Thursday, 15 December 2016

Ina Darajan take? 7th post

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI.....✍🏽
7⃣4⃣

  Maimakon ta ji sauki,sai ma k'ara k'ona ma ta rai hakurin da ya ba ta yayi. Ta buge hannun sa a fusace sannan ta ce "You ar sorry din ka na banza na hofi,tun da ka gama cutata,dole ka bud'i baki ka ce za min zak'in baki,idan har haka soyayyar ka ta ke da cuta da cutarwa tir da irin ta!" A fusace ta yunk'ura za ta tashi daga kan cinyar sa,shi ma kuma wannan karan be hana ta,be kuma sake tanka mata ba har ta kai dab da kofar d'akin za ta shige, idanun sa kan ta ya ce "My Habeebti.." " Wai menene!" Ta juyo a fusace,ta k'ara da "Sunana Aliya! Kar ma ka k'ara kira na Habeebti bare ma My Habeebti!!" Murmusawa yayi,hannun sa biyu sarke a girjin sa ya ce "pls make sure kin sha magani kan ki kwanta.." rolling kwayar idanun ta ta yi,ba tare da ta damu ta amsa ba ta shige ciki har da buga k'ofa. Shi kuwa Haroun nan ya kishingid'a yana sakar zuci dan duk duniya babu wacce ya ke so ya ke k'auna kamar Habeebti,gashi bala'in buk'atar matar sa yake,amma sam ba ya so ta fuskanci haka har sai ta sauko daga dokin fushin da ta hau ta rage tsanar da ta ke masa,adduar sa Allah ya sa ya iya jurewa.
   Habeebti da ta shiga d'aki kan gado ta fad'a,gaba d'aya ta kasa gane lamarin ta. Iyakar tsana ta san ta tsani Haroun,amma duk sanda ya kusanto in da ta ke gabad'aya sai ta ji ta susu ce ta kasa  kwakkwaran tunani,bugun zuciyar ta ya k'aru kuma. Ba dan Allah ya sa ciwan da ya dasa mata cikin ran ta ko da yaushe ta gan sa kamar ya na fama mata ba ne da Allah kad'ai ya san in da za su k'arke. Da ga ita har shi haka su ka raba dare suna tunanin juna,ga soyayyar da za a bari ta fito,amma tsana da k'addarar rayuwa ta hana.
   Washagari,ganin wayar ta ta lalace Yakumbo ma sai wajan Anty Salmah da ta kai Junior ta sami nunbar Haroun ta kira sannan ta samu su ka yi waya da Habeebti. Mai Junior ya siyo mata sabuwar smart phone kirar HTC mai matsakanci kud'i,tare da bata hakuri akan ya so siya mata wacce ta fi wannan tsada amma ya sake sabuwar mota ne ba kud'i a hannun sa. Dan abun da ya kai sa Kano kenan dama,nunwa su Mama motar.

     Da kamar ba za ta karb'a ba,sai kuma ta yi tunanin in ma bata karb'a wata watsattsiya zai bawa a waje..(mata ku kyautata zaton ku ga mazajen ku shi ne mafi alkhairi a gare mu) da wannan tunanin ta karb'a,har da godiya,ta masa Allah ya sanya alkhairin mota. Hakan ya sa Haroun jin dad'i sosai ganin Habeebti duk rigimar ta ashe ta iya godiya idan an mata alkhairi,mace mai godiya ga mijin ta daban ta ke,kuma godiyar shi zai sa ya k'ara mata wani.

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI.....✍🏽
7⃣5⃣
  Bayan sati d'aya,ana sa ran jibi za a tashi da azumin ramadan. Habeebti zaune a falo ta na waya da Aysha Tafeeda,in da ta ke bata labarin rayuwar ta da Haroun cike da k'yeta. Sam ba ta san Mai Junior ya fito daga d'akin sa ba,jin abun da ta ke fad'a ya sa shi tsayawa ya na sauraron ta ba tare da ya yi niya ba,musammam da ya ji ta na fad'in" Wani mu na shan love?ke ni fa ina zaton na nak'asa mai Junior rannan da na aika sa injury......ahahahahaha" ta shek'e da dariyar mugunta.
    Cike da mamaki ya gyara tsayuwa ya na mai sauraron ta. Ita kuwa bilhaqqi wayar ta take,ta k'ara da " Wallahi k'awata,am very sure of that,ya zama fanko,ke ko irin making dan move dinnan ya kebe da matar sa be tab'a gwadawa ba,hana rantsuwa dai ran da na yi fever ya kwana d'aki na shi din ma babu abun da ya min, ina tashi na kara masa speed...." Ko me Aysha ta ce mata,ta sake kwashewa da dariya,ta ce" wani girma ko sojacin shi na banza bayan na buge shi,shi da fanko be da babanci,ke in Mai Junior zai iya tab'uka wani abu,Junior ma zai iya....."

