Monday, 19 December 2016

Yar Ajinmu

'YAR AJINMU CE
RABON DAMU HADU TUN RANAR DA
MUKA KAMMALA MAKARANTAR
SAKANDIRI
(Gajeren labari dan Nishaði)

   Part 1,2,3

Zaidu Ibrahim Barmo MrZaid

Zaune cikin masu neman sadaka
fuskarta gaba daya ta canza tayi baki
in ba saninta kayi sosai ba ba zaka
gane ta ba, Tana rike da robar bararta
a hannu dole ne duk wanda ya ganta
ya tausaya mata.
Saman mashin ðin abokina dana aro
roba-roba sabon yayi ina tafe
kunnuwa na da eyephone ina kallon
bakin titi da gefen hanya, kana
ganina kasan yanayin yana man daði
sosai gaskiya.
Dan Allah a taimaka!
Dan Allah a taimaka!!
Dan Allah a taimaka!!!
Naji suna faði almajiran dake zama
bakin titi harna gifta ta wajansu sai
na sake dawowa dan basu sadaka, Na
zaro dari biyu daga cikin aljihuna
nace ku ansa ku rarraba! Bintu ce tayi
saurin fisge dari biyun har tana
neman ra6ewa gida biyu.
Na kalleta rai na ya gama 6aci nace
ke lafiya kike?
Bata bani amsa ba naci gaba da cewa,
idan ke baki son sadakar su sauran ba
suna so ba! Idan kika yaga kamar
kinyi ma gaba dayanku asara ne fa?
Sai naga ta miqa ma ta kusa da'ita
kudin ta koma gefenta tana matsar
kwallan dake niyyar fitowa daga
idanuwanta, nan take Zuciyata ta
kare tausayinta ya kamani koba
komai abar tausayi ce gaskiya.
Zo nan!
Na kira ta sa'adda na matsa gaba da
sauran mabaratan ta tako kamar
wadda kwai ya fashewa a ciki tazo
kusa dani idanuwanta gaba daya sun
yi ja kila saboda tsananin yunwa kila
kuma wani abun daban
Menene yasa kike haka idan aka baku
sadaka ku duka 'yam mata,
bata ce komai ba illa dukar da kanta
da tayi tana murza yatsun hannunta.
Na sake dubanta a karo na biyu nace,
lafiya ma kike kuwa ko kina rashin
lafiya ne"
lafiya ta kalau
ta bani amsa cikin kuzari tana duban
idanuwana a karo na farko lokacin ne
naji kamar na santa kamar na ta6a
ganinta! Ban san inda na santa ba,
ban san inda muka ta6a zama tare ba,
amma hakika mun ta6a zama da wata
mai kama da wannan in ma ba ita
bace mai kama da' ita ce.

2=
hakika kamar yadda zuciyata ke
fada man hakan ðin ne, naji kamar in
daure in tambayeta wani abu game
da labarin rayuwarta, itace ðiya
macce ta farko dana ta6a gani naji
tausayinta ya kamani. Ya sunanki? Ta
saki bakinta tana kallona kamar
sakaran ango sannan tace, a hankali
fuskarta na dan washewa "Bintu
Ahmad Alkali" itace monita ðinsu
tunanin hakan ya faðo a ransa su
alkali ma suke kiranta dashi Allah
sarki rayuwa kenan mai juyi- juyi na
fada a zuciyata sannan na dube ta
nace kin sanni? Ban sanka ba,
wannan karon ma ta sake bani amsa
kai tsaye ba tare da kwano-kwano
ba, Nayi ajiyar zuciya na kuma yi
hamdala ga Allah domin burina ya
cika ko kuma nace zai cika
   
   3=
Na kara hamdala fa sarkin halitta
buwayi gagara misali sannan na
dube ta nace, Nine Jamilu Ibrahim
Garbati! Ta juyo da karfi tana kallona
bansani ba ko itama tunani ne tayi
cikin zuciyarta sai naga tayi
murmushin da ya fito da kyawun
la66anta tace, Kaine jamilu dan
ajinmu ko sa'adda muna makaranta a
MARIAYAMOH AJIRI INTERNATIONAL
SCHOOL. Sai naji dadi a zuciya ta da ta
tuna ni koba komai Xata tuna
shakuwa da halaccin dake
tsakaninmu sa'adda muna
makaranta, Ba karamar sadaukarwa
tayi a kaina ba a sadda dai muna
makarantar Bintu alkali! Naji sunan
ya su6uce daga cikin bakina kece? Na
faða ina sake dubanta bintun dana
sani kyakkyawa ce amma ace itace ta
koma haka gaskiya abun da tambaya,
bintu class kamar yadda kawayenta
suke kiranta, kana ganinta kaga ðiyar
manya mahaifinta alkali ne mai
zaman kansa a birnin tarayya abuja.
Duk ina yin waðannan tunane-
tunanen ne dan mai karatu ya
fahimci cewa nasan bintu ba karamin
sani ba. Bintu ce macce ta farko da ta
fara taimakaman a rayuwa badan
bintu ba da ban kammala makaranta
ðina ba a waccan lokacin, itace ta
dawo haka take neman sadaka, diyar
girma bintu class, Zufar dake zubo
man nayi saurin sharcewa nvkagu
naji abinda ya sa bintu ta koma haka.
Mai karatu kaifa?

No comments:

Post a Comment