ABINDA AKE GUDU🙆🏽19
Batul Mamman💖
Hira suka zauna yi wadda duk tafi karkata akan rayuwar Asmau ta baya. Zubaida ta gyara zama tana karara jaddada mata kada ta kuskura ta biyewa rayuwar gidan. Idan da hali ma ta koma gidan iyayenta.
"Kinga ni a gidan nan na budi ido. Bansan kowa ba sai Mama kuma ban taba jin ko da wasa ta ambaci sunan wani gari a matsayin garinsu ba ko ta ce wane ne mahaifina. Tun abin yana damuna har na hakura. A 'yar fitar da nakanyi wani lokacin ne nake jin wa'azi a wurin masallacin bakin kasuwa. Sannan Mama ta koya min abinda ta iya na ibada kamar sallah da azumi. Bata yinsu dai sosai kuma bata matsa min akan inyi. Haka kawai Allah Yasa min kyamar wannan kazantar. Kowane katon banza yazo yayi amfani da mace idan sun ga dama har dukan matan suke yi. Ban saka rai da cewa nan gaba wani zai aureni ba don Mama tace ba'a auren mata masu zaman kansu da 'ya'ya marasa uba. Burina daya ne a rayuwa Asmau, in sami wani wurin da zan kira gidanmu ba wannan ba".
Asmau taji Zubaida ta kara shiga ranta. A duk inda Allah Yaso sai Ya halicci shiryayye.
"Ba'a son raina na baro gidanmu ba nima. A lokacin ji nayi tafiyar ita kadaice mafita gareni da abinda ke cikina. Bana tsammanin su Umma ko Mama zasu taba karbar cikin. Shiyasa na zabi na haife shi a wani wurin da babu wanda ya sanni na kula da shi."
Kofar dakin suka ji an turo wata kyakkyawar mace ta leko da kanta. Cingam take taunawa yana kas-kas kana ganinta kaga wadda ta rasa mafadi. A dakile tace "kije Uwargida tana nemanki".
Zubaida ta tabe baki "tashi muje nasan batun kudin haya ne".
Asmau ta janyo jakarta ta bude. Dubu goma ta kirga ta mayar da jakar gefe duk akan idon 'yar aiken.
Suna fita 'yar aiken mai suna Darling ta ruga dakin kawarta ta sanar da ita irin abin arzikin da ta gani a jakar bakuwa.
Dakin Uwargida ciki da falo ne. A falon su Asmau suka sameta. Sai yanzu da hasken rana ya wadata ta karewa matar kallo. Suna kama sosai da Zubaida sai dai fatar jikinta babu kyan gani saboda tsabar mayuka da ta sha. Ganin da tayi mata a cikin hasken farinwata ya rufa mata asiri.
Uwargida ta nuna mata kujera ta zauna. Falon sai ka zata na amarya ne saboda irin kayan alatun dake ciki. A darare Asmau ta zauna suka gaisa Zubaida ta zauna a hannun kujerar da Asmau take.
Uwargida tayi murmushi
"Ya bakunta? Ki saki jikinki indai zaki bani kudin haya to nan gidanku ne."
Asmau dai bata amsa ba ta dauko kudin ta mika mata. Ta karba ta soke a cikin riga tana dariya.
"Yarinya ki ce da arzikinki kika fito. Yau sai naga har kinfi jiya sheki ma. Dole na karawa Bulayi kudi don da alama baiyi zaben tumun dare be."
Zubaida ta ce "kinga tashi mu fita"
Uwargida ta tsayar dasu
"Na ce ba, idan kin yarda ki fara sana'a na zaba miki suna 'Yar Da6as. Naga jikin naki a mulmule ki hakura da hijaban nan, babu abinda zasu kara miki sai gumi da rufe kyakkyawan jikinki."
"Mama ita fa ba irin abinda tazo yi ba kenan." Zubaida ta fada tana yiwa babarta kallon raini.
Asmau ta dan gyara tsayuwa "dama ina so inji ko akwai gidan da kika sani masu wadatar da zasu iya daukar mai aiki. Kudin ko ba mai yawa bane zan iya".