  Ganin Haroun ya zo ya wuce ta gaban ta ya sa ta katse wayar da sauri,dama kuwa abun da ya ke san ta yi kenan dan  cin fuskar da ake masa ya ishe shi,ba dan ogan sa ke kiran sa akan tafiyar da za su yi gobe zuwa Abuja taron sojoji da za a yi da ya tabbatar mata da lahanin da ta masa.

   Tsayawa yayi ya na k'ok'arin saka takalmi sanye cikin kaki,ga kyau ga kwarjini. Gaba d'aya Habeebti ta tsure,sai kallan sa ta ke ko za ta ga wani alamar na jin wayar ko rashin jin sa. Amma sam ta kasa gane komai dan kuwa fuskar sa a sake ta ke. Sai da ya gama sannan ya mata sallama ya fita abun sa. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai sake kiran Aysha,jin abun da ya faru Aysha har da taya ta murna ta na mai mata dariyar mugunta,ita dai Habeebti Allah ta godewa da ya sa Haroun be ji ba,nan kuwa ba ta san ai ta bari biri ya ganta ba.

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI.....✍🏽
7⃣6⃣

   Daren ranar Haroun be dawo gida ba sai wajan shabiyun dare. Wankan sa ya je ya tsala ya shirya tsaf da shirin Maman Junior cikin ran sa,wato dan saurara mata da yayi ya sa ta tunanin nak'asa ce ke damun sa,nak'asar ma wai ita ta masa....be san sanda ya jefa kan sa baya ba ya saki dariya mai karfi har da k'yakyacewa sannan ya ce "you asked for it yarinya!" Ya duba agogan sa,Karfe d'aya. Har da wakar sa ya nufi d'akin Habeebti da ta jima da yin baccin ta,haka kuma ta manta ba ta rufe kofa ba.
    Kamar cikin bacci ta ji ana tab'a ta,jin abun yayi yawa ta farka a gigice,idanun ta tsurutsuru su ka sauka kan fuskar Haroun da hasken fitilar toilet din ta da ya ke bude ya haske fuskar shi, sakon murmushi yake aika mata. Ganin haka da wannan tsohon dare ya sa ta yi firgit za ta kunna wutar d'aki,yayi saurin rik'o hannun ta ya na girgiza mata kai ya ce " ki rufawa kan ki asiri mu zauna haka cikin duhu my Habeebti.." cikin inina ta ce " Maaaala-aam me me ka zo min d'aki haka da tsohon daren nan?"

  Sai da ya saki mik'a mai cike da lalaci sannan ya ce " D'azu da na fita ne Oga na ya gane my wild wife ta nak'asa ni,hakan ya sa ina cutar da ita ta hanyar rashin ba hakkin ta,shi ne ya bani magani ya ce in zo in gwada....." Sai da kwakwalwar ta ta yi booting sannan ta gane in da gizon ke sak'a. Ta wuf za ta tashi ta gudu,ya na daga kwance ya cafko ta,sai ga ta fad'o kan sa ta na mai magiya. " Ka ma Allah ka yi hakuri,dan Allah Haroun Allah ya baka hakuri....." muryar ta har rawa ya ke.
   Ganin haka ya sa na fara ja da baya dan kamar dai ba hurumin Sidiya ba ne. Mai Haroun ne wanda ke kok'arin tsaida Habeebti da ta dage kokawa ta ke da shi,ya ce " shhhhh...hakurin me kuma?babu zance Hakuri fa My Habeebti,ai hakurin ki ya yi yawa har ya k'are tun da ki na iya ba da labari a waya,dole na gwada mi ki bugu d'aya yayi kad'an ya nak'asa man kamar ni,i knw you want it,as much as i do...." Cikin kuka har haki ta ke saboda kokawar da ta ke yi,gashi Mai Junior ko a jikin sa dan da hannu d'aya ya ruke hannun ta,Habeebti ta ce " Dallah malam ka sake ni!" Maimakon ya sake ta sai ma fara aika mata yayi da sakonni da d'ayan hannun. ta yi kokuwan har karfin ta ya kusa k'arewa,rik'on da Mai junior ya mata ko kwakkwaran motsi yanzu ba za ta iya ba,ta na kuka ta ce" Dama ka saba ai,ba wannan ba ne na farko,go ahead nd rape me again." cikin rad'a ya ce " no i will love you 2nyt Aliya nd make love to you,ba maganar rape..."

