Thursday, 1 December 2016

KARNINMU 2..


KARNINMU ....

©Fikra Writers Association

BABI NA BIYU

CIKIN KASUWA...

"Hajiya Lanto! Hajajju! "

Ya faɗa yana washe bakinsa  makare da goro bisa akasi ruwan goron ya watso kan fuskarta. Cike da masifa ta ja baya tana mazurai tamkar damisa.

"Kan uban can Lado ni ka watsawa miyau? Wannan bakin naka mai kama da shada dan hamami, al kur'anin Allah ba zan yadda ba".

"Wato Lanto baki da mutunci ko?"
  Ya faɗi cike da mamaki.

"Ban dashi! ban gadaba!"
Ta faɗi tana mai murguɗa masa ɗan mutsilin bakinta.

Nan da nan waje ya hautsine Lanto bata yi aune ba ta nemi bokitin wararta ta rasa, ai kuwa nan da nan ta ɗora hannu a ka tana kwarma ihun taimako. Babu wanda ya bi takanta dama samarin duk haushinta suke bata bari a rage zafi da ita. Haka taja kafa ta wuce gida tana tararrabin yadda zata fuskanci mahaifiyarta.

Mama Hanne tun fitar Lanto take tunanin yadda ta zuba mata wara ta jaka uku tana kiyasta ɗiyar ta kawo mata jaka goma sai ga Lanto ta faɗo gidan babu ko sisi balle tarai. Don kuwa kukan da Lanto ke yi ya sa ta fahimtar haka.

Cikin hargagi tayo kanta tana kunfar baki tamkar zakin dake jin yunwa ya hango budurwar barewa ɗauke da karamin ciki,

"Lanto me zan gani?"

Cikin rawar baki kamar an kaɗa mata gangi ta furta

"warar ta ɓare...."

Kafin ta dire ta ɗauketa da giggitacan marin da yasa numfashinta yin tafiyar burgu ya dawo. Wasu taurari suka dinga kewaya idanuwanta ta yi suman wucin gadi ta dawo.

"Kije ki nemomin kuɗina duk in da suke dan ubanda ya haifeki"

Kuuu! Cikinta ya bada wani sauti mai karfi, da da dama sai ta zaga banɗaki ta huta da masifar mahaifiyarta. Kafaffunta na rawa ta juya calau-calau zuciyarta na tukuki fal takaici.

Cikin tashin hankali ta soma tafiya, ga duhu ya soma yi cikin ranta tana ji ina ma zata haɗu da mahaifinta da takaicinta ya kare. A haka ta gota hayin majaja wajan shake da tsoffin banza sunata karta masu zukar sigari na zukar kayarsu. Gabanta ya faɗi ganin tana gab da shiga hayin sawayawa. Hayin da duk cikin hayin da ke daga waje-wajen babban birnin Dunotsi  ba wanda yayi suna wajan taruwar marasa mafaɗi da dama tare da kangararru kamar sa gashi dole saita haye sannan zata je gidansu kawarta Laraba ta lallaɓa ta ara mata kuɗi ta kawowa Mama Hanne in ya so daga baya Babanta ya biya kuɗin.

Cikin ikon Allah ta tsallake hayin lafiya ta nufi gidansu Laraba, abin takaici bata sameta a gida ba haka ta jawo kafaffunta tamkar mai zazzaɓi ta nufo hanya gabanta na dukan tara-tara. Gab da zata tsallake hayin sawayawa taji tayi karo da wani abu kamar itace ta hantsila zata faɗi taji an riketa gam ta ɗago a rikice cikin tsananin tashin hankali. Warin sigari ya mammaye mata fuska, hayakin ya nemi ɗauke mata numfashi ta ja shi da karfi ta ware ido su huɗu ne sun zagayeta fuskokinsu a rurrufe babu abin da zata duba ta shaidasu bata gama sauke idanunta taji an yi sama da ita...........

