yi da shi ko. Mene? "

Cewar Ahmad ya na mai jinjina kai.

"Assha an yi haka kuwa,na manta ta ce za ta ɗauko shi a makaranta kila ta biya wani wajen ne"

Munari ce ta amsa masa. Juyawa Ahmad yayi ya na mai faɗin

"Bari na je na samo mu ku abinci, tabbas Balkis za ta ga fushi na"

Ya na jin Munari na faɗin

"Ka dai bi abin a hankali"

Bai tsaya ba ta amsa ba ya fice tuni. Maryam ce ta dubi Munari ta ce

"Yaya ki ga fa yanda ya fusata ya fice sai ka ce wani mataki zai iya ɗauka. Mutumin da a gaban matar sa kwakkwaran tari ma bai iyawa!"

Murmushin takaici Munari ta saki ta ce

"Ke rabu da ita, ai Allah ya fita, kamar yanda ba za ta fasa raba shi da yan uwan sa ba, mu ma kuwa ba za mu fasa bibiyan dan uwan mu ba, ai na san da niyya ta bar mu da yunwa, kuma shi Amadun ta riga ta shanye shi, amma da sannu za ta gane kuran ta, ta Allah ba ta ta ba"

Maryam na mai jinjina kai cikin gasgata maganar Munari ta furta.

"Kwarai da gaske"

Ahmad kuwa ko da ya fita, kai tsaye gidan abinci ya garzaya, dan kuwa gani ya ke idan ya ce ma zai yi aike wani ɓacin ran zai kwasa, zuwa da kai ya fi aike. Ya siyo abinci mai tsada aka shirya masa a matsayin "take away". Ba tare da ɓata lokaci ba ya dawo gida. Wanda hakan yayi daidai da shigowar ɗaya daga cikin motocin sa da direba ke ja. Habi ce ta fito sanye da hijabi, tana rike da hannun Hanif ga jakar sa rataye bisa kafa ar sa,ayan hannun ta ɗauke da "food flask" din Hanif,da ke irin makarantar nan mai haɗe da islamiya ya ke.

Ahmad na daga zaune cikin motar sa ya ke kallan su. Kallo ɗaya za ka mu su ka tabbatar suna cikin nishaɗi, dan kuwa Hanif dariya har da kyakyatawa. Shi kan shi Ahmad ya tsinci kan sa ya na mai sha'awar son jin shin me wannan sabuwar yar aikatan ta Hajja Bilkis ke faɗa ma ɗan sa da har ya sa shi darawa haka, har ya kusa shagala da kallan su, jin sun kusa tadda motar shi ya sa shi yunkurin fitowa, nan da nan murmushi ya bayyana a fuskarsa gannin Hanif ya saki hannun Habi ya nufo shi da gudu ya na faɗin.

"Dady oyoyo"

Hannu Ahmad ya buɗe masa, in da ya ɗan sunkuyo, Hanif ya shige jikin sa da sauri, Ahmad ya rugume shi tare da ɗaga shi sama. Hakan ba karamin nishaɗi ke sanya daga uban har dan ba, musammam Ahmad wanda ganin Hanif ke ɗebe masa takaicin uwar sa.

Ita kan ta Habi da ganin Ahmad ya sa ta raɓe gefe guda, wanda dama tun haɗuwar su na farko ta ke jin tsoran sa, sai ga ta ta tsinci kan ta ta na mai murmushi,musammam jin Hanif da Ahmad ya ɗaura kan mota ya na faɗin.

"Dady ina san Habi, ta iya tatsuniya, kuma ita ko da rana ta na iya bani, ba kamar iya dudu ba"

Ahmad na shafa kan sa cike da so da kauna,ya furta

"Wacece Habi yaro na?"

Hannu Hanif ya sa ya rufe baki jin tambayar Ahmad kafin ya ce

"Laaa Dady ba ka san Habi ba dama!"

Ya ɗan kyece da dariya kafin ya juya ya na mai nuni ga Habi da an yatsa ya ce

"Ga gan ta can fa,Habi wai dady na be san ki ba"

Idanun Ahmad ne su ka sauka kan Habi,wacce tuni ta yi kasa da na ta idanun, cikin sauri ta karaso gaban Ahmad ta na mai furta

"Bar bar-ka...... da-da dare...."
Ta yi maganar ne kamar mai inina.

