💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣5⃣
A gigice ya aje Hajiya kan kujera kafin ya fita ya kira Doctor. Ko da Doctor ya zo d'aya godan da ke kallan na junior aka kwantar da ita. Sai da aka samu ta farfad'o kafin Doctor ya duba ta,inda ya ke mai tabbatarwa Dawud da be ruk'e Hajiya ba ta kai k'asa da ba k'aramin b'arna ne zai biyo baya ba. Dan kuwa ba mamaki ta zama paralyze,zuciyar ta ce ta kusa bugawa,san samu ta d'an kwanta ta sami hutu nan gadon asibiti. Bayan likita ya mata allure,ya bawa Dawud sunan maganin da za a siya,har shi ma ya k'ara mata da wani da ya san ingancin sa. Har likita ya fita Hajiya ba ta kalli Dawud ba bare ta tanka masa. Sai ma juya masa baya da ta yi. Gashi Habeebti ma shiru tin fitar da ta yi. Nan kuma ga kaka da jika kwance,ya na so fita ya siyo magani ba dama.
Waya ya d'aga ya kira Ayub,ya ci sa'a kuwa ba nisa yayi ba. Ya ce da shi dan Allah ya yi maza ya zo ya same shi,ya fad'a masa asibitin da ya ke. Ita kuwa Habeebti tun fitar ta tafiya ta ke ba tare da ta san in da ta dosa ba,haka har ta bar asibitin ta mik'e k'afa ta d'au doguwar hanya. A haka ta na tafiya har ta zo titi. Kanon dabo yaya da cikowa bare ace ranar sallah,garin cike ya fal,yan yawan sallah na k'afa da mota kowa ya fito sada zumunci. Haka Habeebti ke kutsawa cikin mutane ta na tafiya. Wani mai bike ya zo wuce saura k'iris ya buge ta,amma ita ko a jikin ta. Haka ya k'are zage ta tsaf ba ta ma san yana yi ba,ita dai tafiya ta ke. Allah kad'ai ya san iya kan nisar tafiyar da ta yi,k'afafunta bud'u bud'u saboda k'ura da k'asa.
Ayub ne da ke kan hanyar zuwa asibiti ya hango ta,da har ya wuce ya ga dai tabbas ita d'in ce ya dawo ya yi parking gefan ta. Ganin ta gan sa amma be hana ta cigaba da tafiya ba ya sa shi fitowa ya biyo ta a k'afa. Ya na tadda ta ya ce "Habeebti ina za ki haka a k'afa?me ya faru?" Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta tsare shi da idanu. Ayub ya fuskanci ba cikin hayyacin ta take ba,sai ya ce "Mu je na sauke,ina za ki?gida ko asibiti?"
Sai a sannan ta bud'i baki ta ce " Bichi,Bichi za ni...." Cikin rashin fahimta Ayub ya ce "Bichin za ki a k'afa Habeebti?" Sai kawai ta sa masa kuka,jamar da ke kaikawo su ka fara sa ido,suna shirin taruwa. Ganin haka ya ja hannun ta su ka isa mota,ya bud'e gaba ta shiga sannan ya zaga shi ma ya shiga ya tada motar su ka d'au hanya. Kuka ta ke,tun ya na bata hakuri da tambayar ba'asi har ya hakura yayi shiru. Dawud ne ya sake kiran sa wai ya ji shiru. Jin suna tare da Habeebti,ya ji dad'i cikin ran sa dan kuwa tunanin in da ta ke ya tsaya masa a rai,amma kafin su k'araso ya bar wajan,dan be shirya ganin Habeebti ba tukun.
Da k'yar Habeebti ta yarda su ka shiga ciki,in da ita da Hajiya su had'u suka had'a kai sai sabon kuka. Ayub kuwa duk sun bari sa cikin duhu, kiran Dawud ya yi ya ji ba'asi,jin abun da ke faruwa yace da Ayub yayi sauri ya kira Doctor ya ma Hajiya allurar bacci ko ta samu ta huta,amma ya k'i fad'a masa abun da ke faruwa ya ce ya bari sai sun had'u. Yanda Dawud ya fad'a hakan Ayub ya yi. Bayan Hajiya ta sami bacci ya sa Habeebti a gaba da tambaya,wai menene ya faru ne. Amma ta kasa fad'a masa,har jinin da ake sawa Junior ya k'are,ana cire masa ya farka ya na kukan ciwo,amma Habeebti ta kasa k'arasawa wajan bare ta rarrashe shi. Sai Ayub ne ya jawo shi jikin sa,bayan Nurse din ta sa masa robar ruwa ta fita. Ta na daga kan gadon Hajiya ta ke kallan sa. Har ran ta ji take ta tsani Junior a yau,ta tsane shi fiye da tsanar da ta masa randa ya fara zuwa duniya, ba dan komai ba sai dan cin amana da hainci na uban sa. Hawaye ne ke zuba daga idanun ta,yau ba kukan fyad'en da aka mata take ba,kukan na Haroun ne,ashe Haroun masoyi ne,da ta san waye Haroun da ba ta wulak'an ta shi ba,ta bar jaki ta je ta na dukan tanki. Ta san ta rasa Haroun,me ma zai yi da ita bayan rashin arziki da ta yi masa,da wani ido za ta kalle shi ko Hajiyan shi? Gashi ba tun yau ba ta kamu da son shi,tun sanda su ka yi accident ta tabbatar da soyayyar da ta ke masa,ita ce har da jin haushin kan ta na ta na san wanda ya cuci rayuwar ta,ashe Haroun masoyi ne.......ta d'aga wayar ta,kamar za ta kira sa,amma ta kasa...
Duk abun da ta ke yi akan idon Ayub,ya samu Junior yayi bacci. Yafi zatan Haroun ne ya yiyiwa Habeebti laifi,amma rashin lafiyar Hajiya ne sam be gane silar ta ba. Da wannan tunanin ya kira Alhaji in da ya ke ce masa shi ma ya na tafe Dawud ya fad'a masa.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣6⃣
Haroun be bar gidan Anty Salmah ba sai yamma lik'is,daga ita har shi sun rasa yanda za su yi su fad'awa Mama,dan kuwa idan Mama ta ji ya san auren shi da Habeebti ya k'are. Sun rabu ne akan idan ta zo ranar uku ga salla ta san yanda za su yi da Mama. Sai bayan tafiyar sa Anty Salmah ke jin maganar kwanciyar Hajiya,ta ce ba dole ba Dawud ai ya gama kashe ta da ran ta.
Washagari Dawud ya je Bichi ya d'auko Yakumbo,amma kyememe ya k'i shiga duba Hajiya bare Junior saboda gudun bacin ranta,dan Akib ya ce masa jikin da sauki. Habeebti zaune bisa sallaya bayan ta idar da sallar walha. Tun ta na duba wayar ta,har ta hakura,da ta ji wayar ta yi k'ara ta duba da sauri,ganin ba Haroun ba ne sai ta ji kamar ta fasa wayar ta huta. Har ta rame,idanun ta sun kumbura,duk ma su zuwa dubiya sai tsiya su ke mata,wai rashin lafiyar Junior da Hajiya sun sauya mata kamanni,nan kuwa ba su san tsabagen tashin hankalin da ta ke ciki ba ne ya jawo. Kowa mamakin kwanciyar Hajiya ya ke,musammam Alhaji,wanda sai da Hajiya ta masa bayanin dama ba ta jin dad'i,da aka gwada jinin ta be Doctor ya ba da shawarar ta d'an kwanta na kwana biyu. Sannan Alhaji ya d'an sarara mata da tambaya.
Bangaran Haroun ma hakan ta ke. Dan ko bacci ma kasawa yayi,yanda ya ga dare haka ya ga rana. Kuma ya na san ganin Habeebti ba wai ba ya so ba,haka ma san jin muryar ta,amma idan ya tuna zai iya ganin Dawud can musammam da aka ce Hajiya ma an kwantar da ita,sai hakan ya hana shi zuwa dan kuwa be san me zai iya aikatawa kan Dawud ba. Haka kuma yanda su ka rabu da Habeebti da maganganun da ta fad'a masa ya sa ya ke ji kamar ta fitar masa a rai. Da su Mama za su tafi asibiti ta ce ko za su tare ya ce shi sai anjima za shi,bayan azahar,cikin ran sa ya na godewa Allah da ya rufe bakin Aysha har lokacin ba ta yi magana ba kenan. Zuciyar ta d'aya ta rabu da shi su ka yi tafiyar su.