****

Zaune suke a rumfar gidan Alhaji Nasiru mai hatsi, magidanta ne wainda babu wanda ke kasa da shekara arba'in. Duk wanda ya saba shiga hayin majaja dake can wajen birnin Dunotsi sun san da zaman wannan majalisa.  Basu da abin hira sai tsine ma yaran mutane da zagin gwamnati tunda mafi yawansu sun saba da gwamanatin da ta sauka wajen amsar kuɗaɗe da Sauran kayan hasafi,  amma kuma wannan gwamnatin shiru saboda yaki da cin hanci da take.
    Mota ce kirar marsandi AMG GLC 45 SUV kirar shekarar da ake ciki ne ta dubu biyu da goma sha shida wanda akan same ta aƙalla dollar 54,900. Gaba ɗaya kallonsu ya koma kan motar don ko ba'a faɗa ba sun san wacce ire-iren motocin nan kan kawo wa ziyara.
    Buɗe motar da wani ɗan sanda yayi haɗe da sara ma wanda ke shirin saukowa yasa yan majalisa tsinkewa da wannan.  Duk a tunanin su basu ta ɓa tunanin shaharar ta ya kai nan ba.  Ta fito daga motar a hankali kamar ba ta so duk wannan ɗan sandan na take mata baya. Sanye take cikin shiga ta alfarma, jallabiya take Sanye da shi kamar kullum, sai de wannan karan ɗan kwalin atamfa ce a kanta ta wacce tayi daidai da wacce aka sa a hannun jallabiyar da wani sashi na wuyan rigar, ta kashe ɗauri  fuskanta ya sha durowin da fente-fente,  tayi kyau ainun hakan ya sa ta tafi da hankalin dattawan  da ke zaune a majalisar.

Da ta daidaici wajen yan majalisa sai ta tsaya ta tsuguna har kasa ta fuskanci Malam Yaro ta ce
    "Barkanku da hutawa kawu, ina yininku"
   Shiru duk ya ratsa wajen sai malam sadi ne yayi kokarin amsawa
   "Lubabatu rayuwar da kika zaɓa ma kanki bata dace da ke ba, ki dubi maraicin ki da yan kanninki mata ki samu miji kiyi aure,  Don Allah ba don mu ba"  tana kallon sa yana share kwalla cikin dabara.  Kara ɗago ido tayi ta kalli kawu yaro kanin  kishiyar babarta da ya fara magana a fusace.
    "Ai duk unguwar nan babu yar iska, kai in an ce min babu karuwa da ta kai ta duk cikin Kasar nan ta Haurobiya  bazan Musa ba,  wallahi canjin  nan da ake kira ya kamata a fara da datse karuwanci,  mtswww!"  Ya ja tsaki.
Ga mamakinsu sai suka ga ta saki murmushi ta ce
   "Kawu za'a fara amma sai an fara da tsofaffi da suke lalata yara kanana ta hanyar basu alawa ko kuma naira biyar. Allah Nagode maka da wani bunsuru ne ya zama sanadin shahara ta"

Ta waiga ga  ɗan sandan nan tace
   "ka je ka ce ma kwamishina ina so a ɗaga rumfar nan kan gobe ko za'a huta da munafunci.
   Baba zamanka nan bai kamata ba zan zo gida Anjima in fasa maka wani gurɓatacciyar kwai,  Allah sa warin sa kar ya hana ka sukuni amma na tabbatar zai hana ka zama nan"  ta karasa tana kallon malam sadi,  nan cikin wasu ya murɗa suka yi tsit kamar ruwa ya ci su.
                ***

Babban falo ne na alfarma mai ɗauke da arziki da kayan arziki na kwaran gaske. Kwance ya ke kan luntsumammiyar doguwar kujera,wato sanyin Ac da ke busashi sam bai hana zufa tsattsafuwa daga jikin sa ba. Tun bayan aje wayar da yayi da mai girma Minista kan sa ke ciwo,bayan ya masa miscals ba adadi sannan ya samu ya kira sa. Ya na mai mutuk'ar mamaki da taikacin mai zai rud'i Minista  na birni kamar Dunotsi aikata wannan aika aika haka,  sannan don rashin dabara ya kwashi yan jarida da Sauran tawaga, sannan kamar wanda akai ma sammu ko aka ce je ka ka gani ya wani goya mace a haraban Otal,  kai! kamar ba gogaggen d'an siyasa ba..

"Mtsww! "

ya ja tsaki, a fili

" kin lallai Sadisu ya manta bariki alalar gero ce,har ya yarda za ta kwaɓe masa da goguwar siyasar su!" ya sake faɗi a fili.

Da wannan tunanin ya tashi cikin gaggawa ya shige ɗakin sa ya na mai shirin taron da za su halarta na maraicin ranar, amma tabbas sai sun san yanda za a yi a rufe baki da idanun jama'a idan ba haka ba kuwa akwai matsala babba ma kuwa. Dan yanzun haka ma an dame shi da waya kan batun an ga karuwa bayan minista a yanar gizo,shin menene manufar haka?
   Cikin mintina k'alilan ya shirya tsaf,cikin shaddar sa mai shek'i ta sha aiki da ɗinkin babbar riga aska tara.