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI.....✍🏽
7⃣7⃣
    Jin  haka ya sa na had'a kai na na yi parlour saboda wancan karan ban taimakawa Habeebti ba gwara na lab'e kurkusa kar a kuma. Amma shiru ake ji ko tarin Habeebti ban sake jiwo ba,ni ma na had'a kaya na na yi gama dama gulcy ce ta tsaida ni.
  Washagari da asubar fari Mai Haroun tsaye kan Habeebti da ke kwance ta juya masa baya. Sanye yake cikin kaki,yau har da hula da yar sanda,ga kamashi ya yi kyau kwaran gaske. Haka kuma zuciyar sa ta yi fari fat dan kuwa daran jiya sun raya sunnar ma'aiki duk da dai ko nafila ba su yi bare addua saboda gardamar Habeebti,ya kudiri niyar yin haka da yarda Allah idan Allah ya dawo da shi da rai da lafiya,kuma ya tabbatarwa Habeebti ya fi wani mai lafiyar ma lafiya,daga daren jiya ya san ya wuce raini.

     Jin ya tab'a kafad'ar ta,ta yi saurin kaucewa,ya na dariya ya ce " Maman Junior rigima,ki jiyo mu yi sallama zan tafi" Habeebti da ta bada kai bori ya hau,kuma bayan komai ya lafa sai kuma dana sani,bacin rai da kuma tsanar kan ta da kuma k'ara tsanar Haroun ya addabi zuciyar ta. Dan ko da zai koma d'akin sa ma da masifar Habeebti su ka rabu. Hawayen takaici ne ki zuba daga idanun ta. Jin ya sake cewa " My Habeebti zan tafi,ki yiwa mijin ki addua Allah ya dawo da shi lafiya.." cikin fushi bud'ar bakin ta sai cewa ta yi " Kar ma ka dawo lafiya ma na,ina ruwa na! Idan ka je kar ma ka dawo!" Ya na mai murmushi ya zauna bakin gado,sannan ya ce " haka ki ke so Aliya?" Ta ma sa banza. Jin ba za ta amsa ba ya sunkuya ya yi kissing bayan ta har sai da ta tsaida numfashin ta na wani d'an lokaci,sannan ya tashi ba tare da ya sake tankawa ba ya tafi. Sai bayan fitar sa ta ke jin ba ta kyauta ba,after all ai ita ma daga baya ta bada gudunmawar ta a jiyan da daddare,bare kuma ai mijin ta ne,addua da fata na fari ai wani abu ne. Da wannan tunanin ta yi wanka ta yi sallah. Sai a sannan take godewa Allah da Junior ba ya nan,dan kuwa sai da ta rama bacci,duk Aysha Tafeeda ce ta jawo mata.
     Mota uku su Mai Junior su ka yi,ciki har da tashi,da kuma k'atuwar motar barracks. Tashin an je da ita ne saboda ya gwada tafiya mai nisa da ita,amma sam ya kasa driving saboda tunanin Habeebti,hakan ya sa Emaka jan su daga zuwa har dawowa.

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI.....✍🏽
7⃣8⃣

   Wajan  tara na dare,Habeebti zaune ta kunna rediyo ga tv ma yanayin,duk jira take ko za ta ji ance an ga watan ramadan. Amma fa sam hankalin ta ba jikin ta ya ke ba,bini bini sai ta juya ta duba agogo,haka har tara da rabi,amma shiru Mai Junior be dawo ba. Wayar ta ce ta yi k'ara,har da gudun ta taje d'auka. Ganin number Yakumbo ce ya sa Habeebti buga k'afa,gashi ita ba ta da numbar Haroun ba bare ta kira shi,duk da ya sha kiran ta ba ta tab'a saving ba.
   Sai da wayar ta katse sannan ta tuna Yakumbo ta tab'a neman ta ta wayar shi,ta na da numbar kenan. Hannun ta na rawa ta bi kiran Yakumbo. Bugu uku ta d'aga ta na "Barkan mu an ga wata yanzu sarkin musulmai ke fad'a a gidan televijin...." Sai a sannan Habeebti ta d'aga ido ta gani gashi kuwa ya na jawabi. Cewa ta yi " Toh Allah ya sa a fara da mu a gama da mu,ya karb'i ibadun mu"  Yakumbo ta amsa da "Amen" Habeebti za ta budi baki ta yi magana ta ji ana buga mata k'ofa,har ta far murna Mai Junior ne,sai ta tuna ai idan shi be ya na da mukulli ba zai buga mata kofa ba. Jin bugun yayi yawa ta ce da Yakumbo da ke ta faman mata "hello" ina zuwa.
    Ko kashe wayar ba ta yi ba ta aje gefe ta je ta bud'e. Mama Eze ce da wasu matan sojoji guda biyu,d'aya daga cikin su ce musulma sai salati ta ke,Mama Eze da d'ayar kuwa Jesus su ke kira. Ganin su Habeebti ta yi mutuwar tsaye,musammam jin furucin Mama Eze,fad'i take "Hayye Heyyee Jesus abeg!" Cikin rawar murya ta ce " Mama Eze menene?me ya faru?ina Papa Eze? Ina miji na?" Musulmar ce ta amsa mata da " motocin Army guda biyu sun yi hatsari a hanyar su ta dawowa,yanzu aka kawo wanda su ka yi rauni emergency,wanda su ka mutu kuma........." Ina d'if Habeebti ta dai na jin komai inda ta yi zaman dirshen a k'asa,maganar da Haroun ya mata da zai tafi da amsar da ta furta masa ke mata ihu cikin kwakwalwar ta,  
"My Habeebti zan tafi,ki yiwa mijin ki addua Allah ya dawo da shi lafiya.."
"Kar ma ka dawo lafiya ma na,ina ruwa na! Idan ka je kar ma ka dawo!"