Ganin Mama daga Hajiya har Habeebti da ke ta sak'ar zuci kasa nutsuwa su ka yi,suna tsoran kar dai labarin jini ya je mata ta wajan Aysha. Amma shirun da su ka ji daga gare ta har ta mu su sallama ta tafi ya sa hankalin su d'an kwanciya. Ganin haka Yakumbo ke tambayar lafiya kuwa?ita fa ta kasa gane kan Hajiya da Habeebti bare kuma Dawud da ko dubiya be zowa,kan a zo kan Mai Junior,tun d'azu take zuba ido ta ji shiru. Cike da kunya,Hajiya da ke zaune bisa gado ta fara yiwa Yakumbo bayani,ta na mai fad'in "Ai ba a banza ba na kwanta ba Yakumbo,da ban yi niyar fad'a mi ki ba,amma ya za a yi,ranar wanka ba a b'oye cibi,Dawud dai ya cuce mu,Dawud ya kashe mu da ran mu,ya jawo mana abun kunya da rashin daraja......"
Yayinda Mama ke fita,sannan Huda ke shigowa,inda su ka had'u farfajiyar asibitin Huda na gyara parking. Sai da su ka gaisa,ta tambayi Mama d'akin da su Hajiya su ke sannan Mama ta shige mota,ita kuwa Huda ciki ta shiga ta na mita cikin ran ta,dan dole aka mata zuwa asibitin nan,wai a lalle sai ta zo ta duba Hajiya in ji mahaifiyar ta Ummi. Ita ba ta san shi kan shi Dawud d'in takun sak'a ta ke da da shi ba bare mahaifiyar shi. Abun takaicin shi ne hadda Habeebti da wannan yaran na ta da ta tsana za ta gani,ba dan ba kyau bijirewa maganar iyaye ba da wallahi ba za ta je ba.
Da wannan tunanin ta k'arasa d'akin,amma maganar Yakumbo da ta ke yi cikin ihu da firgici ya tsada ita. Fad'i take "Shin wai ki na nufin Dawud ne uban Haroun k'arami???!k'alu innalillahi wainnailaihirajiun! Kai wannan shi ne kwancewar zani a kasuwa!" Hannun ta tsaye a iska,ita ba ta bud'e kofa ta shiga ba,ita ba ta koma ba,kunne ta sa dan jin Hajiya na bawa Yakumbu labarin da Dawud ya bata,ita kan ta Habeebti sai a sannan ta ke ji,in da ta tsinci kan ta tana yiwa Dawud tsananin tsana,tsana wacce ta so ta wuce hankali. Ta na mai mamakin bakin munafunci irin na sa,ko kallan Junior ba ta kaunar yi,sai a sannan ta gane tsanar da ta tab'a yiwa Haroun ba ma tsana bace,yanzu ne ta tsani Dawud,har ya shafi Junior da be ci ba be sha ba.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣7⃣
Ita kuwa Huda ko da ta gama jin jawabin Hajiya,ran ta fari tas ta juya dubiyar ma fasawa ta yi,ta na jiyo ihu da salatin Yakumbu,in da take fad'in " Kaico ni Aliya,kin ga ta kan ki,ni ce har da bugun Haroun ashe Haroun dan kwarai ne....." Huda na murmushin mugunta ta ce "dan haka kuwa zama da Haroun ya k'are mata ba,dama hez someone borrowed". Da nushad'in ta ta ja mota,ba ta zame ko ina ba sai gida. Ko gidan su ba ta shiga ba ta nufi b'angaran Mama. Haroun na kwance falon Mama idanun sa lumshe,har yanzu ba ta dawo ba. Gaba d'aya abun duniya ne ya ishe sa,ya rasa in da zai sa kan sa. Jin kamar an tsaya kan sa ya sa shi bud'e ido a hankali,idanun sa suka sauka kan Huda wacce daga gani kasan cikin farin ciki ta ke,ga wani murmushi da ta ke masa,tun kafin auren ta rabon sa da ita.
Ganin ta ya tashi zaune,in da ya kwak'ulo fara'ar dole,ya na fad'in Huda,an zo yawan sallah. Bin shi ta yi da kallo,k'ananan kaya ne cikin sa,riga mara hannu da wando three-quarter wanda aka yi da yadin kaki. Ba k'aramin kyau da kwarjini ya mata ba,har ta kusa shagala da kallan sa,sai da ya kira sunan ta sannan ta yi saurin gaishe shi,bayan sun gaisa ta ce "Shi ne tun da aka yi aure na ba ka zo gida na ba" "Am sorry for dat" ya amsa a takaice kafin ya k'ara da" Ga shi kin zo Mama ba ta nan ta je asibiti,Aysha ma ina ga gidan Anty Salma ta je...." Ta na d'an sun da kai ta ce " Dama gun ka na zo,na ci sa'a na same ka,Allah ya kawo mana dama ya Haroun" cikin rashin fahimta ya ce " Ta me fa?" Nan ta shiga zayyana masa abun da ta ji daga bakin Hajiya,ta k'are da "Ka ga kenan yanzu munafuntar ka ake,sun san d'an su ne ya aikata laifi shi ne suke boyewa,Allah ya kawo ma mafitar auren k'ayar da aka ma,Allah ya wanke ka,ba ka da wata dangantaka da zai d'aure ka da ita,ni ma kuwa na san dole Dawud ya sake ni sai mu kasance tare cikin zaman aure...." Tun da ta fara magana ya ke mata kallan sokuwa,bare kuma da ya ji k'arashen maganar ta ta. Fuska tsuke ya ce " Ko ma ina ki ka ji wannan maganar,ina mai tabbatar mi ki yasasshen zance ne,ina fatan zai tsaya iya kunne kawai,ban so ya k'ara zuwa ko ina. Junior d'ana ne,kuma Aliya mata ta ce,kin ga kuwa shi tuwo tuwo ne,ba a sake masa suna. Ke matar aure ce Huda,ko sanda ki ke bud'urea ban tab'a mi ki irin kalar soyayyar da na ke yiwa mata ta ba,ina san ki ne kamar yanda na ke san Aysha,da Maryam da Halima. Bare yanzu da ki ke matar yaya na. Ki tashi ki tafi gidan mijin ki."
Cike da jin d'acin maganar sa ta ce "Wallahi tun daga ran da aka kai ni gidan Dawud har rana ta yau babu abunda ya tab'a shiga tsakanin mu idan ma ka tunanin nima na zama ragowar Dawud ne kamar Habeebti...." "Sht up!" Ya daka mata tsawa yayinda ya tashi a fusace. Ita ma din tashi ta yi jiki na rawa,dan jin tsawar ta shi sai da hanjin cikin ta ya kad'a. Ya nuna ta da d'an yatsa ya ce " Kin ci sa'a bana d'aga hannuna kan mace,da kuma darajar auren ki da kin koka da kan ki. Daga yau sai yau kar ki kuskura na ji kin k'ara ambatar mata ta da ragowar wani,bare ma ta fi ki daraja sau dubu,she is a woman with pride tun da ita ko ba ta da aure ba za ta tab'a k'ask'antar da kanta kamar yanda ki ka yi ayau ba,da auren ki da komai. Ba a banza aka aurer da ke ga mijin ki ba,shi d'in ne dadai ke. Ni da Aliya mutu ka raba takalmin kaza! Get out!" Huda na kuka,ga kunya da ya lullub'e ta ta fita. Daren ranar neman bacci ta yi ta rasa,bakin cikin yanda su ka yi da Haroun ya sa ta lashi takobin wulak'anya Habeebti tin da saboda ita Haroun ya wulak'anta ta. Ai kuwa zuwa wayewar gari ta sami abun yi,ta shirya tsaf sai ga ta gidan Falon Mama.