"Barka dai"

Ahmad ya amsa a takaice, ya kara haɗe gira kamar ba shi ke raha da ɗansa ba yace, 
"ina kuka tsaya tun biyar da rabi da aka tashe su,  ina kika kai min ɗana" ya karasa  da ɗan tsawa

"Hajiya ta aike mu gidan hajiya yaya,  shine ta tsayar da mu" ta faɗa a tsorace,  shiru yayi yana kalonta kafin ya maida hankalin sa ga Hanif. Ya ce.

"Toh yanzu ba lokacin tatsuniya ba ne, maza a je a ci abinci sai a cire kayan makaranta a yi wanka ko?ga abinci nan na siyo mu ku sai aje aci da su Anty Maryam"

Ya na magana ne yayinda ya sauke Hanif kasa, ya buɗe bayan mota ya shiga fiddo da ledar abincin da ya siyo.

"Anty Maryam ta zo? Allah ya sa ta siyo min goriba, wannan ledar abinci ne Dady? Iya dudu ba ta yi abinci ba? Mumy ta na nan?"

Ganin Ahmad na fitar da kaya, ɗaya daga cikin yaran aikin gidan wanda ya ke yaro karami ya zo da saurin sa ya fara kwasa. Sai da Ahmad ya fitar da kayan tsaf ya rufe motar sannan ya ja kumatun Hanif ya na mai fa in

"Magna ɗisu, ko ina hakoran cin goribar sai ka balla hakori ko. Iya dudu ba ta nan,haka Mumyn ka,maza shige ciki,Habi ki ke ko wa?maza ki je ya ci abunci"

Jiki na rawa Habi da Allah Allah ta ke ta bar gaban Ahmad,ta ja hannun Hanif su ka shige ciki. Ahmad ya gama rufe motar shi ya na k'ok'arkarin ya bi bayan su,karar hon da ya ji ya tsaida shi. Inda maigadi ke k'ok'arin buɗe gate. Ahmad ya  jingina jikin motarsa, hannayensa harɗe bisa kirjin sa, yayin da goshin motar Hajja Bilkis ya doso farfajiyar gidan.

Kusa da motar Ahmad ta faka, cikin sauri ta fito da kwallin da bokan ta ya bata, wanda ta je gun sa musammam saboda bakin da Ahmad ya ce za su yi. Cikin azanci ta buɗe idanun ta, ta zizara kwalli ya fito raɗau kamar yanda bokan ya ce ta yi da zarar Allah ya haɗa ta da Ahmad. sannan ta ɗauko wani turare, shi ma in bokan ne ya bata. Kaɗan ta dangwala ta shafa bisa goshin ta. Sannan ta gyara ɗauri ta fito.

Ahmad da shi kan sa be san adadin hukuncin da zai ɗauka akan ta ba, ganin fitowar ta ya sashi daɗa tsuke fuska, musammam da ya ga ta nufo in da ya ke, ji yayi sam ba ya san ganin ta, dan haka kawai sai ya juya ya nufi ɓangaran baki in da su Munari su ke.

Hakan ba k'aramin ɗagawa Hajja Bilkis hankali yayi ba, dan kuwa idan har ba haɗa ido ta yi da Ahmad ba hakin ta ba zai cimma ruwa ba. Dan haka da saurin ta bi shi,sai da ya kai ga shiga falon ta iya cimma sa. Ganin su Munari da Maryam wanda ke cin abincin da Ahmad ya siyo mu su tuni su ka tsaya suna kallan su dan ganin hukuncin da Ahmad zai ɗauka, sun san ba za a yi ta dadi ba yanda ran sa ya ɓaci. Duk da ba haka Hajja Balkis ta so ba, kuma ganin su Munari bai hana ta je ta sha gaban Ahmad ba, hannayen ta biyu bisa kunnuwan ta,ta na mai faɗin

"Afuwa Honourable,me na yi da ko kallo ban ishe ka ba a yau?"

