Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar, hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan, saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi.
"Ummi."
Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da tafiya ba.
"Shigo."
Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi.
"Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..."
"Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata bud'e na mazaunin gefensa.
"Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji, matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa jikinta. Ya soma tuk'i cikin gwanancewa bayan ya maida gilas ya rufe, ya k'ara k'arfin Ac kad'an. Saida suka bar layin gaba daya sannan ya rage gudun da yakeyi ya soma magana tamkar baya so, magana mai cike da nutsuwa da kasaita.
"Bansan da haka ba, idan ma nasani toh watakila zuciyata ce wacce ke jin tsananin tausayi yaran da kuma jin haushin iyaye masu barin yaransu yawan aikatau, ya sanyani kasa nutsuwa nayi tunani mai kyau akan haka. Akan abinda na fad'a, ina neman afuwa, kiyi hakuri kinji?"
Ya karshe yana k'ara k'ank'an da muryarsa tamkar mai rad'a. Wannan yasa zuciyar Ummi cigaba da harbawa da sauri-sauri. 'Nayi hakuri fa yace?' Ta tambayi zuciyarta, ta lumshe ido ta bud'esu, ashe daman masu kudi sukan yi laifi kuma su bawa 'yan aikinsu hakuri? Ikon Allah.
"Kinji?" Ya k'ara furtawa cikin kara kankanta murya, sai kuma alokacin ya dubeta. Gani yayi fuskarta ta yi fayau, hakanan idanunta sun d'an kumbura adalilin kukan da ta ci. Haka kawai ta ga ya gangara gefen titi ya tsaya. Tayi duba da wajen, wajejan gidan gwamna ne na garin Kano, abinda yasa ta rike hakan ma bai wuce adalilin Fahad da ta ta6a ji ya fad'a ba.
Ta dubeshi kad'an, shima ita ya fuskanto. Ta kauda kai tayi narai-narai da fuska tamkar mai shirin yin wani kukan.
"Na hakura, ni daman banyi fushi ba. Ni wace da zanyi fushi da.."
"Ni d'in wanene da na fi karfin ayi fushi da shi?"
Ya katseta ta hanyar jefomata tambayarnan. Tayi kasa da kanta batare da tace uffan ba.
"Ni ba kowa bane face DAN ADAM, kuma duk dan Adam ajizi ne, yakan kuskuro, wani da saninsa wani kuma baisan ma kuskuren bane. A rayuwa, bani da raayin shiga lamuran da bai kasance matsalata ba, ban fiye damuwa da shiga rayuwar mutane har ma na takura musu ba ok? Abinda ya kaini har nayi miki batun bai wuce na fusata..."
Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba.
"Kiyi hakuri." Shine abinda ya k'ara furtawa. Cikin rawar murya Ummi ta share fuskarta wanda zuwa yanzun batasan dalilin kukannata ba, ta dangana da tuna mahaifiyarta da tayi wacce kokusa bata ta6a jin dumin jikinta ba.
"Ya wuce Yalla6ai, don Allah ka daina bani hakuri."
Ya zubawa fuskarta ido kafin ya saki murmushi mai 6oyayyar fassara.
"Thank you." Daga haka ya soma tafiya, tana jin wayarsa na faman ruri. Duk bai dauka ba, sai ana uku ta ga ya dauka. Haidar ne, hakuri ya shiga ba shi ya sanarmishi wani uzuri ne ya hanashi karasowa da wuri amma yana nan tafe. Daga haka sukayi sallama.
Ummi tayi lamo tana tunane-tunanenta, ko a mafarki idan akace mata Faruk nada mutunci har haka, toh zata iya musawa idan tayi la'akari da yanayinsa koyaushe cikin daure fuska, sa'a ce ke sanyawa kaga fuskarsa a sake kamar yanda sa'ar ce ta ci ta ganta dazun dauke da murmushi.
"Mene sunanki na ainahi?"
Ya watsomata tambayar batare da ya maida hankali ga dubanta ba.
"Hasiya." Ta fad'a a tsanake kamar ta karawa sunan dadi domin kuwa babu wacce ta fad'omata a rai alokacin sai mahaifiyarta wacce sunanta ne ta ci.
"Nice name, suna kika ci ne?"
Ta gyada kai.
"Sunan mamana ce."
Da mamaki ya dubeta.
"Mamanki tana nan?"
Ummi idanunta suka k'ara ciko da ruwan hawaye, ta k'ara narkar da murya tana son yin kuka.
"A'a ta rasu wajen haihuwata."
