Monday, 9 January 2017

KARNINMU... 12

KARNINMU...

BABI NA GOMA SHA BIYU

Lokacin da yan sanda suka yi awon gaba da Larai, sai kasuwa ta soma tashin surutai kasancewar wajen da suka zauna keɓantacen wajene da ba kowa ke zama ba ita Larai ta zaɓi wajan ne saboda yafi mata sirri wajan haɗuwa da Lado ita kuwa Lanto ta zaɓa ne saboda gujewa rasa kunyan samari da Dattijai masu mutuwar zuciya irin Lado.

Kasancewar Larai masifaffiya ce yasa bame raɓar wajan sai su yasu wanda ya zama da'im wajan zama a garesu hakan yasa ba kowa ya fahimci su waye suka yi aika aikar da aka yi wa Lado ba.

   Kai tsaye aka wuce da Larai police station, da wasu tsirarun mutane da yan sandan suka yi wa kamun uwa da wabi a bayan kasuwa bayan sun fita da Larai, cikin cell suka watsasu tare da garkama kwaɗo suka rufe kowannansu a ɓangaran daya dace dashi.
Saida komai ya nasa sannan aka fito dasu ɗaya bayan ɗaya ana tambayar kowa adireshinsa sannan aka maidasu. Lokacin da aka gama jana'izar Lado ne aka kaishi aka dawo maigari ya mike ya bada shelar waɗanda suke hannun yan sanda sakammakon bayanin da ya samu daga wani karamin ɗan sanda a nan Sani ya tsinci sunan Larai don haka ya bazama ya shaidawa mahaifansa game da abin da ya ji.
                     ***
Cikin tashin hankali Baba Dije take maimata kalmar Innalillahi iyakar gaskiyanta daidai take karantawa, ilahirin jikinta rawa kawai yake yi tako ina ta rasa ina zata tsoma ranta babban tashin hankalinta yadda zata tunkari mahaifin Larai da lamari yadda ya dage ɗiyarshi bazata yi talla ba ita kuma ta bulawa idaniyarta toka ƙkan kaucewa umarninsa yau gashi A SANADIN TALLA ɗiyarta na garkame a magarkama tabbas tana cike da kaico da da na sanin bijirewa bukatar mijinta. Hankalinta ba'a jikinta ba ta nufi gida tana tafe tana share hawaye da haɓar zani, har tuntuɓe take yi, turus ta tsaya lokacin data karasa gidan ganin maigidan nata tsaye ya haɗe fuska ya kashin shanu ya garkamawa kofar gidam kwaɗo.

Cikin takaici ya nunata da yatsa,
"a sanina talauci ko kuma yawan barace-barace kan sanya iyaye ɗorawa ‘ya’yan su talla ko dai ya zama haka ɗin ne basu da abin hannu wanda za su dogara a kan sa ko kuma ya zama uwa ta sa buri a kan ‘yar ta cewa idan ba ta hanyar talla ba, ba inda za ta samu abinda za ta kai ɗiyarta ɗaki. Dije ki faɗamun dame na rage ki? Ina yi wa ɗiyata ɗinki basai sallah ba, na sata makaranta amma duk kinyi kutu-kutu kin tugeta. Kin cutar dani kaico da rayuwar TALLA wadda bata da wani alfanu sai dana sani mara amfani. Abin da kika kasa fahimta mafi yawa daga lallatattun yara daga talla suke lalacewa daga mazan har mata. Su kan shiga lungu-lungu rariya-rariya sune kasuwanci wuraran gyaran motoci tashoshin motoci da kuma wuraren gine-gine, wanda daga nan idan aka samu lalatatu suka lalata yaran maza ne ko mata da yawa an sha samun waɗanda daga nan suke sake samun ciki.
Za ki iske yara tun daga shekara bakwai har goma sha suna yawon talla shaguna da wuraren taruwar maza don Allah yau da gobe me ki ke zato zai faru? Na sha nusar dake illar abinda ki ke yi kinki ganewa yaya fa amana ne a garemu wannan sakacine wanda in ba sa a akai ba, Sai shaidanu su fara yaudarar yara  da kalmomi masu dadi ko kudi daga nan sai su sami damar biyan bukatar su da su. Daga nan kuma iyaye su fara da na sani ana neman yadda za’a zubar da cikin ko kuma a rufa abinda za’a samu wani a daura mata aure da shi ba tare da ya san abinda ake ciki ba ‘yan watanni sai a ce ta haihu, shi kuma yace sam bai san haka ba don ba nasa bane. Ta tattara ta koma gaban iyayen ta. Abin kunya dai ya samu ! an kuma tozarta dokar Allah an ci amanar yarinya wajen rashin kula da tarbiyyar ta. Duk fa hakan yana samuwa ne a SANADIN TALLA"

Jikinta ya yi sanyi matuka, ta dubeshi idanunta na zubar da hawaye,

"kayi hakuri insha Allahu wannan shi ne karo na karshe da zai kawo SANADIN barin TALLA a gidan nan kayafemin".

Wani daɗine ya kwaranyar masa yau Allah ya amsa addu'arsa, wai Dije ce da kanta take neman afuwarsa kan kuskure wanda a baya ko kallo bai isheta ba tabbas dukkan nasara naga ma abota hakuri. Bai tanka ba suka dunguma zuwa wajan maigari kamar yadda aka bukata.

                DAKIN RABS
Lokacin da su Baaba suka tabbatar da cewa sahu ya ɗauke ne suka mike, Rabs dake gefe ya dubesu, "lafiyarku dai kuka mimmikemin a daki"?.