"haka ki ke so Aliya.....?"

 

  Hannu biyu ta d'aura kan ta tana furta" Na shiga uku ni Aliya,na shiga uku!!!!" (Mu kasance masu fata na gari da addua na gari ga mazajen mu duk tsanani bacin rai.....)

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

7⃣9⃣

     Ta na kuka wiwi ta ke fad'in " Na yi wa kai na,na jawowa kai na,Allah na tuba Allah ka yafe ni.." duk cikin su matar nan ce mai iya ba su hakuri,kasancewar ita na ta mijin dayar motar ya ke wacce hatsarin be rutsa da ita ba,dan kuwa bakin mijin na ta ta ji mummunar labarin shi ne ta zo ta fad'awa su Mama Eze.
   Ganin ana buga k'ofar gashi Habeebti ta yi zaman dirshen a k'asa ta na kuka, ba ta da niyar motsawa bare ta kai ga bud'e kofa, matar ta je ta bud'e. Sojoji ne guda biyu,Bahaushe da Inyamuri sanye da kaki,tsaye bakin kofa. Gaishe ta su ka yi cike da girmamawa,kafin Inyamuri ya ce da ita " Mrs Haroun?" Jin haka ta girgiza ma sa kai yayinda ta ja gefe Habeebti wacce ke jin jikin ta kamar leda ta tashi a hankali,ta k'araso bakin kofar..in da su ka k'ara gaishe ta,sannan Bahaushe ya ce "With all respect Mrs Haroun,za mu tafi da ke hospital in da mijin ki ya ke" baki na rawa ta ce "Hospital?Wanne bangaren exactly?ba dai mortuary ba officer?" Kai kawai ya girgiza mata alamar ah ah. Jin haka ta sami dan nutsuwa,ta ce "pls take me to my husband"  matar ce ta dan mata rad'a na "mayafin ki Madam" sannan ta tuna ta ce da su ta na zuwa ta shige ciki da gudun ta.

   Mama Eze ce ta tambayi Sojojin " Oga my husband nko?" "And who is your husband?" Iyamuri ya amsa mata da wani tambayar. Da sauri Mama Eze ta ce " Ehhhh Emeka"ta dan bugi mama Israel sannan ta ita ma ta ce" and my husband too,Johnson"

    "then you should all come with us" ya ba su amsa a takaice. Yayin da Habeebti ta fito cikin hijabin ta. Gidan ta kulle hannun ta ruke da wayar ta amma ta kasa kiran kowa. Haka su ka shiga motar sojojin su uku a baya,dayar matar ta koma gidan ta tana mai musu fatan alkhairi.

💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣0⃣

     Ba su dad'e ba su ka kai asibiti da ke nan cikin barracks ya ke. Bahaushe ne ya ce da Habeebti da Mama Eze su biyo shi,ita kuma Mama Israel Iyamuri ne ya tafi da ita. Emergency ya kai su,nan Habeebti ta ga tashin hankali iri iri dan ba k'aramin rauni aka ji ba. D'aki d'aya aka shiga da su,in da suna shiga gadon da Emeka ke kwance shi ne fari.
   Mama Eze ce ta kurma ihu inda ta zube k'asa ta na birgima ganin Emeka babu k'afa d'aya,ga shi fuskar sa gaba d'aya ta sauya kamanni.....ita kan ta Habeebti ta tsorata,tabbas idan ba ka mutu ba ba a gama ma ka halittaba. Yayinda Doctors da nurses da ke sanye cikin kaki idan aka dauke farar rigar da su daura,su ke k'okarin ceto ran Emeka Habeebti bazama ta yi cikin d'akin neman Mai Junior. Can kuriya ta gan shi,a hankali kamar wacce ke koyan tafiya ta ke takawa har ta kai ga gadon.
  Jikin sa ba riga sai farar singlet wacce ta b'aci da jini,haka ma wandon sa da ya yayyage daga gwiwa.Kan sa wanda ya kumbura zagaye da bandeji,haka hannun sa na dama,wanda ya sha dauri da bandaje. Idanun sa rufe kamar mai bacci. Hannun sa ta ruke wanda ba ciwo ta na kuka,ta kasa komai sai kuka ta ke. Wata Nurse ce ta zo wajan ganin Habeebti. Kafad'ar Habeebti ta tab'a sannan ta ce "Is he your husband?" Habeebti ta gyad'a kai cikin kuka. Nurse ta ce "Kar ki damu,zai warke by God grace" Cikin kuka ta ce mata " pls tell me,ya jikin na sa?" Nurse ta amsa mata "Toh na shi da sauki za mu ce in dai ba internal injury wanda har yanzu ba mu tabbatar ba so far,sai mun masa x-ray dan da aka kawo shi kan a duba shi, his major complain kirjin sa ne,amma dai ya ji ciwo a kai,kin ga anyi dressing wajan,sai kuma tsagewar k'ashi a wannan hannun na shi"