Hajiya kuma ranar aka sallame ta. Ayub ne ya d'auko ta ita da Habeebti,wacce da kan ta tace ta na so ta zo gida ta d'an yi wanka da kyau,amma cikin ran ta rashin ganin Haroun ke damun ta. Gaba d'aya ya share ta,ta kira sa a waya sau d'aya be d'aga ba be kira ba,haka na biyun,sai ta hakura,badan Ayub ya ce ya gan shi da safe ba da ta yi zatan ma ya kima Kaduna,tun da yau uka ga sallah,an koma aiki. Yakumbo aka bari da Junior wanda shi ma ake sa ran gobe ko jibi za a sallame shi.
Da kyar su ka iya samin hanya saboda dawakai,'yan hawan sarki,da ke yau sarki ke hawan Nasarawa,kuma sun yi rashin sa'a lokacin da su ka fito lokacin ya ke shiga Government house. Hajiya na mitar da Ayub ya bi ta wata hanyar,Habeebti na adduar Allah ya sa ta had'u da Mai junior,dan idan ba ta gan shi ba har d'akin sa da wajan Mama sai ta bi shi. Allah ya taimaka su ka isa gida,in da Alhaji ke shirin fita. Ganin su ya fasa,ya bi bayan su su ka shige b'angaran Hajiya. Ita kuwa Habeebti sai raba ido ta ke ko Allah ya sa ta ga Mai junior,amma ba shi babu alamar sa. Har Ayub ya gane,ya ce da ita "zan je na fad'a masa ki na neman sa,na barshi falon Mama d'azu kafin na fito" ko kunyar ya gano ta ba ta ji ba,bare ta ji kunyar cewa "Yauwa dan Allah Ayub,amma kar ka ce in ji ni pls" ya na d'an murmushi ya ce "an gama" da sauri ta shige d'akin ta,ta yi saurin shiga toilet ta wanke fuskar ta,aka fito aka shafa powder har da lip balm da turare wai fa duk a yau Mai Junior ake so a yiwa kyau. Ta ci sa'a ta d'an yi fes da ita. Sannan ta dawo falo,ba kowa Hajiya da Alhaji suna ciki,sai ta yi zamanta a falo ta na mai raba ido.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣8⃣
Ganin Mama ba ko sallama kamar an jefo ta,bayan ta Anty Salma ce da Aysha sai kuma Huda da ta kunno wutar ya sa Habeebti tashi da sauri. Sai kuma ta sunkuya da niyar gaishe da Mama,amma ta d'aga mata hannu ta na mai fad'in "Ke dalla ruk'e gaisuwar ki,menene gami na da ke da za ki wani sunkuya ki ce za ki gaishe ni,ke asu wa?" Jikin Habeebti na rawa ta kasa motsawa. Yayinda Mama ta shiga dokawa Hajiya kira "Mairo! Mairo!! Mairo!!!!"
Ba shiri sai ga Hajiya da Alhaji sun fito da sauri. Ran Alhaji a b'ace ya ce "Fadi wannan wani irin abu ne haka,ya daga dawowar ta daga asibiti za ki fara irin wannan kira haka,lafiya kuwa?" Mama na murmushi ta ce "lafiyar ce ta kawo haka ai Alhaji,Allah ne ya toni asirin matar ka da d'an ta da kuma d'iyar da take ruk'o,dama hausawa su kan ce munafuncin dodo ya kanci mai shi,yau Allah ya gama min komai,an yi shuka a idon makwarwa,toh wallahi yanda aka tozarta...." "Dallah Fadi yi mana shiru,ya za ki tara yaran cikin ki ki na irin wannan magana ta rashin wayo?menene amfanin wannan?" "Rashin wayo Alhaji?" Mama ta amshe," Idan maganar rashin wayo ne ga wacce ta aikata can "Ta nuna Hajiya da tuni ta sha jinin jikin ta. Mama tak'ara da "Ita da d'an cikin ta yayiwa d'iyar yayan ta fyad'e,ta haifa mata jika,oh ni Fadi wannan INA DARAJAR TA KE?" Hakan yayi daidai da shigowar Haroun da Ayub,wanda Ayub ya je ya masa k'arya Alhaji na neman sa duk dan Habeebti ta samu ta gan sa. Jin maganar Mama ya sa shi tsayawa cak idanun sa kan Habeebti da ke durk'ushe ta na hawaye. A fusace cikin muryar gargad'i Alhaji ya ce " Fadi kar fa ki fad'i abun da za ki yi danasani!" Ta na mai huci ta ce "Mairo dai ita ke fama da danasani har ya kai ta da kwanciya gadon asibiti,ni da na san abun da ya kwantar da kenan Mairo wallahi da ban je na duba ki ba,da ga ke har jikan na ki. Alhaji gaskiya dai ta yi halin ta,d'an shegen da aka lik'awa Haroun,har da sa masa sunan Haroun to d'a dai na Dawud ne,dan haka sai a gaggauta siyan rago a mayar da yaro Dawud Junior,su je can su k'arata!"
Dan mamaki Alhaji da kyar ya iya furta " Me ke faruwa ne?" Ya kalli Haroun ya ce "Wanene uban Junior?menenen gaskiyar al'amarin" Memakon ya bashi amsa,sai gani su ka yi ya nufi inda Habeebti ta ke durkushe,ya sa hannu biyu bisa kafad'ar ta,ta d'aga ido ta kalle shi,ya na mai girgiza mata kai na da ta bar kuka ya tada ita tsaye,kafin ya sanya hannun ta cikin na shi. Huda ji ta yi kamar ta had'iyi zuciya ta mutu,haka ma Mama da indan ran ta yayi dubu ya b'aci. "Junior dan wanene!" Alhaji ya k'ara tambaya cikin d'aga murya,wannan karan Hajiya ya ke kallo, "Na ce dan waanene cikin 'ya'ya na?" Kamar mai rad'a Hajiya ta furta "Dawud" tuni Alhaji ya nemi waje ya zauna dan kuwa jikin sa ya fi k'arfin k'afafun sa. Mama na mai murmushi ta ce "ka zauna Alhaji,ya kamata ka zauna dan kuwa ba kai kad'ai ba,kowa ma ya shammace shi,dan haka kai Haroun,a matsayi na na mahaifiyar ka na haramta auren ka da yarinyar nan...." A gigice Haroun ke duban Hajiya,haka ma Habeebti da ba ta san sanda ta kamk'ak'ame Haroun ba ta na mai girgigiza kai. Inda Anty Salma da Aysha su ka shiga ba ta baki,amma ta ce "wanda ya k'ara magana cikin ku wallahi sai na tsine masa,ku na ina sanda na kwashi bakin ciki saboda wannan yarinyar da Mairo da tsinannan d'an ta?kuna kallo har cuta na yi,idan ba ku sani ba da baki na sai da na rok'e ta(ta nuna Habeebti da d'an yatsa)na had'a ta da Allah ta yi hakuri a rufawa juna asiri ta sa a saki Haroun a musu aure,amma girma na da tsufa na be sa ta k'i amincewa ba,har ta kai ga zan durkusa mata,Halima da wananan d'iyar albarkar Huda su suka hana ni,ba dan Huda ba da maganar nan ban ji ta ba yau dan rufe mun su ka yi,kai kuma shashashan banza wanda aka shanye ka kasa tab'uka komai,maza ka sake ta na ce!"
Haroun ya zube k'asa hannunu sa biyu d'age ya na mai fad'in".Mama ki yiwa girman Allah kar ki raba ni da Aliya,Aliya ba ta da laifi,Aliya ta sha wahala,ba ta da laifi,ina san ta Mama,na rabu da Aliya zan shan wahala,na yarda da duk hukuncin da za ki yanke amma kar ki raba ni da Aliya,Aliya na ke so Mama,wallahil-azim ina san ta Mama...."