Ta yi maganar ne cike da shagwaɓa, yayinda ta ke sakar masa fari gami da wani shu'umin murmushi ganin yanda Ahmad na sanya ido cikin na ta yayi wani sakoko da shi kamar yaro ɗan goye. Wani irin ajiyar zuciya ya saka, in da ya ji yarrr ajikin sa, gaban sa na faɗuwa. Tashi guda wani fushi da ɓacin rai da ya ke ji game da ita ya gushe, sai ma ji yake kamar ita in ya ma ba daidai ba. Sai ga Ahmad ya tsinci kan sa ya na mai riko hannun ta ya na k'ok'arin jawo ta jikin sa cike da rarrashi ya ce

"Ah gimbiya mai gado ni ɗin banza, ah sannu da zuwa, wannan jakar ba ta yi mi ki nauyi ba kuwa?kawo na rike mi ki"

Wato daga Munari har Maryam buɗe baki su ka yi suna duban Ahmad cike da takaici. Cikin jin daɗin yanda aikin boka ya daki Ahmad duka ɗaya, da kuma ganin yanda su Munari su ka yi, ya sa Hajja Bilkis fa in

"Ah ah sake ni Honourable, rufa min asari ka sake ni kar jama'a su gani su raina min kai, yanzu na baka jakar nan ai sai dangin ka su zage ni, su ce na mai da kai zauji k'alat,ma'ana mijin ta ce....."

"Sai dai mijin kan ta ce ne, ba ma ta ce ba, ai dai ni ki ke aure ba su ba, duk wanda ya zage ki kuwa zai ga fushi na"

Ta na mai murmushi ta kai duban ta ga su Munari,ta ce

"Ashe baki aka yi, sannun ku da zuwa, Munari ku ne a gari? an iso lafiya?"

Munari da takaici ya cika ta ta kasa bata amsa sai

"uhummm"

Maryam ce da ta gama fusta jin furucin ta da Ahmad ta ce

"To da ba mu iso lafiyar ba kya gan mu haka!"

"Ke Maryam!"

Ahmad ya daka mata tsawa,wanda tuni Maryam ta ja bakin ta ta yi shiru. Ahmad ya k'ara da

"Ungo nan!"

Yay mata dakuwa.

"Dan baki da mutunci matar tawa ki ke bawa amsa haka dan kaniyar ki,mara kunyar banza mara kunyar  hofi!"

"Ayya mana Honourable, kar ka yi fushi, gajiyar hanya ce, kar ka damu in dai nice ai ba bakuwar zafi bace.... Mu je ka min danna kasan na gaji da yawa"

Cewar Hajja Balkis. Ahmad na mai nuna Maryam da ɗan yatsa ya ce

"Kin ci sa'a da kuwa sai kin yabawa aya zakin ta, mu je Maman Hanif...."

Hannun sa rike da jakar ta, Hajja Balkis na taku ɗai ɗai su ka fice, nan fa Munari ta fashe da kuka ta mai tafa hannu. Ita kuwa Maryam da lafiya ba ta ishe ta ba fa i ta ke.

"Ai dama na fada  mi ki,ga irin ta nan,sai mu haɗa namu ya namu mu koma kauye tun kafin ma azo mana korar kare,kai babu tsinanniya kamar wannan mata ta Ya Amadu!"

GIMBIYA LUBA..

    Kiran lambar Layin ta da ke wayar da ta bari a mota tayi bayan ta sallaci isha'i,  haka ya karaci ringing ya tsinke ba'a ɗauka ba.
  
"Kila zai kira ne" ta faɗi ma kanta tana mai murmushi,  lallai in har aurenta zai yi babu abin da zai hana ta watsar da komi tayi aure,  ko ba komi ta san hotunan bikinsu zai karaɗe duniya.

Tsalle tayi saman gadonta cike da murna,  nan take ta fara Mafarkin ido biyu amma bata yi wani nisa ba gabanta ya faɗi tunawa da tayi yanda za'a iya fitar da Hoton ta a bayan minista kuma.

"Na shiga uku" ta faɗi da karfi amma kafin ta kai ga tuna mafita wayar ta tayi tsuwa

"Ranka shi daɗe mai Luba mai Dunotsi " ta faɗi tana mai kokarin tattaro natsuwa.

" Ya kike mai kyau?  Ya ofishin na ku,  kina jin daɗin sa ko? " ya tambaya cike da kulawa.

" Eh!  Sai de gajiya,  rashin abin hawa,  Ɗazu ma na yar da Wayata.  Ka ga yanda na koɗe ma kuwa? " ta faɗi cikin sigar shagwaɓa.

" gobe zan turo miki da wata kiyi manejin ta kafin motarki ta iso.  Ki kulan min da kanki,  se da safe" ya karasa cikin sauri haɗe da kashe wayar ba tare da ya jira amsar ta ba.
"nan haka Matarsa ce ta kama shi' ta faɗi tana kyalkyala dariya.

No comments:

Post a Comment