Sai da Uwargida tayi dariya mai isarta sannan tace "to ai kin bar kari tun ran tubani. Babu gidan da za'a daukeki aiki alhalin kina zaune a gidan nan. Duk inda kika je koro ki zasuyi idan suka san daga nan kike."
"Niyyata idan na sami aikin na rokesu su barni na rinka aikin kwana."
Kallon mara wayo Uwargida tayi mata.
"'Yar Da6as, bari na baki shawara. Kada ki wahalar da kanki a banza. Wallahi babu matar da zata daukeki aiki kina gidan nan. Idan kin boye musu ma to dole zasu so ganin wata ce ta kawoki ba kawai zuwa kika yi daga wata uwa duniyar ba. Amma kina iya gwada sa'arki".
Daga nan tashi tayi ta shige daki su Asmau suka fita. Zubaida ce ta samo mata ruwan wanka bayan ta shirya suka fita neman aiki. Gidaje masu dan kyau da girma su Asmau ke shiga sai dai har yamma tayi babu inda suka yi sa'a. Da yawan matan da suke samu tambayar da suke fara yi mata shine wace ce cikin masu kawo 'yan aiki ta kawota. Wannan yanayi da ake ciki na rashin yarda babu wanda zai so daukar mutumin da ba'a san komai game dashi ba.
Washegari da zata fita Uwargida ta hana Zubaida bin ta. Duk tsiwa irin ta Zubaida babu yadda ta bata yi ba aka hanata fita. Asmau tace babu komai bazata yi nisa ba don kada ta bata.
Tasha yawo taga kuma mutane kala kala. Wasu da kalamai masu dadi suke nuna basa bukatar mai aiki. Wasu kuwa sai sun zageta musamman idan aka kare mata kalli bata yi kama da wadda talauci ya koro ba.
Ga yunwa ga kishirwa haka ta gaji ta kamo hanyar gida. A cikin kasuwar ta sayi bokiti da tukwane kanana biyu da plate. Har dan risho ta siya na girki da kayan abinci sannan ta koma gidan a gajiye.
Matan gidan babu mai kulata itama banda Zubaida babu harkar wanda take shiga har ta cika sati. A lokacin ne kuma tashin zuciya da amai suka sarketa. Tunda kowace mace girkinta daban take yi yawanci duk a kofar daki sai ya zamana warin girkin yana damunta. Idan taji aman bandaki take tafiya tayi ta fama babu wanda ya sani sai Zubaida. Ita kadai ke tausayinta take zuwa ta taimaka mata. Gashi duk abinda taci sai ya dawo.
Tayi kusan sati biyu tana fama gashi bata hakura da neman aiki ba. Har irin zaman shago da sharar titi duk ta nema. Ta rame tayi baki sosai. Sai dare tayi ta kuka tana kiran Umma.
Uwsrgida kuwa saka mata ido tayi. Jira takeyi Asmau ta kai inda hakurinta zai kare ta aminci ta fara aiki kamar sauran matan gidan.
*****
Hajjo ke kai kawo a tsakar dakinta tana jiran Rabe da ta aiki dansa ya kira shi tun wajen awa daya da ta wuce. Shigowa yayi da tsinken sakaci yana ta sokawa a hakoransa.
"Hajjo kina ta jira ko? Abinci na tsaya ci."
"Babu komai Rabe. Dama nace ya kamata muje gidan yarinyar nan Bara'atu. Kusan sati hudu da batan Asmau mun barta ita kadai tana fama. Duk lalacewa 'ya'yan Shuaibu ne bai kamata mu zare hannu daga kansu haka ba."
Hade rai yayi kafin ya soma magana cikin nuna isa "Hajjo tun rannan kike maganar nan nace bazamu je ba. Ita bata san ta neme mu ba sai mune zamu je kawai saboda rasshin zuciya. Ki kyaleta nasan yarinyar bazai wuce ta tafi yawon ta zubar ba. Kuma da kike tausayinta ai ta raina ki. Tun bayan maganar cikin Asamaun kika ce a turo miki Yassar yake ko wa, da kanwarsa amma ta shafawa idonta toka taki".