Kusa da shi ita ma Habeebti ta durk'usa,ba ta ji ba ta gani kuka ta ke kawai. Haka ma Anty Salma da Aysha,Ayub kuma juyawa yayi ya fice. Ita kuwa Huda rok'on ta kar Allah ya sa Mama ta sauko. Nan kuwa Mama ta bud'i baki ta ce "Yanda ba su tausaya min ba,ni ma bazan tausaya mu su ba,ka sake ta ta je can su aura mata uban d'an ta,wannan kwamala har ina! Ba ka bina bashin ran tsuwa,ba zan yi kaffara ba,wallahi sai ka sake ta!!!!!!!!" A gigice Haroun ya d'ago idanun sa da su ka yi jajur ya kalli Mama kafin ya ce "Kar ki raba ni da farin ciki na Mama,ba zan jure ba....!" Ya dubi Alhaji wanda ya ke zaune idanu lumshe,ya ce "Alhaji ka taimaka min dan girman Allah ka sa baki kar Mama ta raba ni da farin ciki na,ba zan jure ba,ba zan iya jurewa ba....!"
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣8⃣
Mama ce ta dubi Alhaji ta ce "Alhaji ina fatan dai ba za ka sa baki ba,dan ban son bijire ma ka gaban yara,wannan hakki na ne,kar ka toye min shi Alhaji...!" Alhaji na san yin magana,amma kunya da kalaman Mama ya sa a dole ya yi shiru. Mama ta kalli Haroun ta ce "Kai na ke jira,sake ta na ce!"
Hannu Habeebti wanda ke rawa tsabagen firgici ya ruk'o,ya kasa had'a ido da ita,ita kuwa sai girgiza masa kai ta ke. Da kyar ya iya d'aga ido ya kalle ta,ko da su ka had'a ido sai ya kasa jurewa,ya dubi Mama ya ce" Mama ina san mata ta,ba zan iya ba.." " Wallahi idan ba ka sake ta ba sai na tsine ma!" Mama ta katse shi cikin tsawa. Jin haka tuni Mai Junior ya ce "Na sake ki Aliya,saki d'aya" ya na gama fad'a ya zame hannun shi daga na Habeebti,ya tashi zai fita dan kuwa ba zai jure kallan Habeebti da ke kuka har da majina ba,Huda kuwa kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha dan farin ciki,hakin ta ya cimma ruwa. "Tsaya nan,saura biyu! Uku za ka mata!" Mama ce ta dakatar da shi,in da ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba.
Sai a sannan Alhaji ya ce "Wannan ne kuma ba ki isa ba Fadi! Ya za ki sa yaro ya saki matar sa da ya ke so,kuma ki ce ya mata saki har uku?kai je ka abun ka,wannan din ma dan kin rantse ne na kuma san yanda Haroun ke san yarinyar nan ba zai yi fiye da d'aya ba shi ya sa na bari,kai je ka abun ka,Allah ya ci maka albarka!" Da maganar mahaifin sa Mai Junior wanda ke ji tamkar a mafarki wai ya saki Habeebti ya sa kai ya fice. Haka ma Anty Salma da ta bi bayan shi da sauri,kan ta fito har ya shige motar Ayub ya fice.
Mama kuwa kad'e zanin ta tayi ta fita bayan ta ce da Hajiya kad'an ma ta gani,in dai ita ce uwar Haroun saki ukun nan sai ya yiwa Habeebti,in ya so Dawud ya aura su je can su k'ara ta. Sai bayan fitar ta Hajiya ta shiga rarrashin Habeebti,duka su na kuka. Alhaji neman duniya yayiwa Dawud amma babu shi babu alamar sa,hatta wayar sa a kashe ta ke. Haka ma Alhaji Hamisu surikin na sa,in da Huda ta je ta had'a karya da gaskiya kan zaman ta da Dawud har shi ma ya fusata ya ke neman sa ido rufe.
Da yamma sai gashi ya shigo gidan,Maigadi ne ya tsada shi,wanda Alhaji ya dad'e da barwa sallahun idan sa idan Dawud ya sheda masa ya na neman sa. Hakan kuwa ya fad'a masa. Dawud da ya san za a rina,sim sim ya nufi b'angaran Alhaji,in da yayi rashin sa'ar ganin sa tare da Alhaji Hamisu suna kan tattauna maganar ta sa kenan.
Gaban su ya d'urk'usa ya gaishe su. Daga Alhaji har Alhaji Hamisu babu wanda ya amsa gaisuwar ta shi. Alhaji ne ya tashi ya kwashe shi da mari kwarara biyu. Dawud ya na ruke da kuncin sa ya sunkuyar da kai,Alhaji ya ce "Idanun ka kenan mutumin banza mutumin hofi,ina can ina yiwa dan uwan ka kallan mutumin banza,kai mu ka ja a jiki,saboda ganin kamala,daraja,sanin yakamata da rik'on addini,ashe kallan kitse mu ke wa rogo,Allah wadar da hali irin naka,ban tab'a tsinewa d'ana ba,amma kai dai Dawud Allah ya......" "Alhaji!!!" Alhaji Hamisu ne ya yi saurin katse shi ta hanyar kiran sunan sa. Alhaji na huci ya dubi Alhaji Hamisu ya na fad'in "Ka bari na tsine masa in ya so ya lalace da hujja! Menene ban yiwa yaran nan ba?wani gata ne ban masa ba?cikin yara na wa na ja a jiki kamar wannan mutumin banza! Ashe ya ce ni da ka ke k'auna ni ne ajalin ka,toh wlh ka yi kad'an! Ka bari na tsine masa Alhaji Hamisu!"
"Idan ka kasance mai tsinewa yaran ka wa zai yi koyi da kai?ai idan rai ya b'aci be kamata mu bari zuciya ta d'ebe mu mu aikata danasani ba,ka duba sanda ran ka ya b'aci ka sa aka zo har gida aka tafi da Haroun,ba dan Allah ba azzalumin bawan sa ba ne yasa hakan ya zama cigaban Haroun ai da lalle an yi danasani na hakika...."
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
9⃣9⃣
A fusace Alhaji ya ke nuna Dawud ya ce "Idan kan wannan mahaincin ne sam ba zan yi danasani ba,dan wannan ba mutum ba ne shaid'an ne,dan haka shi ma dole a d'aure min shi,ina mai tabbatar maka sai an shiga kotu an nemawa yarinya hakkin ta,dama wani rufa rufa da ake yi idan irin haka ta faru ke jawowa a ta aikatawa yara mata zalinci sanin za a ce a rufa asiri tunda abun na gida ne..." Cikin jinjina maganar Alhaji,Alhaji Hamisu ya ce "Kotu?yanzu ka so ace duniya ta ji ana shari'a tsakanin d'an ka,da kuma d'iyar yayan matar ka akan ya mata fyad'e,hatta kai ga yarinyar ta haihu,kuma matar taka ma mahaifiyar d'an na ka Alhaji? Wannan me duniya za ta kira zuri'a irin ta mu?wannan ai tonan asiri ne,da zubar da kima da darajar zuri'a"
A fusace Alhaji na k'ok'arin kiran waya,ya ce "Toh dama akwai wata daraja da ta rage min?INA DARAJAR TA KE Alhaji Hamisu?na ce ta na ina bayan wannan mutumin banzan ya gama sayar da ita ta hanya mafi muni..." Jin an d'aga waya ya katse maganar da ya ke sannan ya fara magana da na wayan "Hajiya Mairo Aliya ta koma asibiti ne?" Daga d'aya b'angaran Hajiya ta ce yanzu Ayub zai mai da ita,dan ta ma fita,Alhaji ya ce a tsada ita maza ya neman ta. Ya na katse wayar ya kira Haroun,shi ma d'in kiran sa ya yi zuwa b'angaran nasa. Dawud kuwa kunya kamar k'asa ta tsage ya shige.