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣1⃣

   " Innalillahi wainnailaiihirajiun!" Fad'in Habeebti ta na mai sharb'ar hawaye,gani ta ke ita ta jawo wannan masifar ta afkawa Haroun,da ta ma sa adduar arziki da ba haka ba. "Yanzu me ya sa idanun sa a rufe?me ya sa ba ya motsi?" Ta tambaya ta na mai dad'a ruk'e hannun Haroun cikin na ta. Nurse ta ba ta amsa da "an masa allura ne ta bacci dan sami saukin ciwon da ya ke ji" ta bata amsa ne ta na k'ok'arin tafiya kasancewar kiran da wani Doctor ya kwala mata. Habeebti ta kifa kanta kan gado ta na kuka mai shiga rai.

    Wani k'ara da Mama Eze ta sa ya sa Habeebti tashi da gudu ta je wajan. Me za ta gani? Farin kyalle aka ja ana rufe Emeka,rai yayi halin sa..ga Mama Eze nan kwance sumammiya. Da sauri ta juya zuwa ga gadon Haroun,ta shiga jijjiga shi ta na fad'in " Dan Allah ka tashi mu tafi Haroun kafin su zo su rufe min kai!" Wata Nurse ce ta zo da sauri ta janye Habeebti ta na magana cikin fad'a" Haba Madam! You can't do dis hia! Hankalin ki d'aya kuwa!" Cikin kuka Habeebti ta ce "ina kallo su ka rufe Emeka kar shi ma su zo su rufe shi!"

    Sai a sannan ta fahimce ta. Ta fara magana cikin lallami" kar ki damu babu mai rufe shi,idan kuma ki ka cigaba da jijjigasa yanda ki ka yi yanzu shi zai sa a rufe shi,ki zauna abun ki tare da shi,ba mai tab'a shi bare a rufe shi" kamar wata k'aramar yarinyar Habeebti ta nutsu,Nurse ta ja mata kujera gaban gadon Haroun ta zaunar da ita,ta ce " yi zaman ki nan"

     Hannun Haroun ta ruk'e ta na mai baza ido,gani take da ta sake yanda aka yiwa Emeka shi ma haka za a zo a masa. Ta na ji tana gani aka tura gawar Emeka aka fitar. Mama Eze da ta farfad'o sai ihu ta ke,ta na bori har da sab'o,duk abun da ya zo bakin ta fad'a ta ke.
   Habeebti dai yanda ta ga dare haka ta ga rana,mutane kusan uku bayan Emeka ne su ka cika a kan idan ta. Lokacin sahur yayi wannan Nurse din ta kawo mata ruwan tea da bread. Tea din kawai ta karb'a ta ce tabar bread din ta gode. Tea din ma kad'an ta iya sha dandai ta san falalar yin sahur d'in ne. Jin hannun Haroun na motsi ta aje cup din ta matsa kusa da shi da sauri ta na mai k'ura masa ido. A hankali murfin idanun sa ke motsi,kafin daga bisani ya bud'e idanun sa a hankali,yayinda kwayar idanun sa su ka sauka cikiin na Habeebti.

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣2⃣

    Ganin  haka da sauri Aliya ta juya da niyar kiran Doctor,amma Mai Junior ya ruk'o hannun ta,idanun sa kan ta. Juyowa ta yi ta na mai sakar masa murmushin da ba ta tab'a masa irin sa ba iyaka sanin ta da shi. Nan tsaye kan sa ta shiga kwallawa Nurses kira,d'aya daga cikin su ta zo da saurin ta. Duk da ta ga idanun Haroun bud'e be hana Habeebti nuna mata shi ba,ta na fad'in "ya tashi, Mai Junior ya bud'e ido" dariya ta bawa Nurse din,sai da ta fara kashe abun ruwan hannun sa kasancewar ruwan da ke d'iga ya k'are sannan ta kira Doctor.