"Hmm! Bari kai dai aboki ai yau Allahu ya.......". Zungurinsa da Messi ya yi yasa shi ankara yana shirin ɓarka ne, ya yi gum Rabs ya dinga dubansu ɗaya bayan ɗaya alamun tuhuma zuciyarsa na wani zargi amma sai ya kauda zargin da faɗin,

"kunji rasuwar Lado?".

Gaba ɗaya suka haɗa baki, "yaushe?",
sai ya yi turus yana jimami ya jinjina kai,

"ɗazu a kasuwa aka bishi aka kasheshi, amma an rasa gane su waye an ce wai Larai ce kaɗai ta farga da mutanan yanzu haka tana hannun hukuma ana tuhumarta".

                GIDAN AHMAD

Ahmad ya yi jim ya na mai rike da wayar sa a hannu, sakwamakon amsa wayar Minister da yayi. Zaune ya ke cikin motar sa, shigowar sa gida kenan yayi  parking kiran Minister ta shigo wayar sa.

"Bilkis! Bilkis!! Bilkis!!!"

Ahmad ya faɗa ya na mai jinjina kai, Sannan ya k'ara da

"Lalle Balkis wake ɗaya ce mai ɓata gari, mace kamar annoba?"

A fusace ya buɗe motar ya fito, ɓangaran Hajja Bilkis yayi niyar zuwa, amma ko da ya gifta ta ɓangaran baki ya ji yar haniya sai ya tuna da bakin da ya sa direba ya ɗauko daga tasha. Sai ya fara shiga falon bakin ya na mai doka sallama

"Salama'alaikum"

"Wa'alaikum salam"

Mata ne guda biyu, da  babba wacce ta bawa arbain baya, sai kuma yar budurwa su ka amsa. Zaune su ke a falon, in ban da hamma babu abin da su ke jerawa. Ganin Ahmad Munari wacce ta ke Yaya ce gun Ahmad, haka kuma kamar su ɗaya kamar an tsaga kara. Ta na fa a a fara'ar ta tace

"Ahmadu an dawo?"

Ahmad na mai sakin fuska ya k'arasa ciki.

"Maraba da su Munari"

Tsakiyar su ya zauna, ya na mai duban Kanwar sa da ake kira Maryam.

"Kun iso lafiya? ke dai Maryam kullum cikin rama ki ke kamar kuɗin guzuri, ya ku ka baro su baba?"

"Lafiya lau su ke"

Su ka amsa a tare,sannan Munari ta ce.

" Ah ina Maryam za ta yi jiki, yau da lafiya gobe babu, ciwo ya ki ya barta, shi ya sa ma Baba ta ce mu taho nan birni a gwada na asibiti ko Allah ya sa a dace,tun da kai ka ki zuwa Ahmadu"

Ahmad na mai sosa k'yeya ya ce.

"Ah ba haka ba ne,ba wai k'in zuwa na yi ba,kin san yanayin siyasa ne gaba aya babu lokaci...."

"Babu lokacin yan uwan ka Ahmadu?bare rashin lafiya ai ya fi gaban wasa"

Munari ce ta katse shi,ta na mai duban Ahmad da yayi kasa da kai cikin nuna rashin gaskiya. Kana ya nisa sannan ya ce

"Toh shin wai ma menene ke damun Maryaman?"

"Ciwon ciki ne, sai kuma kurarraje masu k'yak'ayi da ke yawan fito min"

Faɗin Maryam kenan.

"Allah sarki, Allah ya sauwake idan Allah ya kai mu gobe sai Hajja Bilkis ta raka ku asibiti, na ce dai kun gana da ita...."

Munari na mai girgiza kai ta ce

"Za dai mu gana idan ta dawo, ba mu tadda ta a gida ba"

Ahmad ya jinjina kai ya na mai kokarin ɓoye bacin ran sa, sannan ya ce.

"Amma dai Iya dudu ta ba ku abinci ko?"

"Ita ma Iya dudun ba ta nan, acewar wata yar budurwa ta kai ɗiyar ta asibiti, amma yar budurwar ta mana saukar kirki, har ruwa ta ba mu, ita ce ma ta siyo mana garin kwaki mu ka sha....."

"Garin kwaki Munari?"

Ahmad ya katseta cike da acin rai.

"Garin kwaki ku ka sha a gidan nawa? duk abincin da ke gidan nan Munari? Bayan sai da nai kiran Balkis in na sheda mata kuna tafe!"

Munari na mai duban sa ta ce

"Duk abuncin da ke gidan na ka Ahmadu ba sai an ba mu ba ko mun gani kafin mu ci ba?"

Mikewa tsaye Ahmad yayi cike da ɓacin rai. Wayar shi ya fiddo daga aljihu,ya fara k'ok'arin kiran waya sai kuma ya fasa,ya nufi k'ofa ya na fa in

"Wannan ai yasashshen zance ne ace yan uwana su zo gida na su sha garin kwaki duk arziki na!"

Har ya kai k'ofa ya juyo ya na mai duban su munari ya ce

"Ina ita wacce ku ka ce kun tadda a gidan?"

Munari ta ce da Maryam

"Maryam kira wannan ɗiyar?ya ma ta ke da suna?"

"Habi"

Maryam ta amsa mata a takaice.

"Je ki yi kiran ta,ina ga ciki ta shige"

Maryam ta tashi ta yi ciki domin kiran Habi. In da ta bar Ahmad ya na mai kunar rai na. Ita kuwa Munari sarautar Allah ta zubawa ido.

No comments:

Post a Comment