💔💘 *SAKACI* 💘💔
2⃣8⃣
© *Fatima A Garba*
Yau tunda suka iso ta ke gyare-gyare domin ta na sa ran zuwan mijinta gareta, hatta zanin gado yau sai da ta sauya, babu abinda ba'a k'alk'aleshi ba.
Kasancewar ya ce ba sai sun dafa komai ba yasa ta na gama gyaran gidan ta shiga wanka, ta jima a ciki toilet d'in kafin ta fito.
Zama ta yi ta tsantsara kwalliya gami da feshe jikinta da turare, wata rigan bacci ta d'auko mai kyau ta sanya.
Ta idar da sallah kenan ya shigo, wani k'ayataccen kallo yake jifanta dashi.
Ita kanta yau ta na bukatar ta jita a k'irjin mijinta, "kinyi kyau" yace da ita,kuma har lokacin idanunsa na kanta.
Sunkuyar da kai ta yi ta na murmurshi, "Faridanaaa" ya fad'a cikin sanyin muryar da saida tsigar jikinta ta tashi.
"Bari na je na yi wanka" ya sake fad'a, "toh" tace dashi yana fita ta janyo ledar da ya shigo da ita ta na dubawa, abincin da yasan ta na so ne, "Dr ka jima kana kyautata min yau na maka alkhawarin faran ta maka.
Ta d'an jira taga bai shigo ba kuma yunwa ta ke ji, don haka ta zuba abincin ta ci bayan ta rage mai nashi.
Ta jima ta na jiran shigowarshi amma bai shigo ba, har bacci ya d'auketa a falon, wurin sha biyun dare ta farka, ranta yayi matuk'ar 6aci.
Ita wai me Dr yake nufi da ita ne, haba itafa ba dutse bace ta na buk'atar mijinta, daurewa kawai ta keyi a wannan y'an kwanakin.
Ranar kasa runtsawa ta yi kewar mijinta ya hanata sak'at, sosai ranta ya 6aci.
Ba ita bacci ya d'auketa ba sai karfe uku na dare.
Sawa kanta dauriya ta yi don bata so ta bada kai, koda ya shigo da safe sam bai mata maganar rashin dawowanshi ba, ita d'in ma bata kawo maganar ba.
Ranar ta re sukaje wurin aiki abun gwanin sha'awa, duk wani motsinta a idanunshi, bini-bini sai ya biyota office wai yazo ganin lafiyar matarshi, ita kuma ta biye mai.
Da yamma bayan sun tashi, ya d'auketa yace suje su gai da Baba, ba k'aramin farinciki Baba da Aunty sukayi da ganinsu ba.
Haka aka dinga tattalinsu, Aunty ce ta ja Farida d'akinta ta ke cewa "d'azu munyi waya da Ummi ta ke fad'a min halin da kike ciki, amma mai yasa baki fara sanar dani ba dota"
"Ayya Auntyna kiyi hakuri wallahi bana so na d'aga muku hankali ne Ummi ma dandai ta matsa ne" Farida ta fad'a.
Aunty ta ce "amma yanzu komi yayi daidai ko" Farida ta ce "eh Aunty" wani kwalba Aunty ta d'auko cike da magani ta ce ungo maza shanye mazan yanzu ba'a musu Sanya, ga wannan shiga toilet kiyi tsuguno"
Da dai kamar Farida bazata kar6a ba tunawa da jiya amma sai ta yi tunanin watakila jiya gajiya ce tasa bacci ya d'aukeshi, kuma yau kam taga k'aunarta fal cikin idanunshi.
Kafin su tafi sai da Baba ya musu nasiha sosai, ta tafi tana kewar Babanta wanda taga ya sake ramewa.
Suna tafiya a mota amma gani ta ke sam tafiyar bata sauri wani irin shauk'insa takeji mai sauk'ar da kasala, bata ta6a shiga irin wannan yanayin ba.
Koda suka isa ce mata yayi bari yaje yaga lafiyarsu Mariya, hannunshi ta kamo gami da cewa "zaka dawo"
Ce ma ta yayi "karki damu kije kiyi wanka yanzun nan ina zuwa my Farida, yau inaso naji matata a jikina"
Kusan awa biyu ta na jiranshi amma shuru, ta rasa me yake damunshi wai shin har yanzu bai hakura bane.
Ita kam gaskiya hakurinta ya gama k'arewa, ta kasa gane ainihi me yake damunta, gaskiya yau bazata iya bacci ba, wani irin tausayin kanta taji.
Kiran wayarshi ta yi har saida ta kusan yankewa ya d'auka, "Farida" ya fad'a muryarshi da alamun bacci.
Wani bakinciki ne ya tokareta wato shi baccin shi ma yake, kuka ne ya kwace mata.
Hankali tashe yake tambayarta, kashe wayar ta yi ba tare da ta bashi ansa ba.
Lokacin da ya shigo ta kifa kanta akan gadon ta na kuka, zuwa yayi ya kamota gami da rungumota, fad'awa ta yi k'irjinshi ta na kuka.
"My Farida kukanki na d'aga min hankali, na rok'eki ki sanar dani abinda ya sakaki kuka kafin zuciyata ta buga"
Ya fad'a hankalinshi a tashe, kukan ta cigaba da yi, kamo fuskarta yayi da hannuwanshi biyu yana cewa "oya bani hawayen na shanye Faridana"
"Bazan iya juran ganinsu suna zuba ba, please ki sanar dani, Farida ina cikin garari"
"Kallonshi ta yi gami da cewa "na tuna da Mama ne na karashe da kuka"
Rungumeta ya sa keyi tamkar zai maidata cikin jikinshi, kafin kuma yace "addu'a za ki musu, na rok'eki matata ki daina tayar da hankalinki ko kinaso zuciyata ta buga"
Girgiza kanta ta yi gami da kwantar da kanta a k'irjinshi, shima dad'a manne ta yayi a jikinshi.
~Ummu Hanan~
No comments:
Post a Comment