Sunday, 25 December 2016

Sakaci 2

💔💘 *SAKACI* 💘💔

                   0⃣2⃣

© *Fatima A Garba*

Zaune ta ke akan sallaya ta na karatun alqur'ani cikin suratul Yusuf, zazzak'ar muryarta ne ya karad'e cikin d'akin, ta jima sosai ta na karatu.

Bayan kammala karatun ne ta d'aga hannu sama ta na kai kukanta ga mahaliccinta, ta d'auki tsawon lokaci ta na addu'o'i har ba ta san lokacin da Auntynta ta shugo ba, sai da ta shafa addu'an ne ta ganta agefen gadonta a zaune.

Cikin jin kunya ta ce "kiyi hakuri Aunty ni ce yafi dacewa na zo na fara gaishe ku amma kullum hakan baya yuwuwa, ina neman afuwa abisa wannan rauni nawa"

Murmushi Aunty ta yi gami da cewa "karki da mu dotana ba komai a ciki, yanzu k'ok'arta kije kiyi wanka sannan kiyi shirin tafiya aiki muna jiranki akan dining domin yin breakfast"

K'arasowa gaban Aunty ta yi ta sunkuya had'e da ce wa "ina kwana Aunty"

"Lafiya lau, kintashi lafiya? Maza toh atashi aje ayi wanka karki makara dota" Aunty ta fad'a gami da tashi don barin d'aki.

Murmushi Farida ta yi, gami da cewa "toh Auntyna".

               **************

Shigowa falon ta yi da sallama, kai tsaye wurin dining table ta nufa.

Tunda ta shigo falon idanun shi na kanta shi dai ya na tsananin k'aunar y'arsa had'e da tausayinta mai tarin yawa, sannan duk lokacin da ya kalleta wasu abubuwa ne da suka shud'e suke dawo mai, a ta ke wani irin tausayinta ne ya ratsa dukkan wata jijiya da ke jikinsa.

Har ta k'araso ta sunkuya a gabanshi had'e da cewa "ina kwana baba" sannan ya dawo daga dogan tunanin da ya lula.

"Lafiya lau Farida ya aiki,Da fatan ba wata matsala ko?" Ya fad'a.

cikin girmamawa ta ce "ba komai baba", ya ce "toh da kyau maza taso muci abinci karki makara" " toh " tace had'e da samun d'aya daga cikin kujerun da ke jere ta zauna.

Alokaci guda taji abincin ya hau kanta bazata iya ci ba, wasu al'amura ne sukaci gaba da dawo mata wanda yayi sanadiyar cunkishewan zuciyarta, gudun kada mahaifinta da Auntynta sushiga damuwa yasa ta d'auki ruwan tea kawai tasha had'e da cewa " baba zan wuce office" cikin damuwa mahaifin nata yace.

"Amma Farida kamar bakici abincin ba, na lura bakyason cin abinci shin bazaki rage damuwa acikin zuciyarki ba?" Ya fad'a cike da damuwa akan fuskarshi.

Murmushi ta yi sannan tace "Babana ka daina damuwa kaga ba ishashshen lafiya ne da kai ba, na k'oshi ne kawai amma badan komi ba".

" To ko adafa miki wani abun ne?" Ya sake fad'a cikin kulawa, murmushi ta yi akaro na biyu sannan tace " a'a baba abarshi kawai idan ina jin yunwa zan nema, yanzu haka ma akwai surgery din da zamuyi ne nan da minti talatin (30mns)"

Ta fad'a had'e da kallon agogon da ke mak'ale a tsintsiyar hannunta, girgiza kai yayi alamar gamsuwa gami da cewa.

" Allah ya bada sa'a, ki kula da kanki kinji Allah ya miki albarka"  " amin baba, Aunty sai na dawo" tace had'e da tashi.

Aunty tace "toh adawo lafiya dotana ki kulamin da kanki" "angama Aunty" ta fad'a da murmushi kwance akan fuskarta.

Farida na fita shima ya mik'e dan barin wurin, cikin kulawa Aunty tace "Alhaji. Baka fa ta6a komai ba, kuma yanzu ka gama yiwa Farida magana akan ta dinga cin abinci, ya kamata ko kad'an ka d'an ci".

Girgiza kai ya yi gami da cewa "Alhamdulillah" tafiya yayi ba tare da ya sake jin abinda zata ce ba.