Maganar ta dakeshi, ya daure ya hadiye abinda ya ji na tausayinta, saidai duk da hakan saida muryarsa ta kasa 6oyewa.
"Allah Yayi rahma agareta."
Ta amsa da amin cikin zuciyarta. Duk da wani 6angare na zuciyarsa tana so tasan fin haka game da ita, saidai bai ga wata hujja da zai kare kansa ba idan ta nemi sanin dalilin tambayar duk da baya zaton haka din.
Har suka isa babu wanda ya k'ara cewa uffan, hakazalika, kowanne da irin tunanin da yake. A zahiri Ummi ta fi karkata ne ga tuna rayuwarta, babban abin tambayar da bata da amsa shine inda zata ga dangin mahaifiyarta, a 6angare guda kuwa, tana mamakin Faruk da halinsa wanda batasani ba. Bata manta gargadin Ihsan gareta a kwanakin baya.
'Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki.'
Wani murmushi mai ciwo ya su6uce mata daidai kuma lokacin da Faruk ya kallota, kawai sai ya tsinci zuciyarsa cikin jin sanyi, ko babu komai bazata fita motarsa da fushinsa ba.
Tsayuwar da ta ji yayi ne yasa ta fahimtar sun iso don gaba daya ta luluk'a tunanin dabi'un Ihsan wanda ya sha bamban da na sauran yaran Mami. Suka dubi juna ido cikin ido, gaba daya sun ji wani iri wanda tsakaninsu babu wanda ya bada tunani na daban.
"Saida safe."
Ya sanya hannu ta 6angarensa ya ciremata (lock). Batare da ta amince sun kara hada idanu ba ta amsa.
"Nagode, Allah Ya tsare hanya. Don Allah ka sanarwa da Mami na taho gida kada ranta ya 6aci, idan da hali kada ka nuna kai ka kawoni don Allah."
Yayi shiru yana mamakin dalilinta na fadin hakan, sai kuma ya ta6e baki ya daga kafada kadan.
"Nifa ban iya karya ba, ba kuma zan fara saboda ke ba ok? Idan ta tambaya zan fadamata."
Ya karashe da murmushi yana dubanta, ta kauda kanta. Banda toh babu abinda tace ta sauka. Ta rufe kofar batare da ta kara kalla ba sakamakon duhun gilashin.
Ya bita da kallo har ta shige ciki, ya numfasa. Mace kam har mace Ummi ta kai. Shine kawai abinda ya ayyana a ransa daga haka ya ja motarsa yabar wajen a miliyan. Mintuna goma bai cika ba ya isa ga wajen party. Ya kuwa iske Mami na nemanta, nan ya sanarmata yanda akayi, yayi kokarin cewa a hanya ya ganta tana kuka tana tafiya ya taimakamata baisan abinda ya faru gareta ba. Mami tayi mamaki, karshe ta yanke da zarar sun koma zata ji ko menene.
"Mutuminki gashican ya iso."
Da sauri Iklima ta kai dubanta ga inda kawarta Hassana take mata nuni, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke har tana hamdala a fili. Abin ya bawa Hassana dariya, kawai gani tayi Iklima ta ja hannunta.
"Muje ki rakani na gaisheshi."
Hassana ta so k'in zuwa don gudun kada ya disgata, saidai dole hakanan ta bi bayanta suka nufi inda yake a tsaye bayan amarya da ango suna gaisawa.
Haidar ya dubeshi yana mai kai bakinsa saitin kunnensa.
"Tsaya muyi hoto mana."
Yana murmushi yayi kokarin zillewa, abin saima ya bawa Haidar domin kuwa yafi kowa sanin Faruk bai fiyeson hoto ba. Ya dank'eshi, a hakan ma sunsha hotuna wajen jama'a masu wayoyi, dakyar ya tsaya yana duban Haidar fuskarsa dauke da wani hadadden murmushi, a haka aka daukesu.
Cikin masu daukar hoton, har da Iklima wacce gaba daya ta gama narkewa cikin so da kaunar Faruk wanda ya gama tafiya da ruhinta. Bata bi ta kan Hassana ba ta mara mishi baya da sauri tun baikai ga k'arasawa wajen yan uwansa ba wadanda su yake yiwa kallon abokai domin Faruk ba shi da babban amini ke6antacce da za'a kira nasa akoyaushe. Bazai rasa abokan ba, duk wata shawara acewarsa yayyunsa sun isheshi.