Hajjo tayi shiru ganin Rabe yana fada. Har ranta tana tausayin Bara'atu kuma ta shiga damuwa sosai da batan Asmau. Sai dai tana tsoron batawa Rabe rai. 'Yan uwansa gabadaya yanzu tsoronsa suke yi babu mai son ketare maganarsa.
Zuba mata ido yayi tana tunani. Yana gudun Hajjo ta dena jin maganarsa ya shiga uku.
Ita ma ganin bacin ransa tayi murmushi "nifa dama so nake muje ko rashin mutumci ne muyi mata bawai mu nuna tausayi ba. Duk laifinta ne lalacewar yaran. Jeka abinka kawai"
Rabe yana tsare gira ya shuri takalmansa ya fita hankalinsa a dan kwance da jin maganar Hajjo ta karshe.
Da ya fita dan kashingida tayi sai dai sam baccin yaki zuwa. Tunanin yadda ta kasa rike zuri'ar Shuaibu ne yake damunta kamar ba danta ba. Kuma ta duba iyakar dubawa babu wani laifi da Bara'atu tayi mata. Yanke shawara tayi a ranta gobe zata sake tambayar Rabe ko zata yi sa'a ya barta taje gidan Bara'atun.
*****
Umma ta idar da sallah Aina'u ta fada mata wani dan sanda yana nemanta. Ko addu'a bata yi ba ta tashi da sauri.
Qasim ne ta tarar a falon suna magana da Jafar. Bayan sun gaisa yake sanar da ita har yanzu dai bincikensu bai nuna musu komai game da inda zasuyi tunanin samun Asmau ba. Amma tayi hakuri don yayi alkawari bazai taba dena nemanta ba ko a raye ko a mace.
"Nagode sosai Qasim Allah Ya saka da alkhairi."
Tausayin Umma yake ji duk ta rame ta fita hayyacinta. Gidan idan ka shigo tamkar babu mutane saboda halin da suke ciki. Kuma a ganinsa duk laifinsa ne na ziga Abubakar.
"Umma ki dena yi min godiya. Bani da wani buri a rayuwata da ya wuce neman Asmau da zama uba ga abinda ke cikinta. Tsautsayi ne da kaddara ya jefata wannan halin".
Hawaye ne ya saukowa Umma. "Haka ne Qasim. Dukkan *DAN ADAM* yana yin aiki ne da ya dace da kaddarar rayuwarsa. Fatana Allah Ya kare min Asmau daga fadawa mugun hannu ko shiga duniyar sa6o."
Jafar yace "Umma don Allah ki dena kukan nan. In sha Allah zamu ganta komai daren dadewa."
Har bakin gate ya raka Qasim wanda ya koma gidan Mama. A can dinma zancen Asmaun ne dai. Duk da har yanzu ba wai ta gama amincewa bane cikin na Abubakar ne sai dai zaman tare da Umma yasa suka ajiye komai burinsu kawai a ganta.
*****
Yau ma a gajiye Asmau ta dawo gida ga jikinta duk babu dadi. Kamar sauran ranaku bata yi sa'ar samun aiki ba. Dan kayan abincin da ta siya duk sun kare dama ba da yawa ta siyo ba saboda tunanin barin gidan idan ta sami aiki. Da sallama ta shigo wasu suka amsa wasu kuwa ko kallonta basuyi ba ta wuce dakinta.
Jakarta ta janyo zata dauki kudi ta siyo abinci taga babu ko kwandala a ciki hatta sarkarta babu. Jakar ta zazzage gabadaya bata ga kudin ba ta fito ta tafi dakin Uwargida.
Zubaida na jin sallamarta ta fito da murmushi. " 'Yar uwa an dace yau?"
Asmau ta girgiza kai sai kuka. Uwargida ta shigo dauke da buta da kwandon wankanta a hannu daidai lokacin da Asmau tace an sace mata kudi. Kamshin sabulun wankan Uwargida ne ya bugi hancin Asmau tun kafin ta fita daga dakin amai ya kufce mata.