   Sai da Doctor ya zo sannan Habeebti ta zame hannun ta daga cikin na Haroun,ta ja gefe dan ta bari ya duba sa. Sai a sannan ma ta tuna da wayar ta,ta shiga nema amma sama ko k'asa ta rasa. Da kyar ta samu k'ark'ashin kujera bayan ta ari waya ta kira. Wayar Hajiya ta kira,dan ta san tabbasa yanzu lokacin sahur ne idanun ta biyu. Ta ci sa'a kuwa ta same ta,bayan sun gaisa Hajiya ta ce " Habeebti mura ki ke ne muryar ki ta dashe haka kamar mai kuka?" Habeebti ta amsa mata da " Hajiya Haroun ne su ka yi accident...." Bud'ar bakin Hajiya sai cewa ta yi " Allah ya kiyaye,ke dan Haroun yayi accident shi ne abun kuka?" Ga mamakin Hajiya sai ji ta yi Habeebti ta ce " Hajiya miji na ne fa"

    D'if Hajiya ta d'auke wuta,jin shiru Habeebti ta ce "Hello Hajiya ki na ji na?" Hajiya da Habeebti ta gama gogewa hadda ta ce "Ina jin ki Aliya,ya jikin mijin na ki toh?" Zuciyar Habeebti d'aya ta gama zayyanawa Hajiya halin da Mai Junior ke ciki,ta k'are da "Dan Allah kya fad'awa su Mama da Yakumbu" Hajiya dai ta amsa mata da "Toh Allah ya sauwake,ki duba min shi" sannan ta aje wayar ta na mamakin amsar da Habeebti ta bata,oh yaran zamani sai fa Allah.
     Wajan shad'aya aka yiwa Haroun X-ray,aka kuma sauya masa d'aki zuwa amenity 3,wanda hakan yayi daidai da isowar mutan kano gayyawa guda ba wanda aka bari a gida,hatta Alhaji Shamsu ma be yi k'asa a gwiwa ba sai da yayi tattaki ya zo duba Mai Junior. Dan tun da Habeebti ta fad'awa Hajiya ta ke ta fama da amsa waya.

💫💫💫💫💫

💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣3⃣

   Da  taimakon su Dawud Mai Junior da har yanzu be daina complaining aka ciwan kai da k'irji ba,yayi wanka yayi brush,su ka taimaka ya sanya kayan da Habeebti ta d'auko masa sanda ta koma gida. Farar riga mara hannu da three-quarter jeans. Abun alfahari shi ne yanda d'akin ya cika fal da yan uwa da ke d'akin mai girma ne ba laifi. Shi kan shi Mai Junior duk zafin ciwo da ya ke ji be kasa nuna farin ciki a fuskar sa ba ta hanyar fad'ad'a fara'ar sa,musammam ga mahaifin sa wanda ya fidda rai daga ganin dariyar sa,amma yau gashi zaune kusa da shi har da dafa kafad'ar sa,dan jin yanda ya ke jin jikin sa.

    Hajiya kuwa gefe ta ja tun sanda ta ma Mai Junior sannu. Mama ce da kwalla ya cika idanun ta ganin halin da Mai Junior ke ciki,bini bini sai ta dubi Habeebti ta ce " Sannun Aliya,sannun mu fa..." Ita dai Habeebti na ta murmushi kawai cike da kunya,musammam ganin yawan jama'a be hana Haroun kasa d'auke ido a kan ta ba,bini bini sai su had'a ido,ta yi saurin d'auke kai. Har ta kai Aysher ta gano ta yiwa Huda alama,wacce  sai hura hanci ta ke tun ganin Habeebti,hakan kuma ba k'ara min sosa mata rai yayi ba. Bare shi mijin ta da Allah ya jarrabe shi da san matar k'anin sa,wato Dawud,tun yana b'oyewa yanzu k'arara ya fito ya na mai tsare Habeebti da ido. Ta yanda Allah ya sa ma ba ta sani ba,shi ne kallan da Mai Junior ya ke mata.

   Lokaci lokaci sojoji ke shigowa suna duba Haroun,da masu sara masa da wanda shi ya ke sara musu,amma ba wanda ya masa zancen mutuwar Emeka. Duk wanda kuma ya shigo sai ya jinjina kamannin mutum ukun nan,wato Alhaji Shamsu,Dawud da Haroun,musammam Alhaji Shamsu da Haroun dan sun fi Dawud fari da manyan idanu.