Had'a plate d'in ta fara yi dan ita kanta baza ta iya cin abincin ba, d'aga hannu sama ta yi had'e da cewa " ya Allah na yi tawassali da sunayenka ya Allah ka kawo mana farinciki a gidan nan, ka yaye mana dukkan damuwar da muke ciki wanda mu ka shafe shekaru masu yawa a cikinta"? Haka ta cigaba da addu'a.

             ********************

Tanayin fakin d'in motarta a wurin da aka tanada don ajiye motoci, wata attender tazo ta kar6i jakan kayan aikinta had'e da gaisheta ta ansa cikin sakewan fuska. Office d'inta ta zarce don yin shirin shiga operation d'in da ke gabanta.

                       ***

A kanshi idanun ta suka sauka, a ta ke gabanta ya bada rasss, k'ok'arin saita kanta ta yi.

" good morning" ta fad'a cikin siririyar muryarta, shikam bai ansa ba asalima ko kallonta baiyi ba sauran likitocin ne da nurse d'in dake d'akin  suka ansa.

Ita sam ta kasa nutsuwa, jikinta har wani kar-karwa ya keyi.

Suna tsaka da aikin nasu cikin k'warewa, ta zo mik'a mai wani almakashi cikin rashin sani jikinsu ya had'u da juna, a ta ke jikinta ya hau rawa har yayi sanadiyan fad'uwan almakashin hannun na ta.

Shima hakance ta kasance dashi amma saboda shi namijin duniya ne bai bari ta gane ba sai ma tsawa da ya daka mata had'e da cewa "

wannan wani irin hauka ne bana son rashin hankali da rashin kan gado kuma bana aiki da masu shi, idan kinga bazaki iya ba ki fita kibamu wuri".

Ya fad'a cikin d'aga murya ba wacce ya yiwa ba, duk wani mahaluk'in da ke d'akin tiyatan nan sai da ya shiga FIRGICI, domin dama shi ba mutum ba ne mai d'aukan wargi,

Hakan bai isheshi ba ya sa ke zuwa dai-dai kunnenta yace " duk mutumin da yasa jaraba aranshi ya shiga uku" fuskarshi a tamke ya kuma cigaba da aikinshi tamkar ba shi yayi maganar ba.

Kallon shi ta yi cikin k'unan rai, lura da yayi ta na kallonshi yasa ya kuma had'e rai tamkar bai ta6a dariya ba, sauke idonta k'asa ta yi, ita to mai ta tsare mai, Kuka ne ya ke shirin kwace mata, hanya fita ta yi ba ta re da ta kuma kallonshi ba, haka kuma ba wanda ya dakatar da ita.

Ta jima ta na kuka a office d'inta kafin daga bisani ta wanke fuskarta ta kuma gyarata sannan ta umarci ma'akantan da su fara turo mata marasa lafiya.

Cikin gwanancewa ta cigaba da duba marasa lafiya, har ta zo kan wata yarinya wanda suka shugo tare da wani saurayi, ta musu umarni da su zauna sannan ta fara tambayansu abinda yake tafe da su yarinyar ta ce.

" dama ina tsarin iyali ne (family planning) ne to sai ya fara bani matsala shine dalilin zuwana" cikin tsananin mamaki Farida ta ce "tsarin iyali? Wanne ki keyi?"

Yarinyar tace " dama inashan wani  magani ne, mai suna combination 3 kuma maganin yana yawan saka min ciwon kai wani lokacin harda jiri, gashi idan zanyi al'ada (period) sai na yita zubar da jini (bleeding)"

Cikin mamaki Farida ta ce " toh ina saura ran ki " yarinyar ta muskuta sannan ta ce " ni inaga zan bar shan maganin ne sai na koma allura" damm!! gaban Farida ya buga k'ok'arin saita nutsuwarta ta yi sannan tace

"Haihuwanki nawa ne"

Sai ayanzu saurayin da suka shigo yayi magana " a'a bamu ta6a haihuwa ba hasalima karatu ta keyi shiyasa zamu tsaya da haihuwa har sai ta gama karatun tukunnan"

Farida tace " OK, yanzu shekaranku nawa da aure?" Ita tace "shekara uku (3)" shikuma ya ce "shekara d'aya (1)"

Anan ta gane basu da gaskiya, cikin hikima ta ce wa saurayin ya basu waje zata duddubata.