Habeebti zaune bayan mota,idanun ta sun yi jajur dan kuka,ga margarine din ta da ya tashi. Hajiya ta yi ta yi ta huta a gida,amma tak'i dan baza ta iya jure kwana gida d'aya da Haroun ba alhalin ba ya matsayin mijin ta,yanzun ma Allah Allah ta ke Ayub ya zo su tafi,har za su tafi aka kira shi a waya,bayan ya d'aga ya ce mata ya na zuwa ya sake komawa ciki. Ko da ya dawo sai cewa yayi da Habeebti Alhaji na neman ta. Gaban ta yayi mummunar fad'uwa dan ta san dai ba zai wuce maganar Mai Junior ba,Allah ya sa ba sauran saki biyun Mama ta sa aka cika mata ba. Da wannan tunanin ba da san ran ta ba ta fito ta bi bayan Ayub,in da ya kai ta b'angaran Alhaji,ya ce da ita in ta fito ta same shi a mota sannnan ya juya,ta shiga.
Sa k'afarta a falon tare da sallamar ta lokaci guda ta yi. Gaban ta yayi mummunar fad'uwa sanda idanun ta su ka sauka kan Dawud,wanda shi ma d'in jin shigowar ta tuni ya d'aga kan sa zuwa gare ta,kwayar idanun sa cike da sakonni kala kala. Sauri ta yi da d'auke idanun ta daga gare shi,inda hakan sam ba sauki ta samu ba,dan kuwa dai sai gashi sun yi ido hud'u da Mai Junior,wanda tun shigowar ta ya ke kallan ta,kuma ganin kallan da Dawud ya ke mata da kuma wanda ta masa ba k'aramin tsaya masa yayi a rai ba. Ta na ji su Alhaji su ka amsa sallamar ta ta,tare da bata izinin shigowa,amma ta kasa motsawa daga in da ta ke tsaye,yanda Mai Junior ke kallan ta cike da so da kewa ya rud'a ta,ji take kamar ta koma dan kuwa yanda ta ke ji za ta iya fashe masa da kuka ta had'a har da rok'an sa na da ya dawo da ita d'akin ta. Dawud kuwa bakin ciki da kishi ne ya kusa kashe shi,ji ya ke kamar ya je ya fizgo ta ko ta daina kallan Haroun,shi ma Haroun din ya d'auke ido kan ta. Jin Alhaji ya ce da ita ta shigo mana ya sa Dawud sakin ajiyar zuciya. Ita kuwa Habeebti k'arasawa ta yi can gefe,in da ba za ta na gano Haroun ba ta zauna.
Alhaji ne ya ya ce da Haroun "Ka yi hakuri ban iya hana mutuwar auren ka da matar ka ba..." Dawud ya d'ago da sauri ya na mai duban Habeebti,wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar shi dan kuwa be san da batun sakin Habeebti ba,"kai mashaAllahu,ashe dai da rabo" abun da ya fad'a cikin ran sa kenan,dan da ya san zai so Habeebti yanda ya ke san ta yanzu,zai kuma so Junior kamar ran sa da be bari an aurar da ita ga Haroun ba.
Alhaji be gushe ba ya cigaba "Ka kuma yafe mu akan kuskuren da mu ka aikata kan ka,bisa rashin sani,ga dan uwan ka nan,na yanke hukunci shigar da k'ara kotu,amma kafin nan,ga shi ga ka,yanda na sa aka d'aure ka,shi ma ka d'aure,in ma can Kaduna za ka tafi da shi fani'imal"
Murmushi Haroun yayi dan maganar ta Alhaji dariya ta bashi,ya ce " Alhaji in dai b'angare na ne ba sai an kai ga haka ba,ya je dan kasa,Allah ya kaddara dama hakan zai faru shi ya da ya faru" Jin haka shi kan sa Alhaji Hamisu sai da ya jinjina halin daddako irin na Haroun. Alhji na duban Haroun ya ce "Ka tabbata?" Haroun ya amsa da ya tabbata. Kai Alhaji ya jinjina kafin Haroun ya nemi izinin tafiya dan sam xaman be ma sa ba. Bayan tafiyar sa aka tambayi Habeebti zan cen shigar da k'ara,bud'ar bakin ta ta ce "Alhaji ba sai an kai ga haka ba,ku bar shi da sakayyar ubangiji ma kad'ai ya wadatar" Alhaji Hamisu ya ce "Shikenan kin gama magana yarinya" Alhaji ya dubi Dawud ya ce "ka ji yara masu daddako,sun barka da Allah,amma ka ji tsoran sakayyar ubangiji. Kuma na ba ka daga yanzu zuwa wayewar gari ka saki Huda,dan kuwa ba ka canci auren ta ba!" Alhaji Hamisu ma yayi na'am da wannan batun,dan dai ba zai iya bud'e baki ya buk'aci hakan da kan sa ba ne da tuni ya furta. Shi kuwa Dawud ruwa ne ta sha,dama hakan ya ke so.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
1⃣0⃣0⃣
Ba kunya bare tsoran Allah sai gashi ya bi bayan Habeebti,gaban motar Ayub ta tsaya jin ya na kwalla mata kira. Da saurin sa ya k'araso gare ta,ganin yanda ta ke kallan sa cike da tsana ya ce "Habeebti.....Aliya na san ban kyauta mi ki ba,ban san da wani baki zan baki hakuri ba,amma pls ki saurare ni,kar ki tsanane ni,ni masoyin ki ne,na kuma yi alk'awarin gyara kuskure ni da zarar na aure ki kin zama tawa,na san kina sona Habeebti shi ya sa ba ki goyi bayan Alhaji ba,kuma kin ji Huda ma sakin ta zan yi,sai ta je can ta tak'arata da Haroun...."
Tas! Habeebti ta kwashe shi da marin da sai da ya ga wuta a fuskarsa,kan ya gama jin zafin marin ta k'ara masa wani,ta k'ara da "Wannan na Haroun ne,na haintar sa da ka yi,amma ka sani a sanadin wannan zaluncin na ka,Allah ya saka min da miji na gari,mai sanin Allah,kuma Allah ba zai raba ni da shi ba ya musanya min da azzulumi kamar ka ba(ta tofa masa yawu)Aure yanzu na fara da miji na,shi ya sa Allah yayi igiyar aure har uku, ina da ragowar biyu kuma ina fatan komawa ga mijina,Allah ya min tsari dagaa najasa irin ka,d'an ka da na haifa Allah ya min masalaha kan sa" ta bud'e gaban mota ta shiga,Dawud ya na kiran ta,tambaya ya ke "Me ki ke nufi Allah ya mi ki masalaha akan Junior Aliya?" A fusace ta rufo kofar ta na huci ta ce "Ayub mu tafi dan Allah" sai ji ta ti yace "Be kamata ki na dukan uban d'akin ki ba Aliya..." A hankali ta juyo,maimakon Ayub,Haroun ne zaune gaban motar,ganin haka Aliya ta yunk'ura da sauri za ta bud'e motar ta fita,tuni ya sa lock ya rufe motar,duk da ya ji kuma ya ga yanda ta yi da Dawud,ya ce da "Wato kin gwammaci ganin shi da tsayuwa da shi akan zama in da na ke ko Aliya?" Cikin rashin fahimta ta juyo ta kalle shi tare da fad'in "ka bud'e min k'ofa na fita kafin Mama ta gani dan Allah" shi kan shi Dawud sai a sannan ya lura Haroun ne cikin motar ba Ayub ba.hankalin sa ya dad'a tashi,dan ya san kowani lokaci Haroun mai iya dawo da Habeebti d'akin shi ne,musammam ya na ganin ta haka,nan fa ya fara kwankwasa mu su glass d'in mota. Haroun har ya niyar fita ya yi maganin sa,sai kuma ya ga ai kam be da lokacin sa yanzu dan kuwa ya san tabbas akwai ta shi da Dawud musammam yanda ya ga ya na bibiyar Habeebti,da kuma abun da ya ji ya furta mata. Amma ba yanzu ba,ba kuma gaban Habeebti ba,Saboda Dawud yayan sa ne,duk da ya zubar da girman sa,respect irin na Haroun ya sa ba zai iya taka shi gaban Habeebti ba.