"Ina wuni Yaya Faruk." Muryar da ya tsinkaya kenan daga gefensa. Ya kai dubansa gareta, take kuma sai ya tsuke fuska tamkar ba shine ke murmushi ba yanzun. Kansa kawai ya gyada sannan yayi gaba. Da sauri ta juya itama tun baikai ga bata kunya ba. Tun kafin ta kai ga Hassana, take watsa mata harara har ta dangana da mazauninta. Alokacin ne ta samu damar yi mata magana.
"Ai ga irinta, saida nace kada kije amma kika k'i saurarona, yanzun da ya jefeki da kallon banza ai kinji dadi."
Tana maganar a fusace. Iklima idanunta akan Faruk wanda ke hira abinsa hankali kwance, ta murmusa.
"Yasan ya had'u ne shiyasa yake shan kamshi ga yanmata. Wallahi ina sonsa fa."
Hassana ta ta6e baki. "Shi kuma baisan da zamanki ba."
Sai alokacin ta dubeta tana harara.
"Wai me kikeson ki cemin? Kin manta alak'armu da shi ne?"
"Naga Ihsan ma k'arewar alak'a da shi ai." Hassana ta fada gami da jan dogon tsaki sannan ta cigaba da maganarta.
"Shi namiji idan yaga kin fiye zakemishi rainaki zaiyi wallahi, ki kula dakyau leema, kisan dai dabarar da zakiyi ki shawo kansa, amma idan har zaki cigaba da yi mishi irin wannan shishshigin agaban jama'a, toh fa zaki raina kanki."
Iklima tayi shiru tana sauraronta, ga dukkan alamu dai maganganun Hassana yana shigarta. Tayi na'am da shawararta na cewa ta dinga yi mishi ladabi a fili da kuma online.(chatting), a sannu idan suka saba sai tayi kokarin shawo kansa.
Haka aka tashi taron kowa cike da farinciki idan an cire Iklima wacce bataji dadi ko kadan ba na yanda Faruk ya gwatsaleta ba.
Koda su Mami suka koma gida, ta tuntu6i Ummi akan dalilinta na barin wajen (party), bata 6oyemata yanda sukayi da Ihsan ba, da kukan da Faruk ya ga tana yi ya taimaka ya kawota gida. A take Mami ta nemi Ihsan a waya amma fir ta karyata tace batasan ma da zaman wata Ummi awajen ba. Ranar duka ne kawai Ummi bata ci ba, amman ta sha fad'an Mami sosai, acewarta bazata lamunci a dinga yiwa yaranta karya ba akan abinda bai zama halinsu ba.
Haka Ummi tana ji tana gani aka k'aryatata aka bata laifi, dole ta bawa Mami hakuri sannan ta bi umarninta ta chanjawa Fahad kayan bacci ta nemi makwancinta. Bacci gaba daya gagararta yayi don ta kasa tsaida hawayenta, sai wajen asuba ta samu ya dauketa.
Washegari suka shirya tafiya Abuja kai amarya. Da yawansu ta mota zasu tafi, ciki harda Mami. Hakan yasa da sassafe ta kammala komai, kasancewar kwana daya zasuyi ta amince Ummi ta zauna agidan tare da su Adnan. Ta mascara mata cewa ta rik'e amanarta. Daga haka sukayi sallama, ita da Ramma na binsu da adduar sauka lafiya.
Misalin karfe biyar na yamma, babu kowa a sashen Mami sai Ummi dake kwance a tsakar gida. Fahad da Adnan sun fice yawo, Ihsan kuwa har lokacin bata dawo ba, da alama da ita aka nufi Abuja, Ramma kuwa daman tun tafiyar Mami tana kammala ayyukanta ta bar gidan.
Muryar da ta ji tayi sallama ne yasa babu shiri ta mike zaune a matukar razane. 'Hajiya Binta?' Ta fad'a a ranta cike da mamaki. To mene ya kawota sashen Mami alhalin a baya ba shigowa takeyi ba?
Fuskar Hajiya Binta a sake ta k'arasa shigowa ciki tana d'an waige-waige.
"A'a Ummi, ba kowa ne sai ke kadai?"
Ummi ta russuna cikin ladabi ta amsa mata.
"Eh Hajiya. Ina wuni."
Hajiya ta zauna a saman wata kujerar roba cikin karamar murya kamar mai rad'a ta amsa.
"Lafiya lau Ummin Hajiya. Sai kyau kike k'arawa Masha Allah."
Murmushi ta dan yi mai kama da yak'e domin ba wani sabo tayi da ita ba, banda munanan kalamai da take watsamata aduk haduwarsu, babu abinda ke shiga tsakaninsu. Maganar Hajiya Binta wacce ta k'ara matsowa dab da ita ya katse tunaninta.