Ahmad kenan wanda ake ma kirari da " Kyakkyawan Yaro da kud'i abokin manya!" Duka duka shekarun sa arbain a duniya,kasancewar sa mai ilimi da wayewa a harkar siyasa sai ya zama na hannun daman babban minista, mai bada shawara na musamman ne a gurin minista, kuma aminin sa, duk da kuwa minista ya girme masa nesa ba kusa ba. Ahmad dogo ne,baki mai kyawun halitta da karamci, hakan ya sa ya yake da farin jini musammam a gun mata.

   Bayan ya gama shirin sa tsaf,ɓangaran matarsa ya nufa, domin ya shaida  mata zai fita. Ga mamakin sa sai ga ta sun yi kacibus tsakiyar farfajiyar gidan. Ta sha ado cikin bakin leshi, abun ka da farar mace ya haska ta sosai,ga wani yololon mayafi da ta yafa,duk da dai ta na da ɗan  da yanzu haka ya kai shekaru biyar a duniya  ka iya rantsewa matar Ahmad wacce ake kira da Hajja Bilkis budurwa ce.
   Sai da ya k'are mata kallo tsaf,ita ma ɗin kallan sa ta ke, kafin ya ce

"Maman Hanif ba dai fita za ki yi da wannan maraicen haka ba?"

Ta na mai tauna cingam ta ce
" Yes! Fita zan yi, toh a wannan Karnin namu idan ban fita na yi business ba, na zauna a gida na yi me Honorable ? Kasan dai ni business woman ce ko?"

Ahmad na mai gyara tsayuwa ya ce

"Haba Bilkis,duk business in ya wuce safiya ko rana ya kamata a hakura da shi, ke fa matar aure ce, yanzu ina daɗi a nan na fita, ke ma kin sa k'afa kin fita, shikenan yaro sai dai a bar shi da masu aiki, abun takaicin shi ne masu aikin ma kullum cikin sauya su ki ke...."

   "Da ka ta Honourable!" Ta tsaida shi ta na mai ɗaga masa hannu.

"Ba fa bariki na ce zan fita ba! neman halal zani, idan dan ɗan ka ne kai ma mai iya zama ka kula da shi ne, Dan ma ka samu na haifa ma ka shi,  mata nawa ka na aura ka na saki dan ba sa haihuwa?  kar fa ka takura min fa! Ba na buk'atar shawarar ka, ka aje shi sai ka haɗu da mai girma Minista, dan kuwa a yau ya raba mana abin kunya a yanar gizo,  Don Allah kuna ba shi shawara, Allah  kuma ya sa ba duk kanwar ja ba ce"

Baki buɗe ya ke duban ta, ya ma kasa mai da mata da martani ya na ji ya na gani ta wuce shi, hatta kai ga shiga motar ta,maigadi na buɗe mata gate ta fice kamar zata tashi sama.

Rai na sosawa Ahmad ya jinjina kai, wai a gidan sa kenan ake yada masa magana bare a kai ga abokan hamayya, tabbas Sadisu ya ja mu su yau, kai ba dan ya kai k'ololuwa wajan son Bilkis ba, da tabbas yau ya bata takardar saki.

                       ***

       Babban tsakar gida ne mai wadataccen fili. Turken awaki a gefe,in da fitilar  acibalbal ke aje tsakiyar turken kasancewar an iddar da sallan ishai kenan gari yayi duhu, dan matashin yaro mai kimanin shekara goma sha biyar ke ciki ya na gyaran wajan, Can gefe guda kuma yaro ne mai kimanin shekara bakwai tare da kanwar sa suna  wasan oji oji. Ga kuma tabarma shimfiɗe can gefen ɗakin inda mai gidan wanda ake kira Malam Tanko ke zaune tare da uwar gidan sa Ta-assubi.

   Rai bace Malam Tanko ya ke duban ta, kana ya ce
"In ma ki wata tambaya mana Ta-assubi?"

"Ina jin ka Malam" Ta-assubi ta bashi amsa ta na mai tsuke fuska.

Be kula da yanda ta amsa masa d'in ba ya ce

"Na ce ni dinnan ni na haifi Habi ko kuwa?"

Ta-assubi ta kada baki ta ce "Mu dai mu ka haife ta Malam ba kai kaɗai ba,k'arewar ta ma ni na yi nak'udar ta!"

    Cikin jinjina kai Malam Tanko ya furta
"Toh idan har ni ne uban Habi aure zan mata,bazan yarda a tura min ɗiya uwa duniya har birnin Dunotsi da sunan aikatau ba,a wannan K'arni na mu na haulai!"