   Wajan k'arfe uku su ka yi haramar juyawa Kano saboda azumin da ke bakin su. In da aka ce Ayub da Aysha za su d'an zaunawa Habeebti,musammam ma Ayub saboda jinyar namiji sai namiji. Habeebti ta so kai su gidan ta,amma su ka ce wani karan sa je. Mama ce ta ce ya kamata Habeebti ta je gida ta d'an huta dan kuwa idanun ta sun nuna alamar rashin bacci. Har mota ta rako su,sannan su ka juya ita da Aysha.

    Ganin sun dawo Haroun ya mata alama da hannu na ta zo gare shi. Bayan ta k'arasa ya ce ta d'an sunkuyo ta ji,zuciyar ta d'aya ta sunkuya sai ji ta yi cikin rad'a ya ce "hav you bn crying? my Habeebti?" Harara ta sakar masa in da ta d'ago ta ce " No i hv bn celebrating your accident Mai Junior!" Dariya ya sa sosai wanda hakan ya sa kan shi sarawa,sai gashi shi da Habeebti suna riga rigan dafe kan nasa,hannun Habeebti k'ark'ashin na Mai Junior. Ganin haka Aysha da Ayub su ka kalli juna su mai magana da idanun su,dariya ta kusa sub'ucewa Aysha...sai sannan Habeebti ta lura da inda hannun na ta ya ke,ta yi saurin cirewa tana mai kawar da kan ta da ga barin kallan Mai Junior dan wani murmushi ya ke mata mai cike da lalaci.

💫💫💫💫💫

. 💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣4⃣

   Aysha ta kalla tare da fad'in "Aysha zo mu je gida mu huta sannan mu had'a na iftar kin ji?" Cike da shagwab'a ya ce "Ayya mana tafiya za ki yi ki bar mijin ki cikin ciwo haka?" Idanun ta ta yi rolling kafin ta ce "shi ya sa aka aje Ayub,ba ka ji me Alhaji ya ce ba?jinyar namiji sai namiji..."

   Kallan Ayub yayi fuska tsuke sannan ya ce " Kai tashi ka bi su Kano tun kan su yi nisa!" Gaba d'aya dariya su ka sa,ban da Habeebti da ita harara ma ta watsa masa. Ya rangwabar da kai tare da fad'in " Ayya mana Habeebti,ban da lafiya fa!" Matsowa ta yi kusa da shi cikin rad'a yanda su Aysha ba za su ji ba ta ce " like i care!" Amsar ta ta ce ta k'ara sa shi darawa yayinda ya mata nuni ga wajan su Ayub da su ka yi tunanin soyayya su ke,su ka d'auke kan su cikin wayencewa,sannan ya k'ara da "I love you more my angel" ji ta yi kamar ta nutse dan kunya,tuni ta had'e d'an abun da ba za a rasa ba,ta ce da Aysha tashi mu tafi. Har ta fita idanun Haroun na kan ta.

    Da k'afa su ka tafi gida da ke Allah ya taimake so ba rana a gari sai ma hadari. Tun da ta baro asibiti ta ke tunanin Mai Junior,dan haka suna gama girki ko baccin ma ba ta samu ta yi ba ta ce da Aysha su koma asibi,sa sha ruwa a can.

    Komawar su suka tadda Haroun ya sami bacci. Sai kawai su ka zauna suna dan tab'a hira,inda Ayub ke can gefe ya na karatun alquran. Bini bini Habeebti ke tashi ta duba Haroun ko ta gyara masa hannun sa mai ciwo kar ya kwanta a kai. Ita kan ta Aysha yanda Habeebti ta ke ma sa burgeta ya ke. Ashe dama Habeebti za ta so Haroun? Gaskiya ne babu kyau tsananta  k'iyayya,haka kuma ba kyau tsananta soyayya. Saboda shi soyayayya na iya zama kiyayya,haka kuma k'iyayya na iya timid'ewa ya zama soyayya.
    Nan su ka sha ruwa,kafin lokacin asham Haroun da be jima da tashi ba ya ce Habeebti ta koma gida ta huta. Sai da ta tabbatar ya d'an ci abunci,Doctor on call ya duba shi,sannan ta yarda ta koma gida. Ai kuwa ko asham ba ta iya yi ba,tun da ta sa hak'ark'arin ta a k'asa sai bacci.

💫💫💫💫💫

: 💫INA DARAJAR TA KE ?💫

KHADIJA SIDI......✍🏽

8⃣5⃣

    Washagari aka bada result din x-ray. Allah ya taimaka babu abun da ya sami k'irjin,tsabar ya bugu ne. A ranar Mai Junior ya sami labarin mutuwar Emeka. Ya ji mutuwar har ran sa kwaran gaske,dan kuwa Emeka mutumin shi ne,gashi ya bar Mama Eze da yara k'anana har uku.

     Ita kan ta Habeebti ta san halin da ya shiga na bakin ciki,dan haka ko takalar sa ba ta yi ba. Da ya hau fad'a kuma ta ce "Allah ya ba ka hakuri" dan abu kalilan Aysha ko Ayub su ka yi ba daidai ba sai ya hau su da fad'a.