Da wannan tunanin ya tada motar abun sa, ya na mai bad'e Dawud da k'ora,sannan ya fice ya d'au hanya. Habeebti ta tsinci kan ta tana mai farin cikin kasancewa da shi na d'an wannan lokacin. Haka su ka isa har asibiti ba tare da sun yi maganar arziki ba. Isar su murnar Habeebti ya koma ciki jin Haroun da ke parking farfajiyar asibitin ya cewa "Aliya gobe zan koma Kaduna,kin san an koma aiki yau...." Tsabagen yanda ta ji maganar ta sa sai ga hawaye na bin kuncin ta. Shiru Mai Junior yayi kafin ya ce "Ki yi hakuri,duk da na san ba ki sona,ina san ki Aliya,kuma ba zan bar ki ba,ba zan jima ba zan dawo,fata na Mama ta huce sai na shawo kan ta.... Ki kare mutuncin kan ki" kai kawai ta girgiza masa kafin ta yunk'ura za ta bud'e kofar,ta ga har yanzu be bud'e ba,ta sa hannu ta na k'ok'arin ja da kanta,amma zufar da ya cika hannun ta ya sa ta kasa. " Aliya?" Ya kira sunan ta a hankali,ta juyo su ka had'a ido,ganin yanda idanun sa su ka yi ja,da kuma yanda ya ke kallan ta a raunane ya sa ta yin k'asa da na ta idon. Haroun ya ce "Ni Haroun ni kad'ai ne mijin ki,wallahil-azim idan ki ka gan ki da wani mijin bayan ni to ki tabbatar ba na doran k'asa,ina numfashi ba zan iya jure rashin ki ba ko da kuwa ba kya so na...."
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
1⃣0⃣1⃣
Kai Habeebti ta gyad'a masa,kafin ta ce "Allah ya tsare hanya" ya amsa mata da amen. Sannan ya bud'e mata k'ofa ta fita, a hankali ta ke tafiya, ta d'an juyo su ka had'a ido. Murmushi Mai Junior ya sakar mata,ya na mai d'aga hannu ya ce "wait for me my Habeebti,I will be back for you" ita min hannu ta d'aga masa,ta na jinjina kai duk dai ba ta ji abunda ya ce ba saboda nisan da ya mata. Sannan ta juya ta shige ciki. Sai da ta k'urewa ganin sa sannan ya iya tada mota ya juya ba tare da ya shiga ya ga jikin Junior ba.
A daren nan ya koma gun Mama,maimakon ta sauko sai ma dad'a hawa ta yi,wai ko zuwa yayi ya ga Habeebti Allah ya isa ba ta yafe masa ba. Dan haka ko sallama be mata ba,ya had'a na sa ya nasa,ya ce da Ayub ya kai sho tasha,suna shirin tafiya ya hangi motar Dawud ya na shigowa,nan ya dakatar da Ayub,ya fita ya je ya same shi.
Ganin sa Dawud ya faka ya fito ya na wani shan kamshi. Gaban sa Haroun ya tsaya,duk tsayi da fad'in Dawud sai gashi ya zama k'arami gaban Mai Junior,sai d'aga kafad'a ya ke a lalle sai ya kamo Mai Junior. Mai Junior fuska d'aure ya kalle shi ya ce "Dawud ni k'anin ka ne,duk da kai ba ka da girma sai na jikin ka,toh ka saurare ni da kyau,Aliya ba macen da ka tab'a zalinta ba ce,ka sa a ranka macen da ka cuta ta mutu tun randa ka zalunce ta,Aliya mata ta ce......" "Ba dai matar ka ba ce,sakakkiyar matar ka dai,ina dai ka sake ta?ko ka dawo da ita ne dan Mama?" Dawud ne ya katse shi. Ran Haroun a bace,hannun sa dunk'ule dan har ga Allah ba ya san tab'a lafiyar yayan sa,darajar girman sa da yayi. Da kyar ya shanye,ya ce "Ina san mata ta fiye da yanda na ke san kai na,ga kashedi na ko da wasa sam kar ka k'ara zuwa in da ta ke,wallahil-azim Dawud zan aje girman na ka a k'asa,na rufe ido na in maka dukan b'arawo a hannun soja,I dare you!" Ya na gama fad'in haka ya juya zai tafi,Dawud ya tsaida ta hanyar fad'in "Idan ka hana ni kusantar yar uwa ta wacce ta ke tsohuwar matar ka,nd you don't even have dat ryt,za ka hana ni ganin d'ana,takwaran ka ne?eh Haroun...?da ka ke wani fariya kan ta,ni na fara zama da ita cikakkiyar mace,ni na fara sanin ta budurwa,kuma guna za ta k'are aran ta ka samu....." Wani wawan naushi da Haroun ya kai masa,tuni ya yi shiru. Idanun Haroun sun kad'a sun yi ja,dama ga b'acin ran Mama,abun da ya guda shi yayi,dan kuwa tuni ya shiga kai wa yayan sa duka. Tun Dawud na iya ramawa,Ayub da ya taho a guje dan shiga tsakani na k'ok'arin rabasu Dawud na fad'in "Rabu da shi Ayub ba shi ya yi k'arfin da zai iya duka na ba" Har ya zo ba ya iya ramawa sai kare kan shi kawai dan kuwa ba bugun hankali Haroun ke kai masa ba. Dama yaya Haroun da zafin hannu bare ga b'acin rai. Ayub da ya ga babu sarki sai Allah sai yayi ciki da gudu dan neman taimako,in da Dawud ya yi zaton ya gudu ya bar shi ne da Haroun,be sanda ya fara kwalla masa kira ba ya na ihu da kururuwa, "Ayub dan uban ka guduwa za ka yi ka barin da wannan mahaukacin,wai ina jama'a ne,Haroun zai kashe ni,kai ba ka da hankali ko kashe ni ka huta! Jama'a a zo a raba mu"
Kai tsaye b'angaran Alhaji ya nufa,jin abun da ke faruwa Alhaji ko motsawa daga in da ya ke kwance yana karanta jarida be yi ba,sai ma cewa yayi "Dawud ke dukan Haroun ko kuwa Haroun ke dukan Dawud?" Ayub da ke rikice ya ce "Haroun ke yi wa Ya Dawud dukan kawo wuk'a" jin haka Alhaji ya ce "Toh madallah,ka rufo min kofar nan da kyau idan ka fita,ka ga aikwai sauro a waje da yawa.." ya d'aga jarida ya cigaba da karantun sa. Ganin haka Ayub ya juya da sauri dan ya san tun da Alhaji yayi haka ba fitowa zai yi ba. Dakin Hajiya ya je,amma har gwara Alhaji akan Hajiya,dan ita cewa ta yi duk wanda ya k'ara kawo mata maganar Dawud sai ta sabar masa,a ma kashe shi ina ruwan ta. Ko gun Mama be ma nufa ba,gidan Alhaji Hamisu ya shige,shi ne ya biyo shi da sauri ya na salati. Amma ina kan ya k'arasa ya had'a masa jini da majina,Dawud kwance sai nishi ya ke.Allah da ya so ya san yanda zai masa lilis ba tare da ya karya shi ba. Abun takaici sai a sannan maigadi ya shigo a guje ya na salati.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
1⃣0⃣2⃣
Haroun da ke duban Dawud wanda ke kwance k'asa,ya nuna shi da d'an yatsa sannan ya ce "Wannan na Aliya ne,ka kuma ruk'e kashedi na" ya juya a fusace ya nufi mota,ya na jin Alhaji Hamisu na tambayar ko kansa d'aya kuwa,ya masa shiru,kayan sa da ya sa motar Ayub ya d'auka yayi gaba abun sa ya bar Alhaji Hamisu da tunanin yanda za su yi Dawud,sai fad'a ya ke yiwa Maigadi wai yana ina haka ya faru?Maigadi ya ce "Alqurani bawali na zaga".