"Malam in dai kan wannan maganar ne kwarankwasa sai dai mu yi ta, dan kuwa ba za ka nuna min iko ba ina ji ina gani, shi Muazzen da ka ke turawa almajirci birnin Dunotsi na taɓa tanka ma ka ne? Ko ko shi ba rai gare shi ba? Gashi i wannan karan ka ce har Hamze za ka haɗa, sai yanzu da ka ji batun samuwata ka yi kucin-kucin ka ce za ka hana?"  Ta-assubi ta faɗi ta na mai nuna jajircewarta akan raayinta.

   Cike da takaici Malam Tanko ya kada baki ya ce
"Ke dai tunanin ki k'alilan ne,shi Muazze ba namiji ba ne? ko ina zan iya tura shi hankali kwance, bare shi ilimi ya ke zuwa nema ba aikatau ba, ke bar ta wannan ma, Muazze da Habi da Hamze haka ma Hansai duka 'ya'ya na ne, saboda haka sai abun da na yanke kan su!"

Ta-assubi ta dubi Malam a hasale, "Zancen ka ke so ance da gauro wai ya iyali! Tun tuni yarinya na zaune gidan nan,duk sa'annin ta sun yi aure,mak'o ya hana ka fidda kuɗi ka mata aure, yanzu da ka ji hanyar samun arziki ya zo mana, ka na so ka hana tsabar bakin ciki irin na namiji!"

Cike da mamaki,ya na mai nuna kan sa da ɗan yatsa ya ce

"Ni? Ni Tanko ni na ke mi ki bakin ciki Ta-assubi?  Gaskiya ne ita tururuwa idan ta tashi lalacewa fuffuke ta ke  sai ta tashi sama,na fuskanci abin na ki da wata manufa ciki, kin kuma wuce gona da iri, ina mai tabbatar mi ki muddun Habi ta tsallake mu ta tafi birnin Dunotsi aikatau ba da yawu na ba, kuma duk abin da ya je ya dawo ki kuka da kan ki!"

Ta-assubi na mai tafa hannu ta bashi amsa da "Sai alkhairi! Alkhairi shi zai je ya dawo Malam! Sai alkkhairi!"

  Cike da takaici Malam Tanko ya yunkura zai tashi,fitowar Habi daga d'aki, yarinyar yar shekara goma sha huɗu, fara kakkaura, ya sa shi tsayawa ya na duban ta,ganin ta durk'usa gaban sa ya ce 
"yaya ke kuma menene?"

Kai sunkuye ta ce

"Dama Baba shawarace na ke so na baka kan makarantar Muazze da Hamze"

Ta-assubi ta kame baki
"Toh fa ana wata yarinya ta kawo wata!"

Malam Tanko be kula da maganar Ta-assubi ba ya ce
"iyye?ke kuma da me ki ka zo?"

Nan fa Habi tayi shiru. Sai da ya ce "Ke fa na ke sauraro ki barni tsaye kamar  wanda ya haɗiyi gatari"
   Cike da tsoro,Habi ta kada baki ta ce,
"Dama Baba cewa na yi tunda akwai makarantun allo cikin wannan kankara ta mu,me zai hana a bar su nan gida suna makarantar je ka ka dawo, almajirci a yanzu ba karamin musiba ba ce....."
Kan ta k'arasa Malam Tanko ya buge bakin ta,cikin bambami ya ce
"Uban ki ne zai hana! Jaira! Toh ki ce ban isa zama uban ku ba toh! Yar butun uwa! An ki a bar su ɗin! Tashi bani waje kan na haure ki na huta!"

Jiki na rawa Habi ta tashi da sauri ta yi ciki. Bin ta yayi da kallo,ya na mai faɗin
"Yaran zamani! Yaran yau! Wannan KARNINMU! Yanzu Ta-assubi wannan yarinyar ki ke son turawa birnin Dunotsi? Ni Tanko ba da yawu na ba!"
Ta-assubi na mai gyara zama ta ce

"zuwa kam kamar ta je ta gama"

Buta Malam ya ɗauka, ya zaga kewaye ba tare da sake tankawa ba. Shigar sa Ta-assubi ta yi kiran Muazze,wanda gama gyaran turken tumakin ke nan ya fito ya na wanke hannu. Gidan Lande mai jigilar yan aikatau ta tura shi,ya je ya shaida mata bana dai har da Habi za a tafi,ko ita ma ta samu arzikin da iyayen da yaran su ke zuwa aikatau ke kwasa.

No comments:

Post a Comment