"Ummi ina neman wata alfarma daga gareki, matuk'ar kika amince kika yi yanda na sanyaki, toh ina miki rantsuwa da Allah zakiji dadin rayuwarki. Ina tabbatar miki sai kin samu 'yanci agidannan kamar kowace 'ya matukar kikayi yanda nace."
Ummi ta ji kanta yayi dumm. Ta rasa gane alkiblar da maganganun Hajiya Binta suka dosa. Ta dubeta duba na neman karin bayani. Hajiya Binta ta kara lek'en bayanta, bata ga wani ko wata dake tahowa ba. Ta fiddo wata bak'ar leda daga zaninta ta bud'eshi gami da nunawa Ummi. Ummi ta zaro ido cikin matukar kad'uwa ganin wani abu wanda aka duk'unkule da farin zare mai yawa wanda har ya zamana baka ganin komenene aciki sai zaren da yayi kamar bal.
Ji tayi ta soma gumi cikinta kuwa wani hautsinewa ya yi na ban mamaki.
Hajiya Binta wacce gaba daya ta gama kwadaituwa da samun cikar burinta ta cigaba da magana.
"Wannan kadai zaki ajiye a k'ark'ashin gadon uwardakinki, daga tsakiyar gadon, shikenan kin kammala mini komai. Wallahi Ummi zakiji dadin rayuwa fiye da zatonki. Zaki samu duniya yanda baki ta6a kawowa ba. Za kuma ki jera da yaran gidannan a zuwa makaranta mai tsada, a fannin ci da sha da kuma sutura. Rik'e kiyimin yanda nace."
Ummi na k'ok 'arin magana ta tsaidata ta hanyar damk'a mata abin a hannunta. Ta jefeta da murmushi.
"Zan nemeki gobe." Daga haka ta mik'e sai kuma ta dawo baya. Fuskarta a murtuke ta dubeta, duban da ya k'ara hautsinata.
"Karki soma yunk'urin tonamin asiri, muddin kika soma sai na lahira ya fiki jin dadi. Ki kula." Daga haka ta fice da sauri. A nan kofar shiga ta tarar da aminiyarta ta, Hajiya Luba wacce ke tsayuwar gadi kada wani ya taho ya iskesu. Tana ganinta cikin rad'a tace.
"Angama?" Hajiya Binta tayi dariya.
"Ta isa daman ta k'i?"
Sukayi dariya k'asa-k'asa gami da cafkewa sannan suka bar wajen da sauri.
Ummi ta shiga tsaka mai wuyaaa....!
Gaba d'aya gigicewa tayi, tayi sauri yarr da kullin a kasa kafin ta cigaba da ambaton Allah a fili. Ita kuwa Hajiya Binta me take nema haka a duniya da har zata iya yiwa wani asiri? Ummi a iyakar tsawon rayuwarta ta tsani mugunta ta tsani mai yinsa.
Ta k'ara kallon kullin cikin zubar hawaye, tunanin kada Adnan ya dawo ya isketa da shi yasa ta mike a gaggauce gami da daukarsa da hannun hagu don kuwa tsoro da kyankyaminsa take. Allah Yayi mata tsari da aikata mummunan aiki irin wannan. Shine addu'ar da take ta nanatawa a ranta. Kai tsaye ta nufi dakinta da shi ta kulle cikin bak'ar leda da zummar washegari idan zata makaranta ta yarr koda acikin kwata ne.
Bayan ta adana shi inda babu mai gani tunda ba mai shigowa dakinta, ta fito ta zauna jigum, gaba daya a tsorace take. Kuka kam ta sha, a karshe dai tayita addua akan Allah Ya ku6utar da ita daga sharrin Hajiya Binta.
Bayan dawowar su Adnan dole ta saki ranta kada su gane. Ya damkamata karamar robar (ice-cream) da suka siyo, suma suka zauna a falon suna kallo suna shan abinsu hankali kwance. Ita dai sha takeyi amma kokusa kallon baya gabanta, koda ta soma jin dadinsa da zarar ta tuna da Hajiya Binta sai jikinta yayi lakwas. Karshe rufe robar (ice cream) din tayi gami da shigewa daki bayan ta nemi zubomusu abinci sun tabbatar mata sun k'oshi. Daman ta ga alama, kawai dai gudun kada ace tayi laifi ya sanya ta tambaya.