Ranar dai sai Ayub da Akib aka bari da yiwa Dawud gashin jiki,dan kuwa Huda dai ya sake ta bisa umarnin Alhaji,Hajiya kuma ta kaurace masa. Dan haka sai dai su Ayub d'in. Ana masa gashi ya na ihu,da k'arewa Ayub zagi,wai shi ya tafi ya bar su da abun be kai har haka ba. Har Ayub ya fusata ya bar shi da Akib. Sai daga baya Mama ke jin zancen. Jin Haroun ya bugi Dawud ta san tura ta kai bango,dan har da na ta zafin aka sauke kan Dawud. Ta kira wayar shi a kashe,har ta gaji,sai washagari ta ke ji bakin Ayub wai ai ya wuce tun jiya. Abun ba k'aramin ciwo ya mata ba. Amma sai ta danne ta ma daina kiran sa,idan aure be kawo sa ba,saki ya kawo shi.
Bangaran Habeebti kuwa ana sallamar Junior ta had'a yan kayan ta da ta zo da su,sai Bichi. A bakin Yakumbo ta ke jin labarin rashin lafiyar Dawud sanadiyar kashin da Mai Junior ya ba shi. Ta kuma ji dad'i sosai,ta so ace ya karya shi ma. Sai da ta kai kusan wata guda,ba Mai Junior babu alamarsa. Wata sabuwa shi ne ta kan tsinci kanta ta na mai masifar buk'atar shi kusa da ita,kuma kullum da ta zauna ba ta da tunani sai na shi,zaman ta da shi,da yar diramar da su ka sha tare,kuma kullum cikin tsara maganganun da za ta fad'a masa ta ke idan ya zo gare ta ko ma ya kira ta,da kuma irin soyayyar da zai sha gun ta idan ya maida da ta d'akin sa yanda ya mata alk'awari. Gashi har ila yau wayar shi kashe. Rabon ta da shi tin daren da ya isa Kaduna,ya yi kiranta ya ce ya tafi,be sake neman ta ba. Tun ta na zuba ido ta na sa rai har ta hakuri,ta fara yanke kauna daga ganin sa,Amma kullum san Mai Junior ambaliya ya ke cikin ran ta. Ita kan ta Yakumbo ta na tausaya mata musammam yanda ta rame ta lalace,dan kyan da ta yi kwanaki duk ya ragu.
Ga wani kwalafacin ganin Junior da Dawud ta tsira duk bayan kwana biyu,sam be ji kashedin Mai Junior ba. Tun yana shan zagi da wulak'anci gun Yakumbo,har ta gaji ta kyale shi. Sai dai gun Habeebti ne sai abun da ya k'aru,ya na ganin tsana k'arara amma hakan be hana shi sake dawowa bayan an kwana biyu ba.
Yauwa ma sai gashi ya shigo sa'in da Habeebti ke ruk'e da hannun Junior,ta na mai dukan yatsun sa da d'an yatsunta guda biyu,saboda dak'uwar da yayiwa Yakumbo akan ta hana shi wasa da ruwa. Yakumbu na "ya isa haka Habeebti",amma sai da ta masa kwarara uku. Ganin haka Dawud ya fusata,da sauri ya k'arasa ya na mai huci ya fizge hannun Junior ya aje shi gefe,sai a sannan ta ankara da shigowar sa.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
1⃣0⃣3⃣
Cike da b'acin rai ya ce "Me ya sa baki da imani ne?ya za ki kama hannun yaro ki na duka haka!me ya mi ki?" Maimakon ta ba shi amsa sai ma kallan banzan da ta watsa masa,kafin ta yi shigewar ta d'aki. In da shi ma ya bita ya na huci,Yakumbo ma bayan shi ta bi. Shi kuwa Junior da ke k'afar gantali gare shi,dama damar ya ke jira,ganin babu kowa tsakar gida ya yi waje abun sa ya na mai sharbar majinar kukan da yayi,abun ku da abu ya had'a da mura saboda tsabar wasan ruwan shi.
Kan gado ya same ta zaune,cikin d'aga murya dan kuwa Junior aka tab'a ya ce " Ni uban Junior,ni za ki daka idan so ki ke ki d'au fansa,ba wannan d'an ficici yaron ba,God Aliya ke ko irin tausayin nan na tsakanin uwa da d'a Allah be hore mi ki ba?" Habeebti ta masa banza dan kuwa in har ta ce za ta tanka masa lalle za a yi ba dad'in da su ka saba,ita kuwa ta gaji,ya bar ta da rashin Mai Junior kad'ai ya ishe ta. Yakumbo ce ta ce "Kai ko an yi mara kunya wlh Dawud,ba a banza Mairo ta kaurace ma ka ba,an daki Junior d'in,na ce ta dake shi d'in!!!! Mutumin banza mutumin hofi wanda be san ya kamata ba! Idan ba ka so a daki d'an na ka da ba kan san ciwan sa ba,sai ka d'auke shi ka je ka ruke ka bar yarinya ta huta ko ta ji da bakin cikin da ka dasawa zuciyar ta,kuma ka ke kan dasawa rayuwar ta!" Rai bace ya ce "Ni Yakumbo? Duk duniya akwai wanda ke kaunar wannan yarinyar kamar ni Yakumbo?" Yakumbo ma a fusace ta ce "Kaunar ka na banza kaunar ka na hofi,tir da kauna irin na ka,tir,wallahi ina bakin cikin kasancewar ka jika gare ni Dawud...." Da wannan kalamai na Yakumbo Dawud ya ji ba zai iya jurewa ba,ya sa kai ya juya ya fice a fusace yayinda Yakumbo ta bi bayan shi da zagi.
Rai b'ace ya fita har inda ya yi parking,ya bud'e mota ya shiga,ya tada da niyar yin baya yayi reverse,muryar mutanen da ke zaune wata yar rumfa da ke kofar gidan Yakumbo ya ji suna fad'in "Hankali kar ka taka yaro! Hankali za ka taka yaro" sai da ya dan yi gaba ya tsaya a gigice, tsaywar sa da salati da ihun jama'a lokaci guda. Fad'a su ke " Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ku ruk'e shi kar ya gudu,wallahi ya take ruwan cikin shi!" Kamar mahaukaci Dawud ya fito jin ana cewa ya taka ruwan cikin yaro. Ko da ya fito sai gani yayi ana k'ok'arin jawo gawar Junior wanda nan take Allah ya k'arbi ajiyar shi,ko motsawa be yi ba. Dan rud'ewa kasa yin komai yayi,'yan samarin gun kuwa har da mai ruk'e shi kar ya gudu. Jin hayaniya,Yakumbo da ke neman Junior ta lek'o,ganin an d'auko Junior jina jina ba rai,ga kuma Dawud an ruk'o shi,sun nufo in da take dan kowa ya san tattab'a kunnan ta ne. Tuni Yakumbo ta sa kuka,samari su ka ce "Gashi nan Yakumbo,shi ya take Junior da motar sa,Allah ya masa cikawa nan take. Yakumbo na kuka ta ce "Ku sake shi,ku bashi gawar dan sa,shi ne uban sa". Nan kuma sai Dawud ya zame mu su abun tasausayi,nan da su ka sake shi,tare da dank'a nasa gawar Junior,suna masa gaisuwa. Rungume da Junior ya na tafiya kamar mutum mutumi ya shige ciki,dan kuwa kan sa ya tab'u,Yakumbo biye da shi,su ka tadda Habeebti wacce ta ji komai da kunnan ta. Fuskar ta cike da hawaye ta k'arasa ta k'arbi Junior daga hannun Dawud da ya saki baki da hanci kamar wawa tsabar shock. Habeebti ta ce"Innalillahi wainnailaihir rajiun,Allah ya k'arbi d'ana Haroun,na rok'e Allah ya musanya min da wani Haroun d'in,amma dan Haroun,ya kuma sanya wannan da na rasa ya zama mai ceto a ga iyayen sa. Yakumbo sai a gaggauta a yi ma Junior wanka,ko ya je can ya huta har abada..." Jin kalaman Habeebti Dawud ya zube k'asa ya na kuka kamar yaro. Ba wanda ya kula da shi. Tuni mak'ota,musammam wanda Junior ya saba shigar mu su ya na cije mu su yara su ka fara shigowa. Yakumbo ta kira Hajiya wacce ba k'aramin jin mutuwar ta yi ba.