    Kusan kwana uku yayi a wannan yanayin. Amma jiki kam Alhamdulillah ya na samin sauki. Ya na kwance gadon asibiti aka yiwa sojojin da su ka riga mu gidan gaskiya parade. Ranar da za a kai azumi goma ranar aka sallami Mai Junior,Aysha da Ayub su ka koma Kano.

     Bayan an idar da sallar asham,yayyafi ake kad'an kad'an kasancewar gari na damuna hadari ya had'u sosai. Sanye ta ke cikin riga da zani d'inkin atamfa,abun ku da mace mai hips sai zanin ya mata kyau ya zauna mata cas-cas. Wanke-wanke ta ke a kitchen amma gaba d'aya hankalin ta kan Mai Junior ya ke. Ta kasa gane me ya ke nufi na zuwa ya tare ma ta a d'aki tun da su ka dawo. Da wannan tunanin ta gama wanke wanke ta gyara kitchen sannan ta nufi d'akin ta ta.

    Kan stool ta gan shi zaune da gajeran wandan sa iya gwiwa,ya na ta fama da sa botil din rigar da ya sanya amma ya kasa saboda hannun shi da ya sami tsagewar k'ashi. Ganin shigowar Habeebti ya ce "Oya zo ki yi aikin jor!" Cike da tsiwa ta ce "ta ina ya zama aiki na?" Mai Junior ya ce "Kin san dai hannu na d'aya da rabi ne,ko a hospital ma Ayub ke saka min"
    Hannu bisa k'ugu Habeebti ta ce "Nan ba hospital ba ne,ni kuma ba Ayub ba ce!" Yana wannan murmushin na shi mai cike da lalaci ya ce"Wit dat beauty,shape nd curves am very sure ke ba Ayub ba ce My Habeebti...." Sauri ta yi ta sauke hannun ta k'asa ta ma rasa me za ta ce masa,kafin daga bisani ta ce "Malam ka fita ka bar min d'aki da Allah" bud'ar bakin Mai Junior sai cewa yayi "Ni da gida na,in da naga dama nan zan zauna,amma in kin fi son gani na ne ba riga i wil nt mind.." ya fara k'okarin cire rigar,Habeebti ta k'arasa gaban sa da saurin ta,ta na fad'in "ah ah bari na saka ma dan Allah!" Hannun shi  mara ciwo ya d'aga ya sauke,yayinda ya ke mai duban Habeebti da ta kasa d'aga ido ta kalli fuskar shi,hannu na rawa ta fara sanya ma sa botil d'in.
    Ko da ta kai na k'arshe sai ya tashi gami da jawo ta jikin shi,ta fara k'ok'arin kwacewa ya ce "kula fa yan mata kar ki fama min ciwo!"sai kawai ta tsaya tare da b'oye kan ta a kirjin sa cike da kunya. Kana ya ce "kin san wani abu game da ke da na ke so?" Ta yi shiru. Be gushe ba ya ce " Kunya,ina san mace mai kunya,musammam na mijin ta,domin shi kunya ado ne,kuma ya na k'ara soyayya..." shiru su ka yi na wani dan lokaci,yayin da Habeebti ke jiyo k'arar bugun zuciyar shi.

    A hankali ta dan d'ago kai ta kalle shi,murmushi ya sakar mata jin ta furta sunan sa "Haroun?" Cikin jin dad'i ya amsa da "umm?" Ta ce " Dan Allah ka yi hakuri akan furucin da na furta maka randa ku ka yi accident,wlh ba da niya na fad'a ba,i don't mean it,am glad you ar alive...." Tsuke fuska yayi ya ce " ba wannan maganar,dama haka ki ke so,ko dai na yi jinya ko na mutu,hanyar d'aukar fansa akai na,Allah ne ya karb'i adduar ki...." Jin haka Habeebti ta dabarbarce har da rantse rantse ta na " Wallahi wallahi har ga Allah ba haka bane,ayya mana Mai Junior...." Ganin ta na shirin hawaye ya sa Haroun jefa kan sa baya,ya kwashe da dariya kafin ya saki Habeebti ya koma bakin gado ya zauna. Ya kalli Habeebti dake tsaye ta k'urawa carpet ido ta na wasa da k'afar ta kamar yarinya.."Aliya..." Ya kira sunan ta. Ta d'ago sleepy eyes d'in ta da suka cika da kwalla a hankali ta kalle shi. Ya ce " Wow you soo beautiful my wife,yaki nan" ya nuna kan cinyar sa. Habeebti ta d'aga Kafad'a ta sauke,irin na k'i dinnan na yara.

💫💫💫💫💫

No comments:

Post a Comment