A ranar Ummi dai bata runtsa ba, gani takeyi kamar wani abin zai sameta asanadin kullin da ke a dakinnata. Bata ta6a fatan ace tana da wayar hannu ba sai a wannan dare, da babu abinda zai hana ta sanarwa Antinta ko don ta bata shawarar yanda zatayi.
Washegari Adnan suka fice makaranta, ya tabbatarmata su Mami sai wajen yamma zasu dawo. Hakan yasa suna tafiya ta bude dakin Mami don daman mukullin yana hannun Adnan sai a yanzun ya damk'amata. Ta tsaya cak a tsakar dakin tana tuno da mugun aikin da Hajiya Binta ta sanyata. Tausayin Mami ya mamayeta.
"Baiwar Allah kenan, tana zama da ita da zuciya d'aya, ashe tana da wani mugun kulli dangane da ita." Cewar Ummi a fili don bil hakki tausayin Mami ya gama mamayeta. Haka ta gyaramata ko'ina tsaf ta wanko bandaki ta goge duk inda ya dace sannan ta feshe dakin da turare ta kulle.
Tana shirin soma gyaran falon Mamin ne. Ta tsinci sallamar Hajiya Binta. Gaba daya saida ta ji tsayuwa na neman gagararta. Dakyar ta samu nutsuwa bayan karanta addu'o'i. Ta nufi falon tana mai amsawa cikin dakiya. Wani zun6ulelan hijabi ne ajikinta, fuskarta ya nuna bata jima da tashi daga bacci ba. Ta sanya hannunta a k'ugu, fuskarta a murtuke wanda ya rud'a Ummi saidai tayi iyakar kokari bata bari ta fahimta ba. Da sauri ta durkusa.
"Ina kwana Umma."
Batare da ta amsa ba, ta zarce ga abinda ya kawota.
"Kinyi aikin da na sakaki?"
Ummi ta k'ak'alo murmushi.
"Fitowata kenan ma daga aikin Umma, nayi yanda kika umarceni."
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Hajiya Binta don har ga Allah bata yiwa Ummi kallon mak'aryaciya, dari bisa dari ta yarda da cewar ta aikata.
"Tabbas kin biyani Ummi, kuma muddin Hak'ata ta cimma ruwa, bazan watsamaki k'asa a ido ba. Abu d'aya nake gargadinki akai, ki kiyaye bakinki. Wallahi Ummi kikayi kuskuren tonan asiri saina k'ullamiki mummunan sharri."
Daga haka ta fice da sauri. A can kofar da ta raba sashensu da na Hajiya Madina, sukayi kick6us da Ramma. Ta gaisheta tana cike da mamakin ganinta. Hajiya Binta ta amsa cikin basarwa gami da fad'in.
"Ashe kuma Hajiyar bata dawo ba? Na dauka tana nan na aikomata tallar dogayen riguna."
Ramma ba don ta gamsu da wannan shirgaggiyar ba, ta amsa da.
"Ai Hajiya munyi waya sai zuwa yamma tacemin zasu iso."
"Allah Ya kawosu lafiya."
Daga haka ta wuce da sauri don ta tabbatar da wuya idan karyarta ta samu shiga. Ummi wacce tub jiyo muryar Ramma ta biyo bayanta a guje cikin kad'uwa, ta ji tattaunawarsu. Tayi saurin komawa. Bayan shigowar Ramma ta hau kwalamata kira da k'arfi, a rud'e ta k'araso.
"Baba Ramma ashe kin zo, ina kwana." Cewar Ummi ba a nutse ba. Ramma ta zubamata ido, gaba daya zargi ya d'arsu a ranta.
"Lafiya naga Hajiya Binta anan? Ki fadamin gaskiyar abinda ya kawota."
Ummi wacce ta soma had'a zufa ta bata amsa batare da ta kalleta ba.
"Um..nima nayi mamaki, tambayata tayi ko Mami sun dawo nace aa shine ta tafi."
Ramma ta gama hango rashin gaskiya k'arara a fuskar Ummi, saidai kasancewar tasan k'arya baya daga cikin d'abi'arta yasa nan take ta amince.
"Toh Allah Ya kyauta, wannan dai salon munafuncine, tana nan ba'a shigo ba sai bayan da ta k'aura. Mutane dai ba tsoron Allah, Allah Yasa ba wani mugun abin ta..."
Sai kuma ta datse maganar da fad'in.
"Um, Allah na tuba. Bari na kama abinda zai fishsheni."
Daga haka ta fice daga falon, Ummi Ta sauke ajiyar zuciya don gaba daya ta gama tsorata. Ita kanta jinta takeyi wata marar gaskiya
No comments:
Post a Comment