Uwargida tayi galala tana kallonta cike da mamaki. A tsakar gidan ta durkushe tana ta kwara amai Zubaida nayi mata sannu.
Taruwa akayi a kanta Uwargida ta durkusa a gabanta bayan ta gama aman ta gwale mata ido tana gyada kai kamar kadangaruwa sannan ta kalli Zubaida.
"Amma Zuby kin ha'inci sabuwar kawarki da baki fada mata babbar dokar gidan nan ba. 'Yar Da6as ai ba'a ciki a nan. Idan ma ya shiga bisa tsautsayi to sai ki zaba ko ki cire ko ki fita. Sannan da kika ce anyi miki sata to tun wuri ki sani bazan lamunci karya ba. Wannan cikin kuma ki san yadda zakiyi dashi kafin raina ya baci."
Tsaki ta buga ta wuce dakinta tana fadan Asmau zata kashe musu kasuwa.
Da taimakon Zubaida Asmau ta koma daki ta kwanta. Duk yadda taso daurewa kuka take yi sosai. A yanzu bata da wani gata sai Allah. Dan kudin da take takama dashi an sace. Dama tana son siyan kwadon rufe kofa Allah bai nufa ba har aka yi mata sata.
Kwanakin da suka biyo baya ba karamar wahala tasha ba. Rashin kuzari da tashin zuciya kullum dashi take tashi. Ga rashin abinci. Ruwan sallah wannan bata samu sai abinda Zubaida ta dauko a dakinsu batare da sanin Uwargida ba ta bata.
Duk yadda taso daurewa abin ya gagara. Kusan wata guda tana cikin mawuyacin halin nan. Kayanta sunyi dukun dukun kamar wadda take wasan dambe. Ita kanta warin jikinta take ji wanda yake kara sakata jin amai.
Tana zaune a kofar dakinta wanda taci alfarma Uwargida ta daga mata kafa bata biya kudin wannan watan ba. Matar dakin kusa da ita wadda taji ana kira Beauty ce zaune tana cin taliya da manja da yaji. Yawun Asmau duk ya tsinke ta zubawa Beauty ido kamar ta hadiyeta har sai da ta kula ta ja tsaki ta koma cikin dakinta. Haushin Asmau take ji saboda saurayin da yazo wurinta dazu ya nuna yana son Asmaun har yayiwa Uwargida magana.
Beauty na shiga daki Asmau ta rarrafa ta tsinci taliyar da ta zubar a kasa ta cinye tana kuka. Duk abinda take yi akan idon Uwargida tayi murmushin keta. Dama tuni ta hana Zubaida bawa Asmau abinci sai dai a bayan idonta. Karasowa tayi gabanta ta tsaya da alamun tausayin karya a fuskarta.
" 'Yar Da6as kin fiye taurin kai. Zaki iya canja akalar rayuwarki duk sanda kika so. Dazu mutum kusan na tara kenan da ya nuna yana sonki amma kullum sai ki dage ke bazaki amince ba. Ga yunwa tana damunki sannan wannan abin na cikinki yanzu kin amince ki haife shi a wannan yanayin? Ni shawara nake baki nan da sati idan baki zubar da cikin kin fara min aiki ba zaki bar min gida. Na daga miki kafa ne kawai don nayi tunanin zan more ki."
Bayan tafiyarta Asmau ta rike ciki tana kuka. Tabbas idan ta haihu rayuwar danta zata shiga mugun yanayi. Halin da ta tsinci kanta yanzu ji take ina ma bata raye. Shawara daya ta rage mata tunda babu mai tausayinta gara ta zubar da cikin ta nemi kudi kamar yadda Uwargida ta bata shawara.
*****
Karfe biyu da rabi na dare Umma ce zaune akan abin sallah. Addua take yi tana zubar da hawaye....fatanta duk inda Asmau take Allah Ya kareta daga fadawa ga abinda zai zama halaka ga rayuwarta.
No comments:
Post a Comment