Habeebti ce ta wanki Junior da kan ta,ta shirya shi,ta masa rakiya har soro wajan su Ayub da isowar su kenan tare da su Hajiya. Dan kuwa Dawud na can an kasa gane kan sa,dan tabbas kan sa ya tab'u. Amma ko da ta ga Ayub ya mik'a hannu zai k'arb'e shi,ta tuna idan Haroun Junior ya tafi a yanzu,ya tafi kenan,kamar yanda iyayen ta su ka tafi ta na ji ta na gani,sai ta ruk'e shi gam,ta k'i saki,ta na kuka. Da kyar aka iya bambare shi. Ayub ya dauk'e shi aka fice,wanda ko wani taku d'aya da ya ke ba cikin hayyacin sa ya ke ba. Haka har su ka kai Junior gidan sa na gaskiya. ALLAH YA SA MU CIKA DA KYAU DA IMANI.
💫💫💫💫💫
💫INA DARAJAR TA KE?💫
KHADIJA SIDI....✍🏽
1⃣0⃣4⃣
BAYAN SATI D'AYA.
Da yamma likis,Miami market cikin barracks,sojoji makil sai shek'a ayar su ke. Can gefe Haroun ke zaune. Ya lalace,ga gashi duk fuskar sa ko shaving ba ya yi na kirki. Ba dan tsoran Allah da ya wadata cikin zuciyar Mai Junior ba ai da tuni ya lalace da shaye shaye da bin matan banza. Ba k'aramin kadaici ya shiga ba na rashin Habeebti,hatta kai ga idan ba bacci ba,ba iya zama gidan shi. Wayar shi kuwa wata d'aya da sati guda kenan a kashe. Ya yanke huld'a da kowa.
Kamar daga sama ya hangi wani na ya nufo shi,sai da ya k'ura ido ya ga tabbas Akib d'in ne tafe. Har ya k'araso in da ya ke Mai Junior be motsa ba. Cike da girmamawa Akib ya ce "Ya Haroun ina wuni?" " Lafiya lau,idan Mama ce ta aiko ka,tell her am fyn,ka koma gida" ya amsa masa a tak'aice. Hakan be kashewa Akib gwiwa ba ya ce da "Dama post utme mu ka yi a ABU,shi ne bayan an gama na ce bara na biyo na gan ka,mu na kewan ya Haroun" jin haka Haroun ya saki ran sa kad'an in da ya bawa Akib wajan zama,har da sawa wata mai abunci ta kawo masa sakwara da miya. Ya zauna ya take kayan sa,tin ya na firgita idan sojoji su ka yi kuwa ko su ka harba harsashi sama,har ya zo ya d'an saki jikin sa. Nan suna d'an tab'a hira sama sama,Akib ke masa maganar rasuwar Junior. A kid'ime ya tashi,ya na fad'in "ban sani ba,wallahi ban sani ba...Innalillahi wainnailaihi rajiun,ya Aliya ta ke?ya Aliya ta ke ciki?ban kyautawa mata ta ba!" Akib da ke tunanin Haroun be zai damu da rasuwar Junior ba,cike da mamaki ya ce "Wayar ka ce kullum a kashe ya Haroun...." "Tashi mu tafi,Kano za mu tafi sai na ga Aliya ayau komin dare!" Da wannan ya yi gaba,Akib na biye da shi,kan ka ce me tuni ya had'a abun da ba za a rasa ba,sai gasu a hanyar Kano,cikin galleliyar sabuwar benz din Haroun,jeep mai tambarin AMG. Gudu kuwa Akib sai tawassali yayi ya mik'awa Allah lamarin sa,dan kuwa tashi sama ne kawai ba su yi ba. Har Allah ya kai su lafiya.
A falo ya tadda Mama,ita da Anty Salma da Huda zaune. Kamar daga sama sai gashi ya shigo musu. Kafin ma su tambaya ko lafiya ya gaida Mama a takaice kafin ya ce " Na zo neman izini,ina so na je na ga Aliya na mata ta'aziya" zuciyar Mama ta kad'a,wato ba ita ya zo gaisarwa ba,neman izinin ganin sakakkiyar matar shi ya zo,haka ma Huda,wacce ko nunawa ya san ta na wajan be yi ba. Bud'ar bakin Mama sai cewa ta yi "Idan ka je,na baka umarnin ka k'arasa sakin ta,ya zama ka mata uku"
Haroun ya nisar da kai cike da ladabi ya ce "Ki yi hakuri Mama,ina san mata ta,sam bani k'ara sakin ta" ya na gama fad'a ya tashi ya fice ya bar Mama hannu a k'irji baki a bud'e. Anty Salma ta ce "kin gani ko Mama,ai ga irin ta ne,dama shi tura idan ta kai bango ba ta b'ullewa,ni fata na Allah ya sa kar rabo ya kashe mana ke,gashi dai Allah ya d'auke Junior mu na ji muna gani.." A fusace Mama ta ce "Ke dallacan,ba wani rabon da zai kashe ni...."Nan ta rufe Anty Salma da fad'a dan kuwa tabbas ta tsorata kwarai. Ita kuwa Huda ta shi ta yi ta bi Haroun da saurin ta.
Har zai shiga mota ta yi saurin tsaida shi,ta hanyar fad'in "Dakata Haroun,dan Allah..." Juyowa yayi ya na mai duban ta. Huda ta ce "Ban ce lalle sai ka rabu da matar ka ba,ni dai burina kawai ka aure ni bayan na gama idda, ko da kuwa zan kasance mata ta biyu a gare ka.." murmushi Haroun ya yi,sannan ya ce "Huda ni dan uwan ki ne,bazan so ki wulak'anta ba shi ya sa bazan aure ki ba,shi namiji mijin mace hud'u ne,amma ni Haroun mijin mace d'aya ne,saboda masu rauni iri na Allah ya ce idan ba za mu iya adalci ba mu auri d'aya,babu macen da zan aura na had'a da Aliya ta ga adalci daga waje na. Ki koma d'akin mijin ki shi ya fi mi ki alkhairi"
Tun da ya fara magana Huda ke kuka,har ya gama,ya na shiga mota ta ce "Ba ka ji ba ne?tun rasuwar Junior Dawud ya sami tab'in hankali..." Jim yayi dan kuwa maganar ta ta ta bashi tsoro,sai kuma ya yi tunanin ba mamaki k'arya ta ke. Kawai ya ja kofar sa ya rufe nan ya bar ta ta na kuka. Sai gashi a hanyar Bichi.
Habeebti na zaune falon Yakumbo,kayan Junior ne ta gama shirya su cikin akwati uku,ta na kan na biyun,wanda za a bayar. Ita kad'ai ce a gidan,Yakumbo ta shiga mak'ota gaisuwa in da aka sake wata rasuwar. Kamshin turaren sa ta fara ji,kafin ta ji sallamar sa daga bakin falon,amma ta kasa amsa sallamar. Har sai da ya gaji kawai ya d'aga labulai ya shigo. Jin shigowar sa be sa ta d'aga ido ta kalle shi ba. Sai aikin gaban ta da ta cigaba.
Kallan ta ya tsayi yi na wani dan lokaci,sanye ta ke cikin riga da siket,English wears,kan ta rufe da hula. Ta rame sosai. Sai a sannan ya gane kayan Junior ne gaban ta. Be san sanda ya k'arasa gaban ta ba,ya karb'i rigar hannun ta, ya aje gefe ya na k'ok'arin tada ita tsaye. Hannun sa ta buge a fusace ta na "Fadin let go of me!Allah ya haram ta mu ku tab'a macen da ba taku ba!"
Da zafin nama ya jawo ta,sai ga ta ta mik'e tsaye gaban sa,ya kuma jawo ta,ta fad'a k'irjin sa,ya rungumeta kam,ya ce "If i can't hold you ryt now i will die!!!!!!!Ni mijin ki ne,na dawo da ke Aliya" ya dad'a kamkame ta jin hawayen ta na jik'a gaban rigar sa.
💫💫💫💫💫
No comments:
Post a Comment