Bayan fitanshi ta dubi yarinyar da a shekaru bazata wuce shekara sha shida (16) zuwa sha bakwai (17) ba ta ce " Maryam ko" yarinyar ta gyad'a kai gami da cewa "eh".

Farida ta yi gyaran murya sannan ta ce "Maryam mai yasa kika za6i yin planning ba ta re da kin ta6a haihuwa ba, koda kuwa k'waya d'aya ne?" za ta yi magana ta dakatar da ita da "inazuwa" sannan ta cigaba "shin kina da tabbacin ke mai haihuwa ce ko akasin haka? Ama sa a ked'in mai haihuwa ce bakya tunanin ki kashe k'wayoyin haihuwar naki, kizo daga baya kina son haihuwa ita kuma ta juya miki baya, karki biye ta d'a namiji duk lokacin da yaso haihuwa idan bai samu a wurinki ba zai je ya auro wata ta haifa mai kuma alokacin za ki fuskanci wulak'anci"

Yarinyar da aka kira da Maryam tace " hakane" sannan Farida ta cigaba "haihuwa ba zata hanaki karatu ba domin akwai mata da yawa da sukayi karatu kuma alokacin suna haihuwa, wasu ma sai da su ka gama haihuwan sannan suka fara karatun, bakya tunanin hakan da ki kayi butulci ne ga Allah? Karfa ki manta akwai mata masu dukiya wanda Allah bai basu haihuwa ba kuma da za'ace su bada duk abinda suka mallaka dan su haihu zasu bayar, bana so ki cuci kanki kina da k'arancin shekaru, kuma ga dukkan alamu ni banga alamar ke matar aure ba ce, amma kizauna kiyi tunani kada son zuciya ya kaiki ya baro"

Goge hawayen da ya sauk'o kan kuncinta ta yi sannan tace " na yarda da duk abin da ki ka fad'a Dr kuma gaskiya ne ni ba matar aure ba ce hasalima ban ta6a aure ba sannan wanda muka shigo dashi saurayina ne wanda zai aure ni"

Farida girgiza kai ta yi cikin takaici tace " ban san dalilinki na yin hakan ba amma mai yasa kika za6i ki jefa rayuwarki a garari?"

Cikin kuka tace "labarin mai tsayi ne Dr, na yarda da ke zan baki labarina idan har kinada lokaci nasan za ki taimaka min da shawara " Farida ta jinjina kai sannan ta ce "zanbaki address d'in gidanmu kizo ranar asabar kisameni insha Allahu zan taimaka miki" a k'arshe suka yi sallama da alk'awari zata je gidan farida.

Haka farida ta gama aikinta zuciyarta cunkushe da damuwa ga tozarcin da Dr Umar ya mata a gaban mutane ga matsalar wannan yarinyar Maryam a gefe guda kuma zafin da zuciyarta ta keyi a duk lokacin da to tuna wani al'amari da ya ta6a faruwa da ita a rayuwarta.

   Shi kad'ai ne  da idan taji muryar shi zata samu sassauci a zuciyarta, wani irin kewarshi ne taji ya lullu6eta, ta na buk'atar ganinshi amma ba dama, wayarta ta d'auko had'e da d'an latsawa kafin kuma ta kara a kunnenta alamar kira ta ke yi.

Bada jimawa ba aka d'aga cikin zazzak'ar muryarta ta yi sallama ya ansa da nashi salon mai rikitar da ita, cikin kulawa ya ce "dear ya naji muryarki haka".

Murmushi ta yi acikin ranta sonshi yana d'ada karuwa a zuciyarta, tabbas Ahmad masoyinta ne, ya na saurin fahimtar yanayin da ta ke ciki, amma ba ta so yau ta tayar mai da hankali shiyasa ta ce " my man wallahi ina kewarka, ina bukatar ganinka na kasa sabawa da rashinka my man"

"Dear ni kaina hakurina ya fara k'arewa, ina tsananin so nadawo ko igiya ta d'auru atsakanin mu, amma ki k'ara hakuri wani satin iyanzu ina k'asata Nigeria kusa da ruhina, ina dawowa kuma sai batun sa rana kinfa san ba na so ya d'au lokaci" ya k'arasa cikin kwantar mata da hankali.

Ta ce "Allah ya dawo min da kai lafiya my man" haka su ka cigaba da bayyanawa juna irin k'aunar da ke cikin zuciyoyinsu, cikin lokaci k'ank'ani ta nemi damuwar ta rasa.        

             

No comments:

Post a Comment